Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sosai ,ya tako har inda take kwance ya tsaya akanta "uban wa kika tambaya zuwa wani guri ?
"Duk iskancin da zakiyi kiyi amman Karki kuskura kiyi ganganci da aurena dake kanki ,kuma ban amince ba ,ban yarda ki taka ko nan da can ba.

tayi saurin mikewa zaune tana dubansa ranta yayi bala'in ɓaci da maganarsa dan gaba-daya ta sa ran zuwanta , a hankali ta mike tsaye muryata a raunane tace "wannan dokar sai dai tayi aiki akan wa can matar taka saboda ita take da alhakin ɗaukar wannan matsayin amman gareni babu wannan , zuwa kwatono kamar naje na gama ,this is not the right time din da za'a kafa min doka, ka bari idan ina gidanka wata killa dokar taka tayi aiki akaina but for now nothing like that ta juya zai wuce ta barshi ya fixgota da karfi sai gata agabansa ji kake tass tass a kuncinta hagu da dama take ji da ganinta suka nemi ɗaukewa sakamakon zafafan maruka data sha daga hannunsa "matukar ba zaki daina maida min martani ba nima ina nan kamar yadda kika sani ban canza ba wawiya kawai ya hankad'ata tayi luuuuu zata fadi saman katifa cike da matsanancin tsoro ta riko shi gabad'aya suka zube kan gadon sai gashi rashe rashe kwance a saman jikinta ya danne kirjinshi da nata yana fitar da numfashi da huci mai zafi ,yayinda idanunshi ke kallonta , numfashi yake fitar da kyar har lokacin idanunta a runtse suke tana ganin duhu ,cikin lokaci kankani ta fita daga haiyacinta hawaye ne kawai ke zuba a idanunta ,ya tsura mata ido yana kallon kyakkyawar fuskarta daya mara gabadaya ya kasa kwakwaran motsi tare da jin haushin marin da yayi mata , gashi har shashin tafin hannunsa sun nuna , naunauyen ajiyar zuciya ya sauke ganin numfashinta na ƙoƙarin barin jikinta saboda sakar mata karfinsa da yayi ,ya yunkura ya mike tare daita ajikinsa ya rungumeta tsam batare da yasan ya aikata hakan ba "fatlion ya kira sunanta yana shinshina wuyanta " me yasa kika raina ni dayawa ?
" kin sani na sani kowa ma yasan banason raini, banason ina magana na kasa dani na maida min martani ....
"Ban raina na gaba dani ba , ta yaya kike tunanin zan ɗauki raini daga kanena bare ke da kike da matsayi biyu , ya juyo daita suka fuskantar juna zuciyoyinsu na bugawa da matsanancin karfi , hannuwanshi duka rike da kuncinta yana shafa inda mareta " me yasa fat lion kika raina ni ?
" Kina Kasa dani dole ki bini sannan dole kiyi min biyayya, ko ban girmeki ba darajar aurena dake kanki yakamata ki mutuntani me yasa zan dinga faɗa kina faɗa ?
Gaba-daya ya manta kanshi ya dinga furta mata magana masu sanyi a tunsninsa faɗa yake mata yana shafa fuskarta ...

Bangaren mama kuwa da sallama tashiga bangaren hajiya inna ta durkusa har kasa a gabanta tana cin abinci "ina yini inna?
da hannu ta amsa mata,ta maida hankalinta gurin cin abincinta ta zauna sosai tana jiran ta gama cin abinci , tana zaune tsawon minti goma sannan inna ta kammala ta d'ago sosai ta zubawa mama ido ,cike da fargaba ta sake bude baki "daman nazo nayi miki sallama ne Inna gobe idan Allah ya kaimu zamu tafi Cotonou duba jikin mahaifina "ayya Allah ya sauwake ya kaiki lafiya amman naji kince zaku ke da wa kenan ?
Tayi maganar tana kwa'be baki " nida ummita zamu .


"sam ban yarda ba wallahi ki barta anan kije ke kadai ki dawo Allah ya kaiki lafiya amman banda wannan yarinya ....
mama ta sake bude baki zatayi magana ta katseta cikin hanzari "zaki nuna ban isa bane ko me ?
Ta girgiza mata kai alamun a'a "to ban yarda ba ban amince ba ta k'arasa maganar tana juyar da kanta gefe.
mama ta yunkura ta mike tana mata sallama ta zabga mata katuwar harara "aikin banza ni za'a kawowa iskan da munafurci da barikanci, salon aje ayi mata agumu irin na agumawa ajiki a mallake min zuciyar dan jikana ina wallahi bazan yarda ba haka zata kare ita ba bazawara ba ita ba matar aure ba .. .....

Jiki a sanyaye mama ta koma bangarenta ta rasa abinda ke mata dadi har yaushe hajiya inna zata samawar zuciyarta sallama ?
da fari ta ɗauka soyayya ce ta sata hana tarewa ummita gidan mijinta, sai daga baya ta fahimci tozarci ne kawai da wulakanci da tsantsar kiyayya ,tana wannan zance zuci ta nufo kofar d'akin ummita domin sanar mata abinda ake ciki da sauri ta juyo ta nufi hanyar dawowa parlourn kasa sakamakon jin Muryar Mah'ruf ,dake cewa "na sani kin sani kowa ma ya sani bamu son juna but at least mu mutunta auren dake kanmu karki je ko'ina kinji na faɗa miki , naunayen ajiyar zuciya mama ta sauke "na san wata rana zanyi farinciki arayuwata , ya Allah karka barsu haka, ka cusa musu soyayyar juna a zukansu , su rayu cikin farinciki suna masu son juna ,tana zaune ya fito ganinta yasashi sha jinin jikinsa ,ya tsotsa keyarsa da yatsansa tare da gyara kwalar rigarshi " har kin dawo mama ?

Taki dubanshi saboda kar ya fahimci tana tattare da damuwa kanta na kallon wani guri tace "eh na dawo baba ya ɗauki yar saman rigarsa daya cire ya mayar ya ɗauki jakarsa ya rataya "to ni zan wuce mama
Allah ya tsare agaishe min da kowa , karki manta ki amso min sakon coffe gurin Usman "to shikenan ka gaishe da suhaima yace zataji ya sa kai ya fice ....
Har zai nufi doguwar barandar da zata kai shi haraban gidan sai kuma ya fasa ya juya ya nufi bangaren inna ,tana ganinsa ta washe masa baki tana farinciki "a'a ubana yafi na kowa sannu da zuwa k'araso ga guri ka zauna ta nuna masa kusa daita ,yaki zama kamar yadda ta bukata ,ya tsaya haɗe da jingine bayansa da bango hannunsa ɗaya cikin aljihun wandonsa "ka zauna mana kaja ka wani tsaya kamar tsohon soja "ba zama ne ya kawoni ba yaushe za'a kawo min matata ?
"Wace matar taka ai matarka tana gidanka zaune lafiyar Allah babana ,"Kinga Inna bari na fito miki a mutun sak "abinda nake nufi mamata subai'a nake nufi hope kin fahimta yanzu ?
"oh wai wannan yarinyar ?
" zugoka kenan akayi ?
" to wallahi tallahi zan baku mamaki kai da mairo ni za'a turowa kai dan ka tozartaki ?
ta zabura ta mike tana gyara zaninta yayi saurin rikota yana langwa'bar da kai dan yasan tana fita babu inda zata zarce sai part din mama tayi mata ruwan bala'i shi kuma abinda bazai so ba kenan a bata mamansa ,"kai inna daga wasa ,wasa fa nake miki fa ta sha zamanta .
"Sakar min hannu dan ubanka , "dan girman Allah Inna karki tadawa mutane hankali tsokanarki nake ,nifa taimakona kika da baki bari ta kwana a gidana ba "kai babana bana son munafurci da annamimanci dan zama da munafukai yasa kai ma ka koya.
"ko ɗaya Inna babu batun munafurci zauna kiji , "babu zaman da zanyi wallahi dan nasan duk munafurci ne, nan kwanaki baya kafin aurenku ,kace min sonta kake kamar kayi hauka, yanzu kazo kace na baka matarka, sannan kace taimakonka nayi wane hankalina da tunanina zai ɗauka ?
"Ɗauki maganata ta karshe dan ba sonta nake ba sai dai kuma ya kamata ace a matsayinki na babba kin ..
"Amatsayina na babba nayi me?
" ta tare mana Inna " ta girgiza kanta tana kallonsa shekeke tana kwa'be baki "Sai dai bayan raina idan kaga wannan yarinyar ta tare .

Ya tsaya shiru yana kallonta kamar ranar ya soma ganinta
"Bazan taba bari ta tare a gidanka ba domin tarewarta babu abinda zai haifar min dashi sai ciwon zuciya dan bazan juri ganin ana juya min kai ba ....
Ya sake riko hannunta cikin nashi "ki tsaya kiji Inna ba sai ina sonta ba tukun zata samu damar juya ba ,"zafa a juya min kai abinda zuciyata bazata ɗauka ba kenan .
Ta nan ta dinga
zuba masa ruwan bala'i ta inda take shiga ba ta nan take fita ba ,"

Ya sake kwantar da kai "Inna ki kwantar da hankalinki ki saurareni yanzu dan zata juya ni yasa kika ki bari ta tare a gidana tun tuni ? Kwarai kuwa amman idan zaka yarda da sharadin bazaka taba kusantarta ba shikenan sai ka d'auketa , yayi mata wani irin kallo yana dage mata girarsa daya ..
yayi shiru mama yake tunani gashi tafiya zatayi ba zai ji dadi ta tafi da bacin rai a dalilinsa ba if not daya nuna mata tru colour dinsa , duk da haka ma sai ya maka mata rashin mutunci ko ɗaya ne kafin ya wuce , a fusace ya juya "kar Allah yasa ki hakura, ba zaki mutu ba kina raye zata kasance a gidana kuma a matsayin uwar ya'yana karewar sharadin kusanta ..
"ta zama kaza ma karewar haihuwa dan mai shegen wuya awa marikin lema ,"duk asirin da aka maka wanda ke tunziraka da sannu zan karya shi ..
Har ya karasa fita bala'i take zubawa ,har shabiyu dare tana bangaren Abba tare da injiniya da hajiya umma tana zuba maseefa "hajiya kiyi hakuri ki bari a kai masa matarsa tunda har yayi magana inji cewar hajiya umma " oho daman da hadin bakinki yazo ya surfa min rashin mutunci ai gara da kika maganta naji ?
"A'a Inna wai dai ....
"wai din uwarki da ubanki ,ke gaki mai d'a ko ?
"Dan Allah hajiya kiyi hakuri "ku min shiru, ai duk bakinku daya ance muku bansani bane ban san ku ke zugosa ba, to naga ɗan iskan da zai zo yayi min iko , ta mike da kyar ta fice tana sababi tagumi sukayi dukkansu suka bita da kallo injiniya ya mike yana furta "Allah ya kyauta ya bar dakin Abba da umma kuwa kasa magana sukayi ..


Washegari

sai da direba ya kusan sameborda sannan mama ta kira mah'ruf ta sheida masa ta wuce ita kadai umnita na gida yayi shiru tare da cewa "to mama Allah tsare ,
"Ameen dan Allah ka sanarwar ummita dan batasan da fitowa ba nasan tana can tana bacci yanzu "ok mama inshaallahu Allah ya tsare .

sai karfe tara ummita ta tashi agigice dan ko sallah asuba batayi ba da gudu ta nufi bayi tayi wanka da alwala ta fito cikin sauri ta zira hijabi akan kayan baccin dake jikinta ta tadda sallah tana idarwa tayi dakin mama turus taƴi saboda ganin kayanta zube akan gado sabani jiya data shiryasu cikin akwatin daya dana mama,da sauri ta sauko parlour'n sama tana kiran sunanta cak ta tsaya sakamakon ganinsa zaune yana aikin tura sakonnin a system dinsa ....

A hankali ta karaso ta cigaba da kiran sunan mama "kina ina mama mun makara fa kanshi ya d'ago yana kallonta cikin kayan bacci ,gashin kanta zube abayanta "malama ki sausauta muryarki domin kuwa tafiyar mama tayi nisa dan killa zuwa yanzu ta kusan shiga kasarta zubewa tayi kasa kusa dashi tana dubansa da takaici "kina kallona daman ai nace miki karkije a she abun na ranki ?
yayi shiru ya cigaba da aikinsa yana ciza lip's d'insa , aiko tana gama jin abinda yace ta mike zata fita waje , ji tayi kawai ya fizgota ta faɗa jikinshi kadan ya rage system dinsa bai fadi ba haduwar da jikinsu yayi yasa kirjinshi ya cigaba da dokawar da take Ma'hruf ya damke kugunta da duka hannuwansa cikin bala'i yace "dan iskanci da fita zakiyi haka daga ke sai rigar bacci ?
kuka ta rushe masa dashi ,"ni ka sakeni ?
Bakinsa ya kai cikin kunnenta yana hura mata iska bakinsa a hankali sannan yace "saki nawa kike bukata ? A matukar firgice ta dogo idanunta ta zuba cikin nashi ya kashe mata idonsa daya "tell me saki nawa kike so ?
Take gabanta ya shiga faduwa koda bata son shi ,bazata so ya saketa tana gidansu batare da ta tare a gidansa ba "kinyi shiru ko ba saki kike bukata ba ?
kamar ta girgiza masa kai sai kawai ta sake rushewa da wani kuka ", karki sake wannan kuskure sannan karki ga ina magana akanki ki ɗauka ko na fara sonki ne ina kishinki this and that no..no ...that can't be possible ni dake bazamu taba son juna ba duk abinda nake ina yi ne saboda aurena dake kanki ,ya zama dole nayi kishin aurena saboda ni ba addayus bane mutumin da baya kishin iyalinsa ...


TWO FRIENDS BSBS



💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~TRUE LIFE STORY~

FREE NOVEL


AL'QALUMAN



*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*


~DEDICATED TO~
*TA DAN GAYU MRS MUSA*


WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim


PAGE 40


...Yana gama magana ya furza mata iskan bakinsa mai zafi haɗe da lumshe idanunshi , wani abu taji ya tsarga mata ya fara mata yawo a gabadaya ilahirin jikinta ,bai tsaya iya haka ba ya wuce har cikin zuciyarta .

ya ware hannuwansa duka yana buɗe idanunshi ya zuba mata "oya kama gabanki dan kin wani kwanta kina shan rabar jikina , mikewa tayi tana tsaki tayi hanyar sama ta ɗauki wayarta ta shiga neman layin mama na kasar kwatono , kira biyu ta ɗauka , tana ɗauka ta rushe mata da kuka " shine kika tafi kika barni mama .

"kiyi hakuri mamana nima ban so ba ,dole ne gashi da kunnena naji mijikin bai barki ba kiyi hakuri kiyiwa mijinki biyayya , Allah yayi miki albarka , ta katsen kiran saboda kukan dake shirin kufce mata ..
kuka tayi sosai bata san lokacin da mahruf ya ɗauka kafin ya tafi ba , ranar duk a sama ta yini , jikinta yayi sanyi , sai take jin kamar shikenan mama bazata dawo gareta ba ,sai da suka sake yin waya mama sannan ta samu natsuwar zuciya ..

Tunda suhaima ta tare a gidan kafafun mutane yaki ɗaukewa a gidan ba, tun mai gadi na tashi ya buɗe ya kulle har ya gaji ya daina , ya bar musu kofar a buɗe duk wanda zai shigo kawai ya shigo sai yaga lokacin dawowar mah'ruf ya kusa yake tashi ya rufe .
mai gadi ya zabura ya mike daga zaunen da yake , ya soma ƙoƙarin leka hujin dake jikin karamin get sakamakon hon din daya ji ,ganin motar mah'ruf ne ya soma ƙoƙarin bude tangamemen get din ,motar mah'ruf ta sanyo hanci cikin gidan ya shigo mai gadi na d'aga hannu.

kai tsaye rufar da'aka tanada domin ajiye motoci ya nufa yayi parking haɗe da kashe motar ya fito tare da jakarsa ya rataya a kafad'arsa yana ƙoƙarin zare key mota idanunshi ya sauka akan suhaima da wasu kawayenta waɗan da kusan kullun sai idanunshi yayi karo dasu , gasu nan dai babu laifi kamar suhaima suke da matsatsun kaya wuyansu rataye da karamin mayafi ,kallo ɗaya yayi musu ya runtse idanunshi ya furzar da iska kana ya zare keyn mota ya soma takowa a hankali kamar mace , suhaima na hangosa ta soma sallama da kawayenta "kunga sai gobe idan Allah ya kaimu kuyi maza ku wuce mijina ya dawo sukayi murmushi "wannan miji namu dai ana ji dashi suka haɗa baki gurin fadar haka .
"dole naji dashi idan akwai abinda yafi ji dashi zanyi dan samun kamarsa yanzu da wuya, nayi mua'amula da maza dayawa amman banji gamsuwar da nake ji a yanzu agurin mijina ba , "really ?
"Sure ta basu amsa sannan ta barsu tsaye ta nufo garesa , fuskar tashi a murtuke tamakar wanda aka aikowa da sakon mutuwa saboda bacin ran ganinsu ,sai da gaban suhaima ya fad'i , ta dai d'aure ta sanyawa jikinta jarumta ta rungumeshi ajikinta "welcome habibi "uhmmmmm kawai ya faɗa a takaice, ta amshi jakar aikinsa suka jero tare har lokacin su baseera na tsaye suna kallonsu suna murmushi, daf da zai wuce su suka hada baki gurin cewa "sannu da zuwa, ina yini habibinmu ?
" Tsaki yaja tare ɗauke kanshi yayi tamkar bai ga wasu halitta tsaye agun ba , bare ya amsa gaisuwar da suka masa ,suhaima ta juyo da sauri tana musu alama da hannunta su wuce ...
Murmushi sukayi suna kashe mata ido suka nufi get suna kad'a jiki .

Mah'ruf na gama shiga parloun ya juyo a matuƙar fusace yana fuskantartata
"Ke waɗan can me suke zuwa yi gidan nan kullum ?

Take jikinta ya kama rawa ta rasa me zata ce masa aiko ya sake fusata ya sake yin magana cikin daka tsawa "uban me suke zuwa yi ina tambayarki kinyi shiru ?

Bakinta na rawa tace "
Kawayena ne "ya sunansu? "baseera da nazera "a'a suna da wani suna bayan wannan ,"wallahi sunansu kenan tare muka taso "dakata ban tambayeki long talk ba "
kin san sunansu na ainihi ?
tayi saurin girgiza masa qirjinta na dokawa da matsanancin karfi " kashe aure sunansu "
ta bude baki tana kallonsa cike da sansar mamaki .

"zaki koresu ko ni na koresu , dan bana son sake ganin fuskarsu a gidana ke kadai na aura ba kwashe kwashen mutane ba , "gsky bazan iya kirarau da kaina ba ",karki damu ni zan koresu da kaina saboda banason ganinsu wannan banzar fuskar yasu a gidana yana gama fadar haka ya fixge jakarsa dake hannunta ya shige d'akinsa ,da sauri ta biyo bayansa tana bashi hakuri har dare cika kawai yake yana batsewa ko gida gurin ummita bai je duk da zuciyarsa ita kadai take muradi gani ,kuskure kadan zai hau suhaima da bala'i .

Washeari kuwa da rana yana zaune a parloun kasancewar weekend ce babu zuwa aiki ,sanye yake cikin kananan kaya whit t shirt da bakin wando mai tsukakken kasa hannunsa rike da remu sai gasu sun shigo suna kiran sunanta ko sallama babu , a parloun'n ya tsayar dasu yana aika musu da kallon banza wanda take hantar cikinsu ya kad'a suka haɗa baki gurin gaisheshi ",ina wu..........
da sauri ya d'aga musu hannu ta hanyar katsesu "su waye ku ........?
"mu...... mu kawayen suhaima sukayi maganar muryarsu na rawa cike da in ina ...
"tunda ku din ba y'an'uwanta bane kar na sake ganin kafafunku acikin gidan okey ayo ku juya ku koma inda kuka fito yan iskan banza kawai ta samu an rufa mata asiri an aureta shine kuke ƙoƙarin kashe mata aure sun sun suka soma jan kafafunsu a daidai lokacin da suhaima ta fito da sauri saboda jin sound d'insa "dan Allah habibi kayi hakuri ya juyo ya watsa mata kallon banza sannan yace "ko zaki bisu ne ?
Tayi saurin girgiza masa kai ya tsuke bakinsa yana furzar da numfashi da iska atare su baseera suka fita suna tsine masa ...
Har waje ya fito yana bawa mai gadi umarnin kar ya sake barin su shigo masa gida "an gama ranka shi dade mai gadi ya faɗa da hanzari daman ya gaji da ganinsu wata uku kacal da tarewar amarya amman gida yana neman dawowa kamar club "kai basu ba duk wanda yazo bayan yayyenta mutun biyu karka ba kowa ya shigo "an gama yallabai mah'ruf ya juya ya koma ciki yana huci .
Ranar ma bai yi kokarin zuwa gida ba sai washegari yaje ..

Tafiyar mama ya bawa Ma'hruf damar sakewa da ummita sosai har ma ya sha rabar jikinta ta hanyar kokarin kiyaye aurensa dake kanta , kullum safe da dare yana gidan sai goma yake komawa gidansa , yayinda kullun ya d8aura idanushi akanta hankalinsa ke sake tashi wani irin feeling dinta ke bijiro masa,wutar sha'awarta na sake ruruwa acikin zuciyarsa ya rasa wannan dalili ya rasa wani matsayi zai bawa al'amarin ..
koya koma gida da niyyar gusar da bukatsrsa ajikin suhaima baya jin daidai ,dan sha'awarsa bata gushewa sai karuwa ,
sau dari zai ganta sau dari zai ji yana bukatatarta "to ta yaya zaka gusar

2 Comments On WANNAN CE QADDARARMU
avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment