Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

huta sai da safe kaji , ta juya zata fita , yayi saurin riko yatsun hannunta cikin nashi "ina zuwa kuma zaki kike min sai da safe ?
"D'akina ina son na kwanta, ya girgiza mata kai " zo nan mu kwanta tare zai fi kou ?
"na dade ina d'auki wannan rana subai'a ,na dade ina son ganinmu cikin inuwa ɗaya, bazan iya bacci alhalin muna cikin gida ɗaya ba dan Allah ki kasance tare dani ina bukatar jin dumin jikinki .

babu musu tabi umarninsa tana sakar masa murmushinta da yafi kauna, ya sauya wutar d'aki daga mai haske zuwa mai duhu sannan ya kwanta ya kwantar daita a gabansa bayan ya zare zumbulelen hijab din dake sanye a jikinta ,
yayi mamakin jin kayan dake jikinta har lokacin , wato bata canza wasu kayan ba , ya rabbi Allah ya furta a kasan zuciyarsa yana lumshe tsunammun idanunshi tare da kai wa gefen wuyanta kiss ..

take jikinta ya ɗauki rawa sai dai bata ji feeling's din komai ajikinta ba sa'bani yanayin da take ji a duk lokacin da jikinta ya haɗu dana mah'ruf.
tayi shiru tana jin duk abinda yake mata batare da ta hanashi ba,
Ya lalu'bo hannunta cikin nashi yana murzawa a hankali a hankali .
"my princess kiyi min alkwarin kasancewa dani har abada ba zaki barni ba zaki kasance tare dani muddin rai ya k'arasa maganar yana shafo qirjinta haɗe da aikawa saman qirjinta wani irin gigitaccen kiss ..
tun tana jurewa abinda yake mata har tazo ta kasa ,saboda hannunsa dake yawo ajikinta "do you love me zaki karasa rayuwarki da Aminu ?
"i do !
I do !!! ta dinga furtawa tana mayar masa da abinda yake mata duk saboda ta kwantar masa da hankali , ta dinga daurewa tana biye masa dan ta faranta rai .
"baki ce komai ba my princess sai i do , ko bazaki daukar min alkwarin rayuwa tare dani ba ?
"Zan yi ya rayhan zan dangwama tare da kai zan yi rayuwa da kai mun rigada mun zama abu guda kazama ni na zama kai i will spend the rest of my life with you
ta karasa maganar tana damke hannunsa cikin nata .
Ya sauke numfashi tare da lullu'besu bayan ya zare jallabiyar jikinsa itama ya rabata da komai na jikinta suna fuskantar juna duk tabi ta rud'e masa abunka da sabon shiga , tun tana mayar masa har tazo ta kasa , tsam ya matseta ajikinsa yana fidda numfashi sama sama ya cigaba da abinda yake mata ,a hankali ya ɗan sausauta mata yana jin wani irin feeling's dinta da bukatar kasancewa daita , dan zuciyarsa na bashi hadin kai da kawarin gimwiwa akanta ....
Bakinsa ya kai cikin kunnenta ganin yadda ta rude ta gigice "ko baki son nayi wani abu dake ne ?
Ta kasa magana illa jikinta dake rawa "nayi ?
yayi maganar a daidai lokacin da jijiyarsa ke sake harbawa ajikinta ,"tayi saurin girgiza masa kai ,numfashi ya sauke ya sake lullu'besu yana manna mata kisss tare romancing dinta "no zan barki , har ki samu natsuwar zuciya bazan miki komai a yanzu ba wasa nake miki kinji my princess ya k'arasa maganar yana haɗe bakinsu ....
asuba ta gari rayhan da ummita ...

Washe gari gidan ya cika makil da mutane dangin mama da suka zo biki da wasu domin ganin gida , iyayen ummita sunyi rawar gani sosai sun kashe kudi tamkar basu san ciwonsa ba, duk abinda akayiwa ummita shi akayiwa jiddah kuma duk na kasar waje akayi order su .
duk wannan makudan kudin da'aka kashe sai da abba ya ware lokaci yazo tare da mah'ruf da Usman daya zo biki , ya sake tambayarta " me take so ya sai mata na musamman , Usman ma tasata yayi gaba fuskarshi ɗauke da murmushi yayinda mah'ruf ya haɗe rai tamkar wanda aka aikowa da sakon mutuwa ..

ta d'ago fararen idanunta ta tsura masa tana jin gabanta na faduwa shima bangaren mah'ruf hakan yake ji a zuciyarsa, duk sanda zai ganta sai ya tsinci kansa da jin mummunar faduwar gaba shiyasa bai so zuwa ba amman babu yadda zai yi da abba bai isa abba yace ga abinda yake so shi kuma yace a'a ba a kallon da yayi mata ya hango cicciowan
hawaye acikin idanunta ya dauke kanshi zuciyarsa na tsalle
Saurin maida hawayenta tayi ta tsinci kanta da yin murmushi " abbana ka rigada ka gama min komai a rayuwa a yanzu kam bana bukatar komai daga gareka sai addu'arka "Allah yayi wa rayuwarki albarka subai'a ya albarkaceki da samun zuri'a masu albarka, yadda kika min biyayya Kema Allah ya baki ya'ya masu albarka da zasuyi miki biyayya "ameen abbana na gode "

Sannan ta maida kanta ga ya usman tace "ya Usman dina kai dai bazan dauke maka ba dan zanso na dinga ganin wani abu daya danganceka dan haka ka shiga kasuwa duk abinda kasan zan so ka siyo min ai nasan kasan ra'ayina ..?
Wani irin dadi yaji a lokacin da take magana ta kalli inda mah'ruf yake tayi murmushi "kai fa ya mah'ruf baka ce zaka bani komai ba ,me zaka bani ?
Ya waigo qirjinsa na dokawa ya tsura mata ido yana kallonta Abba da usman da rayhan suka tsira musu ido suna murmushi "gaskiya kam ya kamata ya bayar datashi gudumuwar inji cewar Abba , mah'ruf ya lumshe idanunshi yana jin wani irin a sansar jikinsa "me kai shi zuwa "kayi shiru ya mah'ruf ko bazaka bani komai ba ?ta sake tambayarsa ya bude idanunshi da kyar ya zuba mata gabadaya ya rasa abinda zai ce gashi magana yake son yi amman ya kasa so yake ya tambayeta abinda take so daga gareshi ,a hankali suka yunkura gaba-daya saboda jin yaki magana kuma sun san ko za'a a kwana a irin wannan shirun nasa bazai yi magana ....
Haka suka bar gidan jikinsa duk a sanyaye. washegari Usman yace su shirya suje gidan ya yayi masa rakiya kememe mah'ruf yaki ..
frem ya usman ya tsiyo musu manya ita da jiddah mai dauke da sunan Allah da ayatul kursiyyu ya aiko musu dashi shima yaki zuwa ...

*******
Kwanasu uku da tarewa suna manne da juna bayan sun gama shan soyayyarsu , kawai taki jikinsa ya dauki zafi da rawa ya dinga rawar sanyi , ta gigice ta rungumeshi ajikinta "kira wo min Ma'hruf jikinta na rawa ta kwantar da kanshi akan pillow ta duro daga saman gadon ta gyara rigar baccnta ta soma kiran layin mah'ruf a lokacin yana zaune akan daddumar sallah ne yana kaiwa Allah bukatunsu yana ganin kiran qirjinshi ya buga ya soma ƙoƙarin ɗauka "hello rayhan?
"bashi bane nice ya mah'ruf kazo yanzu dan Allah ya rayhan bashi da lafiya karasa mikewa yayi yana doso kofar fita yana kiran layin doctor husain byn sun yi magana ya katse kiran doctor ,Abba da sadam malik da injiniya ya kira a tare motoci su suka karaso gidan
Yayinda shi Malik tuni yana tare da rayhan kasancewar gidansu daya sai dai kowa da bangarensa hatta get dinsu daban ..
Kai tsaye d'akinsa suka nufa dukkaninsu suka hawo kan gadon daya gama cukurkudewa suna kiran sunansa amman da kyar yake iya amsawa ...
Bayan doctor ya dubashi ya bawa su Abba shawarar a fitar dashi abroad din kamar yadda yace ,amman take rayhan yaki " ku barni a kasata karku kaini ko'ina ,ko kun fita dani mutuwa zanyi ku barni cikin gatana , ranar akanshi suka kwana har washegari gari cikin ikon Allah ya ɗan samu sauki ..

mahaifiyarshi ta kasa tafiya tace zata zauna tare dashi ,kowa ma ya kasa barinsa sai dai duk bayan dikika sai su tambayarshi akan abinda yake so da yadda yake jin sai yayi murmushi yace "babu komai shi yaji sauki , daya ga ummita kuwa zai hau kawar da kanshi gefe yana janyo numfashi da kyar ,hankalin ummita yayi matukar tashi to meye kuma matsalar ?

har suka share sati daya madadin jikin yayi sauki kamar yadda yake faɗa ,sai gaba ciwon yake saboda yawon girman ciwon ajikinsa wasa wasa har magana ta ɗauke masa ranar kuwa yi yayi tamkar ya sheka lahira dan ko mgn yaki yi ,halin da ummita da mah'ruf suka shigo bazai musaltu ba, gaba-daya sun dawo abun tausayi sun zama tamkar wasu zararru ,gabadaya kowa ya tare a gurinsa baya son barinsa shi kaɗai .


hajiya saudat ma ba'a magana kana ganinta zaka gane ramar datayi a fili ,Alhaji Aminu ne yazo da kanshi ya takura masa "meye ke damunka takwarana ?
"Me yasa zaka ce kar a fita da kai ?
"ciwo ai ba mutuwa bane takwarana ka bar iyayenka su yi wani abu akan ciwonka ,
,kalli kaga yadda hankalin iyayenka ya tashi ,kalli mahaifiyarka da mahaifinka kalli yadda suka dawo akanka ya nuna injiniya ,ya nuna Abba ya nuna Hajiya umma da mama da Mah'ruf kalli kannenka da yayyenka kalli ni kaina uwa uba matarka subai'a yadda ta dawo ka duba irin halin damuwar da muke ciki duk akan dalilin damuwarka sai lokaci yayi yunkuri yin magana a hankali mah'ruf dake kusa dashi ne ya matso da kunnenshi sosai ta yadda zai ji abinda zai faɗa "duk ina sonku kuma ina alfahari da kasancewarku yan'uwana .....
sai dai kuyi hakuri mutuwa zanyi na barku "mahruf kamin alfarma ɗaya ko bayan raina kada ka bari ummita ta auri wani ka aureta ina son ganinku cikin inuwa daya ......
kanshi kawai yake iya girgiza masa ba dan zai yi abinda yake faɗa ba "ba zaka mutu ba rayhan tare zaku rayu daita kai ne kafi dacewa daita bani ba , plz ka daina ambato mana mutuwar nan bamason jinta .....

"ummana ya furta sunan mahaifiyarsa da kyar ,da sauri mah'ruf ya kirata "umma kizo yana kiranki ta matso jikinta na rawa hawaye Shabe Shabe a fuskarta fadar halin da mah'ruf ya shiga bazai fadi ba duk yadda ya zaci abu ya wuce nan ..

"Gani babana me kake so ? "Dady ...
Shima ya k'araso da sauri tare da Abba "kuyi hakuri ina ji ajikina mutuwa zanyi na barku amman ko bayan raina ku bawa Mah'ruf auren subai'a ina da tabbacin zai bata duk wata kulawa , ummana subai'a tamkar diyar cikinki ce zan so ki daina tsanarta ,saboda baki da dalilin tsanar da kike mata ,ki ɗauketa tamkar diyarki da kika haifa , Abba ka nemammami yafiyar mahaifiyata kasancewar na auri subai'a tana fushi dani ....
"na yafe maka babana baka min komai ba ,duk abinda kamin ma na yafe maka duniya da lahira amman ka daina ambata wa kanka mutuwa bana son ka mutu babana .
"na gode mama ku min alfarma zanyi magana da subai'a numfashinsa ya soma sama sama wani irin qara hajiya saudat ta fasa ummita bata san sanda ta shige cikin mutane dake kusa dashi ba , tsayawa tayi cak saboda ganin halin dayake ciki ,ya daga hannunsa ya mika mata alamun tazo gareshi , da sauri ta karaso ta rungume shi yayinda kanta ke kan kirjinsa tana kuka "karka mutu ka barni dan Allah , su mama da umma kuwa tuni kuka yaci karfinsu , kowa kuka yake babu mai bawa wani hakuri ....
Ummita ta zama tamkar wata birkitacciya a hankali rayhan ke mata magana cikin kunneta yana shafa kanta "matata kanwata hakika bani da abinda zan faɗa miki sai godiya, kin aureni batare da kina tattare da dingon kaunata acikin zuciyarki ba, ta shiga girgiza masa kai "ka daina gode min mijina ina sonka kuma zan rayu da kai muddin rai bazan saba alkwarin da nayi maka ba .
"na gode my princess ko yanzu na mutu zanyi farinciki zan mutu na barki da aurena akanki, zaki min takaba a matsayinki na matata ta sunnah , alhamdullahi duk duniya babu wanda zai min takaba sai ke, bani da kamarki , "na gode na gode "ka daina gode min muna tare , dole na gode miki ,da baki aureni ba haka zan tafi babu aure ...
na gode naso na nuna miki soyayya fiyye da yadda nake ji araina sai gashi Allah ya d'auro mana wata jaraba wa wanda dole mu d'auketa da mahimmanci ....
"Kece mace ta farko da nake kauna nasha fama da ciwon sonki zuciyata tayi ciwo akanki subai'a ina sonki ina neman alfarmar ko bayan raina ki auri Mah'ruf, ki bashi farinciki tamkar yadda zaki bani ,sannan ki yafe min matata, umma ki yafe min Abba ka yafe min, da kyar kowa yake buɗe bakinsa gurin cewa na yafe maka rayhan hannunsa ta rike gam cikin nashi tana
Gunjin kuka "na yafe maka amman dan darajar Allah karka mutu ka barmu wallahi bazan iya zama a duniya babu kai ba, karka mutu mijina ta fashe da kuka daya sake sa sauran mutane kuka .
"karkiyi sabo subai'a ina sonki , ki sa aranki har yanzu da nake numfashi ke nake so sonki karuwa yake a zuciyata sai kiyi mana addu'a Allah ya sadamu da alkhairi a can..
tun yana magana kasa kasa har ya kasa , yayinda dayan hannunsa ke cigaba da shafa kanta idanunshi na kan mahaifiyarsa dake sonshi tamkar tsoka daya a miya saboda sunan mahaifinta dake gareshi , kanneshi kuka , kowa kuka yake kamar ransa zai fita .
"hakika da gata na hana mutuwa da so da kaunar uwa da uba da mata da yaya da kanne da yan'uwa da rayhan bai mutu ba , a hankali bakinsa ke motsi yana maimaita sallatin da Abba ke yi yana maimatawa har yayi shiru take komai nashi yayi sanyi lokacin ne Hajiya saudat ta sake kwalla kara , lokacin ne ummita ta d'ago kanta dake kwance a saman kirjinshi ta tsura masa ido taga idanunshi a rufe sannan baya motsi bare numfashin cikin hanzari ta mike "ya rayhan dina dan Allah ka tashi karka min haka dan Allah wallahi ina sonka bani da wanda nake so sai kai ina kaunarka fiyye da rayuwata abinda ya dinga faruwa kafin aurenmu ba kiyayya bace *WANNAN CE QADDARARMU*
daman bazan soka alokacin ba sai bayan ka kasance mijin agareni ,Abba dady kuce ya tashi wallahi ina sonshi bazan iya auren kowa ba sai shi bazan iya rayuwa da wani ba sai shi ka tashi mijina ina sonka ku faɗa masa cewar ina son shi, ina da tabbacin zai farfaɗo dukkaninsu haka suka dawo kamar birkitattu tana kuka tana shafa kanshi da fuskarshi "yayana mijina bani da kamarka karka tafi ka barni ka soni tun ban san kaina ba ...
"Kace nayi maka alkwarin bazan Barka ba , kai me yasa zaka barni yanzu ?
Ina rokonka da Allah ka tashi gani a gabanka bazan barka ba zan rayu da kai muddin rai
Da kyar mama da umma suka janyeta tana wani irin kuka sukayi waje daita har hajiya saudat .......

A hankali Abba ya dubesa ya tabbatar ya rasu dan haka ya dauki zanin ummita dake ajiye akan durowarsa tare da hijabin sallarta, ya tsura masa ido kafin ya rufe shi ,fuskarshi sharrr tamkar mai murmushi rufeshi Abba yayi a hankali ya maida dubansa ga injiniya da wasu daga cikin yan'uwa yace Allah yayi maka rahma Aminu ,Allah yasa aljanna ce makomarka duk dauriya irinta injiniya sai daya zubda kwalla yana furta kalmar inna lillahi wa Inna lillahi rajiun kowa kalmar ya shiga maimatawa a bayyana ..
take damuwa tayiwa Mah'ruf mummunar kamun da bai san ranar fitarshi ba , wani irin zazzaɓi ne ya rufeshi jikinshi na wani irin rawa ,hankalin kowa ya tashi injiniya kuwa sai furta na yafe maka Aminu yake," kai yaro ne mai biyayya akoda yaushe kana kokarin yi min biyyaya shi kuwa Ma'hruf kasa kukan ma yayi haka yan'uwa suka shiga yiwa rayhan addu'oi ...

Hajiya saudat kuwa sai ihu take tana kukan mutuwar rayhan, kusan zarewa tayi dan shakure wuyan sadam tayi lokacin daya fito yana furta kalmar Inna lillahi "shikenan ya rayhan ka tafi ka barmu daman ciwon nan na tafiya ne ?
Sosai ran injiniya ya 'bace ya dinga mata wani irin kallo mai nuni da gargadi , kowa kuka yake amman irin wanda Muslimci ya yarda dashi, amman banda hajiya saudat dake zunduma ihu tana kiran sun an kashe mata da ......

Ummita na tabbatar da rayhan ya rasu ta sume aka shiga watsa mata ruwa da kyar ta farfaɗo lokacin tuni an shirya rayhan, gabadaya tayi wani iri ta fita haiyacinta fuskarta ta kode saboda kuka, wani irin zafi take ji acikin zuciyarta ,tana zaune aka kirata tayi masa addu'a tayi dauriya sosai gurin yi masa addu'a domin batayi kuka ba, hajiya saudat kam ba'a samu damar kiranta ba saboda haukan da take ,wasu daga cikin yan'uwa na bata hakuri, ummita na baro dakin, shakikansa suka fito da gawarsa waje , nan mutane suka kama aka nufi gidansa na gaskiya ...

Hankali kowa yaki kwanciya , zuciyar ummita data mah'ruf sun kasa sabawa da rashin rayhan satinsu daya tare da hajiya saudat zama yaki dadi tsakanin hajiya saudat da ummita ,dan kullun zagita take da kiran ta kashe mata da, ita zata yi rayuwar duniya ,hajiya ummah ta dinga mata wani irin kallo ,ta tuna ranar da tayiwa mama gori akan haihuwa ɗaya da Allah ya bata ,sai gashi ita mai dan shekara talatin Allah yayi ikonsa akanta, daman haka al'amarin Allah yake shi Allah ba'a masa shishigi , ba shiri aka dawo da ummita gida domin tayi takabarta acan ..
Itama hajiya saudat din kin zama tayi ta dawo gida anan aka cigaba da amsar gaisuwa ....

Mah'ruf yaji mutuwar rayhan sosai dan har kwanta yayi asibiti, babu abinda ke damunsa kamar muradin rayhan da yake bar musu a matsayin wasiha "anya kuwa zai iya ?
"Zai iya auren ummita ?
Shiru yayi a d'akinshi shi kadai ya killace kanshi yana son samun natsuwar tare da tunanin abinda ya kamata yayi, sosai kwalkwaluwarsa tashiga cajin neman mafuta a hankali yake furzar da iskar bakinsa "i don't know what to do ina ji ajikina bazan iya bin umarnin rayhan ba "what wrong with you?
"You are trying to betray what rayhan request from you , you really has to do it muddin kana son ruhinsa ya samu salama "to bama haka ba ai kana jin wani abu akanta ?
" Yes "kenan kai kama kana sonta ?
"No no nothing like that ..
ya mike tsaye jikinshi na zafi yana jin wani irin tsanyi har cikin hanjinshi a hankali ya shiga zariya a dakin hannuwansa duka goye a bayansa haka nan ya ke jin tausayin ummita yana kuma jin babu dadi idan yaki bin umarnin rayhan .. ajiyar zuciya ya sauke" mah'ruf ko kayi kokarin gujewa ummita iyayenku da agabansu komai ya faru basu yarda ba , ya dade yana saka da warwara neman mafuta ya aureta ne ko kuma ya gujewa aurenta ?

******

BAYAN WATA

Bangaren hajiya saudat gani take da zarar ummita ta gama takaba ta kwana arba'in babu wani abu da yayi saura tuminin takabarta kawai za'a bata shikenan ,
sai da aka zaunar daita akayi mata bayani akan yadda Muslim yazo dashi ,"idan mutun ya auri mace sai ya rasu kafin su tare wannan matar zataci gado sannan kuma zatayi masa takaba haɗe da idda shine ya zama wata hudu da kwana goma wannan shine abinda dalilai na Shari'a suke nuni zuwa ga haka .
yazo acikin hadisi ibn yasar Allah ya kara yarda agareshi daga Annabi Sallallahu alaihi Wasallama irin wannan hukunci ,sannan kuma Abdullahi dan Mas'ud Allah ya kara yarda agareshi kafin yasan manzon Allah ya taba yin irin wannan hukunci ,da aka tambayarshi sai ya kalli yanayi sai ya bada wannan fatawar daga baya sai ya gano Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yayi hukunci da wannan hukunci sai yayi faricikin saboda haka lallai idan mace ta tsinci kanta a cikin wannan yanayin lallai zatayi takaba haɗe da idda sannan kuma zataci gado ,tunda dady ya soma yi mata bayani take kuka, magangun rayhan na sake zuwa mata daki daki "mutuwa izina ce kuma aya ga dan adam mai tunani ,baki taɓa tunanin rayhan dinki zai mutu ya barki ba, shin me yasa mutuwarsa bazata zame miki aya ba ?
"Yau ina inna da take d'aure Miki gindin yin komai ita kanta mutuwar ta shigeta tunda akayi mutuwar nan kinji bakinta ?
"Ki daina biyewa inna ko yanzu ya'yanta suka mutu rayuwa nawa tayi mata saura ?
"Ki cire komai aranki ki rungumi kaddarar mutuwar d'anki kiyi masa addu'a ki kuma godewa Allah da yayi aure kafin mutuwarsa dan yanzu zaki iya saka rai da samu gudar jininsa a duniya

2 Comments On WANNAN CE QADDARARMU
avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment