Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

akanta shi kanshi ta taɓa burgeshi alokacin walimarta ...

hafiz ya iso ga kanin mahaifinsa zuciyarsa cike da fargaba da dokin jin labari ,saboda daren jiya sam ya kasa runtsawa , duk wunin ranar zuciyarsa cike yake da fargaba da tashin hankali iri iri ..
Lokacin da sakon ke isa ga kunnuwansa kadan ya rage zuciyarrsa bata buga ba , haukace musu yayi tuburan yana zuba sambatu iri iri dole tasa mahaifinsa yasa aka ritireshi aka turasa a wani daki a kulleshi yana ihun kiran sunan ummita ..
******
Lokacin daurin na karatowa tunanin Mahruf da ummita har ma da uban gayya rayhan na tsanantawa , kowa ne shirinsa yake cike da faduwar gaba da alhini ummita ta shiga damuwa sosai tun tana dauriya har kuka ya kufce mata ganin yadda ake hidimar biki cikin haka rayhan ya shigo d'akin batare da saninta ba , ya isketa tana sambatu "bana sonka ya rayhan amman zan rayu da kai muddin rai zan hana zuciyata faricikin na baka ....
Juya yayi da sauri zuciyarsa na matsananci bugawa ya manne da jikin bango kofar d'akinta,"ya Allah subai'a bata sona kawai biyayya zatayiwa aurena hawaye ne ya ciko a idanunshi ya shiga jan kafafunsa da kyar dafe da saitin zuciyarsa yana ƙoƙarin barin gurin sai ga Mah'ruf ya k'araso garesa da sauri ya rikosa cike da tashin hankali yace "menene kuma ?
"Babu komai taimaka ka kai ni d'aki har suka shigo bangarensa da kyar yake fidda numfashi "kabi a hankali plz kaga gobe ne fa d'aurin aurenka da princess dinka sauniyyar matan duniya ....
rayhan yayi karfin halin rungume shi yana murmushin karfin hali "ina jin kamar zan mutu Mah'ruf dan Allah ko bayan bana raye ka maye ...
"Stop it plz daga magana zaka fara maganar da zai daga min hankali me ya kawo maganar mutuwa yanzu ?
" ka sani ma ko nine zan mutu na Barka bana son kana min irin haka suka sake rungume junansu sosai "ina jin zafi ina jin tsoro d'an'uwana ina tausayawa kaina subai'a bata sona bata son muhd sa'id bata son hafiz bata son kowa sai wa take so ?
"Kullun na kalli cikin idanunta ina ganin wasu abubuwa ...
Mah'ruf ya sausauta rungumar da yayi masa "ya kamata ka daina wannan damuwar da wannan tunani saboda fat lion na sonka Kai ko bata sonka dole ta soka ta zauna da kai .....
Sannu a hankali ya dinga kwantar masa da hankali yana sake rungumeshi ajikinsa yana shafa bayansa "ka kwantar da hankalinka kai da fat lion mutu ka raba ko ka binneta ko tayi maka takaba kuma ina da tabbacin zata soka qiyayyar mace bata zuwa ko'ina ,namiji ne idan bai son mace shine damuwar amman mace na wani dan lokaci ne, barin ma ka bata baby rayhan da wuri na kuwa san shap shuter zakayi karo tayi zakayi nasarar dasa kwanka rayhan ya sake yin murmushin karfin hali yana alfahari da kasancewar Mah'ruf dan'uwa a gareshi ..
'Kaga bari na fita yanzu zan dawo zan turo maka jafar ko da yake bari na turo maka Usman dan Allah karkayi dogon tunani kaji yayi masa magana kamar wani karamin yaro ...

*****
Washegari ya kama ranar Lahadi dandazon mutane ne tun daga farkon layinsu har zuwa karshe layinsu suka taru domin daurin auren ...........


TWO FRIENDS (BSBS)


💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~TRUE LIFE STORY~

FREE NOVEL


AL'QALUMAN



*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*


~DEDICATED TO~
*YAR GATA*

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim


PAGE 32


......Daurin auren MALIK MUHAMMAD SAGIRU EDRIS DA HAUWA'U SHUAIBU EDRIS , DA AMINU MUHAMMAD SAGIRU EDRIS DA SUBAI'ATU IBRAHIM EDRIS ...
Tun kafin a d'aura auren rayhan ke fama da kanshi domin zuciyarsa ta cure guri ɗaya taki motsin daya kamata ,da kyar mah'ruf ya shiryasa suka fito cikin farar shadda iri daya har malik wanda Abba ne ya dinka musu , sunyi kyau sosai .

ana gama d'aurin aure rayhan bai tsaya gaisawa da jama'ar da suka zo masa 8daurin aure ba kamar yadda al'ada take , mahruf yayi bangarensa dashi ya kwantar dashi ya soma magana cikin sanyi murya "yau ranar farinciki ce agareka ka mallaki muradin ranka , farinciki rayuwarka a yau babu wani tawaya a tsakaninka daita ta zama mallakinka halak malak dan haka ka kwantar da hankalinka bana son yadda zuciyarka ke bugawa da sauri ya k'arasa maganar yana zuciyarsa na dokawa da matsanancin karfi shi kanshi yana bukatar kulawa dan shi kadai yasan yadda yake jin zuciyarsa a wannan ranar hawaye suka cicciko acikin kwarnin idanunshi yayi saurin maida hawayen dan bashi da wani amfani da zai mishi ya kai hannusa ya dafa kan rayhan "ina zuwa ka bani minti goma zuwa ashirin zan dawo gareka dan Allah ka sausata numfashinka kaji ya k'arasa maganar muryarsa na rawa da kyar rayhan ya iya daura hannunsa akan na mah'ruf yana jan numfashi da kyar .

Jiki a sanyaye mah'ruf ya fito cikin jama'a , shine ya dinga gaisawa da jama'a a madadin rayhan yayi kyau sosai cikin shigar babbar riga sai daukar ido yake kowa ya ganshi sai yaji ya burgeshi tare da cewa "kai ma fa da yau ne ranar , da yanzu mun kama hanyar zuwa gidansu suhaima, shi dai hannu kawai yake mikawa mutune da kirkiro murmushin dole yana jin wani sanyi da mutuwar jiki mai tattare faduwar gaba tamkar wanda ake bugawa guduma, irin faduwar gaban da mutun yake jinshi har cikin cikinsa ...
A hankali mutane suka soma watsewa fuskokinsu cike da faricikin ..

idan kaga ummita da meenal bayan an gama d'aurin aure sai ka rasa wacce a kayiwa auren dole ko na kaddara acikinsu , sun kulle kansu a d'akin ummita suna kuka , duk wani mai kalmar rarrashinsu daga dangin yayi amman sun kiyin shiru .

Idan kaga ummah da mama suma hakan take a fuskokinsu saboda fargaban hajiya saudat da ta kasance suruka ga ƴaƴansu , hajiya saudat kuwa zuciyarta kunshe take da bakinciki mara misaltuwa abu goma da ashirin sun hade mata ga rashin lafiyar d'anta ga wannan qaddararran auren da idan tana kaunarsa to tana kaunar mutuwarta ,sam babu annuri a fuskarta kallo ɗaya zaka mata kasa wasi wasi anya kuwa yau ranar farinciki ce agareta ?

Babu wani buki da suka tsara yi daga ummita har jiddah ,sannan babu wanda ummita ta gayyata duk yadda iyayensu suka kashe kudi domin kama had'ad'd'en holl hakan bai dadasu da kasa ba ....

Jikin ummita yayi sanyi sosai haka zuciyarta ta dinga ya tsinkewa ga yawon faduwar gaba data tsinci kanta ciki .
Tana kwance har lokacin a d'akinta ta rasa yadda zatayi da rayuwarta wani irin kululun bakinciki ne ya tokare makoshinta ,
yayinda zuciyarta ke bugawa da karfin gaske wani irin kuka ya kufce mata mai taɓa zuciya suka rungumeta junansu da meenal "kiyi hakuri ummita ki ɗauka *WANNAN CE QADDARARMU* babu wanda ya isa ya hana faruwar haka ki tausayawa ya rayhan yana cikin wani hali kinji yar'uwarta ta d'aga mata kai alamun taji ...

A hankali mama ta shigo d'akin ta tsaya akansu tana kallonsu cike da tausayawa meenal na ganinta ta mike ta fita da sauri tana goge hawayenta .

"subai'a .........
Karon na farko kenan da mama ta kira sunanta kai tsaye , ta d'ago jajayen idanunta ta kalli inda take tsaye hawaye taf da idanunta "subai'a mu muslimai ne ya kamata mu yarda da qaddara ,ki duba doguwar nasihar da umma tayi miki, idan baki hakura da wannan auren ba tamkar kina jayayya ne da ikon Allah ,ni mahaifiyarki ce nima ina jin yadda kike ji a zuciyarki amman ban isa na musaya qaddararki ba, ki taimakeni ,ki taimaki yar'uwarki kiyi hakuri, rayhan na sonki tamkar ranshi ina mai tabbatar miki bazakiyi nadamar aurensa ba, zakiyi alfahari dashi kinji mama ,maza tashi ki soma shiryarwa ga mutane can kowa amarya yake son ganin, ta kamota ta mikar daita ta zaunar daita haɗe da zuro kafafunta kasa tayis tana kallon zara zaran yatsun kafafunta masu matukar kyau da sheki hawaye na zubawa daga idanunta" ki shirya kinji diyar albarka Allah yasanya haske acikin rayuwarki da zuciyarki yadda kika yiwa mahaifinki biyayya Allah ya azurtaki da ya'ya masu albarka waɗan zasu zame miki sanyi idaniya .....
"Ameen mama ta amsa muryarta cike da kuka mama ta goge mata hawaye da gefen rigar shadda dake sanye ajikinta "Ki shirya yanzu zan dawo ta juya ta fita tana maida hawayen da suka cicciko .........

A hankali ta mike ta shiga wanka shap shap ta fito zuciyarta na cigaba da dokawa ta sanya kaya ta ɗauki wayarta zata kira meenal ta turo mata mai yin make din da tayiwa aunty jiddah sai ga meenal din ta shigo a guje tana kiran sunanta "ummita !ummita!! jikin ya rayhan fa ya tashi ,a matukar zabure ta k'araso gareta jikinta na rawa ta nufo kofa fita batare da tace mata komai ba meenal ta biyo bayanta da sauri "yana ina meenal tayi Maganar cikin Muryar kuka?
"yanzu naga anyi d'akin mamansu sa'ada dashi , hanyar bangaren ta nufa cikin sauri take d'aga kafafunta .

d'akin cike yake da mutane , haka ta dinga wuce su har ta shigo uwar d'akan hajiya saudat , tana shiga dakin ta ganshi kwance yana numfashi sama sama hajiya ta galla mata wata ƙatuwar harara tana jan tsaki tare da kawar da fuskarta gefe tana nadamar dangatarta da mama a rayuwarta .

a rud'e ummita ta
k'arasa inda yake kwance, idanunta basu gane mata su Abba da injiniya umma da mama da Mah'ruf dake tsaye agun sunyi cirko cirko kowanensu zuciyarsa na cike da fargaba.
ta rungume shi ajikinta tana faman jera masu sannu duk da sannun bashi da wani amfani.

kankace me jikin nashi ya sake yin tsanani da kyar yake janyo numfashi yana fitarwa , iyaye da yan'uwan suka haɗu suka yi asibiti dashi ganin yadda yake jan numfashi da kyar .
Da kyar likitoci suka saisata numfashinsa suna ƙoƙarin suyi masa allura bacci mah'ruf ya hana dan gani yake idan akayi masa allurar shikenan ba zai farfaɗo ba , da kyar su Abba suka shawo kansa ya amince ranar dinner din da ba'ayi ba kenan aka tare a asibiti neman lafiyar ango ..

*****

Tsawon kwana uku rayhan bai san wanda ke kanshi ba ,hankali kowa ya tashi , haka iyaye suka shirya a fita dashi abroad dan wannan karon ba hajiya saudat ba kowa ya nuna damuwarsa a fili , yayinda ummita gabadaya ta sake ramewa ta fita haiyacinta sai kayi mamaki , ta batun wani auren kiyayya ko soyayya baya gabanta ita dai ya farka suyi rayuwarsu haka , ai kowani bawa da qqaddarar da Allah ya tsara masa ,su mama da umma kuwa karatun Alkur'ani da rokon Ubangiji nafiloli ba fashi .

Allah cikin ikonsa ya farfo da ya rayhan , Mah'ruf na rungume dashi ajikinshi yana tofa masa addu'a .....
Ummita kuwa tana rungume jikin ummah sai kuka take ,umma na rarrashinta "ummita meye na kuka bayan ga mijiki can ya farfaɗo sai mu godewa Allah tunda ya farfaɗo .
Babu laifi ya rayhan ya samu sauki bayan yayi sati a asibiti ,ya matsa a sallameshi idan an sallameshi a maida shi gidansa su tare da amaryarsa ...

Babu mutsu Abba ya umarci likita da ya basu sallama batare da ya samu wata ishashiyar lafiya ba, kai tsaye gidan akayi dashi mah'ruf na faman tsokanarshi "wallahi wannan ciwon love din naka na gigita mutune , sannan ga ciwo ga jaraba ko sauki baka gama samu ba amman kace akaika gidanka tare da matarka babu kunya babu tsoron Allah ,rayhan yayi murmushi "mah'ruf kenan bazaka gane ba, "ina fa zan gane kana shirin an gwamcewa da amaryarka ka dai yi a hankali gurin amarci dan har zuwa parcent ne kai .
"Koma dai menene nida ku kai ni kawai ina son na kasance tare da matata sanyi idaniyana mah'ruf ya runtse idanunshi yana matse hannun rayhan dake cikin nashi .


a daren ranar rayhan da mah'ruf wanda ciwon rayhan yasa suka sake dinkewa sosai fiyye da lokacin baya ,suka iso had'ad'd'en gidan da Abba ya gina musu a vwisdom estate dake dopemu cikin wata had'add'iyar jeep dark green sai sheki take acikin hasken lantarkin daya haskaka harabar gidan ,suka fito cikin kaya iri daya brwon din voyal duk cikin d'akin aurensu , a parlour'n Mah'ruf ya tsaya saboda yasan tuni an kawo masa maryarsa "fatan alkhairi dan'uwana "barakalahu laka wa baraka alaika wa baynahuma fil khair yayi masa addu'a ya fita zuciyarsa na wani irin dokawar da tsalle a daddafe ya isa gaban jikin motarsa tunda yake bai taba jin irin abinda yaji ba a yanzu ,jiki a sanyaye ya shiga motarsa mai gadi ya buɗe masa tangamemen get din gidan ya fita aguje tare ciza lip's d'insa na kasa da karfin gaske ....


TWO FRIEND'S BSBS



💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~TRUE LIFE STORY~

FREE NOVEL


AL'QALUMAN



*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*


~DEDICATED TO~
*ZAHRA BANDE BAGUDO*


WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim


PAGE 33

...Madadin ya ɗauki hanyar zuwa gida ,sai ya ɗauki hanyar cement ya dinga sharara gudun mutuwa akan titi , a hankali motoci suka dinga kauce masa saboda irin gudun da yake wasu na zaginsa yayinda wasu ke tausaya masa haɗe da yi masa addu'a .

bai tsaya a ko'ina ba sai adaidai gidan man dake ikeja along yayi parking yana fidda numfashi mai gauraye da tashin hankali yayinda zuciyarsa ke bugawa da matsanancin karfi .
ya kai hannunsa ya kashe motar gabad'aya ya da'ura kanshi akan sitiyarin motar a hankali ya ja tsaki "why am I thinking about her , I don't suppose to think about her ,i will keep my feeling about, I should go on with my life , but am feeling her. ya k'arasa maganar yana dafe daidai saitin zuciyarsa .....
Saurin dakatar dashi zuciyarsa tayi "
"Me kake faɗa haka ?
" to kai sonta kake yi ne ko me da zaka tashi hankalinka ka damu kanka akanta ?
"common mah'ruf stop this nonsense , baka sonta ka daina damun zuciyarka , koda ma kana sonta a wannan bagiren you have to stop saboda ta rigada ta zama mallaki wani,wanin ma d'anuwanka abinda kake yi a yanzu rahamun ne ...
Tsaki ya sake ja yana d'agowa haɗe da dukan sitiyarin daya haddasawa gefen kanshi bugawa bai sanda ya dinga dukan zuciyarsa da karfin gaske ba yana gargadinta "look mahru stop thinking nonsense "fuck you subai'a, live my life I don't love you ya furta a zafafe yana tada mota ya cigaba sharara gudu akan titi .
bakinsa na furta ba damuwar sonta nake ba wallahi damuwar abun kunyar da zuciyata ,
ta aika nake haka ya dinga sambatu har kai
U turn din dake gaban airport kad'an ya juya kan motarsa ya ɗauki hanyar zuwa gida , ya iso gida da taimakon Allah a lokacin da gidan ya ɗauki shiru kasamcewar kowa na bangarensa wasu ma tuni sun yi bacci jikinsa a sanyaye yayi parking ya bude door din motar ya fito ya nufi hanyar part d'insa yana jin ranshi babu dadi gashi tunanin ummita yaki barin zuciyarsa ta huta .

D'akinsa ya shiga ya faɗa a saman timemeyar katifarsa yana sauke numfashi can kamar minti goma ya zabure ya mike jikinsa na kyarma ya shiga bayi ya sakarwa jikinsa ruwa saboda zafin da ilahirin jikinsa yayi, ya dade tsaye ruwa na sauka ajikinshi sannan ya fito ya canza kaya zuwa na shan iska ya zauna tare da d'aga kansa sama yana kallon celling d'akinsa baya ko son kiftawa hotunanta zuciyarsa ke harhad'owa, a hankali ya furzar da iska yana dafe goshinsa ya salam ya furta yana jin yadda qirjinsa ke mahaukacin buguwa tunani iri iri babu wanda bai yi ba
tun daga tasowarta ,
rigimarta tsokanar fad'anta , tsiwa ,rashin ɗaukarsa da daraja , mu'amularsu a lokacin da yan'daba suka kawo mata farmaki , irin rud'ewar da gigicewa da tayi , damuwarta ta farko akanshi lokacin da yan'daba suka ji masa ciwo irin rud'ewar daya ga tayi ,ya kasa fahimtar wannan rud'ewar da tayi , yawon kukanta akan bata son rayhan bata son muhd sa'id , bata son hafiz almustapha ,bata son kowa duk wanda yace sonta zatace bata son shi to wa take so ?
Ya dafe goshinsa da hannunwansa duka , ya Allah ya furta a hankali yana jin yadda qirjinsa ke mahaukacin buguwa da karfi duk tunaninta sai murfin zuciyarsa ta bude haɗe da tsinkewa jikinsa ya sake daukar kyarma
Raba dare yayi tsaye yana sintiri a d'akinsa ,
ya dawo tamkar wani zautacce ..


Bangaren ummita tayi dauriya da namijin kokari sosai domin kuwa ta kawar da komai dake zuciyarta akan rayhan , ta rungumi qaddararen mijinta tare da qudurta yin rayuwa mai inganci dashi .

Tana kwance lamo akan gadonta har tayi shiri bacci ya kirata a waya ,ta zira zumbulelen hijab dinta akan kayan dake sanye ajikinta, ta sanya takalmi flat silifas , ta shiga d'akinsa bakinta ɗauke da sallama "assalamu alaikum .
"Wa'alaikum salam my princess ya taso daga zaunen da yake ya tarota ya rungumeta tsam ajikinsa yana manna mata hot kiss a goshinta .
"Barkanki da zuwa gidan aminu ina miki addu'ar samun nasarori da farinciki mai dorewa gidansa ya sake rungumeta tsam tsam "muje kiyi alwala muyi sallah domin godiya ga Allah ,a hankali sautin Muryarta ta fito cike da rauni "ina da alwala "alhamdullahi ya sausauta rungumar da yayi mata ya rike hannunta zuwa inda ya shimfida musu daddumar sallah ..

bayan sunyi sallar nafilla a ya dade zaune yana yi musu addu'a har sai da yaji gangar jikinsa ta samu natsuwa ,sai dai har lokacin zuciyarsa tana kan tsananta bugawa .
A hankali ya yunkura ya mike tsaye da kyar ya kamo hannunta cikin nashi .
ta rike hannunshi cikin nata da iyakacin karfinta "sannu ya rayhan ka dinga yin komai a hankali kasan baka da ishashiyar lafiya , "na gode subai'a Allah yayi miki albarka Allah yayi miki yadda kike min , "ameen tayi kan bed ta zaunar dashi "ka kwanta ka

2 Comments On WANNAN CE QADDARARMU
avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment