Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta soni, rashin soyayarta yafi komai damuna ,ina ji ajikina fiyye da tunaninka , nasan za dai ta aureni kawai ba dan tana sona b " ka daina biye mata , ka daina biyewa shirmen rashin sonka ,kai me ma zai sa ka damu zuciyarka dan bata sonka ?
"dole na damu mahruf soyayyarta a jinina take sannan akwai ciwo kana son mutun bai sonka ni nasan gangar jikinta zan aura yayi maganar yana runtse idanunshi .....
Mah'ruf ya ja tsaki wannan akwai shegiyar yarinyar wallahi ,duk tabi ta dagulawa mutane lissafi yadda ta bugar maka hankalin da zuciya nima fa ..
Yayi shiru ya kasa k'arasa maganarsa sakamakon sallamar da ummita tayi haɗe da turo kofa ta shigowa d'akin hannunta rike da basket .
ganin rayhan jingine yana magana da mah'ruf yasa farinciki lullubeta ta k'arasa shigowa ta ajiye basket din hannunta tana sakin murmushin dake bayana tsantsar farincikinta .
"lallai ya rayhan ka samu lafiya kaine har da dogon hira ?
"Alhamdullahi ummita na sannu" ya karfin jikin ?
Murumushi yayi mata yana lumshe mata ido "alhamdullahi ,ta samu guri ta zauna a gefen gado batare da ta gaishe da mah'ruf ba ,shiru dukkaninsu sukayi suna fitar da numfashinsa sama sama ......
Can rayhan ya katse shiru ya soma jan ummita da hira tana amsa masa cike da kulawa yayinda mah'ruf ke satar kallonsu ta kasan idanunshi zuciyarsa na tsalle kamar zata fasa qirjinsa .
wani irin yanayi ya tsinci kanshi ciki na zallar farinciki , hakan nan ya dinga jin dadi acikin zuciyarsa , Allah ne kaɗai yasan adadin farincikin da yake ji a yanzu daya gansu tare rayhan yana faricikin ..

Amman fa a can kasan zuciyarsa yana ganin rashin dacewarsu
yayi kokarin cire abinda yake gani akansu tun baya amman hakan ya gagara , ba rayhan ba a halin yanzu duk wanda zai kasance tare daita baya ganin dacewar su amman zai so ganinta rayhan tare daita akan kowa ....
Cike da kulawa ummita ta mike ta buɗe basket din data zo dashi ta zubo masa abinci jollof din shinkafa ce wacce ta wadatu da kayan hadi naman kaza datayi laushi sosai , sannan ta haɗa masa ruwan zafi
ta soma mika masa cup din ruwa zafi cikin sanyin murya yace "na gode my princess Ina alfahari dake ...
"Nima haka ,duban inda Mah'ruf yake tayi haɗe da tsuke ƙaramin bakinta magana take son yi amman bata son ya disgata , cikin wani yanayi tayi karfin halin aro jarumta ta sanyawa jikinta ta sake sanyaya muryata tace "ya mah'ruf....
Wani zirrrrrrrr yaji a gabadaya ilahirin jikinsa mai kama da shoking
Ta tsura masa idanunta tana kallonsa kana tace " a zubo maka abinci ?
Kanshi kawai ya girgiza batare daya yace komai ba .
"my princess rabu dashi haɗa masa coffee nasan zai sha "okay Yaya "idan kin haɗa masa ga zuma can ki d'auko kisa masa ,plet din abincin hannunta ta ajiye ta haɗa masa coffee ta tsiyaya masa zuma ta janyo karamar kujera gabansa ta ajiye masa a gabansa yadda zai iya d'auka, ita kuma ta dawo ta ɗauki plet din abinci ta janyo farar kujera gaban rayhan suna fuskantar juna "kawo cup din kaci abinci ya mika mata ita kuma ta dibo abinci a spoon ta Kai bakinsa ...

Wannan abun ya haddasawa mah'ruf jin rad'ad'i acikin zuciyarta , wani abu mai daci da ciwo ya dinga kawo wa zuciyarsa farmaki amman ya dinga ƙoƙarin dannewa saboda baya son abinda zai sa ya fallasa zuciyarsa dan har lokacin bai san a wani bagire ummita take acikin zuciyarsa ba ,shi dai yasan ko za'a d'aura masa bindiga yasan ba sonta yake ba yafi yarda da abinda yake ji akanta had'uwar da gangan jikinsu yayi a tun ranar da yan daba suka kawo mata ziyara ..
yayita satar kallon yadda suke cikin farinciki yana jin ina ma shine ..
ummita kuwa jinta take duk atakure agun saboda kasancewar Mah'ruf da idanunshi dake yawo a sansar jikinta suna nan zaune har likita ya shigo ya soma duba rayhan bata iya kallon inda mah'ruf yake ba ,ta kasan idanunta taga mikewarsa batare daya sha coffeen ba ...
Barinsa dakin yasa ta sauke naunauyen ajiyar zuciya tana canza mazauni .

Duk yadda ciwon rayhan yayi tsanani likitoci sun kwantar dashi tare da kulawar da yake samu agurin ummita, dan musamma take zuwa tare da had'ad'd'en girkinta ,ko ta samu hajiya saudat da inna bata sauransu abinda ya kawota shi take yi, su kuma gudun abinda zai sake faruwa da rayhan din yasa basa cewa komai har ta wuce ..
Satinsa uku aka bashi sallama .....

Bai sanar da ummita ba suka sanyo kai shi da Mah'ruf tun daga farkon layin shigowa unguwarsu zuciyar rayhan ke bugawa sakamakon dalliyar motar daya hango a kofar gidansu , mutane biyu ya hango tsaye ,tun basu karaso ba yaga kamar subai'arsa ce tsaye da wani daya kasa tuna inda yasanshi shiru yayi yana takure zuciyarsa har sanda suka karaso inda suke ya dai tabbatar ita dince tsaye ,kai tsaye hon Mah'ruf yayi aka bude masa get din gidan ya shiga tun kafin a maida Kofar a rufe ya rayhan ya fito ,take idanun ummita ya sauka akanshi dan a tunaninta Mah'ruf ne .
wani irin bugawa kirjinta yayi lokacin da idanunta ya sauka akansu , take gabanta ya shiga dokawa da sauri sauri ..
Kallo ɗaya rayhan yayi mata ya dauke kanshi cike da faduwar gaba ,shi kuwa Ma'hruf kin kallonta yayi amman misalta yadda ya ji ma ba magana dan wani duhu yaji ya gilma acikin zuciyarsa da idanunshi amman haka ya danne .

murmushi me kayatarwa mutumin dake tsaye kusa daita yayi "ya naga yanayinki duk ya sauya ko akwai damuwa ne ?
Ta daga masa kai alamun "eh .
"Me ye damuwar ya faɗa yana gyara tsayuwarsa idanunsa na kanta "a zahirin gaskiya Malam hafiz akwai damuwar da ita nake kokarin faɗa maka tun jiya daka zo "ina jinki meye shi ...?
"Ki faɗa min yayi maganar yana sake tsareta da idanunshi ..
Cike da in Ina tace
"ita..soyayya ana yinta ne a bisa amincewar mutun biyu sai gashi a bangarena an samu sabanin haka har yanzu dai kamar da ne malam,babu soyayya a rayuwar subai'a ,bugu da ƙari ba zaka sameni a matsayin mata ba kasancewar mahaifina yayi min miji da dan uwana rayhan, ina maka fatan alheri arayuwarka, murumushi yayi yana jin tamkar kalaman soyayya take jero masa "yanzu me kike nufi kuma me kike son hafiz almustapha yayi mutumin da ya ɗauki dogon lokaci yana d'awainiyya da qaunarki ?
"Bisa umarninki na killace kaina naki kawo miki ziyara sai yanzu da nake da tabbanci kin mallaki hankalinki zaki fahimceni fiyye da lokutan baya, what did you want me to do now ?

"Hakuri zaka samu wata cikin nasarar Allah "samun nasara akanki nake ji ,kullun addu'a nake Allah ya bani nasara akanki kuma ina ji ajikina inshallahu zanyi nasara ya k'arasa maganar yana zuba mata idanunshi yana murmushi ...

Shi kuwa rayhan a zahiri Mah'ruf ke hango "bacin ranshi "ka fa ragewa zuciyarka damuwa idan ka bari tunaninta ya illataka bata da matsala hasalima ba hasara zatayi ba wani zata samu ta aura ya k'arasa maganar yana kwantar da murya " ka kwantar da hankalinka plz ummita ta kace nasan duk runtsi Abba bazai bawa wani ita ba ....
Tunda ya soma magana rayhan ke rike da kanshi ya kasa cewa komai "kayi hakuri tana sonka tunda tana gudu shigarka damuwa ko yanzu da ka lura zaka ga damuwa da tashin hankali a fuskarta , dan Allah kayi murna kayi farinciki ango ummita nifa yanzu har nafi d'aukin aurenka daita akan nawa da suhaima ...
Ya dawo gabansa yana d'ago fusksrsa zuciyarsa na harbawa dan shi kadai yasan abinda yake ji "ango ummita ka saki ranka plz ko a fuska karka nuna mata kaji haushi ganinta da wancan dolon ,ka karfafa zuciyarka kune masoyan da kuka fi kowani masoya dacewa , kun dace sosai da junanku ..
murmushi ya rayhan ya sakar masa sannan ya rungume shi yana mai sanyawa zuciyarsa natsuwa , yadda Mah'ruf ke tsaya akan lamarinsa yana saka shi jin farinciki, ya sani ko a can baya yana samun sausauci a gurin dan uwan nasa sai dai adalilin ummita su yi faɗa wanda fadan baya zuwa ko'ina "ko kai fa , da ka wani haɗe rai dan kawai kaganta da wancan soko da shaye shaye ne aikinsa ,masu hankali ma ba'a basu aurenta ba sai dan giya ,dan Allah ka ragewa zuciyarka damuwa ka sausautawa zuciyarka dan har yanzu zuciyarka na bugawa da saurin da ba'a so ... "inshaallahu zanyi yadda kace ina alfahari da kai "nima suka jera suka yi cikin gida kai tsaye bangaren mahruf suka shiga ...

Tun bayan tafiyar hafiz almustapha ta dawo part dinsu ta zauna jigun a parlour'n meenal na bata baki mama ta sauko ta dubesu "har bakon naki ya wuce ta kad'awa mama kai alamun eh".
fatan kin fahimtar dashi gaskiya ko?
"Na faɗa masa mama Amman shima cewa yayi bai san da zance ba kamar muhd Sa'id tayi mgnr hawaye na ƙoƙarin zubo mata "tam sarkin kuka meye kuma abun kuka daga tambaya ?
Ta zauna kusa daita suka sakata a tsakiya
" kiyi hakuri mu tsananta addu'a akan lamari ki dage akan istaharan dana koya miki ,sahihiyar addu'a ce wanda annabin rahma (s.a .w) ya koyar da sahabbansa ,kuma ya umarcesu su yawaita yinta a kowani lokaci amman fa tana da sharadi ,sharadi ta shine mika zabi ga Allah , ki dai kara yin hakuri Allah ya zaba miki abinda yafi alkhairi ,auren rayhan ko waninsa ,maza tashi ki shirya ga abincin rayhan can kuje ke da Amina ku kai masa .."ai sun dawo yanzu kuma ya ga hafiz ......

Mama tayi shiru tana kallonta "ki daina yawon damuwa ta sake gyaran zamanta "ya'ya na wane a d'akinsu rayhan?
"Bakwai " ta bawa mama amsa ta sauke numfashi
"ke fa ku na wane ?
Tayi shiru ta kasa cewa komai "da Allah kaɗai na dogara ummita ,bance Karki damu da rayhan ba amma atlest ki duba lamarina ta k'arasa maganar tana janyota jikinta ta kwantar a saman cinyarta ta zame bakin mayafin dake kanta ta shiga shafa sumar kanta cike da kulawa da kalaman rarrashi ..

Shi kuwa Ma'hruf tun bayan da yayi Sallah isha'i ya shiga dakin mama ya kwanta jikinsa a sanyaye ya rasa gane kanshi a dalilin zuciyarsa dake cikin wani yanayi ,cikin haka kiran suhaima ya shigo wayarsa ya 'daga jin muryarta cikin tashin hankali yasa shi dan mikewa ya jingina bayansa da jikin gado shiru yayi yana sauraronta har sanda ta dasa aya ,ya sauke naunauyen ajiyar zuciya "Allah ya saukewa yanzu yaushe za'a fita daita ?
"Ina saka rai zuwa jibi amman dady yace zai nemi su Abba " okay babu damuwa Allah ya kara mata lafiya zan shigo gobe inshaallahu sannan ya katse kiran yayi shiru yana nan zaune mama da ummita suka shigo ,ummita sanye da hijabi hannunta rike da carbi tana ja .

Shiru mama tayi tana kallon yadda yayi zurfi cikin tunani ,
ba tayi masa magana ba ta wuce inda yalwataccen abun sallarta yake shimfide ta tada sallah, ita kuma ummita ta zauna akan kujerar sofa ta cigaba da jan carbinta tana kallonsa ,bayan kamar minti biyar ta idar ta daga duka hannunta sama tana addu'a ta shafa sannan ta juyo garesa idanunta akanshi ta kira sunanshi "baba ..
Yayi firgigib yana fidda numfashi mai zafi tare da kallonta "lafiyarka na ganka haka ?
Tayi masa tambayar hankalinta a matukar tashe tana son mah'ruf bata son ganinshi cikin damuwa ,shima yana jin dadin yadda take masa cike da karaya ya mike ya sauko ya durkusa agabana bisa gwiwowinsa.

tun da taga yayi haka tasan ba lafiya ba cike da Muryar karaya ya soma kokarin magana, ta dakatar dashi da hannunta "ummita tashi ki koma dakinki ki bamu guri kamar bazata tashi ba sai kuma ta mike tsam ta fice tana yauki "uhmmmm ina jinka ?
Suhaima ce yanzu ta kirani wai za'a fita da mahaifiyarsu kasar india akan ciwonta kuma tare zasu tafi daita ,wai mahaifinta zai nemi su Abba akan a daga biki, Allah mama idan aka taga bikin nan zan fasa auren nan gabadaya ... Cikin rudewa mama tace "asha kai kuwa ciwon mahaifiya fa , hakuri dai zakayi ,kaga yanzu da ka hakura da sakina ba sai ayi daita ba tunda ka matsu da auren"
Zama yayi sosai a gaban mama "nifa mama ba matsuwa nayi ba ..
Ta hararesa , kamata yayi ka duba lamarin sakina amman ka dinga cusguna mata har sai da yarinyar nan ta hakuri da kai .
ya riko hannun mama ya kai daidai saitin zuciyarsa dake bugawa da matsanancin karfin gaske "ki fahimci halin da zuciyata take ciki mama ,a halin yanzu zuciyata bata son sakina haka bata son suhaima "sai wa kenan kake so?
"Ban sani ba mama I don't know but zan dai iya auren suhaima akan sakina ,dan girman Allah mama kiyi min addu'a ina cikin wani hali , zuciyata na yawon bugawa da ciwon da ban san dalilin haka ba ,ya k'arasa maganar hawayen karaya na zubo masa yayi saurin goge hawayensa lokacin da suka hada ido da mama.
ta tausaya masa matuka ,ya mike da sauri zuciyarsa na dokawa "Allah ya bamu alkhairi mama"
tace "dawo ka zauna yayi kamar yadda tace ya sake zubewa a gabanta "da alamun zuciyarka tana son canza shika zuwa wani muhalli wacece wannan yarinyar da ta shigo rayuwarmu?
"Babu mama nima bansan meye acikin zuciyata da tunanina ba "tayi shiru can tace "ka tsananta addu'a sannan kayi istahara tashi kaje Allah ya bamu alkhairi "ameeen haka ya baro d'akin mama jikinsa a sanyaye tamkar wanda bai da laka ,zuciyarsa kuma tamkar ana rurata da wani yanayi da bai san mazaunin da zai bashi ba ..
********
Daga Mah'ruf har ummita addu'a suka tsananta dashi tare da yin istahara da mika alamarinsu ga Allah Shi kuwa hafiz almustapha sati guda yayi yana zariya a unguwar ko a bisa tsautsayi bai yi kuskuren ganin ummita ba sai wasu daga cikin ahlin gidan , ai kuwa hankalinsa ya tashi matuka ya nufi gidansu ya zube a gaban mahaifiyarsa dake hakince ya fashe mata da kuka yana rokonta "dan girman Allah ,dan matsayin annabi da Alqur'ani ki taimaka ummah ki shige min gaba in har na auri yarinya zaki fahimceni "wallahi idan baka tashi ka fita daga gidan nan ba sai na tsine maka "ni ina nan naga maka farauta mata shine zaka zo min da wani batun banza ko dadynka yaji wannan maganar sai ya tsine maka karma kasoma dosansa da wannan banzar maganar yasan halin mahaifiyarsa bazata canza magana ba tunda ta furta.

tashi yayi ya nufi banfarensa ya bude fridge dinsa ya zaro kwalba giya mai sanyi ya kafa a bakinsa bai ajiye ba sai daya shanye duka ya sake dauko wani sannan ya zube kan kujera ,bayan kamar minti goma yanayinsa ya soma sauyawa ya mike yana layi ya d'aga hannunsa sama kamar yadda masha kanyi "ba ..bazan barta ba wallahi tunda ina sonta kuma sai ..sai na aureta zan gina mata gidan giya muyi rayuwarmu a can nida ita ,ina ina sonki ummita saboda rage tunaninki yasa nake shan wannan abar sambatu iri iri ya dinga yi daga karshe ya zube a tsakiyar parlour'nsa sai bacci .

*****

Zaune ummita take a bakin gado sanye cikin kananan kaya farar riga mai budadden gaba da wando bom short iya cinyarta tayi kyau sosai tana gyara wasu kyakkyawan baby guda biyu a gabanta bayan ta saka musu Pampers ta shafa musu farar hoda ,akwatin kayansu dake gefen gado , ta buɗe ta saman akwatin ta ciro farar best mai kyau da wondonta ,ta shirysu fes ta yunkura zata mike daya daga cikin babyn ya riko jelar gashinta data tufke da ribon yaja da karfi yana murmushi ta koma ta zauna da sauri tare da yin wata siririyar ƙara mara sauti ta buge masa hannu ai take yaron ya kwa'be baki ya fara kuka shima dayan take ya bare baki suka sakata tsakiya suna kuka , wani kyakkyawan mutun ne ya shigo d'akin da sauri ,fuskarshi cike da annuri yana sanye cikin wasu hadaddun kanana Kaya irin na jikinta kanshi sanye da facing cap da rufe idanunshi sosai amman hakan bai hanata hango murmushinsa ba "me baby's di nah suka miki kika saka su kuka?
Sai data harari wanda yaja mata gashi ssnnan tace wannan ɗan naka mai kama da kai ne yayi min mugunta irin naka , gashina fa yaja..
kafin ta rufe baki shima mutumin yaja "kai kai kai ai kuwa kaja musu dan akansu zan rama ta juyo da niyyar ta rama akan baby , ya janyota jikinshi ya manna mata kiss har guda uku ta ɗauke kanta da sauri "haba subai'a ramawa fa kika zo yi kika samu abun alkhairi kamata yayi nima ki rama min ya sake manneta da fadaddan kirjinshi tana murmushi batare da taga fuskarshi ba tureshi tayi a lokacin da suka hango babay's dinsu suna niyyyar saukowa daga kan gadon kafin su karasa garesu sai kararsu suka ji sun fado ta kurma wata razananniyar kara da ihu wanda shine yayi nasarar tashinta daga dogon mafarkinta , a filli ta cigaba da kuka da ihun da ya farkar da meenal dake kwance kusa daita ,a gigice ta kunna wutan d'akin tayi saurin kamota tana girgizata a gigice jin batayi magana ba ta d'ago kanta a hankali ummita ta buɗe idanunta hawaye suka gangaro mata ta kasa furta komai sakamakon kukan daya ci karfinta, sai da sukayi mai isarsu sannan sukayi shiru cike da sanyi jiki ummita take labartawa meenal mafarkinta "meenal ina ji ajikina ya rayhan ba mijina bane wannan shine karo na biyar da nake mafarki akan wannan mutumin .....



TWO FRIENDS (BSBS)


💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~TRUE LIFE STORY~

FREE NOVEL


AL'QALUMAN



*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*


~DEDICATED TO~
*ESMAEL SANI*



WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

PAGE 31

.......kuka ummita take sosai irin kukan da ba'a so , dan kuka ne wanda yake fitowa tun daga kasan zuciyar har sai da mama ta shigo dakin bata sani ba tana matse gam ajikin meenal , mama ta dafe kirji cikin tashin hankali "ummita me ya faru da wannan tsakar dare haka ?
kuka suka cigaba batare da sun amsa ba ta k'araso gurinsu da sauri "ku faɗa min mana cikin bacci naji sautin ihun ummita meke faruwa daita ?
tayi maganar a gigice tana zama kusa dasu "ku gaya min me ya faru dan Allah mama ta riko a hankali hannun ummita , meenal ta takaita kukanta ta soma yiwa mama bayanin abinda ya faru , mama ta sauke naunauyen ajiyar zuciya ," shine abun kuka saboda shirme yayi muku yawa ?
" abinda zaku tashi kuje kuyi alwala ku dukufa gurin fadawa Allah bukatunku ,oya maza ku tashi kuje kuyi alwala Allah ya tabbatar mana da alkhairi zabin Allah muke nema ba son zuciyarmu "a hankali meenal ta sakar mata jiki tana riko tafin hannuta har zuwa bayi a lokaci kukan ummita ya fara raguwa , alwala suka d'auro kamar yadda mama ta umarcesu suka fito, mama bata bar d'akin ba sai data ga sun kabarta sallah sannan ta nufi d'akinta itama alwala tayi ta soma nafilfili .

A hankali mah'ruf yake sharar baccinsa hankali kwance sai dai zuciyarsa cike take fal da tunani iri iri .....
A cikin baccinsa yake kallon kanshi zaune akan kujera gabansa table ne dake ɗauke da system da cup din coffee yana aiki yana kora ruwan coffee, sanyayyen kamshin turarenta ne ya soma kawo masa ziyara har inda yake ,bai juyo ba haka bai daina tura sakonnin da yake ba har sanda ta karaso gareshi, ta tsaya ta bayanshi, ta sunkuyo da fuskarta daidai saitin wuyanshi ,kamshin gashi kanshi daya sha gyara ya doki hancinta , gashin nasa banda sheki babu abinda yake haka mayataccen kamshi turarensa komai ya tsaya masa a lokacin da take tsaye akanshi , bakinta ta kai cikin kunneshi ta zira masa harshenta cikin kunneshi haɗe da hura masa iskan bakinta tare da tura hannunta cikin laulausan suma kanshi mai kamshi gaske muryarta cikin rad'a tace "i love you mar'shub tana mai sake cusa hannunta cikin sumar kanshi tana wasa da gashinsa .......
cikin wani irin yanayi mai wuyar misaltuwa ya juyo daita gabanshi suna fuskantar juna ,ya tsura mata manya idanunshi masu matukar kyau da haske yana kallonta wasu had'ad'd'un kayan bacci ne fari sol mai budadden gaba sanye ajikinta tana yauki tamkar tarwad'a a gabansa , gabadaya ilahirin tsigar jikinsa sai da suka mike tsaye .

wani irin sanyi ya dinga ji yana ziyarci zuciyarsa da ma gangar jikinshi ...
a hankali Idanunshi ya sauka akan kyawawan dukiyar fulaninta masu

2 Comments On WANNAN CE QADDARARMU
avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment