Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fito da sauri ya buɗe masa get ya cilla hancin motarsa waje ya fice .. .

"Yana tuki yana mamakin karfin halin Inna ,me yakama nayi wa wannan tsohuwar ?
"Tsohuwar nan ta damu kowa acikin family's da rikinci, tafi ƙarfin zuciyar kowa ,kowa na tsoronta tunkaranta akan zancena da fatlion.
"Nagaji da wannan rayuwar na gaji dan dole nasan abun yi akan aurena , tsoron Allah shine farko akan komai bazan cigaba da biyewa son ran hajiya inna ba .

"Bazan cigaba da sake jin komai daga bakin kowa ba, kawai a bani matata ,idan basu bani nan kusan zan dauke matata tunda abinda take tsoron faruwarsa ba haramun bane ,ya ma rigada ya faru meye amfani cigaba da boyewa ?
Yayi shiru kawai yana tuki yana sake zurfafa tunaninsa zuciyarsa , ke bashi shawara kawai ya bari har sanda cikin ummita zai fito ya bayyana kanshi kowa ya gani ,kada ya ka sake biyewa hajiya inna , da wannan shawarar ya wuce gida .

kamar dai wancan ranar a parloun'n kasa ya iske suhaima kwance hannuta rike da waya bai tasheta ba saboda gudun maseefarta ya shige d'akinsa ....

Duk yadda yayi tunanin zata d'aga hankalinta , sai yaga batayi ba sai ma tarairayarsa tayi wanda bai sani ba tun bayan data yi ta kiranshi bai ɗauka ba ta kira yayarta hajiya rahma , itace ta kwantar mata da hankali "karki ce masa komai idan ya dawo, akwai shirin da nake masa "gaskiya yayarmu bana son aiki irin na wannan babalawo din na mafuluku dan kwata kwata aikinsa baya ci nafi son ki kaini inda akayi miki aikin da kika mallake abbansu Yusuf ...

"Okay ijoko Kenan ? Tace "eh " gaskiya da matsala zaki jira har ya dawo kenan ?
'dan shi baya zama sai bayan shekara shekara yake zuwa amman idan yayi miki aiki sai wani ikon Allah.
"irinsa nake so dan wannan karon har uwar goyonsa da mahaifiyarsa nake son rabawa nan sukayi sallama ta cigaba da neman layin mah'ruf ..

******

Da yammaci ranar ummita da meenal suka kulle kansu a d'aki, ummita na bata labarin abinda ya faru ,meenal tayi dariya har da rike ciki "ai daman nasan kyalesu kawai kikayi da tuntuni kin tada bom ɗinkin da yanzu an wuce gurin "ke dauriya fa nayi kinsan halinsa da hauka da wayo na dinga zuba iskanci ..

"Kin burgeni ta wajena wallahi gara da kika rikeshi ya kwana a agurinki ,nan da zuwa wani lokaci ma da kanshi zai maganta abinda ke ransa ,ke ko bai sonki kiyi kokari ki dasa soyayyarki acikin zuciyarsa dan gaskiya ni banason ku rabu da juna kun dace fiyye da kowani ma'aurata "har ke da abdulshakur ɗinkin ?
Meenal tayi dariya "ina gaskiya anan ban zance komai ba , suka bushe da dariya "kinsan Allah bayan iskancin da n kikayi jiya ki soma kula samari inji cewar meenal zai gane bashi da wayo "me ....? Ummita ta faɗa tana zaro ido waje "samari meenal ta sake maimatawa "gaskiya ban bazan iya ba gudunmawa wannan ba ai kasheni zai yi , ni da nake son na janyo hankalinsa idan ya ganni da wani wallahi zai iya sakina .......
Menal tayi ihu haɗe da rungume ummita ajikinta "wallahi da gaske ta kamu ,ta kamu da son yayana "mtssssss ummita taja tsaki kina da matsala wallahi janyo hankalin da ban soyayya daban tunda yace bazai sakeni ba ai gara nayi abinda zan dan samu matsayi agurinsa amman gaskiya bazan iya daukar wannan shawarar ba ,"ai kuwa dole kiyi , kuma dole ki sanya hannu idan babu saka hannunki komai bazai tafi yadda nake so ba ,kuma ai hakan ma zai sake haukatashi har ki fahimci irin son da yake miki "kai menal bazan iya ba "zaki iya kawo kunnenki kiji shiru ummita tayi tana binta da ido "karki damu ni zan shirya komai nan suka cigaba hirarsu ..


Yana kwance a parlour'nsa kan doguwar kujera mai zaman mutun uku yayi pillow da hannunsa ɗaya yayinda d'ayan hannun ke saman fad'ad'd'en qirjinshi tun daya dawo daga aiki yake kwance agurin yana tunani , abinda ya faru daren
jiya yaki barin kwalkwaluwarsa ,yaki barin zuciyarsa ta huta , duk inda yayi da zuciyarsa tunanin fatlion ne daskare har ta soma masa gizo .

Ya kira suhaima da sunanta yafi sau biyar a dawowarsa gida , shiru dai tayi masa tana kallonsa up and down a lokacin da abun ya faru , shima kallonta yayi kawai dan bashi da mafuta, komai zai faɗa ba yarda zatayi dashi ba ..

A hankali ta sake fitowa sanye da riga iya gwiwarta mai wuyan otanet har lokacin yana kwance a inda ta barshi ta matso gabanshi sosai ta durkusa gabansa tana shafa qirjinshi zuwa kasan mararsa tana murmushin dole wanda yafi kuka ciwo, dan ita kadai tasan bakinciki da zuciyarta take ciki daga jiya zuwa yau

ya buɗe idanunshi da kyar qirjinsa na dokawa yana kare mata kallo tare da kai hannusa ya shafi fuskarta "fat.......... yayi saurin runtse idanunshi tare da furta "oh sorry baby , I don't know what's wrong with me ,but I den mean to hurt you , " ta sauke numfashin bakinciki tana cewa "koma menene bazan damu ba, I don't care about all that saboda nasan soyayyata daban take acikin zuciyarka ,ka soni fiyye da komai , fiyye da kowace mace a duniya ,nice macen ta farko da zuciyarka ta yarda ta kuma amince da ita a matsayin abokiyar rayuwarka , ba wacce aka baka aurenta a bisa sautsayi ba sannan ba dan kana son kasancewa tare daita ba .

"am so different to you habibi ko ba haka ba ? ya lumshe mata idanunshi kawai ,duk da nice na fara dating dinka but zuciyarka ta amince dani , ka sadaukar min da farincikinka...
" duk da haka am sorry nasan babu dadi .

ya k'arasa fadar haka tare da yunkurawa ya mike zaune sanye da kayan shan iska a jikinsa riga hamless da gajeren wando iya gwiwa sai kamshi mayataccen turarensa yake , ta mike ta zauna kusa dashi ya jawo kugunta ya haɗe da nashi yana kissing din gefen wuyanta ,sai lokacin ta ɗan jin sauƙin zugin da zuciyarta ke yi, ya juyo yana fuskantartata hade da sanya kwayar idanunshi cikin nata take idanunsu ya tsarke suna shaƙar numfashin juna , idanunta suka kad'a ta fara lumlumshe su dan bata iya jurar irin wannan kallon daga garesa, da zaran hakan ya kasance komai kwance mata yake taji bata bukatar komai sai shi , shi kanshi ya lakanceta bata iya d'aurewa kallon cikin kwayar idanunshi , "i love you habibinah ta faɗa tana zubewa ajikinshi tana shaƙar Kashim turarensa ,sam bai ji komai ajikinsa ba kamar yadda yake ji idan jikinshi ya haɗu dana fatlion ,ta ƙara shigewa jikinsa sosai ta rungumeshi sun kai kusan minti goma a haka tana shishige masa da yamutsashi , yayinda hakan ke haddasa masa jin haushinta a cikin zuciyarsa, dan shi jikin fatlion dinsa kawai yake muradi a lokacin da zai sameta bakaramin dadi zai ji idan ya tuna yadda ta dinga masa jiya komai kwance masa yake .

Suhaima na kan sarrafa shi qarar wayarsa ta katse abinda take masa, ta kai hannu ta ɗauka tana dubawa , sunan jafar ta gani rubuce akan screen din wayar dan haka ta sauke naunauyen ajiyar zuciya a fili tana mika masa wayar "jafar ne ya amsa yana dubawa ita kuma ta mike ta shiga kitchen .

Tana shiga ta la'be domin jin abinda zai faɗa sai dai bata ji komai ba sai "gani nan zuwa yanzu ta ga ya mike tsaye ya ɗauki keyn motarsa , da sauri ta fito "ina kuma zaka a daidai lokacin nan ta tambayeshi "zan dan fita ne zuwa gurin jafar ,
d'aga kai tayi kawai sai dai da tana da hali gsky bazata barshi ya fita ko'ina ba , dan duk inda zai je yanzu da wuya bai dangana da gidansu ba, amman bata da halin hanashi ya hanu da ta hana "sai ka dawo ka kular min da kanka dan Allah "an gama babynah ya manna mata kiss a goshi ya fice .

kai tsaye unguwarsu jafar ya nufa ,a haraban gidansu suka haɗu yana zaune akan daya daga cikin fararen kujeru hannunsa rike da waya , jafar na ganinsa ya saki murmushin mugunta "kaga na fatlion bada kanka a sare kaje gida kacewa su.......
"dakata dan Allah malam banason haka ya fad'i haka a daidai lokacin daya k'araso inda jafar yake , jafar ya nuna masa kujerar dake kusa dashi "zauna Sarkin miskilanci , kana son yariya kana kaiwa kasuwa , wallahi mah'ruf ka fito ka fitar da abinda ke ranka .

"matsalata da kai kenan jafar rashin fahimta ,"kai ne dai baka da fahimta amman ni tuni nagama fahimtar inda zuciyarka ta dosa, baka taimakon kanka idan ka tsinci kanka cikin damuwa , koda yake wannan kamar a jininku yake kuna cikin matsala amman sai ku bar abun acikin zuciyarku har sai abun yayi muku illa .

"dan Allah jafar me kake son nayi ? Kai da ni musan halin da zuciyarka take ciki akan yarinyar nan ,kana son matarka itama kuma da alamun tana sonka,kai fa gabad'aya na gama fahimtarka so kake sai itace zata fito ta furta tana sonka .......

"Exactly abinda nake so kenan amman batun so babu ina dai son kasancewa tare daita a koda yaushe ...
"ai kuwa wannan matartaka ta fika dakiyar zuciya da d'aurin kai bana tunanin zaka samu wannan damar , sannan ka daina yaudarar zuciyarka akan baka sonta ,kai bani ba har matarka idan tana da hankali da tunani zata fahimci halin da kake ciki ,soyayyar subai'a ta gama kama zuciyarka da komai naka tunda har kana bukatar kasancewa tare daita me kuma ya saura ?
"Ban sani ba ajiye wannan maganar me yasa kace nazo kana son ganina ?

Ajiyar zuciya jafar ya sauke sannan ya maida kallonsa ga mah'ruf yana murmushi yace "abinda yasa na kiraka ina son nayi aure ....kallonsa mah'ruf yayi yana murmushin jin dadi sannan ya rungumeshi "amma naji dadi "a ina yarinyar take ?
" A family dinku take tun lokacin bikinka naganta naji ta kwanta min a rai ya karasa maganar tare da yin shiru .
"uhmm ina jinka "wacece acikinsu Sa'ada , maryam aslamiyya ko Khadeeja?
"Duk babu ko ɗaya acikinsu sakina yarinyar da kaki aurenta a gaskiya ni tamin kuma ina son na aureta ......
"Sakinar gidan baba sarki ......?
"Yes wallahi ina sonta ,soyayyar da bazata misaltu ba nan dai ya kwashe duk yadda yake ji akanta ya faɗa masa ,kallon mamaki mah'ruf yake masa shima jafar tuni ya lura da irin kallon da yake masa " jafar hauka ka soma ko me ?" sakina yarinyar da age mate dinmu ce " so what ina ruwan soyayya da wani age , shekaru ai ba wani abu bane ni dai na gani kuma ina so ,na sanar maka ne dan ka shege min gaba idan kuma bakinciki zaka min sai na sane .
"sorry my friend walkahi haukan naka ne ya bani mamaki "kai aboki ka bar wannan maganar na makance akanta nayi istahara yafi sau babu adadi akanta still the same thing nake ji akainata ,ni bana neman wani kuruciya ko shahararren kyau blessing nake nema arayuwata , idan na aureta zanji dadi .

"lallai kam zakaji dadi ajikin tsohuwa "ka cika maida abu baya wallahi yanzu haka ma so nake ka rakani gurinta ka faɗa mata da bakinka ..

"Baka da hankali wallahi kuma idan ni kake jira na shige maka gaba agurinta zaka dade baka aureta ba sun dade suna tautaunawa daga bisani sukayi sallama jafar nayi masa dariya dan shi da wasa yake masa ɗaya ce ya rakashi gurinta ...

Daga gidansu jafar hanyar gidansa ya dauka yana cikin driving kira ya shigo wayarsa ya dauki wayar ya duba yaga babu suna da kamar bazai ɗauka sai dai ya maida wayar ma'ajinsa sannan ya ja koren maddani ya manna bluetooth a kunneshi "hello ..
Daga can bangaren aka asma da hello mah'ruf ne ?
Yace "eh "
" to wallahi kayi maza kazo gida ga matarka ummita can tare da wani tana zance a bayan conpaund"what ya furta hankalinsa a matukar tashe "wacece ke ?
"Sanin ko wacece yake da mahimmanci agurinka ko matarka ?
Bai sake cewa uffan ba,
hankalinsa a matukar tashe ya dauki hanyar unguwarsu wani irin kishi ya dinga jin yana taso masa "waye wannan ?
"Uban waye ya isa ya wulakanta aurenna ?
yau shi kaɗai yasan yadda zai yi dasu a haukace ya dinga tuki...
Taimakon Allah ne ya kawo shi gidan ..

Yana shigo gidan ko gama daidai tsayuwar motarsa bai yi ba ya fito zuciyarsa na wani irin dokawa da karfi ,jikinsa har tsuma ya nufi inda aka fada masa tun daga nesa idanunshi yake kansu har ya k'araso inda suke ,lokacin da ta ganshi sai da hantar cikinta ta kad'a taji wani irin kuluuuuuuuuuu wani abu ya tsarga mata a ciki take jikinta ya soma rawa, a hankali ya ɗauke idanunshi akan matashin saurayin dake zaune kusa daita ya maida kan ummita dake zaune qirjinta na dokawa da matsanancin karfi .

zuciyar mah'ruf cunkushe da bakinciki jin haushin ganin ko alamun tsoro bata nuna da ganinsa ba ,wani irin zafi zuciyarsa ke yi shi kasan matashin ya firgita da ganin irin kallon zakin da mah'ruf ke masa "wanene kai da har kake da karfin zuciyar zuwa gurin matata ....?
Tambayar da yayiwa matashin kenan wanda yasa ya zabura ya mike tsaye jikinsa na rawa yana duban ummita, ganin bai bashi amsa ba ya nufeshi gadan gadan "uban wa ya naka izinin zuwa gurin matata ?

"malam me kake faɗa ne wacece matarka anan ni sam bam fahimceka ba ka wani gigice ka fita haiyacinsa haka ......
Ai bai dasa aya ba yaji yayi masa wata muguwar shaka " uwarka ce wannan da kake tare daita ko matarka ce ?



TWO FRIENDS BSBS

💗💗💗💗💗💗
     WANNAN CE
   QADDARARMU
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~TRUE LIFE STORY~

FREE NOVEL
            
      
AL'QALUMAN


*AYSHA  A BAGUDO*           
*FAIZA  HAMMADU*

~DEDICATED TO~
*MUHAMMAD SALIS BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Page 48

"how   dare   you  tost  my   wife  ?  "dont  you    know   she's   married   ?
"I will   teach  you a lesson  today , not my wife   even  the  dog  in  my  house     u  can't tost ,    "don't   don't ever   try   ......
da   ganin  yadda mah'ruf    yake  maganar   kasan gaba-daya  ya  gama fita haiyacinsa,  zuciyarsa ban da  tuttukin    zafi  da zugin  kishin matarsa  babu abinda  yake   .

Shi  kuwa matashin  idanunsa  gabad'aya  sun yo  waje , yayi  bala'in  galabaita   a hannun mah'ruf  ,sai  da mah'ruf  ya   tabbatar   da  yaji  jiki sosai   ta  yadda  gobe  idan  yaga  mai  kama da ummita   a guje zai  falla sannan  ya sausauta rikon  da yayi  masa  ...

A  matukar  firgice ummita  ta   rike damtsen  hannunsa,  tana  fad'in "ya  mah'ruf   ka  sakar  masa   wuya   wallahi  bashi  da  laifi , bai  san  hawa  bai  san komai  ba  karka   kasheshi  pls   ta  fad'a hawaye  na zubowa  kan fuskarta . 

Mah'ruf  ya maida   idanunshi   kanta yana watsa  mata  wani kallo mai  haɗe  da  harara  idanunsa   yayi   ja sosai, fizge    hannunsa   yayi yana   ƙoƙarin   buga kan matashin   da  bango, ta saki  wani   razananniyar ƙara   tana  faɗin  "Shikenan  zai  kashe   amad".... ......

zaman   dirshan  tayi a kasa  tana  ihu  tana  yarfa   hannu  cikin  rawar   murya   take  furta  "ya   mah'ruf   karka  kasheshi   amad  ne  fa  wallahi  babu  ruwansa ,  duk  shirin menal    ne  , menal     ki kira mama  tazo , na  shiga uku  duk  ke  kika  jawo  sai  da  nace  miki  no ! no !!"   ta k'arasa  magana numfashinta  na  sama  da kasa,  gani  numfashinta  na  ƙoƙarin  d'aukewa   ya  saki  wuyan   amad   tare  da kai wa  fuskarsa  naushi amad   yayi  saurin zubewa kasa   hannun mah'ruf  ya naushi bango  runtse  idanunshi yayi yana  furzar   da  iska mai  zafi  daga bakinsa ,tsayawa yayi yana  kallon  ummita da idanunshi  da suka kad'a sukayi  jajur kamar garwashin wuta, saboda tsansar  ɓacin ran da yake ciki......
take   jikinsa  ya kama rawa    yana  jin wani matsananci  kishinta from  know  where  yana sake  bin  jinin   jikinsa.

da ɗan saurinsa  ya  matso   gabanta    kamar  zaki ya gurfana   a gabanta, ya sanya  tattausan hannunsa  ya  tattarota zuwa  jikinsa ya  rungumeta tsam tsam    yana   kiran  sunanta cikin  wata  irin  murya  mai  cike  da   tsantsar   tashin hankali .......
"Fatlion! Fatlion !!    kin kuwa  san   yadda nake jin  aurena  dake  kanki  ? "you are  so  much  to me  fatlion ,"mai  yasa zaki tsaya  da wannan  da  bai kai ni  komai  ba ? "  ki buɗe  idanunki  nasan kina  jina   ki bani amsa ...?   ya ƙarshan tambayar  cikin  ƙaraji da masifa  tamkar  zai shaƙeta saboda haushinta,   ba dan darajar  cikinsa  dake  jikinta  ba  da shi kaɗai yasan  irin  mugun hukuncin da  zai mata,
ko wani  namiji  ta gani sai  ta  firgita ....

naunauyen  ajiyar  zuciya  ummita  ta sauke jikinta  na  wani  irin kyarrrrma saboda  tsawar  da  mah'ruf ya daka  mata ta gigitata, cikin  fizgo numfashi ta buɗe   kyawawan  idanunta  fes akanshi 
"Ki    min bayani akan  furucin da naji ya fito  daga  bakinki  mai  kama  da alamara  ya k'arasa  maganar yana zuba  mata kyawawan idanunshi  da suke ƙara narkar  mata  da zuciya a hankali  ta shiga  girgiza masa  kai  tana lumshe idanunta ........

Duk   abinda  ya  faru akan  idon  meenal  ne  ,take  cikinta   ya  duri ruwa ,a hankali ta furta "Wayyo  Allah"  aguje ta falla  tayi  hanyar bangaransu   jikinta na rawa ta shige uwar d'akan  hajiya ummah tana  sake  furta "na shiga  uku shikenan  ummita  zata   tona min asiri   ,nasan muddin    ya  mah'ruf  ya ji shirinsu akan shi  sai yaci ubansu ta   ƙarshen maganar    tana kai kawo a d'akin kamar wacce tayiwa sarki karya   , zariya ta dinga yi daga farkon d'akin  zuwa  karshen d'aki  domin  neman  mafuta, kafin ya gama  da  ummita ya dawo kanta .

A matukar  firgice mama ta  fito  sakomakon ihun ummita data  jiyo  , tana gama  isowa  inda   suke ta  tsaya  cak  tana  duban   amad  dake rike da  wuyanshi    yana  cire  wata   fuska  daban yana   fitar  da  numfashi  da kyar  kayan dake jikinsa yasa ta  fahimci shine ,  sannan  ta waiga inda  mahruf  da  ummita suke  suna  kallon  fuskar  juna kai  tsaye  wajen amad ta nufa ta riko shi   tana  tambayarsa,  shi kuma yana ƙoƙarin  cire fuskar da yayi amfani daita.

" amad  lafiya  me  yasa  meka  haka kake numfashi da kyar ? "Wannnan face din fa na menene  tayi masa tambayar   gabadaya   hankalinta  bai  Kan   ummita  da mah'ruf  dake durkushe a kasa ..

Shiru amad  yayi yana dubanta hankalinsa a tashe "shikenan bashi da mafuta  dole sai mama tasan komai   kamoshi  tayi ta zaunar dashi  akan  kujera  tana sake  tambayarsa   "Ka fada  min me ya same ka?   Sannan karar  me  naji yanzu  ? naji  Ƙara  Sautin ummita  tana ihun kiran  sunanka?
  Da  hannunshi ya nuna mata inda suke , tsura  musu   ido   tai  tana kallonsu  tare  da neman Karin   bayani "na gansu ai  ka faɗa min me ya faru  ...?

A hankali ya soma yiwa mama  bayani  cikin yaren agumanci  "Wallahi mama   Ina  zaune  d'azu   ummita  da meenal   suka  sameni da wata  mgn   wai suna son na  zauna  tare da ummita  a matsayin saurayinta ita kuma a matsayin  budurwata sannan  ko  ya mah'ruf   yazo ya  tambayeni  na nuna masa  bansan ko ita din wacece ba....... nan  ya korowa  mama duk  abinda  suka  tattauna a tsakaninsu  har zuwa  sanda  mah'ruf   yazo ya damki wuyansa   .  

"Shi wannan face din fa a ina kasamoshi ?
"Menal ce ta bani ya k'arasa maganar yana shafa wuyansa dan ba ƙaramin jin jiki yayi a hannun mah'ruf ba ,
mama  tai  shiru  cike da  mamaki jin abinda ya faru  dama da meenal da ummita zasu iya aikata  wannan dayen  aikin  ? muryarta a matuƙar  sanyaye   ta  kira sunan mah'ruf  " baba"
ya d'ago idanunsa  da kyar  ya  maida  gefen da mama  take  wanda sai lokacin  yasan da zuwanta  " ka kwantar da hankalinka  amad  ne  fa"
ya  bude  idanunshi  sosai  yana  kallon mama da  amad  ya nuna sa da yatsana yana son yin magana amman ya kasa "ka natsu kaga abinda yasa baka ganeshi  ba  ,ya sake runtse idanunshi  gaba daya  shi   bai  ma tsaya tantacewa   ba   sbd  tsabar   kishi  daya 

2 Comments On WANNAN CE QADDARARMU
avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment