Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

?
"ko ba zakiyi hakurin ki fawwalawa Allah komai daya zartar akanki ba ?
A sanyaye kamar kazar da kwai ya fashewa aciki ta girgiza kai da sanyin murya tace " Alhaji na amince da qaddara ,Allah yayi masa rahma zanyi duk yadda kace gabadaya babu wanda bai tausaya mata ba daga haka baba Sarki ya mike tsaye "Allah yayi miki albarka sai anjimanku ta gyada kai da cewa " Allah ya kiyaye ya gyada kai yayinda yake karasa ficewa daga parloun'n inna ,Abba da injiniya na biye dashi ....

Kuka hajiya saudat tayi sosai tamkar ranta zai fita inna na rarrashinta ",kiyi hakuri nasan makirci ne kawai irin na mairo amman zanyi maganinta dan auren babana da yar banza yarinyar nan bazan amince ba, zamu hada karfi da karfi ni dake muyi komai gara ta zauna haka takare rayuwarta babu muji uwarta taji yadda kika ji .

"a'a inna ki bari ayi auren nan abinda rayhan ya bukata kenan ,ni dana rasa d'ana sukunta guda me kuma zan iya yi?
" ni yanzu abinda rayhan dina yake so shi zan yi daman ina kin ummita babu wani dalili yanzu wa gari ya waya ?
Cike da tausayawa hajiya inna ke rarrashinta ...
Ta dade zaune a parlour'n inna tana rarrashinta zuciyarta cunkushe da rashin danta ,ita kuwa Inna ta rasa yadda zatayi neman mafuta take akan al'amarin ,ita idan ba an fi karfinta ba bazata yarda da wannan hadin ba ,da kyar hajiya saudat ta taushi zuciyarta ta koma bangarenta .. ...


Bangaren ummita kuwa har lokacin tana cikin damuwa da kunci tattare da bakincikin mara misaltuwa haka ma mama tunda taga baba Sarki yazo gidan ta rasa abinda ke damunta ta kasa zaune ta kasa tsaye domin tun da taga sun kulle a bangaren inna tasan ba lafiya ba, da kyar ta samarwa zuciyarta salama ta nufi dakinta inda ummita ke kwance akan gadonta ,ta tambayeta ko akwai abinda zata ci tace "babu komai ,tasan har lokacin akwai damuwa a tattare daita dan haka ta zauna jigun a kusa daita tana tunani duk abun duniya ya dameta gabadaya duniyar ta tsaya mata cak saboda ganin tilon diyarta cikin damuwa ,cikin hk mah'ruf ya shigo d'akin ya gansu fuskarsu babu walwala ,take tausayinsu ya kamashi yasan mama duk tafi kowa shiga damuwa , shi kansa yana cikin damuwa tun daga lokacin da abubuwa sukai ta faruwa yake fama da matsanancin ciwon kai baya dai nuna wa kowa ne ,mama ta kafeshi da idanunu "sunnu baba da kokari , kana gida ashe ?
"Yanzu na shigo mama ya mai jiki ,?
"Da sauki gata nan dai taki cin komai tun safe nake fama daita taimaka min ko zata sakawa cikinta wani abu ,ya ɗan saci kallonta zuciyarsa na tsananta bugawa yaga wani guri take kallo , zuciyarsa yaji tana budewa da karbar wani abu mai sanyi da natsar da zuciya wanda bai san ko menene ba furzar da iska yayi sannan yace "ina abincin mama ?
"Bari naje na kawo ta mike cikin sauri "ki hado mata da ruwan zafi.
"to ta fice daga d'akin ,
Kujera ya janyo gabanta , sannan ya janyo kujerar mirrow din mama ya soma kokarin zama a gabanta tun kafin ya zauna jikinta ya soma rawa yayinda kirjinta ke dokawa da matsanancin karfi ya zauna yana kafeta da manya idanunshi masu bugar da zuciya "Malama ki samu natsuwa ,kina sane da shawarwarin likita akanki kou?
Tayi masa banza tamkar bata san da zaman mutu ba ,"ki taimaki kanki ki kwantarwa kanki da hankali, idan ba haka ba zaki mutu idan kika mutu mahaifiyarki kika yi domin sai tafi kowa shiga damuwa ,rayhan ya mutu babu wanda ya bishi duk son da muke masa haka muka hakura ,kema kina da tabbacin idan kin mutu babu wanda zai biki wallahi bancin mama da ni da kaina zan karasaki ki huta tunda kin gaji da duniyar....

ta d'ago da sauri ta tsura masa idanunta da suka fara ciccikowa da ruwan hawaye ta soma shesheka kuka yayi shiru yana kallonta kukanta na taɓa zuciyarsa batare da yace mata komai ba ..
Mama ta hado mata irin abincin da likita ya bukaci ta dinga ci da flask din ruwan zafi akan dan wani madaidaicin tire .
Mah'ruf ya amsa tiren ya ajiye a tsakiyarsu cikin sauri mama ta juya ta sake ficewa tana addu'ar Allah yasa taci abinci sosai ..
Har lokacin idanunshi na kanta flasks ya ɗauka ya tsiyaya ruwa acikin karamin cup ya hada mata ruwan Lipton ya kai bakinta ta lumshe idanunta tana bude bakinta dan babu halin yin musu kurba daya biyu tayi ta kawar da bakinta tana sauke naunauyen ajiyar zuciya tana jin wani iri ajikinta sai daya tabbatar data sha ruwan zafin sosai sannan ya bude
Kular abinci , white rice ne ya bud'e k'aramin kular shi kuma farfesun dayen kifi ne a hankali ya zuba daidai wanda yake bukatar taci ya zuba miya sannan ya rufe yana maida idanunshi akanta, yana jin wani wani irin yanayi a jikinsa ya kai spoon bakinta still Bai ce mata komai ba tayi shiru tana kallonsa ita so take ko sau daya ne ya rarrashinta ya nuna tausayawarsa gareta amman yaki duk abinda yake mata tasani ba dan ita yake yi ba darajar mama ne ....
Taki bude bakinta tana jiran yace mata wani abu hawaye na zubowa daga cikin idanunta yadda ta tsura masa ido yasa ya dinga jin tsigar jikinsa na mikewa yayi kokarin dannewa, a hankali ta soma rera masa kukanta "oh my god ya furta a matukar fusace "ke ..ke wacce irin ma.....
sai kuma ya katse maganarsa yayi shiru yana tunanin abinda zai faɗa mata bayan kamar second biyu idanunshi da suka Kada ya dinga lumshewa sannan ya bud'esu yayi mugun kafeta da idanunshi yana huci ya sake kai spoon bakinta babu shiri ta bude bakinta yana kallonta yana dura mata abinci yasan halinta bata jurar kallon idanunshi na tsawon lokaci kusan minti goma ya ɗauka yana ciyar daita har ta kusan cinye rabin plet sannan tace na koshi cikin sanyayyiyar muryata mai matukar kashe jiki ,tuni jikknsa ya mutu ya janyo numfashi da kyar ya sauke yayinda ita kuma tayi baya ta jingina bayanta da pillow tana kallon yatsun kafafunta ,"ki shirya na kaiki gidan aunty .
batayi magana ba ta sauko ta ya zira junbulelen hijabinta batare data saka nikaf ba bare safa ya kalleta bai yi magana ba , take tabi jikinta da kallo dan tana fahimtarsa koda bai ce komai ba ,shiru tayi tana son gano ma'anar Kallon take kwakwaluwarta ta fahimtar daita "nikaf dina yana d'akina nan ma bai yi mgn ba , ya wuce ta biyoshi kai tsaye d'akinta ya nufa yana shiga ya tsaya jikin bango har ta shigo yana kallonta tana dube dube har ta gani ta saka nikaf da safa ta fito ya tasata gaba suka yiwa mama sallama ..

Ko a moto babu wanda yayi wa wani magana har suka kai gidan yana tsaida motar ta buɗe murfin motar ta fita a hankali shima ya fito ya biyo bayanta ..

Yana shiga ya ci karo da Ahmed da gudu ya k'araso gareshi ya ɗauke shi ya daga shi sama yana juyi dashi bai sauke shi ba har sai da yashiga parloun'n aunty sannan ya direshi a kan kujera hadi da manna masa kiss a goshi Allah bai yi shi da son mutane ba amman yana matukar so yara most especial ahmed.

aunty ta kallesu cikin qauna ta murmusa tace "kai baba kamar dama shi kadai kayi kewa ?
da sauri cikin dry ya duka gaban ita da mijinta ya gaidasu , cikin farin ciki suka amsa , tana jin dadin yadda mah'ruf ke da tsakanin biyayya ya fita daban cikin abokan watsanshi , zafi ta ji sosai a ranta in yadda taga duk sunyi tamkar basu ganta ba sai ta mah'ruf suke .
Zama yayi kusa da aunty Yana faɗa mata abinda ya kawo su ,
Sosai taji dadi saboda yadda ya sauke duk wani amatsayinsa yake bawa ummita kulawa ,amar ne ya shiga janta da hira kafin kace me tuni hira ta barke tsakaninsu tun tana maqale jikin har ta hakura ,shi kuma Mah'ruf hankalinsa naga Ahmed ,
aunty ta kalli maryam tace "toh baku kawowa ummita komai ba kun zo kuna ta zuba mata surutu, ku kawo mata abincin , da sauri Maryam ta mike ta shiga ta dauko abincin Mah'ruf dake gefensu yasan wahalar da kansu kawai zasuyi sai dai yayi shiru ya zuba ido.
Duk yawan uban surutun da suke bata fiyye cewa komai ba sai dai ta saki ranta ..
Kusan awa daya
Su maryam da aslamiyya
Suna zuba uban surutu kamar parrot , ko bakinsu bai gajiya da magana ne oho , cikin kosawa da surutun nasu ya miqe ",aunty zamu wuce "daga zuwanku ko abinci fa bata ci ba dan dai kai nasan ba ci zakayi ba amman ita ai ka bari taci wani abu ?
"itama a koshe take ya ɗan saci kallonta yaji ko zatace wani abu a daidai lokacin da itama ta kalli inda yake idanunsu ya sarke cikin juna take zuciyoyinsu ya buga da matsanancin karfi da sauri suka janye idanunsu .....


TWO FRIEND'S (BSBS)



💗💗💗💗💗💗
     WANNAN CE
   QADDARARMU
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~TRUE LIFE STORY~

FREE NOVEL
            
      
AL'QALUMAN


*AYSHA  A BAGUDO*           
*FAIZA  HAMMADU*

~DEDICATED TO~    *AYSHA SHEHU MAMAN 2 (MAI DADDAWA) IYA WUYA TAKWARA MUNA JONE*

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

PAGE 36

.......Akan  hanyarsu ta komawa   gida  ummita ta  juya  masa   keya  tana  kallon  bangaren titi , haushin  abinda tayi yaji   dan kallo  ɗaya Za'a  musu  a fahimci   rashin ɗaukarsa   da mahimmanci  ne ya jawo haka.

take  ya soma tunanin abinda  zai mata  dan   ya  dawo  da  fuskarta gareshi  ko kuma ta maida  idanunta ga kallon   gaban  motar ,
A hankali  taji  saukar muryarsa  cikin kunnuwanta  " kada ki jefa  min  uwa cikin fargaba  da  zullumi da wannan  banzar tunanin naki.
"ita  din  fa mahaifiyata ce,  kuma  kowa  yasan soyayyar  dake tsakanin uwa  da d'a , tayi maganar  batare  data juyo ta dubi inda yake ba .

"ko  ma dai  menene  ki adana damuwarki  ta tsaya  iya kanki kawai batare da ta shafi  mahaifiyata ba   ..
     Bata  sake ce masa komai  ba  ta girgiza kai tare  da ɗaukar goran ruwan  roba  dake ajiye tsakiyarsu   ta kora  tare  da  ƙoƙarin  kawar da damuwar  data soma bayyana  a fuskarta.
a  watanin baya  ta hangi  abubuwa  dayawa a tattare  dashi  data  rasa a  sikilin da zata d'aura domin son  sanin   gaskiyar abinda ke tattare da zuciyarsa ,
sai  dai  a yanzu da take cikin  halin damuwa  ta sake  fahimtar komai ,ta kasa  amincewa  kanta mah'ruf  mai  kaunarta ne kamar  yadda  mutane dayawa  suka sha faɗa mata "ina  ma rayhan bai furta  abinda ya furta agaresu ba ...
  Wasu  siraran hawaye suka  gangaro  mata suna  isa  gida tun bai gama  tsaida motar ba ta soma  kokarin fitowa  amman  dole  ta koma ta zauna  saboda  yayi lock din motar .

tana  zaune  ya gama daidaita  tsayuwar motar  haɗe  da shareta har sai daya  gama shan kamshinsa  sannan ya yi unlock  ta  fito tana fidda numfashi..
duk  da cikin hajib take hakan  bai hanashi fahimtar  kuka  take ba "ya  sallama  ya furta a hankali "fat lion  me yasa kuka  baya miki wahala ?
"Me yasa kike son damun zuciyarki ?
"Banason kukan nan yana bala'in ci min rai ...
Ya  fito  yayi  key din motar  yana  kallon bayanta   kai tsaye   part din mahaifiyarsa  yaga ta nufa ,shi  kuma ya nufi part  din mama  bakinsa ɗauke  da sallama "Assalamu alaikum "
ya  iske  mama tana kokarin  cin abinci ta kai   spoon  bakinta ta ajiye tana  fad'ad'a fuskarta  wa'alaika Salam "har kun dawo baba  ?
"Eh mamana ya ɗauki spoon  din da take cin abinci ya kai bakinsa "ina ummita ?
Yayi  shiru  ya cigaba da cin  abinci , itama shiru tayi  tana dubansa "kada ki  tada hankalinki  mamana   ta shiga bangaren umma  har lokacin  idanunta na kanshi  "me kake gani akan  ciwon ummita ?
"Babu komai  mama komai normal  ya sake kai cokali bakinsa 

"mamana  gurinki  zan kawo  suhaima ta koyi  irin  girkinki  dan gaskiya girkinki babu karya "kai baba   tace maka bata iya  girki bane  ?
"Mama  dayawa fa yammatan  nan  basu iya komai  ba  sai fente fuska   ni Kuma akan haka  za'a iya samun matsala dani  "ka jika kai da  ba wani abinci kirki kake  ci ba  ,ya labarin jikin  mamanta kuwa ?
Ya  had'iye  abinci ya kora  ruwa sannan yace "taji  sauki sosai dawowarce  dai baza suyi  ba  ni addauta ma suyita  zama a can  karsu dawo , saboda aureta ma ya soma fita akaina.

  "duk  akan  zaman jinyar ne kake fadan haka ?
Yayi shiru batare da yace uffan ba "kafa dinga hakuri baba   uwa fa tafi ƙarfin komai   "no mama  ba akan shi bane akan wata yar matsala ne amman  shima nayi solving  dinta  ki tayani da  addu'a  mamana .
"inshaallahu  amman wuce matsalace wannan ?
"To ko akan  batun aurenka  da ummita ne ?
Ya  girgiza  mata kai  dan baya  son tashiga damuwa ko kad'an, mama  bata yarda  ba amman  ganin  yaki gaya mata  dole ta hakura tayi shiru  sai  dai  ta kasa samun  natsuwa  abinci ma  tsakura ta koma yi  ..

******

Acikin  kwanaki ummita ta gama  iddarta rana babu  wanda  bai yi kuka ba , mutuwar rayhan ta dawo  musu  sabo  barin mahaifiyarsa  da duniya tayiwa  war'bar kunu, bata  san  iya son da take wa  dan nata ba sai data rasashi  ta fahimci duk cikin ya'yanta tafi son shi ..
Bangaren  ummita  bata sauya  ba   ganin damuwa tayi mata  yawa  yasa  mahruf  ya  tausasa  zuciyarsa akanta ,  yana son ya jawota  jikinsa amman yanayin  da yake ji ke hana  hakan faruwa.

kayan  marmari  yasa mama  ta kawo mata,   bayan    ya  ta sata  gaba taci  abinci da ba wani na kirki  taci ba ,ta dan zauna na kamar minti goma   sannan     ya  turo mata  kayan fruit " ki sha  kafin  ki  kwanta  yatsina fuska  tayi  amman ganin yadda  ya haɗe rai tamkar  hadari  yasa ta soma  sha , bayan ta  gama  sha sai da tayi minti   goma  sannan ta  kwanta   haɗe da  kamkame  jikinta guri ɗaya  ,bargo   ya janyo mata  zuciyarsa na harbawa  , lokacin da yayi  kusa  da kunnenta  ya  soma  magana saboda ya gama karantarta  tsaf rarrashi take  buƙata  daga gareshi   " haba  fatlion me yasa  ba zaki sauya ba ,ki  sanyayawa  ranki,  likita  ya  faɗa miki illar damuwa  a gangar jikinkin  .
"duk  abinda  kike so ki fada  min   ko  mama  numafashinsu  ya  nemi tsarke guri daya   saboda kusancinsu  da juna ,
yayi saurin  mikewa ya  zauna  adaidai  fuskarta idanunshi  na kanta  "wai ma  menene abun damuwa fatlion  I think before  baki son rayhan ?
"Yaushe  na  faɗa maka bana son shi ?
"Idan  ma  bana son shi maganar  da  kenan, yanzu  da  zan ganshi zan  soshi   fiyye  da komai  dani  kaina , tayi maganar  tana lumshe idanunta  tare da ƙoƙarin boye  damuwar    data bayyana  a fuskarta .
   ya  ta'be  baki  yana harararta  dan yasan duk gulma ce  , "wa yasan alkibilarki ?
"Sai  Allah daya halicceki  zuciyarsa  ta  bashi amsa   da   hakan.
Da  hillata  da salon soyayyar  da  shi     kanshi  bai san yayi  ba yasa   ta soma samun  sauki  da sakin  jiki amman   har lokacin zuciyarta cike take da fargaban  aurensa .....

Hajiya   inna  ta zubawa mahruf   Ido na  tsawon lokaci   kafin  daga baya  taja   naunauyen ajiyar zuciya tace " babana  me yasa  bazaka  gujewa auren nan ba tunda nasan  kai ba  son yarinyar  nan  kake yi ba  ,kama  rasa wace zaka  aura  sai matar da ciwon sonta  ya kashe  d'anuwanka  ,da tunaninta  da rayhan ya bar duniya , mata  ya dubi inna  zuciyarsa  na masa kunci  yace ",haba inna ki daina cewa haka babu wanda  ya isa ya kashe wani , wannan maganar kowa  yasani alkwarin rayhan  za'a cika dan   yarinyar bata sona  ... ......
  " Ina ruwana  da rashin sonka da batayi ai abinda nake so kenan kai da ita karku so juna
ni  dai wallahi  wannan haɗin  bai  yi min dadi ba, ni kaf zuria ta  bana son kowa  ya aureta  bare kai haka  kawai  ana son aka Kaba  maka  ita  .
Haushi ya turnuke zuciyar  mahruf ,amman ya   ya saki fuskarshi   sosai  dan karta fahimci yaji haushi  yace" dan Allah  inna  kada  ki damu   kanki   daman ni  ina sonta ,  kuma gashi ummah  tana  son had'in  kowa ma yana so kema ke  so kawai  ayi auren cikin  farinciki ...
     "Amman  ka cika babban   munafuki  shine kake nunawa  mutane  baka  sonta "yaushe na nunawa  mutane  bana sonta ?
"Ko na taɓa faɗa miki bana sonta  ?
Yayi magana yana tsareta da idanunshi
ta  kad'a  masa kai "duk abinda kake mata ai kowa  yasan kiyayya ce zalla   "anaki  ganin  ba amman ni nasan bamu ta'ba  yin  haka  dake ba ya  k'arasa maganar yana furzar  da iska .
"aiko  idan dai haka ne  ka  bala'in cin  baya wallahi , ai gara auren sakina  da  dai ka auri secon-hand

"ko ma dai menene inna  ina  sonta a haka ,in dai son  da kike   kirarin  kina min  gaskiya ne      to  daga yau  ki fara son fat lion  a zuciyarki  .....

"Allah  ya  tsareni  gara na  so wancan yarinyar da  zaka aura wallahi akan naso jikar agumawa  masu tallan kifi  , yayi murmushi "to shikenan  hajiya inna kiyi duk  abinda  kike so ai duk  daya ne da suhaimar  da fat lion agurina ..
"Kai  dan  Allah rufe mana  baki,   bakin munafuki kawai  mai fuska biyu mayaudari  kawai ..
"kai  kai inna duk ni kad'ai   Kar fa ki  bari mutane sujiki  fa "
"suji  mana , kowa ma yaji mu  wallahi in  dai akan wannan  auren ne,kuma wallahi  gudunmuwar  da zan bayar na fasa  bayarwa ..

Yayi shiru yana kallonta Kullun  cikin  damuwa da fargaban  auren ummita yake , kuma  duk abinda ya  faɗa mata  ya dai faɗa  ne  ba  wai hakan bane  acikin zuciyarsa   sai   gashi  yayi nasarar tsintar   kanshi farinciki da  nishadi  ..
Ya  gyara  zama  tare da  haɗe fuska  yace
"Shikenan   tunda haka kikace  nima zan saka kaina  cikin damuwa  da tunaninta  daga karshe ciwon  zuciya  ya kamani ta  sanadin  soyayyarta na  mutu kamar yadda rayhan  yayi   Kinga  kinyi hasarar  jikokinki  biyu daga  karshe ta rayu ta auri  wanda  ya fi mu  komai .
Hajiya inna nagama   jinsa   ta  rushe  masa da kuka  "yaya  zanyi haka zan  hakura    na zuba muku  ido,  duk abinda ka shuka  ai shi zaka gurba wala  khairan  wala sharran  duk abinda uwarta  take  Allah na kallonta  dan  bata haifa dayawa  ba  ,shine  zata dinga  bin  jikokina   da bita  da  kulli  ta cigaba  kuka  "kai  inna  ki daina kuka  dan kukanki  ma wallahi  karamin kaunar fatlion  yake abinda nake so  dake  kiyi  hakuri kiyi mana  addau kawai.

"Allah  ya sanya  alkhairi  kuma  Allah ya dawo da kai  cikin haiyacinka ,
kada  ka taba  cutar  wacan yarinyar  ka sanya ido  sosai a gidanka dan an  rigada  an shanyeka yanzu   kowani  irin zalinci  za'a yi  ba sani zakayi  ba  "yana murmushi   yace " to hajiya  inna  zan kula na gode  da addu'ar da kikayi  naji  dadi naji dadi da  kin shiga zuciyata da zaki fi tabbatar da dadin danaji  akan wannan addu'ar taki  , ta  kalleshi da sauri  ",lallai  an gama da kai tausayinsa ya kama  inna, tasan Mah'ruf da  kiyayyar ummita, ba'a son ranshi zai  aurenta ba ,zai dai aureta ne dan an gama dashi da kuma  wasihan rayhan.

Ya mike  yana  duban fuskar  hajiya inna "to hajiya  inna ni  zan  wuce  sai  wani lokaci kenan  takaici da  bakincikin ya turnuke  zuciyarta ko kallonsa  bata sake yi ba tace  "jeka  babana Allah ya saka  mana   har  ya fice  zagin  mama take.. ..

Part  din  Abba ya  zarce sun  dade suna magana har  suka  gangaro kan aurensa  da ummita Abba  yayi  masa nasiha sosai  akan  yayi adalci akan  matansa kada ya sake ya cutar  da suhaima  dan ba yar'uwarsa bace ,Abba ya tamabayeshi "kamar nawa  za'a bayar  sadakin suhaima  a  bada dubu ɗari yayi ?
"Abba  duk  yadda kuka yi daidai ne,  tausanyinsa ya kama Abba , Mah'ruf yaro  ne mai tsananin biyayya  yasan bada son ranshi  zai auri diyarsa ba sai  dan biyayya .
"to  shikenan  baba  zan kira mahaifin  ita  yarinyar   duk  yadda mukayi  zan  nemeka Allah  ya tabbatar da alkhairi  ya amsa da "ameen " batun guri  zama  kuma  kayi amfani da  duka bangaren ,bangaren rayhan dana naka  ita ummita  sai  ta zauna inda take , sai batun kayan  lefe  karka ita ba sai an sake yi mata ba  tayi amfani da wanda na haɗawa rayhan  y
  kaje Allah yayi maka albarka ..

Jikinsa  babu  kwari ya mike  ya  shiga part  din Hajiya ummah, suna gaisawa  babu abinda ta fara  tambayarsa sai  "kunyi  magana da abbanka  kuwa  ?
Ya gyada mata kai  "zuwa  nan  da  sati biyu za'a daura auren , tayi murmushi ta saki ranta sosai, ya  jima tana yi masa  lissafi kudaden da zai kashewa ummita "amman hajiya Abba yace bai sai na kashe komai ba  ,tayi  amfani da kayan rayhan "ina....
ta  girgiza  kanta" kayan rayhan  daban naka daban  zaka hada mata lefe  kamar  yadda ake wa kowa ,shi daya hada wancan shi zai sake hada wannan idan ma bazai yi kai dole kayi  ,dan  wannan auren naka   ya fiyye min kowani  irin aure  ,duk auren da zakayi bazai kai kamar  wannan a zuciyata ba dan haka kayi duk wani abinda zai sakani farinciki, idan ma baka da kudin ne ka faɗa min zan baka .
"a'a ina dasu zan je bank na ciro ya mike jikinsa babu kuzari kamar wasa yake kallon abu  wai shine  zai   auri mata biyu ..
Cikin kwanaki  mama ta  kasa gane  kan ummita  kullum  cikin tunani ,haka shima  mah'ruf duk yabi ya rame ,  duk yadda taso ya faɗa mata abinda ke damunsa kin sanar daita yayi  ...

****
A can  bangaren suhaima iyayenta  sunata  shirye shiryen  ba da wasa ba tsiyaya kuwa tayi kamar hauka  tana bala'in son mahruf  fad'ar kudin datayi  tsiyaya dashi  bata  lokaci ne, tunda ta dawo kasar  bai zo ba sai ana sauran sati d'aurin aure shima ita ta matsa akan  yazo  suyi shawarar  yadda za'a gudanar   da biki.
yana zaune sitroom  cikin  farin yadi mai shegen  kyau da shara shara  har ana iya hango farar siglet dinsa , ta  shigo ta same shi taci kwaliyya  cikin riga da siket  na less wanda ya kama  jikinta  sosai  har ya  bulloko da saman dukiyar  fulaninta waje wanda  basu da maraba da na mace mai yaya biyu  zuwa  uku taimakon    bra mai ciko   da Kuma yanayin  shigarta ya bulloko dasu  ake ganinsu zunduma zunduma ,  tasa kayan ne dan ta burgeshi  sai dai   ba wani farinciki yayi ba , da kyar take juyawa saboda  yadda kayan suka  matseta dif yayi mata  yaki cewa komai gabadaya  ya sauya mata kamar ba mah'ruf dinta ba  ,itace tayi ta surutunta  daga karshe yace  ta fadi abinda take buƙata shi dai babu abinda  zai yi walima kawai ta wadatar  ta marairaice  murya kamar zatayi  kuka "haba habibi haka zanyi biki babu komai bikin aure sau daya yake zuwa a rayuwar mutun.
ya  daure fuska sosai yace "oho ashe bani kaɗai  rashin lafiyar mahaifiyarki   ya dama   ba  har dake ?
Tayi sororo tana kallonsa "Yes kina kallona ko ba haka kika faɗa

2 Comments On WANNAN CE QADDARARMU
avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment