Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kwayar idanunta kamar zatayi kuka "magani fa ?
"Na sha ta faɗa atakaice yayi shiru yana kallonta zuciyarsa na rawa akanta yana jin kamar ya wuce office daita domin ya samu damar kula daita a halin yanzu yana soma tausayawa kanshi dan zuciyarsa a shirye take da tona asirin dake cikinta saboda yaki bata hadin kai ko'ina ajikinsa yayi sanyi , mikewa yayi idanunshi na kanta "shikenan ni zan wuce office babu abinda kike bukata ?
"Babu ta faɗa a can kasan makoshi ,"okay dan Allah ki kular min da kanki ya soma takawa a hankali har ya kusan fita tace "Allah ya tsare .....

Ya juyo da wani sauri yana kallonta , kanta na masa tana kallon yatsun kafafunta sam ba zaka taba cewa maganar daga bakinta ta fito ba ya girgiza kanshi kawai ya fice yana furta "miskilili kawai ..


*******

Mama da tace zatayi sati biyu sai gata tayi wata daya cikin na biyu saboda yanayin yadda ta tarar da jikin mahaifinta, zuwa Abba uku dubo jikinsa a daidai wannan lokacin aka saka ranar auren meenal da abdulshakur , wasa wasa sai da mama ta lashe wata biyu cif da sati biyu wanda yayi da cikin ummita nada wata biyu sannan ta dawo , ranar data duro ranar mah'ruf ya taso suhaima gaba suka zo yiwa mata sannu da zuwa sosai taji dadi ganinsu ta tarbeta cikin mutuntawa bata nuna mata tana da wata halaka da ummita ba ,Mah'ruf kuwa baza ido yake yaga ta inda zai ga fitowar ummita amman yayi shiru ya kasa tambayar mama ,cikin haka wayar mama tayi kara ta dauka da sallama daga yadda take amsa wayar ya fahimci ita da aunty ne ta karashe maganar da cewa "Ummita sun fita ita da meenal karbo result din jam din data yi tana gama wayar ta mike ta shiga kitchen, yayi shiru kawai tare da runtse idanunshi yana jin haushi yadda bata mutunta aurenshi dake kanta ...

yana nan zaune har suhaima tashiga bangaren hajiya inna da Hajiya umma har ma da bangaren hajiya saudat ta gaishesu ta dawo basu dawo ta zauna kusa dashi tana zuba masa surutun yadda hajiya inna take matukar sonta "gaskiya habibi kayi dacen dangi ,ni kuma nayi dacen family's miji kowa na sona ko da yake nasan albarkaci soyayyarka ne tayi maganar tana shige masa "meye haka ko kin manta a ina muke ne ? Ki koma can plz banason damuwa "haba habibi ai duk abun bai kai haka ba meye ma aciki dan mama ta ganmu nasan ita kake ji ?
banza yayi mata zuciyarsa na turnukikin bakinciki ganin haka taja bakinta tayi shiru .

kusan awonsa biyu a gidan sannan ya soma jiyo sautin muryarta suna sallama da meenal ta shigo hannuta rike da farin envelope bakinta ɗauke da sallama "assalamu ......
Kasa karasawa tayi sakamakon ganinsa zaune yana kada kaga matarsa na zaune a gefensa, kallon kallo suka shiga yiwa juna daga suhaima har ummita kowane zuciyarsa na bugawa da karfi ,ta sauke numfashi da kyar sannan ta ajiye takarda akan hannu kujera "yaya ina yini ?
Yayi mata banza tamkar bai ji ba sannan yaki bude idanunshi ya dubeta , hakan kuwa yayiwa suhaima dadi har ta saki murmushin farinciki ta kai hannunta saman chest d'insa "habibi ana magana fa yana jinta ya shareta .

Ummita taji zafi da ciwon abinda yayi mata har tayi data sani ,sai dai ta danne 'bancin ranta mama ta fito daga kitchen "yauwa ummita kin dawo ?
"Na dawo mama sannu da gida "sannu da zuwa shiga kitchen ki k'arasa girkin can zanje sama nayi sallah tun kafin ummita ta amsa suhaima tayi tsigil ta mike "bari na karasa mama "a yi haka suhaima kiyi zamanki ki huta ta k'arasa a duk yau batayi aikin komai ba "ai babu komai ki bari nayi aikin albarka , ta mike ta shige kitchen wani irin bakinciki ne ya mamaye zuciyarta ummita ta tsani yadda mama take sakewa da suhaima " hankalin na kan ummita taga duk ta canza fuska "ki cire hajibin ki huta ko tace "to "
Mama tabi bayan suhaima har ranta taji dadin yadda take nuna mata ,ta sake fad'ad'a fuskarta "na gode kwarai Allah yayi albarka "ameen ta amsa a zahiri, a bani kuwa cewa tayi ", shegiyar mata kawai uwar iyayi komai albarka da sannu zanyi maganinki duk kin bi kin kanainaye min miji da saka albarka karya baya ganin kowa da gashi sai ke .....
mama ta juya ta fita ta haura sama a daidai lokacin da ummita
ta soma kokarin cire hijab dinta bata an kara ba taji ta fado jikin mutun " ta d'ago a gigice tana kallonsa idanunshi a runtse har lokacin fuskar nan tashi a hade tamkar hadari ,take jikinta ya soma rawa a hankali muryarsa ta soma fita ta yadda suhaima dake kitchen baza taji ba "daga ina kike ?
"Uhnmmm ammm muje bangaren hajiya inna ne "ni zaki rainawa hankali ?
" wai ina tarbiyar da mama ta baki ne?
"ina saninki da Alqur'ani yake ?
"Okay da abinda zaki sakawa kanki kenan ?
"Just tell me the truth daga ina kike ya kai hannunsa ya rike mata naman gefen wuyanta , ta saki ƙara mara sauti tare da shigewa jikinsa suhaima dake kitchen ta bar abinda take ta dawo kusa da bakin kofa ta la'be .

"uhmmmm ina sauraronki? gabad'aya tsoronsa ya kamata bata son ganin fushinsa yanzu yana matukar d'aga mata hankali "kina jin mutane kinyi shiru "munje amso result ne tayi maganar muryarta na rawa "me za'a yi dashi ? Jin abinda ya faɗa ta mike daga jikinshi a hassale zuciyarya a dake tace " me ake yi dashi baya ga karatu,karatu zanyi dashi yasa kafafunsa ya hardota sai gashi ta sake dawowa kirjinshi "na sallameki ne da zaki tashi kina wani kad'awa mutane jiki ?
"tsaya tukun na ma da izinin uban wa za'a soma karatun ?
"Ni dai dan Allah karka rusa min tsarina ka barni nayi karatu na gaji da zama haka ...

"Baki gaji ba yarinya tunda takamarki girman kai da miskilanci "ki cire batun karatu aranki dan Ma'hruf bashi da ra'ayin barin mace yin karatu suhaima ta sake kasa kunne dan taji abinda zasu ce sai dai kash duk nacinta bata iya jiyo komai .

idanunta suka cicciko da hawaye "ni dan Allah ..... "karki wahalar da kanki sannan karki sake fita ko nan da can ba da izinina ba ya karasa fadi haka yana fadi get up my friend ta mike tana harararsa "Allah an takura min gaskiya , nifa na gaji idan aure aure idan rashinsa rashinsa ta yaya za'a dinga tauye min hakina ?

ya yunkura zai cafkota ta kwasa aguje tayi hanyar sama dafe goshinsa yayi da duka hannuwansa yana sauke numfashi da karfi yana kallon bayanta da idanunsa dake a rine da zallar damuwa ,bai ce komai ba ya nufi hanyar step nan hankalin suhaima yayi kololuwar tashi , ta fito da sauri ta tsaya a parloun'n tana kallon step har ya bacewa ganinta kamar tabi bayansu amman ta kasa ..

Yana isa bakin kofar dakin bai tsaya wata wata ba ya banko cikin dakin a tsaye ya ganta tana haki tana ganinsa ta nufi bayi da sauri tana kurma ihu " wayyohlly Allah ... taku biyu yayi ya cafkota ta kamkameshi a jikinta , take wani abu mai kama shocking ya ziyarci jikinsu yayinda kowani part na jikinsu ya sake budewa da karbar juna acikin zukatansu ya daga hannu zai zabga mata mari ta sake rungumeshi "dan girman Allah karka min komai , wallahi bani da lafiya "baki da lafiya amman kin iya rashin kunya ko "to kayi hakuri Allah na daina amman ka barni nayi karatuna kaga ya rayhan ya barni kai ma ...
"Shiiiiiiiiiii bazan iya ba... "saboda ka fara sona kuma kana kishin na shiga jikin maza nayi karatu ko ..?
yaji maganar kamar saukar aradu wani irin sanyi ya dinga ajikinsa, sosai ta narke masa ajiki tana fidda numfashi haɗe da sauke ajiyar zuciya , shi kuwa mah'ruf da kyar ya samu ya saisaita kanshi da rikon da yayi mata ya tsura mata ido hannuwanta duka tasa ta tallabo fuskarshi dashi tana kallon cikin kwayar idanunshi "kana mamaki jin abinda nace ne ?
Yayi shiru ya cigaba da kallonta yana mamakinta "a yadda kake ikirarin baka son ummita zuwa yanzu ya canci ka sauwake mata aurenka dake kanta bawai ka zauna kana gindaya mata dokoki ba har ga Allah ina bukatar rabuwa da kai saboda bana sonka ina son nayi rayuwata kamar sauran mutane nayi mua'amula da kowa a karshe na samu wanda zai soni nima na soshi muyi .. .....
bai san sanda ya shako wuyanta cikin matsanamcin tashin hankali ba ya hanata karasa maganarta "kina hauka wallahi baki da hankali da har kika yi tunanin ni mah'ruf ina sonki ,ki sani ina rike da igiyoyin aurenki ne darajar mama ba wai dan so ba ,amman saboda tsabar rashin hankali irin naki kike tunanin ina sonki ya karasa maganar yana furzar da iska tare da sake shake mata wuya gabadaya ta narke ajikinshi tana kokarin yin kasa gashi numfashi na kokarin d'aukewa kamota yayi ya manneta da jikinshi a gigice yana shafa fuskarta gabadaya ya dawo ya rikice ganin numfashinta ya tsaya "oh my goodness ya rude ya gigice da sauri ya kwantar daita saman gadon ya shiga bayi ai tana jin motsin shigarsa ta sake lefewa ya fito hannunsa da robar ruwa yana nad'e hannun rigarshi ya haura saman gadon ya matsota ya daura kanta a saman cinyarsa ya dinga diban ruwan yana shafa mata a fuska ganin taki farfadowa yasa daura bakinsa kan nata ya shiga busa mata iskar bakinsa da numfashinsa wani irin zirrrrrrrr ta dinga ji ajikinta kamar ana jonata fatar jikinta da wutar lantarki...

ya runtse idanunshi gam "ba wai soyayya kawai yake saka mutane killace matansu ba fat lion ..Ina dai kishin aurena dake kanki shi yasa bazan lamuncewa zuwa karatunki ba wai so bane , gabadaya ya rasa me zai mata dan dawo da numfashinta sai surutai yake yana jaddada baya sonta kishin aurensa dake kanta yake...
Duk yadda ya dinga busa mata iskan bakinsa taki farkawa sai ma sake lafewa tayi tana jin wani iri ajikinta sosai ya shige jikinta yana shaƙar kamshin turarenta gabad'aya ta soma dauke wuta ahankali ya kafa bakinsa cikin nata ya soma tsotsan lip's dinta yana ƙoƙarin bude bakinta ,ya zira harshensa ya soma tsotsan bakinta tamkar wani tsohon maye a kokarinsa na dawo da numfashinta ganin abun nashi na neman wuce ka'ida ta bude idanunta aiko sukayi four eye's dashi a gigice yake kallon cikin idanunta ga bakinsu manne cikin juna ....

Naunauyen ajiyar zuciya ta sauke ta kai hannuta kirjinshi alamar ya d'agata babu mutsu ya mike jikinsa a sanyaye yana dubanta ta zuro kafafunta ta sauko ta tsaya gabansa dukiyar fulaninta na kadawa tare da kai yatsan hannunta daidai tsaitin zuciyarsa "kace baka sona ?
"Wannan taimakon shima duk cikin kiyayya ne ko ok naka na fahimta salon naka kiyayar kenan ?

"Gsky haka ysyi , a kiyayya za'a iya yin komai sai dai ka yarda ko karka yarda wannan zuciyar ta faɗa tarkon son subai'a so kuwa mai girma ......
yayi saurin runtse idanunshi haɗe da dunkule hannush zai kai mata naushi ya tuna tana dauke da cikinsa take ya naushi iska "me yasa ka fasa ka naushina ?
"Ka naushe mana ta matso jikinshi sosai tana fidda numfashi kasan Allah idan ka sake kuskuren kai hannuka jikina ka tabbatar da ka duke wannan dan iskan auren naka dake kaina tana gama fadar haka ta koma jikin kofa ta bude "kazo ka fitar min daga d'aki bana son ganinka ta nuna masa hanyar fita da hannunta tana hura hanci ......

Ya soma takowa yana magana a sanyaye
"Yanzu har kiyayyar da kike min ta Kai ki Kira aurena dake kanki da kalmar iskanci?
"Iskanci kamar wasu masu zaman daduro
fat lion ya k'arasa maganar yana damkar kafad'arta "why why did you said that ?
"Bana sonki amman me zan miki ki soni fat ....?

"Yadda baka sona haka babu abinda zaka min na soka final decision baka sona bana sonka ka sauwake min dan ban ga amfani zama da igiyar aurenka akaina ba ta karasa maganar hawaye na zubo mata "me yasa zuciyarki tafi bukatar ki rabu dani fat lion ?
"ban sani ba kai ma ka tambayi zuciyarka meye amfanin aurenka akaina ?
Ya sake matsota sosai "okay yanzu na fahimceki kina son kasance tare dani a gidana ko ba haka ? "wannan tunaninka kenan tunanina ka sakeni na cigaba da karatuna daga karshe na auri mai sona kuma wanda nake so.

"to baza'a sakeki ba kiyi duk abinda zakiyi ta tsura masa idanu tana tsayar da hawayenta "kinga yadda rayhan ya mutu ya barki da takaba to kisawa ranki haka zaki tabbata da aurena akanki amman bazan soki ba kuma bazan sakeki ba sannan babu batun karatu yana gama fadar haka ya juya ya fita ...

Ta dade tsaye agurin tana sauraron zuciyarta wallahi ko rantsuwa tayi bazayi kaffara ba yana sonta tunda yake tsotsar bakinta a duk taimakon da zai mata wannan shine karo na sau babu adadi da yake shan bakinta da sunan taimako..
Yana fita ta zube akan gado ta kwanta ruf da ciki ta runtse idanunta tana kuka ..

A gaugauce ya fito yana huci hankalinsa a matukar tashe ya iske mama da suhaima suna hira suna murmushi wanda ita suhaima na dole ne dan hankalinta gbdy naga Mah'ruf daya bi byn ummita , kwarai taso bishi tasan me tsayar dashi agurita na tsawon lokaci .

Da kallo suka bishi dan sosai bacin ranshi ya fito fili "ki tashi mu wuce
"ai bata ci abinci ba tukun ,ka bari taci abinci idan kuma kana da uzuri ne ka barta ka dawo anjima ka dauketa ,
bai sake cewa komai ba ya fita a zuciye , mama ta maida hankalinta ga suhaima "maza ki soma cin abinci , jiki a sanyaye tace"to mama ,amman acikin zuciyarta tsine mata ta dinga yi tana kallo ana ƙoƙarin janye mata hankalin miji amman take wani yi mata mgn abinci ,abincin banza abincin iska taji kamar ta daura hannuwanta duka bisa kanta ta rusa ihu.

Yana fita unguwarsu jafar ya nufa zuciyarsa na matukar zafi tun akan hanya ya tambaye shi ko yana gida "ina nan Mah'ruf lafiya naji muryarka haka ?
"kai dai bari nazo "
A parloun'nsa suka haɗu ya zauna yana huci ganin haka yasa jafar bude fridge ya dauko masa goran ruwa ya bashi "sha kaji sanyi tukunna bai yi musu ba ya amsa ya kafa abakinsa bai ajiye ba sai daya shanye tas yayi wurgi da roba yana sauke ajiyar zuciya "jafar kai aminina ne da muka taso tare tsawon shekaru kasani fiyye da komai jafar sai kuma yayi shiru yana dubansa zuciyarsa na bugawa.

"me ke faruwa da kai ne Mah'ruf duk kayi wani sukuku ka faɗa min nasan akwai abinda ke damunka tunda naganka
jafar ya faɗa yana gyara zamansa kallonsa mah'ruf yayi "kai dai bari abun ne ya dameni dan Allah yaya ake jin feeling din soyayya bayan soyayya da mukayi suhaima har ta kai mu ga yin aure ?
"Abubuwa dayawa Mah'ruf nan ya shiga lissafa masa daki daki kamar yadda meenal ta karantawa ummita yana dasa aya yace "no it can be impossible ....
"as how ?
Jafar ya tambayeshi "ba zai ta'ba yiwu na sota ba."Ita wa kenan bayan matanka ?
"wai yau ni fatlion zata kalla tace ina sonta har da ikirarin tunda bana sonta na saketa yayi maganar yana furzar da iska mai zafi .....

"To ka saketa mana tunda kasan baka sonta ta samu wani dan abinda kake yi sam bai dace ba, ka ajiye yarinyar mutane a gida tsawon wata biyar me kake especting ta faɗa maka bayan wannan ?
"Gsky koni na goyi bayanta wallahi shiru sukayi dukansu na wani lokaci kafin daga baya Mah'ruf yace ",bazan iya sakinta ba ko dan mama da kuma rashin so..... "dakata dan Allah malam
Kalli cikin kwayar idanunka mah'ruf ,kalli yadda tsantsar soyayyarta ke d'awainiyya da kai ,kalli yadda hankalinka ya tashi saboda ta bukaci ku rabu amman duk wannan ace ba so bane daraja ce....
"Abokina ka natsu sosai ka shiga hankalinka ka rike matarka hannu biyu many people's out there suna can cikin tashin hankali rashinta da sukayi wallahi kana rabuwa daita koni sai na shigo cikin masu neman aurenta "kallonsa mah'ruf yayi da sauri yana watsa masa harara "kana hauka ne kake faɗa min haka?
"kai ne dai mahaukaci wallahil azim ka so matarka idan ma baka sonta bare kana sonta " ka daina cewa ina sonta plz...

"kana sonta ka daina yaudarar kanka Mah'ruf zuciyarka na son subai'a ba tun yau na lura da hkn ba ...
"Let me ask you something Idan ka ganta kana jin bugawar zuciya da faduwar gaba ?
Yayi shiru yana tunani can ya d'aga masa kai , zuciyata na bugawa sosai in har na tunata haka ma ganinta wanda ban san dalili ba nan ya shiga faɗa masa yadda yake ji akanta .

"Ka daina cewa bakasan dalili ba ,kaje kawai dan komai zan faɗa maka ba zaka yarda ba amman ranar nadama na nan zuwa duk kuma abinda ya faru karka nemeni dan bani da abinda zan maka a lokacin yana gama fadar haka ya mike shima ya mike suka fita tare suna sake tautaunawa ....


Tana kwance taji an turo kofar d'akinta ta juyo a hankali suhaima ta gani ta mike zaune akan gado ita kuma ta shigo ta kulle kofar tare da murd'e key "kallon juna suke "shegiya makira wato kina ƙoƙarin dauke min hankalin miji kou?
"na rantse da girman Allah baza ki taba samun wannan damar ba ,bari na faɗa miki zuciyar Mah'ruf ni kadaice a cikinta , baki da muhalli ba kuma zaki yi shi ba har duniya ta nade a haka zaki kare rayuwarki a wannan dakin ....

"Ke ko Mah'ruf na sonki sai na raba wannan soyayyar bare bai yi ,a tarihi kin taɓa ganin amaryar da aka wulakanta kamarki ?
Ummita ta tsura mata ido batare da tace komai ba.
"Babu amarya da ake fara wulakantawa a daren farkonta saboda rashin mahimmancinta sai ke tayi taku daya biyu ta isa gabanta ta tsaya tana harararta "bari ki kiji nice Ummul khabaisin wannan al'amari muddin ina raye subai'a kike ko fatlion zaki dangwama cikin bakinciki domin bazaki samu dama irin damar dana samu ba an san
kwantai zakiyi shiyasa aka kakabawa ... mijina wahala ..

Murmushin ummita tayi tace "da kyau dangin matsafa da yan tsubu ni subai'a bana bukatar irin wannan damar da kike daita "ni da mahaifiyata bamu iya bin bokaye da Ya tsubbu ba bare har musa a wulakanta wani...
suhaima tayi sororo tana kallonta da mamaki "kina mamakin yadda nasanki nasan halinki ko ?
"To ki daina mamaki suhaima saboda kusan kowa a cikin garin nan yasanku da wannan halin zama ku iya yin fiyye da abinda kika faɗa, amman kisani bazai taba yin tasiri akaina ba , batun dauke hankalin miji ko me ko me wannan baya gabana saboda yadda kike ikirarin mijinki bai sona haka nima bana sonshi, idan ma shi ya faɗa miki ki koma ki fada masa subai'a bata son shi , sannan ki tambaye shi mijin naki maza nawa sukayi haukan son subai'a akan idanunshi ?
Ki tambaye mijikin maza nawa ya sha gani suna shawagi a kofar gidan nan zai faɗa miki ni yanzu da zakiyi asirin da zai sakeni wallahi wallahi duk duniya bani da kamarki useless mad woman kawai mai dakikiyar kwakwaluwa .

"kuma kisani idan ina da muradin mijinki ya soni cikin second biyu zai soni ,kuma ya haukace akaina har sai duniya tasani mukulla idan kin ce karya daga yau mu soma .......

a matukar tsorace suhaima take kallonta "lallai duk yadda ta dauketa ta zarta haka ..
"Get out from my side mai kwakwaluwar kifi kawai wani irin tsalle tayi zata damki wuyanta tasa duka hannuwanta ta tureta tana dubanta "kalleni da kyau kinga nayi miki kama da irin waɗan kishiyoyin da'ake duka ?

"Dan ubanki ni kike fadawa haka ?
an faɗa miki dan kutumar ubanki da wacan shegiyar uwartaki mahaukaciya .....
"Ni kika zaga ?
",An zage danginku gbdy kiyi uwar uban da zakiyi ke nifa nafiki tashanci ajiyewa nayi saboda babu riba, oya fitar min a daki idan ba haka ba zaki ga haukan dayaci uwar na uwar taki ,mahaukaciya dangi mahaukata shegu masu

2 Comments On WANNAN CE QADDARARMU
avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment