Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

ba  zubawa dukiyar fulaninta idanunshi , tayi saurin lumshe idanunta tana zumburo masa baki "dan Allah ka bari na sa kaya , ya harareta yana dallare mata baki  sannan ya kai bakinsa saitin nata ya fara tsotsan lip's dinta har yayi nasarar bude bakinta ya fara tsotsa tamkar ya samu lolly Popp  yana shafa sumar kanta zuwa qirjinta shiru tayi jikinta na rawa tana jin dadin yadda yake tsotsar bakinta ya kai hannunsa zai shafa qirjinta  ta rike hannunsa gam tana girgiza masa kai idanunshi cike da shaukin qaunarta  ya zare bakinsa cikin nata  yace "why me yasa baki so na
ta'baki  ? " Bana son abinda zai saka mahaifiyata cikin  damuwa "kamar ya ?"kamar yadda hajiya Inna take buƙata, ya ja tsaki ke yanzu idan na ta'baki  wa zai sani ko zuwa zaki yi ki faɗa mata ? "Ni dai a'a banaso, bana so bana son damuwa da tashin hankali ,ganin bashi da niyyar magana ta janyo rigarta ta zara daga kwance da take yana kallonta ta rufe masa abinda yafi kauna daga gareta ya kai hannunsa zai zare rigar ta saka masa kuka dole ya kyaleta zuciyarsa na tafarfasa ya janye jikinsa yana janyota jikinsa ya k'arasa saka mata riga ya mike ta riko hannunsa ya juyo "meye kuma ya faɗa a fusace? "ka bari t shirt dinka da wandoka ya bushe "baza'a bari ba ya fixge hannunsa a fusace  ya maida wandonsa ya dauki rigarsa ya kakkabe ya zira ya fita daga d'akin ta sauke nannauye ajiyar zuciya ta rufe kanta  da hula  dan kar mama ta fahimci wani abu daban,  ta fito daga dakin zuwa parloun kasa gabanta na fad'uwa  bata ga mama ba ta  zauna akan kujera tana tunani kala kala  can kamar minti goma sai ga mama ta sauko tayi saurin cewa "mama da wani aiki zan soma dan na gama da wuri ?"kinci dan wanke ne ? ta girgiza mata kai "ki ci tukun sai muyi aikin tare,ummita  ta yatsina fuska yama fita araina wallahi  da dai ma zan samu mangaro ko tsamiyar biri mama ta bita da kallon mamaki " mangaro ko tsamiyar biri anya kuwa ba ciki ga  ummita ba ?" Tace wannan tace wancan  Allah dai ya taimaketa ba wani abu ne ya shiga tsakaninsu da mah'ruf ba ta shiga uku a gurin hajiya Inna ,ta matso da sauri ta zauna kusa daita ta kamo yatsun hannunta tana dubawa  da idanunta "ciki ne dake ummita ? Tayi mata tambayar hankalinta a tashe .
  Wani irin luguden bugu qirjinta yayi da matsanancin karfi a tsorace ta kalli mama "a'a wallahi mama  bani da komai "kinga samu natsuwa wani abu ya taɓa shiga tsakaninki da baba ne ? ta sake girgizawa mama kai "ki bude baki kiyi min magana mana  "wallahi a'a mama, haba mama kamar wata wawiya ina ji fa ina ganin abinda hajiya Inna take miki acikin gidan nan  dan me zan aikata wani abu wanda  na san zan sakaki cikin wahala,shiru mama tayi batai magana ba , Allah ki yarda dani wallahi babu abinda ya taba shiga taakaninmu "ni ba wai ina  yaki da aikata sunanh ma'aiki bane    ina jin tsoron fitinar tsohuwar nan ne duk da Allah shine abun tsoro "karki damu mama Allah babu komai banida  komai, naunayen ajiyar zuciya mama ta sauke "bazan hanaku ba  tunda ba haram bane ... "kai mama wallahi babu  wannan a tsakaninmu muje muyi aiki , idan zakiyi aike kasuwa kisa azo min da mangaro tana  tafiya gama  ta faɗa kitchen mama ta bita da kallo" ummita yanayinki  ya nuna kina dauke da  ciki  ,idan kici abinci sai kinyi amai ga yawon bacci da za'bar abinci  ,duk abinda bakya ci da shi kike ci yanzu ta zan yarda ?"ta yadda ta rantse miki mana ai tasan mahimmanci rantsuwa kuma ma ta yaya  baba zayi  mata a ciki a gidan nan ? Kitchen din ta biyota .

*****

duk  sati  suhaimai  take   zuwa gidan  gaishesu wanda   rabin yinin  tana yinsa ne a bangaren inna ko ta shiga bangaresnsu ummita bata dadewa bisa umarnin hajiya inna kuma duk shigowarta bata haduwa da ummita har ta gama abinda zatayi ta fita , shi kuwa mah'ruf duk abinda take bata burgeshi yanzu gabad'aya hankalinsa baya gareta  yana kan ummita da cikin jikinta, ya zubawa sarautar Allah  ido ne har sanda  cikin jikinta  zai bayyana kanshi yaga yaya hajiya  inna  zatayi zata yarda ummita ta tare a gidansa ko kuwa ?
 
Sannu a  hankali cikin ummita ke fitowa  kasancewar lokacin ya shiga wata na biyar  ,kowa ya ganta yaga me ciki sak  , a wata  ranar asabar din karshen wata , suhaima ta kawo ziyara , ta soma da bangaren mama tana shiga  ummita na karasa saukowa a take gabansu ya fadi, tayi sororo tana kallonta da mamaki ganinta , tayi saurin murza idanunta tana sake kallonta cike da mamaki saboda ganin abinda ta gani ,ummita ta  kawar da idanunta akanta ta soma tafiya zuwa dining area da sauri suhaima ta karaso gareta tasha gabanta  "ke meye wannan ajikinki kamar ciki "ummita ta watsa mata katuwar  harara " uwar ciki ne ba ciki ba  , ta sake kura mata ido "ta yaya ga ciki ina gani ki karyatani "ina ganin kin soma   soma shaye shaye  ko kuma  haukan gado ya soma taɓa tunaniki  shiyasa kikaga haka dan Allah Malama ki ban hanya na wuce tayi maganar tana bin gefenta da sauri suhaima ta fice daga dakin ta nufi bangaren inna nan ta shiga labarta mata abinda ta gani "ke suhaima ba dai ciki ba cikin lafiya kar  kishi ya rufe miki ido fa? "wallahi inna ciki ne ajikin yarinya kuma na haihuwa "bari naje na ganowa idanuna idan kuwa ciki gareta da gaske zataci bantar uwarta a gidan ta fadi haka tana gyara daurin zaninta ta fita ta bar suhaima da zullumi da faduwar gaba "wayyohlly na shiga uku Allah kasa cikin bana mahruf bane ta furta jikinta na rawa .

kai tsaye part din mama hajiya inna  ta shiga ko sallama batayi ba  ta soma kwalwa ummita Kira "ke ummita kina ina fito nan  munafurkar Allah, ummita  data shiga kitchen d'aura Ruwan zafi ta fito tana yatsina fuska "lafiya kike min irin wannan Kiran mafarautan "Kiran uwarki da wadan can dangin uwarta take nake miki tayi maganar tana kura mata ido wani iri razanannen  ihu ta kurma
"Dan uwarki cikin waye ajikinki  a she da  gaske ciki gareki  makira  uban wa yayi miki ciki ?
Kan kace me parlour'n mama ya sauya da mutane har mama da hajiya umma da hajiya saudat
"ba zaki faɗa cikin uban waye ajikinki  ba yar banza, wato  abun kunya zaki janyowa mutane  a gidan nan  ?Inna ta sake kurma ihu wannan karon har injiniya da Abba sun shigo sukayi cirko cirko suna mazurai " wayyohlly Allah na shiga uku duk irin tarbiyar da Ibrahim ya baki ki rasa  abinda zaki saka masa dashi sai da wanna ......
"kinsan Allah ko fadi uban da yayi  shiri shiri ya dirka miki ciki ko kuma yau kubar  min  gidan  dana ke da uwarki bayan ki amshi takardar  sakinki daga hannun jikana, ita kuma wannan shashar  uwar taki  ta  amshi sakinta daga dana daga  yau bana son ganinku cikin  ahlina  ,dan wallahi bazan zauna gida daya daku ba  ....

"Kai Ibarahim ka saki mairo ko na tsine maka albarka  muddin bata fadi wanda yayi mata ciki nan ba gabad'aya jin haka yasa ummita ta rude ta gigice idanunta suka rufe dan tuni hawaye ya ɓalle a idanunta ta matsa kusa da inna Dan tasan yadda abbanta ke gudun bacin ran inna zai iya yi mata komai ciki kuwa har sakin mahaifiyarta, bata jin nata sakin bakinta da jikinta suna rawa tace "
wallahi inna   bani da ciki bani da komai ta ina zanyi  ciki  ?
"Ta uwarki da ubanki ta fixge hannunta da ummita ta riko " na rantse  da girman Allah inna  bani  da ciki idan kuma tabbas inda shi to bansan wanda yayi minshi ba ta k'arasa gurin  hajiya umma  "dan Allah ummah ki faɗa wa inna gaskiya  wallahi  bani da ciki  karta sa Abba ya saki mama  gara ni tasa ya mah'ruf ya sakeni "dukkaninku za'a saka kuma a yanzu, ina bazai yiwu ba  cikin shege a gidan dana .. ......





TWO FRIEND'S (BSBS)

💗💗💗💗💗💗
     WANNAN CE
   QADDARARMU
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~TRUE LIFE STORY~

FREE NOVEL
            
      
AL'QALUMAN

*AYSHA  A BAGUDO*           
*FAIZA  HAMMADU*

~DEDICATED TO~
*MUHAMMAD AUWAL JININ JIKINA  INA SONKA  FIYYE DA SON DA NAKE WA KAINA, ALLAH YA RAYA MIN KAI YA KARE MIN KAI A DUK INDA KAKE  ,GABA'DAYANMU MUNYI KEWARKA JIDDAH MENAL UWA UBA NI , ALLAH YA DAUKA YA HASKAKA RAYUWARKA  YAYI MAKA SUTURA*

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

PAGE 53

... Gabad'aya  mutanen  dake  tsaye   a parloun hankalinsu yayi  matukar tashe   sannan fuskokinsu   cike   yake da  matsanancin  mamaki  furucin hajiya inna ga ummita .
"  dan me hajiya inna   zata dinga  irin  waɗan nan magangun mai tattare da cin zarafi da tozarci  akanta ? " ta  ya  mace da aurenta  zata dinga tuhumarta   ? kallon hajiya inna suka ci-gaba yi babu wanda yayi magana a cikinsu gudun jaraba da  bala'inta .

A gigice cikin tashin hankali tace "kai injiniya kira min  Ummu  salama a wayarka   kace  tazo yanzu yanzu ina son ganinta , injiniya ya kalleta  yana  son yin  magana  ta d'aga masa  hannu da sauri" dakata bance  ka karanto  min  dogon turanci  ba , abinda na saka kawai  zakayi min  idan kuma bazakayi bane  ka sanar dani  nasa wani ya kira  min  salama  ...?
Take injiniya ya soma neman number aunty Kira ɗaya ta ɗauka ya isar mata da sakon hajiya inna tare da katse kiran ya tsaya rungume da hannuwansa ya zubawa hajiya inna idanunshi hankalinsa ya rabu kashi biyu   .

"Ko cikakken minti talatin ba'a  ɗauka ba  sai ga aunty ta  k'araso gidan  hankalinta a tashe  tace " me ya faru na ganku haka duk kunyi   cirko cirko? babu wanda ya buɗe baki  yace uffan  sai  hajiya  inna   "ina fa lafiya   salama  wannan yar iskar  yarinyar ce take ɗauke da ciki ,abinda  ya bani mamakin shine a ina ta samo cikin  ita da ba tarewa ta yi a gidan mijin ba ?
" gata nan ta tsaye ta kafe mutane da idanuwa kamar na agolar nufawa ta  gaya miki uban da yayi  mata ciki  dan wallahil azim baza'a likawa  babana cikin shege ba tunda nasan ko giya iyamurai ya kwankwad'a bazai aikata komai da wannan abar ba ..
a lokacin daya abba da hajiya umma har ma da mama suka runtse idanunsu tsabar bakincikin jin kalmarta ta karshe, wani irin numfashi mama ta dinga  saukewa mai haɗe da  tashin hankali jikinta na daukar rawa ta bude idanunta ta zubawa Ummita tana kallonta qirjinta na dokawa " tabbas ciki ne ajikinta  .

Aunty    da ranta yafi na kowa ɓaci  tace" haba hajiya inna ta ya mace da aurenta zaki ce  a ina  ta samu  cikin ?
"  a matsayinki na babba  bai kamata  kiyi  wannan tunanin ba ,sannan ba abun  mamaki bane aga  ciki ajikin ummita  bare har ki  dinga dangata jikarki da cikin shege  ..
Ummita   ta matso kusa da  aunty  ta riko hannuwanta duka hawaye na zubowa daga idanunta    "aunty   ki fahimceni  wallahi  bani da  ciki ,  dan  Allah karki   yarda da maganar  Inna  wallahi  sharri  take son  min saboda bata sona ,bancin haka   ta ina zan samu ciki  ?

"Ta  gidan  uwarki da ubanki shegiya mai kan maciji , wallahi idan  baki fad'i inda kika kwaso wannan abun kunyar  ba sai  kun bar gidan d'ana yau  ba  gobe ba  irin tsiya irin jaraba kawai irin danasani har kullum bazan daina bakinciki hada iri da uwarki ba  ,Kallon inna ummita take hawaye na cigaba da gangaro mata jikinta na mazari tamkar mai jin sanyi .

Jiki aunty a sanyaye  ta riko hannu ummita cikin nata   saboda rawar da jikinta yake  "kin kwantar da hankalinki  saboda cikin jikinki zai iya samun matsala , ummita  tayi saurin  girgiza mata kai wasu sabbin  hawayen na gangarowa bisa kuncinta  "bazan iya  ba ! Bazan iya kwantar da hankalina ba aunty ,ki taimakeni  duk abinda zai faru karki bari abbana  ya saki mamana  gara ni  tasa ya mah'ruf ya sakeni.....
  "shikena  amman kiyi shiru  ki natsu ki bar kukan nan haka bari na kira wanda   zai raba wannan gardamar domin inna ta tabbatar da gaskiyar lamari  .

" Wa zaki kira ?
inji cewar hajiya  inna da maganar ta kaiwa kunnuwanta ziyara
"Mah'ruf zan kira dan shi  ne wanda zai faɗi  uban cikin  jikinta , nashi ne  ko akasin haka "
"Ke salama  fita daga cikin  idanuna na rufe, Kema  an koya miki munafurci da  makirci  ko ?
"na kiraki  a matsayinki na diyar cikina    shine   ɗan munafurci zaki  d'aurewa karya gindi  kice sai  ma'hruf yazo ,yaron da kin san halinsa ko cikin banashi bane haka zai  kakabawa  kanshi , wallahi   karki soma   kiran shi dan  ko an kira shi cewa  zai yi nashi ne    ni kuma ko sama da kasa zasu haɗe  bazan yarda  a lika masa mugun iri ba, ki dai tambayeta uban da yayi mata ciki .... 

nan take zuciya ta ɗauki ummita  ta saki hannu aunty tayo gurin inna dake tsaye tana yatsina fuska  "wai hajiya  inna me na kashe miki  a rayuwar duniya ?
"me   nida mahaifiyata muka  tsare  miki  a rayuwa?
" wace irin tsana ce wannan ? "wace irin kiyayya ce  haka ? idan  ma kina  tsanar mahaifiyata  dan ta kasance yare nifa  me nayi miki  tunda daga tsatson d'anki na fito ?

"Baki sona baki son ganina cikin farinciki ,kin  fifita  sauran jikokin akaina kin fifita bare akaina me nayi miki ? "Ban  cancanci  ki tsaneni  ba saboda  ni din  jininki ce  kece  kika  haifi  mahaifina   ,  kina kin  mahaifiyata  amman ita tana   sonki kullum .... "mahaifiyarta tana miki biyayya, tana  gudun 'bacin ranki  duk abinda kike  mata  bata taɓa  d'aga ido ta kalleki  bare ta furta kalmar  ta gaji dake ba ,  hajiya  inna  ya kamata a ce kin rangwanta mata   wannan kiyayyar da ki ke  mata   wacce ta ja nima kike min  ....

kuka take sosai    tana farfad'awa  hajiya  inna duk  magana da tazo bakinta  mama ta k'araso gareta cike da sarewa  "Ummita kiyi shiru  bana son  sake jin bakinki  idan kika sake fad'awa hajiya inna wata kalma  bazan  yafe miki duniya da lahira ba, ta kare maganar tana zubar da kwalla mai zafi tana jin wani zafi a qirjinta bazata iya cigaba da ɗaukar wannan nauyin ba dole ta bar zuri'a hajiya inna haka ,koda kuwa hakan zai zamo sanadiyyar rasa rayuwarta ......

Baka jin sautin komai a parloun'n  sai na sheshekar kukan ummita a hankali mama ta isa gaban hajiya inna zuciyarta na zafi "kiyi hakuri inna dan Allah bazata sake ba...

"Dakata........
hajiya  Inna ta katseta tana  kallonta  shekeke "ni za'a kawowa gulma da munafurci da tsigudidi da annamimanci  wanda aka  gada  sai da yarinya ta gama  ɗebe min albarka  sannan zaki ce baki yafe ba ,Allah yasa ki  tsine mata  karewa rashin yafiya wannan ba matsalata bace matsalarki ce  da ita kadai gareki  , ciki kuma  sai dai kusan yadda zakiyi dashi  dan wallahi babana bazai amshi cikin da banashi ba .

"hajiya  Abba ya kira sunanta  ban ce ka saka  baki  ba idan kayi kuskuren saka  min baki zan tsine maka wallahi  "Idan kuma  kafi bukatar tsinuwar tawa ne  bismillah  , take Abba yaja bakinsa yayi shiru gumi na cigaba da tsatsafo masa  ta ko'ina ajikinshi bai taɓa bakinciki da nadamar kasancewar hajiya inna mahaifiyarsa ba sai yau , zuciyarsa zafi take masa a hankali gefen kanshi ya soma sarawa ya kai hannusa  ya dafe goshinsa  yana jin wani irin zafi mara misaltuwa "ya Allah wannan wace irin uwace gareni ...? "Allah kaga halin da nake ciki Allah ka kawo min ɗauki da gaugawa..

  "Haba Inna abinda kikeyi sam bai dace ba duk fa abinda   kayi na alkhairi ko sharri kanka kayiwa ba wani  ba , sakayyar duniya kuwa tun a nan  duniya yanzu  ake ramawa mutun "to zageni agabansu suji dadin zagina daman ai kune kuka fara  bada kofar zagina a gidan nan , ku dana haifa kun  zageni  waye ma ba zai zageni ba ?"ku cigaba da zagina har muhammadu Abdullahi mahdi ya bayyana  , Allah yasa kuma kun  haifa duk abinda kuka min shi za'a  yi muku, "inna lillahi wa Inna lillahi rajiun suke furtawa gabad'aya  jikinsu na ɗaukar rawa  tare da zubewa a gabanta injiniya yayi ƙoƙarin riko  hannunta ta fixge a fusace  haka ma  aunty "karki soma kai hannunki jikina ke kaɗai Allah ya bani mace  acikinsu  amman baki  da amfani agurina , har  ki tsaya gaban waɗan nan     kina  faɗa ina faɗa  ai ke kika bawa wannan  jairar damar zagina  ku cigaba da zagina karku daina ta karasa mgnr  tana zubda kwalla  katseta aunty tayi  "kiyiwa girman Allah kiyi hakuri Inna ki fahimceni ,wallahi wannan cikin na  jikin ummita na mah'ruf ne shi ....
"Dakata  Allah ya isa ban yafe miki ba tunda  kika ce cikin shi ne ,kuma kika  sake cewa cikin jikinta  na shi ne  na rantse da girman Allah zan tsine miki  salama ....

Babu abinda Abba da injiniya suke furtawa sai kalmar Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun , idanunsu ya rikide yayi jazir , ita kuwa hajiya umma bakinciki da takaici ya hanata magana  ta juya ta kalli inda suhaima ke tsaye  kamar wata  photo copy tana kallon kowa tana nad'e magana , a  matukar fusace tace "tsayuwar  me kikewa mutane, ana maganar family issues meye naki na tsayawa  ?
"Maza kama gabanki ta karasa maganar da  tsawa,tsawar da hajiya umma tayi ne ya dawo daita haiyacinta take jikinta ya kama rawa   simi simi taja  jikinta a sanyaye ta fice tana addu'ar Allah yasa cikin bana Mah'ruf bane dan idan cikin ya kasance nashi wallahi sunan shi zubabbe  , tana fita umma ta  bar parlour'n  itama  zuwa part dinta  ..

Ko second biyu ba'a yi da   fitar Hajiya umma ba   sai ga ma’aruf ya  shigo, a natse yake kallon kowa daya bayan daya sanye  yake  da   blue jeans  blueblack da   t-shirt ja mai kwala, yayinda kwalar ke zagaye da kalar   blueblack da bakin hannun rigar   kamar yadda wandon jikinsa yake , kallo ɗaya yayi musu ya fahimci kalar tashin hankali da suke  ciki .

Gaba-daya ya maida hankalinsa akan mama saboda fahimtar da yayi kuka take,   da idanunshi ya soma tambayarta  abinda ke faruwa  bata iya ce masa komai ba har sanda ya maida idanunshi kan ummita wacce ta dawo tamkar wata  zautacciya tana sambatu .

aunty  ta kira sunanshi a tsanake "babana..........
  ma’aruf ya waigo a hankali  zuwa inda  take durkushe gaban hajiya inna  ka samu guri ka  zauna, ya kasa  bin umarnin aunty dan   babu abinda yake son ji sai abinda ya sa mamansa  kuka da fatlion dinsa  ,kusan minti goma  ma’aruf yaki  zama yana tsaye qirjinsa na dukan tara tara .

A hankali  aunty  ta soma magana kamar haka    "a halin yanzu hajiya  inna  taga  ciki a jikin   matarka  shine take son sanin  cikin waye a jikinta ,naka ne ko akasin haka  ...?
Parlour'n ya sake d'aukar shiru baka jin motsin komai sai na sheshekar kukan ummita kowa so yake yaji abinda zai ce ,  ya tsurawa ummita idanunshi cike da tausayawa  itama zuba masa rauraunun idanunta tayi wanda suka karaya  cike da tashin hankali  "kayi shiru  kana kallon mutane cikin waye ajikin matarka  ?inji cewar injiniya yayi maganar a fusace ......

"Karku matsa masa ku gigita shi ya fad'i abinda ba daidai ba  ,kai babana kalleni  nan  ka faɗa min cikin jikin ummita na waye ?ya sake yin shiru yana kai hannunsa bayan keyarsa ya tsosa  yana  mai tsananin jin kunyar mama dake  gabansa wacce  ta langwa'bar da kanta  idanunta cike da kwalla .....
  "Karka cuci kanka ka faɗa min gaskiya duk  da nasan cikin nan ba naka bane amman zan so naji daga bakinka  ..
Idanunsa ya ɗauke akan mama ya tsaida akan hajiya Inna  "nawa ne  Inna ,cikina ne a jikinta  na tsawon wata biyar da sati biyu wata irin zabura hajiya inna tayi daga zaunen da take   ta mike  tsaye tana dubansa jikinta na rawa.
"cikinka  ?
Lumshe mata  idanunsa yayi tare da d'aga mata kai alamun eh .

"Shikenan  hajiya inna kin ji gaskiyar lamari daga bakinsa dan ha.......
tasss  tasss kake ji akan kuncin injiniya daya soma magana , yayi saurin  zaro idanunshi  waje tare da dafe kuncinsa "kai na tambaya dan ubanka ? ko da kai nake magana ? Tayi maganar a fusace sannan ta dawo gaban ma'hruf ta tsaya kyam tana huci  "kai  kalli cikin kwayar  idona ka sake maimaita abinda ka faɗa  yanzu ,dakewa yayi    yana  kallonta cike da dakiyar zuciya yace " Allah Inna cikina ne ajikinta  "Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun "a gidan ubanwa kayi mata ciki d'aukarta kake zuwa hotel ko me ?
Ya watsa mata harara "ta ya zaki min irin  wannan tambayar nida matata ta sunnah, koma a ina nayi mata tunda nace   nawa ne ba shikenan ba  nifa banason matsala da damuwa, to meye ma abun   tara mutane kan ɗan wannan abu saboda Allah  ? Kamata yayi ki kirani ni dake na fahimtar dake ba wai .....yayi shiru ya kasa karasa maganar saboda idanun mama dake yawo ajikinsa dan
tunda ya soma magana idanunta ke kansa sai data yayi shiru sannan ta  sunkuyar da kanta  tsabar  kunya da farinciki  daya lulku'beta, ta dinga  jin kamar kasa ta tsage ta shige ciki  sai dai  me yasa ummita zata karyata maganar a lokacin data tambayarta ?" me yasa zata karyata   hajiya inna alhalin tasan gaskiya, dan taya za tayi ciki  batare da ta aikata abinda zai sa cikin kasancewa ba ? "Har da rantsuwa akan bata da ciki  kai dan yau sai  dai ka barshi kawai ,ta fadi hk a cikin zuciyarta .

ummita kuwa wani irin  shock ne ya kama  ilahirin jikinta    ta tsaya tamkar wata wawiya  tana kollon bakinsa   da yake  musu bayani cike da mamaki , take  hajiya inna ta rusa  ihu  da kuka a lokacin daya .... ..
Abba da  injiniya  kuwa hamdala  suka dinga yi a cikin zuciyarsu tare da bawa hajiya inna hakuri, katsesu tayi cike da maseefa  "ku daina bani hakuri munafukan banza kawai  tayi maganar kamar wata zautacciya ..

ummita  na  gama jin bayanin mahruf  wanda ya tabbatar musu da cikin da hajiya inna take magana akanshi gaskiya ne ta sake shiga rud'ani da tashin hankali "yaushe hakan ta faru bata sani ba ? a sanita  dole sai mace da namiji sunyi auratayya sannan za'a iya samun ciki ta ya ita nata cikin ya samu babu auratayya ?
"Kai impossible wannan cikin ba gaskiya  bane ,dan haka  bai taba faruwa   a tsakaninsu da mah'ruf  ba bare ya kai ga ciki  ,ya dai faɗa ne kawai dan ya kareta daga maseefar hajiya inna  amman  ina ita ina wani  ciki ana zaman kalau "

aunty  tace " inna ki daina kuka yarinyar nan fa  matarsa ce halak malak  da jama'a suka sheida haka ,ciki kuma na faɗa miki gaskiya saboda ni na  dade  da  tabbacin  cikinshi ne saboda tun lokacin da cikin ya samu ma’aruf ya zo  har gida ya faɗa min  sai dai    yace kar na sanar da kowa......

"Amman kuwa  kin cuceni salama kinsan da wannan abu shine kika boye min saboda baki kaunata "ba haka bane inna sirrinsu ne wannan "ki min shiru munafukar Allah ,shi sirrin yaci kutumar ubanshi Allah  ya isa ban yafe ba "kai kuma munafuki kana  tafiya suki suki  kamar mutumin kirki ashe sharri ne fal acikinka   ya d'age mata girasa ɗaya yana cizan lip's d'insa na kasa  alamun meye illar abinda yayi  ...
"Ai  dole kayita zariya a bangarensu  tunda  an yi maka d'and'ani haukaci kana zariya kamar zatiyar wando  wallahi zaka san ni kake dagewa gira, dan wallahi sai na baka mamaki akan wannan ganganci da kayiwa rayuwata  ,sau nawa ina maka kashedi akan haka ?" kace kiyi maganarki a banza na d'auketa .....

Juyawa Ummita tayi bayan ta gama jin bayani   hajiya inna    tana kuka ta nufi d'akinta  nan take  ma’aruf ya biyo bayanta  yana kiran sunanta "fatlion ! fatlion !! taki tsayawa  ta shige  d'akinta .
ko da ma’aruf ya shigo  dakin ya sameta  tsaye ta bawa kofar d'akin baya tare da  rungume  hannunwanta duka a qirjinta   tana  kuka...
   ya k'araso   kusa da
DOWNLOAD
DOWNLOAD

2 Comments On WANNAN CE QADDARARMU
avatar
amina-4

11 months ago

Reply

Interesting novel

avatar
amina-4

11 months ago

Reply

Interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment