Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

min ba ban  damu da rashin lafiyarta ba , kin je kinyi zamanki a wata ƙasa da sunan jinya yanzu kuma kin dawo kina shirin yin bidia alhalin bata gama samun isasshen lafiya ba, well duk ma abinda zakiyi  kina  iya yi  wannan damuwarki ce amman ni babu ni ciki kamar zatayi kuka tace "dan Allah kayi hakuri nasan shine ma yasa kake son hadani da wata ...
A zuciyarsa yace" duk ke kika jawo   ...
"Ni dai kayi hakuri  hajiya  ta samu  sauki  sosai kamar yadda na faɗa maka yan'uwana zasuyi biki idan baka zo ba abun zai zama su...
Saurin d'aga mata hannu yayi "kinsan Allah babu inda zani kuje ke da ya uwanki marasa tunani kuyi duk abinda zakuyi yayi wa account dinta transfer din kudi masu yawa ya mike ya fice.

da Kuka ta shiga parloun'nsu ana suka kusan  cin karo da hajiya rahma yayarta  ta faɗa jikinta tana kuka,hajiya rahma   ta tambayeta "menene kuma ?
"Yayarmu ki taimakeni Mahruf baya tatawa hankalinsa na wani guri ..
"ki kwantar da hankalinki zai zo hannu ne  wannan shegiyar yarinyar da zai aura bama zata gane kanshi ba,duk cikinmu wa kika ga ya zauna da kishiya ?
Ta girgiza mata  kai  "to Kinga  kuwa babu yadda za'ayi ki zauna daita ,ke dai kisa ido akwai dabaru masu yawa da zan koyar dake , kin shafa masa maganin  kuwa  ?
Ta girgiza  kai "ko fuska yaki saki bare na shafa masa ,"okay duk ki rabu dan burouba  zai gane kurenshi ne ,  ni addauta a soma d'aura naki aure "shine  yayarmu ,  nima nafi son haka, daki suka karasa  tana rarrashinta ..

****
Tana  kwance  a parlour'n hannuta  rike da carbi  tana  ja  taga  ana  shigowa da wasu hadaddun  akwatina   sai da aka  gama shigowa  da akwatina  aka jeresu a aguri daya  site  shida shida  ne kala iri daya guda biyu  sannan aunty  ta  shigo ta zauna kusa da mama, ummita  ta mike a hankali ta gaishe da aunty "ya karfin jikin ummita ? Ta tambayeta cike da tausayinta
"Alhamdullahi aunty  naji sauki sosai ya su maryam ban gansu ba ko sai zuwa gobe zasu zo?
"Eh sai zuwa gobe zasu zo "ok  tayi hanyar sama tana  cigaba da jan carbi

"Waɗan  kayan fa aunty ? Inji cewar mama ,
Cike da fad'ad'a murmushi aunty   tace "lefen ummita ne da suhaima  har an kai can bangaren hajiya ummah tace aka su duka nan domin gurinki  yafi cancanta aka kawo  "yanzu ita ummita har wani  lefe za'a yi mata bayan ga na rayhan can  ko ta'basu baayi ba dan kawai a wahalar min da yaro ?
" Kai kinji jiki da  wata magana  rabon diyata ne dole  kuma ayi mata na rayhan daban nashi daban ai bashi yayi yaya ne yayi  hajiya umma kuma ta dage lallai sai anyiwa diyarta  mama tayi murmushin jin dadi tace " Allah ya sanyawa auren albarka yanzu yaushe za'a kai na suhaima ?
"Da  dai  gobe  da yamma nace  amman me kika gani ?
"Babu wani abu ai duk yadda  kuka ce daidai ne ...
Washegari  gidan ya cika da  wasu  daga cikin dangi  domin kai lefen suhaima , mota uku suka tafi  dashi  an tarbeshi cikin  mutumtaka bayan an dan yi barkwanci dangin  suhaima suka soma  duba kaya sosai suka dinga  yaba  kaya, da  zasu  wuce aka  basu tukuici  dubu ashirin   ,  dubu  hamsin suka kawo musu   da  buhun shikafa biyu  da akwaiti shida da kayan lalle ...

akan hanyarsu ta dawo gida ne  daya daga cikin makotan  aunty data gayyata tace "maman aisha  gaskiya d'anku bai yi  dacen gidan aure ba ,gashi zaku had'a diyarku  kishi da yar gidan ,kowa ya san  yan gidan basa zama da kishiya ,haka suka  taso  har uwarsu  duk auren da ubansu  zai nema sai an gama  komai ake fasa shi "da gaske  hajara  ?
"Kwarai  kuwa ai ingaya miki  ciwon uwar ma mutane  cewa suke tsabar  bin bokaye ne  ya mai daita  haka kullum ciwo  ba'a wannan kasa daita  ba'a wancan kasa daita duk dan neman magani , ku dai ku tashi tsaye  da  addu'a dan ko peper chicking  din da sukayi bazan  ba ta k'arasa  maganar tana dariya  har.
"kudin fa ko  shima kin yafe ? " Kudin kam zan amsa tunda cikin wanda muka  kai musu ne har suka kawo gida hirar suke  dan haka bayan an bawa  Kowa takuici  ya kama  gabansa aunty take sheidawa mama sannan  ta karasa maganar da  "ki  tashi da addu'a muryarta a sanyaye tace "addu'a kullun  cikin yinta muke salama  sai  dai zan sake dagewa  na gode sosai da kulawa  Allah ya  yara zuri'a  har  harabar gidan mama  ta rako aunty inda tayi  bangaren mahaifiyarta hajiya inna ita  kuma mama ta  dawo part dinta  cike da zullumi..

Da  daddare hajiya ummah  da kanta  ta  shigo  duba jikin ummita  har  dakin  ummita ta shiga  ta isketa zaune cikin  halin nata data saba na tunani ,tayi gyaran  murya da sauri ta dawo hankalinta  tana ganinta  ta zube kasa ta gaisheta  kamar koda yaushe  ,ta  karaso ta kamo  hannunta ta damke  cikin nata ta mikar daita  ta zaunar daita , itama ta zauna a gefenta  murya a sanyaye  tace "kiyi hakuri da  duk hukuncin da Allah  yayi miki ,ina kaunarki ummita kamar yadda  nake kaunar mahaifiyarki  kauna  irin wanda bazan iya misaltawa ba , ina farinciki da wannan auren  ummita na dade ina  mafarkinsa  a she zai  faru ina raye  ,na rokeki  ki  kiyi farinciki dashi  ,nasan nan gaba dukkaninmu   zamuyi alfahari dashi , wannan auren  wani qaddararen al'amari ne   daga Allah  dan haka ki saki jikinki ayi  duk wani shirye shirye  da za'a dake   Allah yayi muku albarka ku  ruke juna  da amana dukkaniku  abu daya ne  agurin  mamanku  duk abinda yayi miki kada ki boye  min  ki sanar dani  kinji  ni din tamkar mahaifiyarki ce  zan ɗauki  mataki ,bazan yarda ataka min ke  ba .....
Har ta gama dogon bayaninta ummita  bata ce  komai  ba   kanta na sunkuye  a kasa  tana wasa  da yatsun hannunta hawaye na zubowa  daga cikin idanunta  tashi muje bangarena  ki daina zama  ke kadai  ,tare suka fito ta ta sata gaba ...

*******

Kira  ɗaya hajiya rahma  babbar    yayar  suhaima  tayiwa  kanwarta zulaihat dake binta ,  bayan sun gaisa tace "har yanzu baki k'araso bane me kika tsaya yi   ?
"ina kan shiryawa ne yayarmu gani nan zuwa bazan bata lokaci ba saboda  nasan mahimmanci abinda ke gabanmu ..
Ko cikakken minti goma batayi da ajiye wayar ba, ta karaso suka fito  Cikin had'add'iyar  motar hajiya rahma   ,babu abinda suke  tautaunawa  sai yadda  zasu mallake Mah'ruf  ya zamo sai abinda  yar'uwarsu tace ..
Hanyar  mafoluku suka  ɗauka dake unguwar oshodi  ..

TWO FRIENDS ( BSBS)


💗💗💗💗💗💗
     WANNAN CE
   QADDARARMU
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~TRUE LIFE STORY~

FREE NOVEL NOT FOR SELL
            
      
AL'QALUMAN


*AYSHA  A BAGUDO*           
*FAIZA  HAMMADU*

MY  QAUNA  KINA  RAINA  , INA  YINKI OVER  DA  BADAN   BA   DA NACE KAF MEDIA ..................
WASU ZASU YI TUNANIN TO ME YASA  BANYI  MAGANARKI A TUN FARKO BA , NO NO QAUNA  NAKI SAUDAKAWAR TANA CIKIN ZUCIYA , ZUCIYA DA ZUCIYA NE KAƊAI ZASU FAHIMCI HAKA MUCH LOVE
WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

PAGE 37

..bai   fi  tafiyar  minti talatin   daga  cikin  agege ba suka k'araso mafoluku  ,
Can  nesa  da  gidan babalawo  dinsu  suka yi parking  ,Suka  fito  suna cigaba  da hirar abu ɗaya  , sun  iske  babalawo  zaune  cikin wani kangon  d'akin   da  yake  tafiyar da aikin  tsaface  tsafacensa  jikinsa sanye da    kaya masu matukar  datti kamar  koda yaushe  farar siglet  ce data koma ruwan brown tsabar kazanta   da dogon  wando   yana  cin namiji  goro    yana kur'ban  ruwan giya.

yana  ganinsu  ya  bushe da  wata  mahaukaciyar  dariya  yana musu marhabun  da zuwa  " Ramota   (e,ma wole)  yau  kune a garin  ?
"  kwana  biyu  najiku dif (bawoni alaja )  ya hajiya  take ?
zama  sukayi  tare da cewa "wallahi  rashin lafiyarta  ne ya hanamu zuwa  ,gabadaya  bama cikin natsuwa  da kwanciyar hankali .."shongo awo  afun  ni alafiya .
   tun   kafin  su  fad'i bukatarsu   ya  soma buga  kasa  yana wasu zane zane  a cikin kasa da yatsunsa  biyu  "kanwarku  ce  zata auri wani  mai shegen  taurin kai  kuma  zasu kasance su  biyu a gurinsa  sannan mahaifiyarku   na  bukatar a fasa  aurensa da wacan yarinyar   sannan  kanwarku  ta mallakeshi mallakewa ta har abada  sai yadda  tayi dashi .

hajiya rahma  ta girgiza masa kanta  alamun   haka  ne  "boka  mai gani har  hanji  dubanka haka ne  sai  dai  bana bukatar  a fasa  auren  a yanzu saboda mutane zasu iya fahimtar daga  garemu ne ,  ayi auren amman muna son  suhaima  ta zamo  tauraruwa a gidansa   har acikin zuciyar  miji  da danginsa gabadaya,  yarinyar tazo  amatsayin  yar  aikinta , mijin  ya  tsaneta , bayan ta  zamo  ba kowa  ba agurin  miji  ,ta zamo baiwa  ga yar'uwarmu  suhaima  ta  dinga jin tsoronta sannan a cire masa  tunanin  kowa ce mace  a duniya idan ba na  suhaima ba,  duk kuma  abinda ta umarce shi, yayi mata  cikin rawar jiki..

(Babalawo
ifa to ri  ifun owo eyon)
( Boka  mai  gani har hanji)  ya sake bushewa da  wata mahaukaciyar dariya har yana  buso  musu  warin giyan   bakinsa .

" duk abinda kika lisafa babu wanda  zai gagara hajiya  rahma  ta sauke naunauyen ajiyar zuciya mai hade da farinciki ," zanyi  aiki amman  dole  wani aikin zai soma aiki   ne  bayan ita yarinyar   ta kasance a gidansa,   za'a  bene  aikin   a tsakankanin  d'akinta  na bacci   ta haka ne   zaman  gidan zai  gagareta   sai  ta zama  abar  tausayi, sannan  zan  baku  wani abu da kanwartaku  zata saka agabanta  tayi tsawon kwana biyu   tana  sakashi  a gabanta  sannan  ta cire ,wannan  ruwan  kuma  ya d'auko wani  kwalba dake ɗauke da ruwa da  duk  tsutsotsi ne  aciki  ya ajiye  a gabansu  ,," zata dinga  fitsari  acikinsa   ,amman sai  ta kalli gabasa ta ambaci  sunanshi da abinda take buƙata akanshi    shima  na tsawon kwana biyu da wannan  itacen  zaiyi  a gabanta  ,sai tayi mishi girki yaci  kafin a d'aura aure  amman banda bismillah  matukar  yayi bismillah  aiki  ya karye sai dai wani aikin bashi ba  .

  nan  take  ya  dinga musu   bayani   yana  haɗa masu  tsafinsa  ya   bawa hajiya  rahma  layar da za'a benne  da sauran magani  asiri  kala kala ya haɗa , hajiya rahma  tace "babalawo ina son ayi mata gbere  a gabanta  kamar yadda aka mana  ta  yadda zata kara  mallakeshi "wannan  ba matsala bane  bayan  bikin  sai  ku  zo daita  ayi mata suka  zube  masa kudi masu yawa    sukayi gaba  cikin farinciki ...

Kai tsaye gida  suka nufa suka  tasa  mahaifiyarsu gaba  suna mata bayani , ta  dinga saka musu albarka "rahma  Allah yayi muku albarka gabad'ayanku   nasan ko bayan  raina zaki rike kannenki , ina alfahari dake  saboda  kina wanke  min  zuciyata da farinciki   "kina  ma raye  hajja   , idan  bakya  raye duniyar  ai  bazata mana dadi ba,  Allah dai ya ƙara miki lafiya  nan suka shiga  tautaunawa agaban  suhaima.

"  yanzu ya za'a yi a benne  layar nan ? "wannan  ba damuwa bane idan  mun je kai kayan  suhaima ko balla part dinta  nayi   a abenne,  wuyarta dai  mu shiga gidan , "haka ne rahma  sai dai na so  a fasa  d'aura auren  yarinyar  ,na saka rai  suhaima   ita kaɗai  zata zauna a gidanta  tayi mulki kamar yadda kowanne ku  yake a gidansa   .

"Hajja  Ki kwanata da hankalinki duk yadda kike son tayi mulki zatayi ,kun gani nan   bana da ra'ayin korar kishiya  nafi son  ta  zauna taga rayuwa  ,ta rayu ina  bautar daita   har zuwa sanda zaki   mutu ..

"Yayarmu  ya zanyi dana abinci  ?"yanzu ba fa son  zuwa gurina yake ba wallahi  ,tayi maganar kamar zatayi kuka "ke dan Allah kiyiwa mutane shiru da anyi magana ki narke fuskar kamar wata mai takaba , dan durin uwarsa  da kafarsa  zai zo ance miki mu na wasa ne  ,gwada   cewa  yazo kiga  aiki da cikawa ,  rungume  y'an'uwanta tayi  tana  farinciki "na gode na gode yan'uwana Allah ya bar min ku rungumeta sukayi  suna suna shafa bayanta hajja ta sake fadada fuskarta da murmushi tana sake jin tsananin qaunar ƴaƴanta akan yaranta babu abinda baza iya ba ..

Cigaba da  shirye shiryen biki sukayi bayan sun aiwatar da abinda ke ransu   ,sun balla bangaren  ummita sun binne  layar da babalawo  ya basu  a bakin uwar d'akin ummita  sannan suka bawa  kafintar  da suka zo  dashi umarnin ya rufe kofar ....

sauran  kwana uku  a daura  auren ummita  ta ɗan  saki  ranta ta shiga cikin y'an'uwanta hakan kuwa yayiwa Hajiya umma da mama dady   ,tana zaune a dakin mama  ya shigo  d'akin  ya ganta  zaune hannuta rike da  plet  tana shan  farfesun kifi,  ya  tsura mata  ido  tausayin kanshi ne  ya kamashi saboda   ganin gabadaya ta sauya tamkar babu abinda  ke damunta lamaran  gabanta  kawai take , ya ja tsaki yana kiran aikin banza kawai tare da   sunan "mama .....
sai  lokacin tasan ya shigo cikin natsuwa ta d'ago  ta kalleshi da fararen idanunta  ,   kallo ɗaya  tayi masa   haɗe  da  mikewa  tsaye ta soma wata  irin tafiya mai daga hankali da ita kanta bata san ta iya ba    ta  ajiye plet din  hannunta da spoon ,    tayi wata irin   mika  da sallati  ta nufo inda  yake  , take   yaji   wani iri ajikinshi  a sanadiyyar mikar data yi , jijiyarsa ta soma harbawa  ,idanunshi ya tsura mata yana  mamakinta   ta karaso  daf  dashi tana cigaba da mika  da  tsura masa idanunta tana kallon cikin idanunshi ,kallonshi take eye's to eye's babu wata fargaba ko tsoro  , saurin ɗauke  numfashinsa yayi  yaki  ce mata   komai     yana ƙoƙarin   juyawa  zai  fita  daman mama   yake  son gani  tunda  bata nan  bai ga amfanin cigaba da tsayuwa 
yana kallonta tana daga masa hankali a banza  ba ,  har zai fita tayi  wani  tunani   dan haka ta  kira sunansa  cikin sanyayyiyar muryata  "ya Mah'ruf ya  tsaya cak ba tare daya juyo ba,  ta zubawa bayansa   ido  tana kallonsa  zuciyarta na harbawa da sauri    "ma..mama kake nema ?
Tayi maganar cike da in ina ya juyo a fusace  yana tsare gida  "Ban sani ba , da iskanci  sai yanzu zaki min magana  ai kinsan ita na shigo  nema da tsaya kina kina wani shirme .
"Allah ya baka hakuri mai da wukar  ta matso  gabanshi ta tsaya zuciyarta cike da tsoro  a hankali ta kai hannunta fuskarshi ta shiga  goge masa gumin dake tsatsafo masa "wannan gumi menene  ...?
Sannan ta cigaba da magana "amman sai nake ganin kamar na wani abu da .....
"Dakata dan Allah  malama bana son zakewa plz ina ruwanki ko a cikin teku kika  gani ba gumi ba ?
"Wai da  zan fahimtar da kai  ..
Ya sake katse mata hanzarin  zuciyoyinsu na dokawa a lokaci daya, "fahimtar dani me ?
"ki shiga hankalinki sannan ki kama kanki  dan  ban son shishigi da rainin hankali  Yana  gama fadar haka ya juya ya fice , shiru tayi tana kallon kofar daya bi  ,"me ruwanki da shi?
" me ma yasa kikai masa  magana shiru ta cigaba yi tsaye  tana wa kanta Allah ƙara, sai dai a kashi dari na tsoronsa  kashi hamsin da wani abu ya kau kuma tana jin duk runtsi zata tsaya tsayin daka akan rashin jin tsoronsa .

A  kwanakin asirin yan'uwan   suhaima  ya soma  tasiri acikin kwakwalwar sa 
wani kallon gani gani yake kowa  , yana cikin tunanin kai  kanshi gareta  ,kiranta   ya shigo masa   kasa ignoring din Kiran  yayi ya  ɗauka  cikin  rawar jiki  ta lura  duk kwanaki idan ta kirashi   yana ɗauka, dan haka yanzu daya ɗauka ta sakar masa kuka ita lallai tana son ganinsa cikin  rawar  jiki yace  "an gama gani nan zuwa ki bani  wasu yan  mintiuna .

cikin shigar  kananan kaya ya isketa kwance a sitroom tayi lamo tana jiran karasowarsa   ta zuba masa ido tana  cikin kololuwar farinciki   da ganinsa da  sauri ta mike ta shige jikinsa bai wani damu ba ya rungumeta tsam ajikinshi   yana shafa bayanta  , wani kukan munafurcin ta sakar masa ",habibi ina sonka bakina yayi kadan ya misaltan irin soyayyar da nake maka , sai dai  idan na tuna mu biyu zaka aura duk farinciki da nake ciki  sai ya gushe   amman   kai sai naga kamar  farinciki  kake  zaka hadani da wata ...
Ya sake kamkameta ajikinshi "am sorry my suhaima nasan irin zafin da kike ji wallahi nima ina ji zafin abun a zuciyata ina daurewa ne kawai, dan bin umarnin iyaye , ko kadan  aurena daita bazai sa na canza miki ba, babu macen da nake so kamarki babu macen da zata sha gabanki ,kece zabina ita kuma zabin rayhan ce biyayya zanyi kece zabin zuciyar Mah'ruf  batun kamar ina murna wannan zargi kike dazaki shiga zuciyata da zaki tabbatar da gaskiyar lamari , sosai ranta yayi sanyi da jin dadaddan kalaman dake fitowa daga bakinsa.

ta saki murmushi tana sake shigewa jikinsa tare da shimfida masa manya dukiyar fulaninta da suke a narke acikin bra  "am so happy Habibi ka sanyaya min zuciya muje kaci abinci ta janyo hannunshi a koshe yake amman bazai iya cewa  ya  koshi ba, duk da abinda yake son fadi Kenan.

   gaban kular abinci  ta zaunar dashi akan  wani ratsantsen kafet mai shegen kyau ta bude kular  abinci sai kamshi jollof din shinkafa  data sha kayan hadi da kori ya  tashi , ta  zuba masa tana masa fari da idanunta ,ta rufe kular , ta rike spoon a hankali tana fuskantar shi "bude bakinka da kaina zan baka yayi murmushi ta kai spoon bakinsa ya bude tare da furta Bismillah rahmanir rahim .........

Take gabanta ya fadi ,lumshe idanunta tayi saboda jin haushi  abinda yace , hankalinta yayi kololuwar tashi  tasan aikinsu na daf da karyewa , taki bashi tana buɗe idanunta tare da janye spoon din ta rausayar da idanunta cikin nashi tana jan hankalinsa ta sake kai hannunta bakinsa ya rike hannun yana kai abincin bakinsa tare ambaton sunan Allah   batare da sanin ta ba loma uku yayi yace ya koshe bata damu ba tunda ko loma daya yaci bukata zata biya .

kan kujera ta dawo dashi tana haɗe fuskarsu guri ɗaya, shiru sukayi bayan sun zubawa juna ido bakinsa da hancinsa da idanunshi  take kallo cikin tsananin sonshi ,a hankali  ta sake matso da fuskarta daf da nashi har tayi nasarar haɗe bakinsu ta soma tsotsa , a hankali ya dinga yawo da  harshensa cikin bakinta, ta rike fuskarshi sosai da hannuwanta duka tana tsotsan miyon bakinsa yayi mamakin yadda ta kware gurin shan baki gaba-daya ta manne masa ajiki ,ita kuwa a zuciyarta addu'a tayi dan daman   ta san  zai iya fiyye da yadda take hasashoshi gurin  iya sarrafa mace, iya shan baki ma kenan ina ga mai gabadaya suka yi ,
sosai suke tsotsar bakin juna tamkar zasu hadiye bakin  junansu  da kyar ta kwance bakinta saboda ba karamin cafka yayi musu ba numfashi suke fitarwa idanunshi sun yi jawur tamkar wanda aka xubawa garin barkono aciki ,ta shafa fuskarshi lokacin da yake kokarin sake kamo bakinta "no Habibi akwai zafi fa "
Ta fadi hk tana kashe masa idonta daya  murmushin yayi ",zaki san akwai zafi iya wannan kike wa raki gabad'aya ta zube   jikinsa tana rudashi   bashi  ya bar gidan ba sai gurin 12 ya koma gida tamkar  bugage ..


Ranar daurin aure da safe mah'ruf ya shirya cikin sabuwar  farar shadda   da hula abokinsa  jafar da sauran abokansa  duk shiga fararen kaya sukayi na Mah'ruf kawai ya bambamta da nasu sai kamshi yake zubawa ya dinga Allah Allah  su wuce gidansu suhaima amman baba sarki ya nuna auren gida za'a fara daurawa sannan suje ga iyayen suhaima ,
An daura auren ummita lafiya sannan iyayenta suka zarce da biki.. yayinda maza suka wuce  gidansu suhaima  domin daura aurenta   da Mah'ruf , Diner da yayita cika baki baza shi ba sai gashi  shine  kan gaba  wannan ne  ya bawa su aunty  damar mika  ummita gidan mijinta kafin aka wo  suhaima bayan sunyi mata huduba ta gari  ,da haka ne ummita ta kasance uwar gida a gidan mahruf  yayinda suhaima zata kasance amarya.

Daga gurin diner gida aka yo da amarya suhaima  inda aka nufi dakin mahaifiyarta  daita ,ta canza wasu kayan sannan hajiyarsu ta soma yi mata magana "duk  da muna da madafar dafawa amman   ki sake saka wa zuciyarki  natsuwa ,ki zamo mai fuska biyu a tsakani
ta yadda zaki san sirrin danginsa  da nashi , ki dinga shiga ko'ina acikin danginsa har ma daita kanta  yarinyar  ,hajiya rahma  tayi saurin karbe maganar da cewa " ni Kuma zan  dinga zuwa miki da salon sihiri iri iri  da koyar dake makirci wanda zaki dinga kulla mata,  ina tabbatar miki wannan yarinyar bata isa ta tsallake tarkonmu ba kina zaune zai korawa iyayenta  ita, gida  ya zama namu mu kadai, idan kuma bata fita ba zata  zamo tamkar  baiwa ce agaremu ,  acikin y'an'uwanta babu wanda yayi mata hudubar arziki  daga nan aka mikar daita  tsaye  bayan sun yi mata hudubar tsiya suka taho gidan mahruf  tare da yan kawo amarya  ..


gabadaya  dangin ummita  suna  gidan aka kawo suhaima amman babu wanda yayi kokarin fitowa  .
  wannan abu bai yi musu ciwo ba , dan kuwa  a banza suka d'auke shi ,su dake da ragamar gidan gabadaya , batare da wata damuwa ba hajiya rahma ta riko hannun suhaima zuwa ga   family  Mah'ruf  , a  parlour'n  suka iskesu  gabadaya da alamun tunda suka zo amarya  bata  shiga dakinta  ba  ,ummita na zaune a tsakiyar wasu mata biyu  meenal da maryam suna gefe  guda tsaye suna kallon suhaima dake lullu'be cikin mayafi , an yi musu faɗan  su zauna lafiya sosai , inda daga karshe  aunty  ta   nunawa suhaima ummita ce uwar gida  duk da karancin shekarunta,  y'an'uwan suhaima  suka mikar daita  tsaye suna cika suna batsewa suka koma   zuwa bangarenta  .
suna shiga hajiya rahma tace "kai da alamun  mutanen  nan fa yan zafi kai ne, kalli yadda wancan  kanwar uban nasa  ke wani tada jibiyon wuya  tana maimaita ummita ce uwar gidan ," mu ina ruwanmu da wata uwar gida ko amarya   bayan mu  baiwa aka kawo mana , suka kwashe da dariya "kai yayarmu Allah ya barmana ke " ai ko amarya aka kawo mana  gida sai mun bankadota waje  bare wata uwar gida  .....
"Ta dauki mayafinta ta rataya a kafada  da jakarta "kunga  tafiya wanda ya  tashi yazo mu wuce ,zulaihat ta mike tsaye "muje   yayarmu  ki saukie ni  wannan mayataccen ma  ya soma dumuna da kira  Hajiya rahma  tayi kusa da suhaima "karki
yarda ya  kwana agurinta , ki san duk makirci da zakiyi   ya kwana agurinki shi  asiri sai da makirci da jan hankali yake kara tasiri  tana gama fadar haka ta juya suhaima ta riko hannuta "yayarmu sai naga kamar bata shiga d'akin ba "eh nima haka na lura amman ai zata shiga  ne dan ubanta tunda baa parlour'n zata kwana ba ,karki damu tsalakar kawai ake bukata kuma ina da tabbacin zata yi  .......
"Ke dai ki janyo hankalinsa ya kwana agurinki Allah ya tashemu lafiya mun wuce tana gama fadar haka suka fice  ..

TWO FRIENDS ( BSBS)


💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~TRUE LIFE STORY~

FREE NOVEL


AL'QALUMAN



*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*


~DEDICATED TO~
*AYSHA MUSA TILLI*

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim


PAGE 38

.... a cikin mota ma babu abinda hajiya rahma da zulaihat suke facce maganar akan makirci da tasirin sihiri har sanda hajiya rahma ta sauke zulaihat a kofar gidanta ta murza kan sitiyarin motarta ......

Kowa ya watse a bangaren ummita daga aunty sai meenal Maryam da aslamiyya da aunty jidda wacce ita daman a d'ayan ɓangaren baya take " sosai aunty ta sake yiwa ummita faɗa akan rayuwar aure "ki yawaita addua azkar din safe da yamma kada ki kuskura ya wuceki duk da nasan kina yi amman ki sake dagewa kiyi hakuri irin na mahaifiyarki matukar kika yi hakuri irin hakurin maryam ina tabbatar miki babu wata mace da zata sha gabanki

2 Comments On WANNAN CE QADDARARMU
avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment