Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

kice ya barni har ayi suna "shikenna tana jin motsin shigowarsa ta  kwanta da sauri tayi kamar mai bacci .

"assalamu alaikum ya shigo bakinsa ɗauke da sallama"wa'alaikum Salam "barka da yamma hajiya "barka ya aiki ?"alhamdullahi ya faɗa yana leka bayanta inda ummita take  "ita wannan bacci me take  da yamma ta tashi mu wuce gida ?
" tana nan har sai anyi suna ,ta faɗa tana haɗe rai ,yayi shiru yana kallon ummita dake  kwance shi da yayi niyyar cin kaniyarta yau "ko ba zaka barta bane ka tsaya kana kallona    ?  "shikenna sai anjima "mujima dayawa yana fita ummita ta mike cike da jin dadi  ta rungume hajiya umma "shiyasa nake sonki ummana, hajiya ummah  ta shafa kanta karki damu diyata  ki saki jikinki cikin yan'uwanki kinji karki damu kanki , babu abinda zai yi , tayi murumushi tana barin dakin..

Tun daga ranar mah'ruf bai sake takowa gidan ba ,haka bai kirata a waya ba  ya tattarata ya watsar , ta soma  damuwa  duk ta kasa sakewa acikin mutane , sosai hankinta  ya tashi da rashin  ganin  kiransa sai tayi kamar ta kirashi sai zuciyarta ta hanata  , ta danne zuciyarta   ta cigaba da shirye-shiryen sunah ..

Hajiya rahma taji shiru Alhaji Umar bai sake mata batun aurensa ba ,kwata kwata harkan gabansa yake dan haka ta ɗauka aikinta yaci  ,tana zaune a kusa da mahaifiyarta kasancewar ita ke jinyarta tare da matar dake kula daita , ya kirata yace "zai yi tafiya zuwa dubai  wata daya zai yi zuwa biyu ya tura mata kudi ta account dinta tayi fariciki sosai tana duba karamar  wayarta da take ganin alert  500k ta gani ta lumshe idanunta tana narkar  da murya "na gode mijina  Allah ya kara budi ,allah ya kai  min kai  lafiya ya dawo da kai lafiya abinda aka tafi nema Allah yasa a samu "ameen ya faɗa yana mata sallama .. .

kullum  sai mah'ruf ya  sauke suhaima asibiti  sannan ya wuce aiki  haka zasu tasa mahaifiyarsu gaba suna kuka saboda surutan da take ya soma  over , "suhaima rahma  Kunga yadda na dawo ko ? " an yanke  min yatsa sannan  aka dawo kafata daga yanzu bani da  idon sawu , tayi maganar tana dariya  shikenna na dawo mai  dungulumi bazan taka da kafafuna ba  ,kuyi hakuri ya'yana  ina nan  tare daku bazan  mutu yanzu  ba sai naga auren jikokina da ya'yan auta  tana magana tana tsotsa tsakiyar  kanta da jikinta  suna cikin haka kawar hajiyarsu ta shigo tana ganinta ta washe baki tana zazzaro ido "a'a  hajiya  hasana  ! hasana ce ! hasana ce !!  sannu da zuwa hasana ki zauna mana  ga guri nan Kinga yadda na dawo ko   ? "Na gani  kawata Allah ya kare mu da lafiya ta fadi tare da zama  , suhaima da hajiya rahma  suka amsa da "ameen suna gaisheta "ya jikin zulaihat ance itama tayi  karaya a kafa "wallahi amman ta soma jin sauki inji cewar hajiya rahma ta ɗan dade suna tautaunawa akan ciwon sannan tayi musu sallama ta wuce  ..


Ranar suna baby yaci sunan kakan  abdulshakur Muhammad Auwal  ,suna yayi dadi sosai yan'uwa da abokan arziki sun hallara ,dangin  abdulshakur sun yi bajinta, haka ma ta bangaren menal y'an'uwanta sun yi abun arziki babu wanda bai yi rabo  ba, ummita tayi kyau sosai duk inda tayi idanu suhaima na kanta dan gano ko  tana dauke da wani  cikin  duk sanda suka hada ido sai gaban ummita ya fadi  yayinda suhaima  ke sakar mata murmushinsa mugunta take ta shiga karanto addu'ar neman tsari daga sharrinta dan tsoro take bata sosai  ..

Bayan  anyi suna mahruf yaki cewa ummita ta dawo, ita kuma tana jin tsoro  komawa  yaci ubanta ,dan haka ta cigaba da zama   a bangaren Hajiya umma tare da menal sai duk abun duniya ya isheta tana kewar mijinta , ganin an tafi wajen  kwana goma ga yanayin ummita ya nuna tana bukatar komawa ga mijinta, yasa Hajiya umma  ta kira shi, bayan yazo ta dinga zuba masa ruwan bala'i  a gaban ummita ta inda take shiga bata nan take fita ba "kiyi hakuri Hajiya "karka bani hakuri laifi kamin da zaka bani hakuri "ina lura da kai baka qaunar ganinta cikin y'an'uwanta dan tana aurenka sai akace maka bazatayi zumunci ba ?   wallahi idan  baka saki ranka ba  zan hanata dawowa gidanka gaba-daya naga ta tsiya da gaba , daman ina bakinciki  da zubewar da cikinta yake a koda yaushe ,ga jarabarka gata matarka ina dalili da me zataji ko dan kunga akwai ido an saka muku  , dan Allah idan ta koma kayi mata wani abu  kaga abinda zanyi   ,ko kallon banza ban yarda dashi ba,  ya dinga kallon ummita dake zaune tana kallonsa take ya  dinga  zabga mata harara  "ki tashi kuje ko harararki yayi ki faɗa min..

Ta narke fuska cike da shagwa'ba tana rungume da abban abba sunan da suke baby dashi kenan , ta nuna shi da yatsan hannunta ɗaya   "ai gashi nan ma hararata yake gara kawai nayi zamana ,  ta karasa maganar tana kuka , ya zaro ido yana Kallonta "kina hauka ne ? Ya buga mata tsawa" wallahi idan kika sake furta  wani abu anan  zaki ga yadda zanyi dake  ",oho tun agabana  ma ka fara nuna halin da zaka mata idan ta koma   ke tashi ki shige uwar dakana kiyi kwanciyarki    abunki  ,jikin ummita yayi sanyi da jin abinda hajiya umma tace  ta juya tana tafiya  tana shafa bayan baby  tana waiwayinsa kamar tace bazata shiga daki ba  ,"haba hajiya wai me yasa kike biye mata ne ?  ke kuma wallahi idan kika shiga sai na fito dake daga dakin ta karfin tsiya ki ajiye musu da mu   wuce , "kayi tafiyarka kawai babu inda zata  a dan rikice ya kalli Hajiya umma  yace " babu abinda zan mata "da   kyar Hajiya umma ta yarda suka fito ..

Ya shiga part din mama bata shiga ba  ta nufi haraban gidan ,lallabawa tayi ta shige gidan baya  gabanta na faduwa  dan bata son wani sabon tashin hankali , kusan minti goma suna zaune babu wanda ya kalli fuskar wani  sannan ya fito ya bude motar ya shiga suka bar gidan ..

Koda suka isa gida jikin ummita yayi mugun sanyi ta bude mota ta fita duk a tsorace take  dashi sai data yi datasanin biyewa zuciyarta ,shima fitowa yayi ya biyo bayanta suna shiga part  din ya zauna parlou'n  ya daura ƙafarsa akan daya yana  harararta , simi simi  tashiga  d'akinta ta cire mayafinta ta ninke ta  soma share d'akinta ta shimfida haddaden zanin gado mai kyau da alfarma   ta fito gyara  parlou'n lokacin tuni ya fita   , bata huta ba sai data gyara ko'ina ta fesa tuttarare kala dabam dabam ko'ina ya canza ya dauki kamshi   ,ta  shiga wanka  ta fito tana goge jikinta tana addu'ar Allah yasa kar yayi mata maseefa doguwar    riga ta saka ta shiga kitchen ta dafa jollof din wake da shinkafa , bayan ta gama ta shirya dining table sake shiga bayi tayi watsa ruwa tayi alwala ta fito tayi sallah magariba  duk a tsoroce  take dan  gabanta sai  faduwa yake ,a hankali ta zare hijab din jikinta ta haye gado ta kwanta ta lumshe idanunta tana jin wani irin yanayi mai cike tsantsar sha'awar mijinta bata jima da kwanciya ba wani bacci mai dadi ya ɗauke cike da tunaninsa ..

A kwance ya shigo ya sameta tana sharar bacci hankalin kwance cike da tsantsar mamaki yake kallonta kafin ya duba agogo dake daure da tsintsiyar hannunsa karfe tara saura ya gani yaja tsaki "wato ma har ta samu damar yin bacci ? Ya tako ya isa bakin gadon ya tsaya yana kare kyakkyawar fuskarta kallo, take yaji duk bacin ran data haifar masa ya kau  ,a hankali ya raba ya kwanta a gabanta  ya shiga hura mata iskar bakinsa a saman idonta  motsa ido  idanunta ta fara yi har ta budesu fess akan kyakkyawar fuskarsa dake daf da nata tana hamma alamun bacci  mikewa tayi a firgice tana haɗe hannuwanta duka  ",dan girman Allah kayi hakuri karka min  komai wallahi bazan sake ba ta karasa maganar tana hawaye alamun nadama, ya tsura mata ido kawai , kuka take har da majina tana rokonsa cikin zuciyarta tana addu'ar da kiran sunayen Allah  "kayiwa alfarma Manzon Allah kayi hakuri karka hukuntani  gabadaya ta bashi dariya ya kai hannuwansa wuyanta zai shaketa ta rungumeshi ajikinta  ta rukunkumeshi ,  gashin kanta mai laushi da kamshi ya rufe masa fuska "karka ka kasheni dan kaima mutuwa zakayi idan bana raye ....

Jikinsa yayi sanyi  ya zagayeta da hannuwansa ya matseta da karfi sai data saki ƙara  cikin sanyayyiyar muryarta tace"am sorry  ya zareta ajikinsa yana haɗe fuska "kinci daraja Manzon Allah da mahaifiyata wallahi da kin gane baki da wayo wai a gabana kika haye bayan wani kato kinsa yadda naji ? tayi saurin girgiza masa kai "kayi hakuri  ta faɗa tana wasa da hannunta  shiru yayi kafin daga baya ya mike zai fita ta sauko da sauri ta rungumeshi ta baya  ta kife hannunta akan nipples d'insa ,cak ya tsaya yana fidda numfashi , tasan muddin bata sauko dashi ba tana ruwa dan gaba a zarce dashi  "kayi hakuri mana bazan sake ba  nasan nayi kuskure idan na sake kayi fushi fiyye da haka ya juyo yana fuskantartata "dan kinsan bana iya dogon fushi dake ko ? yayi maganar yana jan karan hancinta ta narke ajikinsa tana shafa kirjinsa gabadaya wani sanyi yaji yana ratsa sansar jikinsa ya rungumeta tsam, bai an kara ba yaji tana yawo da hannunta a jikinsa ya ɗan sausauta rungumar da yayi mata ta tallo'bo fuskarsa tana kallon kwayar idanunshi  "i really miss you ta had'e bakinsu nan wasan ya canza salo suka zube kan gado tun daga rana basu sake samu matsala ba  ....

Bayan wata uku

abubuwa dayawa  sun faru ciki har da warkewar zulaihat  , da cigaba da bin bokayensu  , yayinda  jikin mahaifiyarsu ke cigaba da rurewa ta hanyar sababbin cuccutuka dabam dabam  hauwan jini  ,sugar  Wanda shine dalilin da yasa a'ake yanke mata kafa ,a halin yanzu ma ciwon gaba yake suna zaune a parlou'n mahaifiyarsu zulaihat tace "yayyarmu har yanzu batun auren ya umar shiru?  " an ce miki ni  din  ta wasa ce ai muddin ina raye bashi ba ƙara aure sai dai idan na mutu suka kwashe da mahaukaciyar dariya "ke ya labarin wannan tsinanniyar yarinyar kuwa ...? Hajiya  rahma ta dubi suhaima aiki na tafiya yadda ya kamata ko ? "Kai bari yayyarmu mutumin nan ya iya aiki ,abu kamar maita  wallahi muddin tayi ciki sai na gani sai dai idan bamu haɗu daita ba, shegiya kamar tasan halin da'ake ciki gudun haduwarmu take suka sake fashewa da dariya "ai haka zata kare baki haifa ba itama bazata haifa ba daga karshe ki korata da makirci matso kiji sabon makirci da zaki mata wanda nake da tabbacin  wannan dan iskan mijin naki mai bakin kishin tsiya yana gani sai yayi gunduwa gunduwa daita sannan ya korata gidansu  suhaima ta matso ta kasa kunne tana murna dariya ta fashe dashi lokacin da hajiya rahma tagama zayyano mata "kai yayyarmu kin kawo shawara wallahi haka za'a yi nan suka ci-gaba da tautaunawa akan tuggun da zasu haɗawa ummita ..

bayan sati daya da   yamma ummita  na zaune  a parloun kan doguwar kujera tana kallo wanda azahiri ba kallon take ba tunani take mai zurfi gabad'aya  zuciyarta ta  amince mata da saka hannun suhaima gurin   zubewar cikinta ba wai mafarki ne kawai ba akwai lauje cikin nadi   duk randa tayi mafarkin suhaima sai cikinta ya fita kuma bata mafarkinta sai idan tana da ciki  ,tayi shiru tunani yaki barin zuciyarta tana cikin wannan tunanin mah'ruf ya shigo ya wuceta a haukace  bataga shigowarsa ba sai   sautin muryarsa taji yana kiran sunanta "subai'a  ta zabura ta mike jikinta na rawa tana furta "kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun saboda faduwar da  gabanta yayi ta  shiga d'akinta nan ta iskesa tsaye  jijiyoyin kanshi da jikinsa duk sun mimike idanunshi sunyi jazir tamkar garwashin wuta yana zare ido.

cike da tashin hankali  ya damki wuyanta "manufakar Allah muguwa  me yiwa kanta bakinciki  yau asirinki ya tono ta firgita tana ƙoƙarin cire hannunsa a wuyanta  jikinta na wani irin rawa sai daya ga idanunta sun yo waje sannan ya sausauta rikon da yayi mata ya ingizata baya tayi taga zata  fadi , Allah ya taimaketa ta tsaya bisa kafafunta tana fidda numfashi "lafiya me nayi maka ?
Tayi magana da kyar tana shafa wuyanta "ka dinga samun natsu..bata karasa ba saboda wani gigitaccen marin da taji ya sauka akan kuncinta kafin tayi wani yunkuri ya sake d'auketa da wani mai rai da lafiya a kyawawan fuskarta ,take ta gigice ta nufi hanyar bayi a madadin ta nufi kofar fita daga dakin .

yayi  saurin janyota ta makake a jikinshi  tana kuka "dan Allah karka sake marina kunnena zafi yake min ka faɗa min abinda nayi maka "kiyiwa  mutane shiru  munafuka shasha   ya rike  kafad'arta da karfi jikinsa na rawa "dan girman Allah kayi hakuri idan wani laifi nayi maka wallahi bazan sake ba ya turata baya ta faɗa saman katifa ya daura kafarsa daya gefen katifa   yana zaro mata ido kana ya lalubo kwalin postonu 1 2 har 3  akan fuskarta  "wannan maganin na mene ne ? a gigice ta mike ta ɗauki magani tana dubawa kana ta shiga girgiza masa kai dan bata fahimci komai ba "kin bani mamaki kin cuceni amman bani kika cuta ba kanki kika cuta kowa na tausaya miki ashe ke kinsan abinda kike kallonmu kawai kike yi  muna hasarar hawayenmu  ,wai  yau kece kika shan maganin zubar da ciki saboda dakikanci wallahi dakikiyar kwalkwaluwarki  bata faɗa miki gaskiya ba "da kinsa tsawon shekaru da mama da Abba sukayi suna neman haihuwa wallahi ko cikin shege kikayi zaki  barshi bare dan halal.

take ta soma ganin dakin na jujjuyawa daita idanunta suka dinga ganin biyu biyu  jikinta na rawa ta sauko ta zube gabanshi "ka yarda dani yaya wallahi ban taba shan wani abu dan na zubar da ciki ba  ,ban taba ganin  wannan maganin ba sai yau na rantse maka da girman Allah ban san yadda zan zubar da ciki ba ..
Ya watsa mata harara cike da jin haushinta "yi min shiru me fuska biyu kawai  kinsa na  rasa cikin ya'yana na farko kin    zubar min dasu  duk yadda  meenal tace karki  zubar  tayita baki hakuri   sai da kika ga bayan rayuka biyu yanzu kuma kinata zubar min da ciki saboda bakinciki me nayi miki dana cancanci wannan hukuncin daga gareki ...?

"Inna Lillahi wa Inna ilaihi rajiun kawai take furtawa tare da sake daukar kwalin maganin tana dubawa   "banga amfanin zamana dake gara na sawwake miki kije ki auri wanda zuciyarki ke so tayi saurin mikewa ta rungumeshi ajikinta "karka min haka yaya karka sakeni  karka yanke hukunci cikin fushi Allah baya son haka ta rike fuskarshi da hannuwanta duka "ban taba kin hada zuri'a da kai ba ,kai  din kamilin mutun ne mai daraja a idanuna  ,me ye ribata Idan na zubar da gudan jinina da naka wallahi sharri ake son min bani da masaniyya da zubar da ciki ,yayi mata wani banza kallon cike da jin haushinta "ka yarda dani mijina kalli cikin kwayar idanuna subai'a tayi kama da wacce zata iya kashe kadangare ma  bare dan mutun kuma jininka jinina "zan yarda tunda idanuna sun gane min kin hainceni kin zalunci rayukan da basuji ba basu gani ba  ta sake kamkameshi ajikinta ganin zai zareta cikin sheshekan kuka tace  "dan Allah ka ji tausayina ka tausayawa halin da mahaifiyata zata shiga idan ka sakeni "dan Allah kayi bincike kafin ka yanke hukunci saki akaina kada kazo daga baya kana dakasani ...

"Ya Allah ka fahimtar da mijina ya fahimceni wallahi bani da masaniyyar laifin da yake tuhumata kai "Allah duk wanda yake son had'ani da mijina Allah kayi gaugawan yi min maganinsa, Allah idan ina da sa  hannu cikin zubewar cikin jikina Allah ...
Shiru tayi sakamakon fizgeta da yayi ajikinsa yana huci "kiyi min shiru makira maci amana ko mama taji abinda kika yi sai tsine miki tare da yin Allah wadai dake ya fice ya bar dakin zuciyarsa kamar zata tarwatse ..

Da sauri suhaima ta juya a guje ta koma part dinta tana hakin gudun datayi ya shigo yana mazurai "maganarki gaskiya suhaima wallahi naga kwalin maganin yarinyar nan ta dade tana cutata "ai kai ne  ka yarda daita bayan wannan fa har maza take kawowa gidan  nan duk randa kake dakina ita kuma tana tare da tsohon saurayinta bari na nuna ma ka gani .

ta kunna wayarta ta shiga vedio sai ga hoton hafiz almustapha ya bayyana yana zaune akan gadon ummita jikinsa babu kaya daga shi sai boxer Yana murmushi can sai ga ummita kwance da rigar bacci iya cinyarta yayi mutuwar tsaye jikinsa na rawa  ,ta sake lalubo wani vedio  still hafiz din ne yake  sandar  shiga part din Ummita wani irin ihu yayi tare da kwace  wayar yayi wurgi daita  akan tayis "kenan haukan banza nake cikin ma ba nawa bane yayi maganar itama yana damkar makoshinta "me yasa baki faɗa min ba "nima  me gadi ya fadi min  tana aikensa dan ta shigo dashi  ,ka tambayi me gadi shi kuma yace tsoron faɗa maka yake  ya wujijigata  yayi jifa daita  ya buga kanta da  bango kamar itace Ummita ta dawo ta zube kasa take bakinta da hancinta ya fashe ta saki wani kara "sorry ya faɗa cikin tsananin tashin hankali "dole na rabu da yarinyar nan hakuri  kawai mama zatayi , daman nasan batun yanzu zuciyarta hafiz take so  ya sake fita. .

Yana fita ta mike bata damu da raunin da taji ba ta soma tikar rawa   da shewa"yau yarinya dole kiyi kwana gida kwana jikin mah'ruf ya kare ta kira hajiya rahma yayarmu gobara fa ta kama da wuta  a gidana "kice bom ya tashi "tashin ma babba ne yau dai na huta ,za'a koma gidan gyatuma "ke hirar waya bazata yi ba bari   nazo "gara kam yau akwai kwaso shoki  ta katse wayar tana kwanciya akan kujerar wayyo  Allah dadi ..

part din ummita ya koma ya isketa tana risgar kuka  "ki tashi muje dan idan na cigaba kallonki zan iya kasheki bata masa mutsu ba ta zira hajab dinta ta fito bakinta na ambaton sunan Allah  kai tsaye  gidan ya wuce yana parking ya fito  ya shiga part din mama ita kuma ta wuce part din hajiya umma .

Mama  na kwance akan kujera tana  ganin  shigowarsa tayi saurin mikewa saboda tsananin tashin hankalin da hango tare dashi   da hanzarinta  ta kamo hannunsa "lafiya baba ?
Bai iya amsa mata ba ya kife kanshi akan gwiwarta ya shiga kuka har da shesheka yana cewa "mama ummita ta cuceni ta hainceni taci amanar zuciyata  "Baba me Ummita tayi maka kake fadan irin wadannan maganganu jikinsa na rawa ya d'ago da idonsa yana kallonta ,idanunsa da zafafan kwalla  kansa kuwa wani irin sarawa yake tamkar ya rabe gida biyu,  gabadaya ta sake rudewa ta kai hannunta tana goge masa hawayen dake zubowa a fuskarsa tana cewa "dan Allah ka faɗa min abinda ke faruwa hankalina yayi bala'in tashi..  ya sake watsawa mama jajjayen idanunshi muryarsa a kausashe yace "Ummita ............

TWO FRIENDS BSBS

💗💗💗💗💗💗
     WANNAN CE
   QADDARARMU
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~TRUE LIFE STORY~

FREE NOVEL
            
      
AL'QALUMAN


*AYSHA  A BAGUDO*           
*FAIZA  HAMMADU*

SUBSCRIBE TO MY YOUTUBE CHANNEL *HAUSA BAKWAI*

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

PAGE 66

"Ummita    na  kama dumu dumu  da  laifin    zubar   da   ciki  ta hanyar shan   kwayoyin   ,  tare da  aikata  abu mafi muni da  kaskanci arayuwar aurenmu     gayyatar  hafiz  almustapha   har cikin  gidana   da zumar keta haddin  au  ....

"Dakata  ...
Hajiya    Umma  ta katse    shi  ta hanyar fadar haka  tare da  k'arasa   shigowa parlou'n  rike  da  hannun ummita    dake wani irin kuka mai haɗe  da shesheka    "wannan   maganarta  banza ce kuma   karya  ce   har   abada  subai'a  ba zata taɓa   aikata  haka ba ,    makirci  kawai  ake son had'a mata   tare  da kawo wa rayuwar aurenta  tsaiko .

"Yau  kasan halinta  da har dakikiyar  kwakwaluwarka ta kasa ƙaryata  wannan mummunar aika aika   " ka sani na sani kowa  ma ya san halin  ummita   ba zata taɓa  aikata  wannan mugun aikin ba ,tana budurwa ma bata aikata zina ba sai da igiyar aurenta "ko ba cikakkiyar  buduwar ka sameta  ba  bai kamata ka amincewa zuciyarka ta aikata haka ba ,bare nasan karya ne  kai ne ka fara saninta diya mace ta karasa maganar cikin fushi tana watsa masa kallon banza ..

Zaune  kawai  mama take akan kujera jikinta na wani irin  kyarma , hawaye  kuwa   tuni  sun  gama wanke mata  fuska  ,wannan hawayen da mahruf ya gani  yasa  jikinsa  ya  kama  rawa ya shiga  girgiza  mata kanshi yana sake riƙe yatsun hannunta gam  ,  tsoro da matsanancin firgici yaga ya bayyana a  fuskarta yayinda a zahiri yake iya hango yadda zuciyarta ke bugawa da karfi , zare hannunta tayi cikin nashi ta shiga    share  hawayenta,  muryarta  na  rawa tace    " hajiya  ummah karki   ce  haka    karki  karyata shi   dan  baki san abinda kwayar  idanunshi suka gane  masa  ba dan......

   "Dakata maryam  banason irin wannan maganar  da bata dadin ji    , banason ji  komai  daga bakinki ,  tayi maganar da karfi  wanda   hakan  ya janyo  hankullan mutane  dake  cikin   gida ,  kafin kace   me  duk sun hallara  tare da yin zuru zuru   fuskarsu  dauke da  alamun tambaya   ....

A  matukar  haukace hajiya  umma  tayi kan shi tace  "tashi  daga gaban mahaifiyarta  tantirin mara  kunya  da  bai san abun  arziki  ba  ,ta shi nace  dan iska  tayi magana jikinta na  rawa tare da chakumo wuyar rigarshi  ta mikar dashi tsaye  bisa kafafunsa ta   ɗauke  shi da  mari har biyu a jere tana huci tana kokarin kai masa wani marin  mama  tayi saurin  mikewa ta rike hannunta  "dan  girman Allah ki barshi  haka   wallahi nasan haka  kawai  baba bazai fad'i  abinda ya faɗa a yanzu ba  akan ummita  , ya   kamata    ki natsu  ayi  binkici domin a  gano  inda gaskiyar take bai  kamata  ki dinga yanke  hukunci akan ra'ayi ki  ba ..

"Maryam nace miki banason irin  wannan maganar mai barazana da rayuwarmu ki daina ma tunanin abinda ya faɗa gaskiya ya faɗa  tana girgiza mata kai bazan taba yarda ba wannan sharri ne da makirci aka mata .

naunayen ajiyar zuciya mama ta sauke tare tsura mata ido "wani irin soyayya hajiya umma ke mata ?"Ko uwarsu daya ubansu daya iyakar abinda zata mata  kenan "Ki daina asarar hawayenki a banza  dan ko bindiga za'a daura min a wuya bazan taba amincewa ba ,shi wannan ɗan iska zaki yiwa gargadi  ya ƙaryata abinda ya faɗa yanzu  kafin yasa zuciyata ta buga ganin yadda ranta ya ɓaci yasa hajiya mama ta kamota ta zaunar daita akan kujera tana huci ..

Ransa a matukar 'bace yake  kallon  mutane  da suke  tsaye  agurin , Abba injiniya   hajiya saudat  mama  da  ummah     "ga ta  nan tsaye a gabanku ku  tambayeta idan karya nayi  mata , ku tambayeta  ban kamata da  laifin da nake tuhumarta dashi  ba ,  ku
tambayeta  karya ne  banga  maganin  zubar da ciki  a dakin ba?
" gata  nan  bata gayyato hafiz   almustapha gidana    da sunan aikata zi .......
Tass tas tass Hajiya  umma ta    tashi  daga zaune da take  ta  sake dauke shi da wani gigitaccen mari har uku  a jere  "Idan ka sake danganta min yarinya   da  wannan kalmar  sai  tsine maka albarka .....

yayi  shiru tare  da  juyo inda ummita ke tsaye  tana  wani irin kuka mai taɓa zuciya , fuskarsa   cike  da hawaye  yake kallonta idanunshi  sun yi jazir tamkar garwashin wuta, takowa yayi   a hankali  har inda  take tsaye "akan idanunki  ake ƙaryata  abinda na  tabbata da  gaskiya ne  ...

Zuba masa fararen idanunta   tayi  waɗan da suka kode tsabar kuka tana kallonsa tana jin zallar bacin rai na ratsata hawaye na sake gangarowa bisa kuncinta, ji take duk duniya mahruf  ya gama tozarta   ya gama wulakantata  tun daya danganta da laifin zubar da ciki sannan da laifin aikata zina da aurensa  ..."ta yaya zata aikata hakan gareshi  ?
"Me take nema arayuwata da har
DOWNLOAD
DOWNLOAD

2 Comments On WANNAN CE QADDARARMU
avatar
amina-4

11 months ago

Reply

Interesting novel

avatar
amina-4

11 months ago

Reply

Interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment