Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saboda ganin shirinta na son rugujewa "kuka na tambayeki ko key nace ki bani na bude kofa na kama gabana?
gabadaya muryarsa ta gigitata , kukanta ya karu yayi saurin runtse idanushi ta riko hannunsa ya fixge "wai meke damunki ?
"wani kwalla ya tsiyayo mata ya kalleta "da kyau kina nufin ba zaki yi abinda nace ba ?
Ta sake girgiza masa kai "ni ba keyn din ne bazan iya baka ba ni dai dan Allah ka kasance dani yau kawai zuciyata na min zafi over ...

Furzar da huci mai zafi yayi ya motsota sosai har suna iya jiyo numfashin juna "kina ta maimata kalma daya na kasance dake na miki uwar me ?
Tayi shiru "common tell me what do you want from me ? Yayi maganar a fusace
Muryata na rawa tace "Ina bukatar wani a kusa dani ka sani likita yace duk sanda nake jin haka na samu wanda zai kasance dani yana dibe min kewa yanzu idan ka tafi wa kake tunanin zai kasance dani ? ta karasa maganar tana kuka , juyawa tayi da sauri zata haura sama taku biyu yayi ya damkota ta juyo ta faɗa fad'ad'd'en kirjinshi ..

"me yasa ba zaki shafawa kanki lafiya dani kaina ba " ka taimaka ka san lalurata wannan kuma zai iya haifar min da komai ..
"Ki shafawa kanki lafiya dani kaina "ki daina bata min lokaci dan nasan lafiyarki lau duk sanda zuciyarki ke cikin wani hali nakan sani ki dai faɗa abinda yasa kike son ki kasance dani a daren yau idan ba haka zan wuce na barki ..... "

ai kamar jira take ya fad'i haka ta shiga kwakwulo kuka daga cikin kasan zuciyarta har wani sauti na daban kukan ke fitarwa ga wani shesheka da take kamar ranta zai fita rungumeta yayi tsam ajikinshi yana shafa kanta zuwa bayanta batare da yace mata komai ba, sun dade tsaye agurin har tsayuwa ta soma neman gafarar su ya jata zuwa kan kujera tana jikinshi yafi minti talatin bai ce qala ba , kuma bai d'ago kanta ba ya manne gefen kanta da saitin zuciyarsa inda take jin bugawar da take, gabadaya yanayin bugun zuciyarsa yaki saisaita haka ma nata ya lumshe idanushi ....

Bayan kamar awa daya yaji saukar numfashinta ya sauya jikinta ya sake alamun tayi bacci naunayen ajiyar zuciya ya sauke tare da rungumeta sosai ya mike daita ya kwantar daita akan doguwar kujera yana kallonta yana girgiza kai "fatlion kina da rigima over ,haka kawai ki takura rayuwarki da abinda ba samu zakiyi ba nima kina neman ki takura min yanzu me kike tunanin zan fad'awa suhaima yayi maganar yana duba agogon parlourn karfe daya ta wuce da wasu yan mintinoni ...
Ya kai hannu ya janyo hijab dinta dake ajiye a hannun kujera ya lulku'beta ya rage karfin ac parlourn ya nufi kofa fitar ya murda handle yaji kofar a kulle sai lokacin ya tuna kofar kulle take ya juyo ya dawo gurinta ya tsaya ya rasa yadda zai yi, shi dai baya jin zai iya tashinta daga bacci sannan bazai iya zuwa gurin mama adaidai lokacin ba koda kuwa yasan key yana hannunta bare yasan baya hannuta .

sunkuyowa da jikinshi yayi ya ciccibeta ya rungumeta kamar bai dauki komai ba haka yaji, ya nufi dakin dake manne da parlourn ya kwantar daita , ya zauna a gefen gadon kusa daita yana kallon kyakkyawar fuskarta yana jin wani shauki a hankali ya kai hannunsa ya gyara gashin kanta daya rufe mata fuskarta ya zarce da shafa fuskarta yana murmushin da bai san dalili ba haɗe da kai hannuta daya fuskarshi yana shishinawa haka nan ya tsinci kansa da kiss din tafukan hannunta ...
Mikewa yayi sakamakon wayarsa dake kara ya ciro ya duba suhaima ya gani yayi shiru ya kasa ɗauka kiran ,kiran na katsewa ya kashe wayar gbdy yana ciza lip's d'insa na kasa gara kar ya d'auki kiranta idan ya koma gida ya fahimtar daita komai ..
Madadin ya koma ya zauna sai ya dauko bargo ya shinmfa a kasan inda take kwance yayi pillow da duka hannuwansa ƙwaƙwalwarsa ta shiga caji "anya kuwa maganar jafar bazata zama gaskiya ba da yace son fatlion yake ?
Abubuwan da sukayi ta faruwa atsakaninsu tun farko har zuwa sanda yan daba suka kawo mata ziyara , yadda hankalinsa ya tashi moment din da suka tsinci kansu kusantarta da yayi irin dadin da yaji tsiwanta da rigimarta babu abinda bai tuna ba "mah'ruf Kana son yarinyar nan ka sadaukar kawai inji cewar kyakkyawar zuciyarsa, take dakikkiyar ƙwaƙwalwarsa ta shiga kin amincewa da haka , bacci yake son yi amman ya kasa runtsawa sai dai idanunshi a runtse suke cikin haka yaji fadowar mutun jikinshi agigice ta bude idanunta shima haka suka tsurawa juna ido na kusan minti goma shine ya soma runtse idanunshi ita kuma ta soma ƙoƙarin mikewa amman ta kasa saboda hannuwansa dake zagaye da kugunta gyara kwanciya tayi ta runtse idanunta ta dinga mutsmutsu ajikinsa hannuta ɗaya kife adaidai nipple d'insa tana murza kan wani irin numfashi mah'ruf yake fitarwa idanunshi gbdy sun rufe sun birkice babu abinda yake muradi kamar ya jishi cikin jikinta yadda suka ga rana haka suka ga dare tana murza nipple d'insa da shafa qirjinshi , kiran sallar farko ya kai bakinsa cikin kunneta ya zira harshensa ciki yana tsotsa a matukar firgice ta bude idanunta saboda abinda taji yana yawo ajikinta "ki tashi plz Ina son na wuce bana son mama ta fahimci anan na kwana ya yunkura tare daita bani key ta haɗe fuska "tun da asuba kamar wanda ya kwana a wani guri "ke bafa fahimci inda kika dosa ba kin bukace na kwana na kwana me kuma kike son nayi miki ?
"Ka tsaya har gari ya waye kayi wanka ka sauya kaya if possible ma kaci abinci "you're very stupid dake da wanka da abinci common give me key kafin na bata miki rai ta turo masa baki tana girgiza jiki janyota jikinshi yayi ganin tana son bata masa lokaci "fatlion .....
Tayi masa shiru "karki bari mu samu matsala dake fa na soma jin bacin rai "me akayi na bacin rai daga nace ....
"Keep quiet ya kstseta atakaice "bani key kawai ya shiga yamutsa jikinta wanda take jin kamar romancing dinta yake , babu shiri tace "tsaya tsaya tana ja da baya "a she dai ke din karamar yar.... tayi saurin toshe masa baki "karka ce min yar iska ga key, ta juya masa baya ta tura hannunta a kasan tsakankanin boobs dinta, ya juyo daita suna kallon juna yayi saurin runtse idanushi ganin yadda dukiyar fulaninta sukayo waje da sauri ta kamo hannusa ta damka masa key ta zube ruf da ciki saman katifa tana fidda numfashi ...
Tsaki yaja ya fita da sauri ya bude kofar ya fita Inna dake tsaye a parlounta taga wulgawar mutun kamar shi aiko da sauri ta fito ....

TWO FRIENDS BSBD

💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~TRUE LIFE STORY~

FREE NOVEL


AL'QALUMAN



*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*


~DEDICATED TO~
*AUNTY KHADEEJA UWAR GIDAN ALHAJI MUKTAR IDIARABA*


WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim


Page 47


....Binsa hajiya Inna
ta dinga yi a baya har sai daya kawo haraban gidan sannan ta daddage ta kira sunansa da iyakacin karfinta "babana ........
A matukar tsorace ya ja ya tsaya haɗe da juyowa qirjinsa na wani irin tsalle da dokawa da karfi ,ya tsura mata idanunshi yana kallon fuskarta cikin hasken daya haskaka gurin .

tsaye kawai mahruf yayi yana bin hajiya inna da ido gabansa na cigaba da fad'uwa kafin daga baya jiki a sanyaye ya zuba hannuwansa duka cikin aljihunsa wandonsa ya k'araso gabanta ya tsaya yana kallonta zuciyarsa na dokawa da karfi .
a hankali ya kawar da damuwar daya tsinci kansa ciki ya kirkiro murmushin dole ya kai hannu ya tsotsa keyarsa sannan ya soma gaisheta "barka da asuba hajiya inna ..

"Lafiya babana menene ya kawoka gidan nan a daidai wannan lokacin ?
"Ina cikin d'akina naga fitowarka daga wancan bangaren da alamun ma kamar a nan ka kwana ?"Ko zan iya sanin gaskiya daga bakinka ?

Yayi shiru hade da zuba mata kyawawan idanunshi dake cike da matsanamcin tsoro da firgici yana mai girgiza mata kanshi haɗe da cewa "ammmm uhmm ba wani abu bane yan....yanzu na ......
cike da takaici da 'bacin rai hajiya inna ta katse shi ta hanyar cewa "kamin shiru da wannan ammm uhmm din ka faɗa min ,me kake yi a gidan nan a daidai wannan lokacin daya kamata ace kana gidanka tare da matarka ?

Girgiza kanshi ya sake yi yana furta matsala a kasan zuciyarsa yayinda a zahiri yace "ki kwantar da hankalinki nayi miki bayani abinda ya faru "ina jinka ai bayanin nake bukata daga bakinka shiyasa ka ganni a gabanka dan ban san iskanci daya kawoka da asuban fari ba , kullun kai kenan zariya a wancan bangaren kana rawar gindi da 'bare 'bare akan waɗan can banzayen .....

Take yanayinsa ya sauya zuciyarsa ta soma tuttukin bakincikin , ya dinga jin kamar ya shake wuyan hajiya inna a fusace yace " don't ever try to call them fool in my present ,tsura masa ido tayi tana jiran karin bayani dan sam bata fahimci abinda ya faɗa ba ,"babana ni kake zagi da turanci akan mairo da yarta ?

" Kinga dan girman Allah ki saurara min ni banzageki ba amman karki ƙara kiransu da banzaye banaso yayi maganar yana furzar da iska mai dumi daga bakinsa , ya kalli hajiya inna yana mai tsura mata idanunshi sosai.
" dan Allah ki daina damuna da shiga rayuwata me ruwanki dani da rayuwata ne ?wallahi tsohuwar nan kina da matsala da damuwa , kullum ke kike kawo wa family's din nan matsala yana gama fadar haka ya juya a fusace zai wuce tace "dawo nan ina zaka baka yi min bayanin uwar uban da kazo nema a gidan ba ?

"Kinga hajiya inna ki koma ciki ki gaida Allah tukun alabashi duk abinda za'a yi sai ayi daga baya lokacin sallah na karatowa ni zan wuce ....
Ta rike hannunsa cike da tsigar rarrashi tace
" kwantar da hankali babansa banason wannan fushin naka .. "dole kiga fushi hajiya inna ni yaro ne da zaki dinga min irin haka ?

" to kayi hakuri dan Allah ni dai ka dinga bi a hankali bana son wani abu ya sameka shiyasa kaga duk hankalina ya tashi, ya furza da huci mai zafi sannan yace " don't worry hajiya Inna amman ke me yasa bakya son na kasance tare da matata ?
" kina ganin Allah zai barmu daga ni har ke akan abinda ke faruwa?
" Daga mama har fatlion basu da wata matsala duk abinda kike tunani akansu ba haka bane kin yi mis understanding
dinsu ne amman wallahi basu da wata .... ...

"Dakata dan Allah malam cewa nayi ka karanto banza da wofi akansu , babu ruwana da komai nasu kai din ne dai banason na ganka tare daita saboda banasonta daga ita har uwarta .. .....
" Enough Inna ya faɗa a fusace ya kai yatsan hannunsa qirjinsa " ni ne dai baki so ba fatlion ba , me yasa lokacin da zata auri rayhan baki hana ba sannan baki nuna bakinciki akan haka ba har tarewa yayi daita a matsayin matarsa amman ko sau daya ban taɓa jin kinyi magana akan haka ba sai da al'amarin ya juyo kaina?

"da zarar anyi magana kice ni kike so akan sauran jikokinki ,idan dai har wannan shine son da kike ikirarin kina min banaso dan so din banza ne bashi da amfani ,dan ba haka ake nuna soyayya gaskiya ba , tunda ba zaki barni na sauke nauyi daya hau kaina ba?
" kina tunanin Allah zai barni ne akan hakkin yarinyar nan da nake dannewa ?
"Wallahi Allah ba zai barni ba matukar bata
ya femin ba saboda itama mutun ce kamar sauran mutane .....
A fusace hajiya inna tace "Idan baka min shiru ba zan ci mutumcinka babana tun dazu kake faɗa min son ranka tunda ni ka raina ne barima naje na somu wancan sakaran uwar taka idan baka yi abinda nake so wallahi zanci mutunka da mutanen gidan gabadaya ..

Yayi saurin shan gabanta "wannan maganarmu ni dake dan me zaki sako mutanen gida ki tsaya muyi magana "dole na sakosu saboda kafi jin tsoronsu barin ma wacan agumawar ....
Ya sallama ya faɗa yana rikota dan yasan muddin yayi kuskuren barinta sai kowa ya san halin da ake ciki .

ran hajiya inna ya sake ɓaci matuka fiyye da farko sai farfad'an bakaken zantuttuka take yayi kokarin sausauta zuciyarsa a kanta ya riko d'ayan hannunta ,ta fixe a fusace "karka ta'bani "kiyi hakuri hajiya inna tashi hankalin mutane da asuba ni kuma tunda dai kin fi so a sanadin gudun 'bacin ranki na shiga wuta zan cigaba da bin dokarki ......
Take jikinta yayi sanyi saboda jin abinda ya faɗa tayi saurin girgiza masa kai "haka ne mana , nasan hakin aure amman kinki barin na sauke abinda ya ratayya akaina kin fi son wutar Allah ta cini sai dai kisani lokaci nake jira hajiya inna dan dokar yi miki biyayya baya kaina darajar iyayena kike ci, mman lokaci zai zo da zan nuna miki nawa rashin mutuncin ya zarta naki ya juya a fusace ta riko hannunsa "ka tsaya tukuna mana ta fadi tana karyar da wuya "nayi miki me hajiya inna ?
"Kina kawowa zuciya rud'ani kullum ,da zarar anyi wani motsi ki dinga cewa kina so ....

"Wallahi Ina sonka babana ai son da nake maka ne ma yasa kaga ina kaffa kaffa da rayuwarka kuma bana son wani mummunar abu ya sameka ta k'arasa magana ta tsigar rarrashi ..
"Ni wallahi kin zamemin matsala arayuwata da wannan son suna tsaye sai ga abba ya fito zashi massalaci sanye cikin farar jallabiyya hannunsa rike da carbi ya k'araso mah'ruf na ganinsa ya rusuna masa cike da tsananin jin kunya dan yasan dole sai yaji abinda ya faru "yauwa Ibrahim gara da kazo , wai wannan yaron nake tambaya me kawo shi gidan ,ni a ganina ma kamar anan ya kwana shine ya tsaya yana gaggaya min magana son ranshi ko bai san daga inda na fito ba ai ya raga min har da cewa na zame masa matsala arayuwarsa ta k'arasa maganar tana kuka .

abba ya dubi mah'ruf tun kafin yayi magana mah'ruf yace "abba ka manta da wannan tsohuwar ba gidan nan na kwana ba ya fadi hk saboda gudun jarabar inna , dan zata iya sauke musu bala'i a karon banza , naunayen ajiyar zuciya ta sauke "ko kai fa da ka faɗa min haka tun farko ai da babu me jinmu Ibrahim ta kira sunan abba "muddin wani abu ya faru to lallai zai zamo daya sanya hannun kai da matarka ciki kuma wallahi zaku haɗu da fushina "karki damu hajiya ai duk abinda kike so muke so ko raba auren nan kika yi babu me cewa komai "da kyau dan albarka zaka gama da duniya lafiya ,asuba kenan ban sanya komai acikin bakina ba nake maka addu'a duk abinda kake nema anan gidan duniya sai Allah ya dafa maka "ameen hajiya Allah ya kara miki lafiya "kai kuma kasan abinda nake muddin ka kuskurewa maganata sai naci mutuncinka tana gama fadar haka juya fuuuuuuuuu tayi cikin gida .

Mah'ruf furzar da iska yana takaicinta a hankali suka jera da abba yana masa murmushi dan shi jikinsa ya bashi a gidan mahruf ya kwana " ka cigaba da hakuri , kasan kowa da irin yanayinsa, haka Allah ya bamu ita, haka kuma zamuyi hakuri daita , duk da wannan fani babu uzuri akan haka , amman zakayi mana hakuri saboda duk abinda yaje ya dawo kanmu zai faɗa mah'ruf ya sake furzar da iska cike da jin haushin inna .
"Duk yadda zaka ki mutun abinda Allah ya tsara shi zai tabbata ,
Ka ɗauki wannan a qaddara komai mai wucewa ne duk ni na jawo da kuma qaddara tun farko ta nuna bata son aurena da mamanka amman Allah ya hukunto ,"kayi hakuri Abba amman gaskiya qabilanci ke damun hajiya kuma bashi da kyau a addani ,tabbas haka ne ba tun da nasan hajiya inna nasan bata son wani yare bayan hausa fulani nima qaddara ce auren mairo ban isa na gujewa qaddarata har suka karasa massalaci suna tautaunawa bayan sunyi sallah suka dawo still tare abba na sake kwantar masa da hankali
ya nufi inda yayi parking din motarsa ya shiga " Allah yayi maka albarka d'ana "ameen Abba yayi hon mai gadi ya

2 Comments On WANNAN CE QADDARARMU
avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment