Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bin bokaye da matsafa kuma idan kika yi wasa shi mijin da kike takama dashi na kwace shi babu boka babu malam naga uwar uban da zakiyi .
",wannan kuma karyaki karamar karuwa mijina yafi karfinki ko da asiri "aiko ummita taji zafin kalmar karuwa data kirata dashi ranta a matukar 'bace tace "ai wacan mahauciyar uwartaki ce ta koya min harka karuwanci ki koma gida ki tambaye , mijikin kuma babu boka babu malam zan kwashe ki zuba ido daga yau zaki ga aikin daya fi na boka tasiri ,tana gama fadar haka ta nufi kofa fita ba tayi parlourn kasa ba ta ta shiga dakin mama ta kwanta akan gadonta ta rushe da kuka "kowa sai ya fadawa baya sona, me nayi maka ya mah'ruf ?
",Me yasa ka fadawa matarka baka sona ?
"nafi matarka komai me yasa bazaka soni ba ?
"Ummita ki natsu ki janyo mijinki gareki koda kuwa baki sonshi zuciyarta ke bata wannan shawara "ki janyo shi ko dan ki nuna wacan matar ita din ba kowa bace
"Ta mike tsaye tana zariya hawaye na zubo mata "zan yi kokari na dauki shawarki kyakkyawar zuciyata ..
A hankali ta k'arasa jikin window mama ta tsaya wasu sabbin hawaye na zubo mata ko cikakken minti goma batayi da tsayuwa ba ta hangi tsayuwar motarsa tana tsaye taga ya kira saifullahi da sauri ta fito daga d'akin zuwa kasa a daidai lokacin da saifullahi ke faɗa suhaima sakon shi "aunty suhaima wai ki fito inji ya mah'ruf mikewa tayi tsaye saboda daman a shirye take ta rataya jikarta tayi wa mama sallama tayi gaba mama ta biyota har harabar gidan ta kawota da tsarabarta cike da leda yayinda tuni ummita tayi nata shirin cikin doguwar riga da mayafin abaya ta la'be a bayan bangaren mahruf tana kallon mama ta juya zuwa cikin gida .

tayi saurin fitowa ta fito wajen gidan lokacin tuni suhaima ta shiga gaban motar yaja suka fice , da hannunta ta tsaida mai mashin "kaga wancan motar zaka bi duk inda tabi kabita "babu matsala hajiya hau muje da kyar ta hau machine din saboda rashin sabo ..



TWO FRIENDS BSBD


💗💗💗💗💗💗
     WANNAN CE
   QADDARARMU
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~TRUE LIFE STORY~

FREE NOVEL
            
      
AL'QALUMAN


*AYSHA  A BAGUDO*           
*FAIZA  HAMMADU*

~DEDICATED TO~
*AUNTY MODA ABUGA*

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

PAGE 45

....  Duk    inda  motar Mah'ruf   yabi    sai mai  mashin   yabi  hanyar ,  yayinda suhaima da  Mah'ruf   dake  zaune cikin  motar  zuciyoyinsu   ke  cike   fal  da tunanin  ummita ,  maganganun  data   faɗa  musu a yau   ya   bala'in   tsayawa kowannensu  a rai, idanunsu   gabad'aya  sun  kad'a  sun yi jajir tsabar  'bacin  rai   .

  ya  ɗan  waigo  inda suhaima    take  zaune yaga   gabadaya yanayinta   ya  sauya fuskarta   tattare  da damuwar  da   bai san ko ta  meye  ba ,kamar  ya tambayeta  dalilin sauyawarta    sai   kuma ya  share  ya cigaba da murza  sitiyarin mota yana cigaba da   tunanin maganganu   ummita dana   jafar .

Ummita   dake   zaune  zuciyarta   na  tafarfasa  a bayan   mai   machin  tace "malam   dan  Allah ka dan  qara   sauri,  idan ka  isa  daidai  mazaunin direban  motar  ka  daidaita  ta yadda  tafiyarku yazo daidai  koda na  second  biyu  ne sai   ka  wuce   gaban   motar     sannan  ka  dawo  baya  ka  cigaba  da binsa  a baya  "an  gama  ya fadi haka  yana  fixgar  machin din   aguje    yayi  kamar  yadda ta faɗa masa ..

   kamar   ance  mah'ruf   ya  duba gefen  madubin  motarsa   a daidai  jection   din  depomu express   ya  ganta   zaune  a bayan mai  machin   kamar  a mafarki  tana  hura   hanci take  gabansa    ya fadi ya shiga dukan  tara tara  ware  idanuwanshi yayi  sosai  domin tabbatarwa  kanshi  itace  ko  me   kama  daita  ya gani  a  bayan  wani kato .

     Cikin  d'acin  rai haɗe da  bakinciki  ya  soma rage  gudun  da yake,  ya  gangara   gefen  titi  yayi  parking  sakamakon tabbatar  da  ita din ce
  ya  soma  dai-dai  tsayuwar  motarsa   domin   yaga   wucewarsu  sannan  yabi  bayan   mai mashin dan sanin  inda  zata a daidai wannan  lokaci
yana   gama  daidaita tsayuwar    motarsa  yaga  mai  machin  ya  tsaya   daf   dashi   "yauwa   gaskiya   kana da hankali kuma ka  iya aiki   ya  karkata   mata  mashin  din  ta sauka da  kyar   tana  yi  masa magana   tana  tafiya yayinda  mai mashin  ya soma  biyota  abaya  .

Runtse  idanunshi  yayi zuciyarsa  na wani irin   tafarfasa , matarsa  ta  sunnah  ce  abayan   wani  kato , katon  ma ɗan okada har da  magana atsakaninsu  ? Ya ilahil alameena
mamakinsa   bai  kare ba  sai daya ga  ta nufo  inda  motarsa yake ,  suhaima ta ɗan dubeshi  tace "lafiya habibi  naga ka  tsaya anan  ?
Ai  ko  gama rufe bakinta  batayi   ba  taji ana 'kwan'kwasa  glass  din motar, da  kamar  ba zai buɗe  mata  ba  saboda bakinciki  abinda tayi , sai kuma   yayi  tunanin  halin  da  take ciki , ko babu  komai  akwai cikinsa  ajikinta  idan wani  abu  ya  samu cikinsa   ba  zai ji dadi ba, hasalima  shine zai yi  hasara   dan  haka yayi kasa  da  glass din  motar  idanunshi na kanta   cikin  doguwar   riga   sai  lokacin suhaima  ta fahimci abinda  ya  tsaida shi , kallon  ummita  kaɗai   sai  daya   saukar  mata  da  mummunar  fadawar gaban  da  batasan dalili ba ....

    Kallota  ya  cigaba da yi  yana  jin  zallar 'bacin rai  mara  misaltuwa  saboda  shigar dake jikinta  sun  maseefar yi mata  kyau  bayan bayyanar  da  surarta da sukayi   filli    kusan minti biyar   ya ɗauka  yana  kallonta batare da   yayi  magana ba     fuskarsa  a  haɗe kamar  wanda aka aikowa  da sakon mutuwa  , yayinda  zuciyarsa  ke kunshe da  bakinciki  da azaɓaɓɓen kishinta  .

Ta  lumshe masa  idanunta kana  ta bud'esu  fess  akanshi  sannan   ta  juya ta dubi inda  mai   mashin yake tsaye     "ga wanda  zai  biyaka  kudin aikinka  ta  sake  maida idanunta  kan mah'ruf cike  da  yauki  tana kad'a masa  kwayar  idanunta "ka  biyasa  kudin aikinsa .....

  "Akan  wani  dalili kenan da zan biyasa   na  aikeki ne   ? yayi  maganar  yana  ƙoƙarin buɗe murfin  motar   zuciyarsa na  tuttukin bakincikin mara  misaltuwa,   yana gama  fitowa  ya  sauke mata  yatsunsa  biyar  a kuncinta  "ubanwa   yace ki   hau  mashin  din  wani  kato ?
"ina  ma  zaki  a daidai wannan lokacin  ? yayi mata  tambayar  a matukar  fusace  jikinsa na  rawa tsabar 'bacin ran da   yake ciki .

   Zubewa  tayi  kasa     tana  mai  kife  kanta  bisa  kafafunsa ta soma  rera  masa  kuka  mai  tsayawa  a  rai  wanda  da  jin kukan kasan  na  zallar shagwa'ba   ne , aiko  take   hankalinsa  ya tashi   ya  dimauce  haɗe da gigicewa  ya  tsuguna  gabanta  ya kamo hannuwanta  duka cikin nashi  ,ta  fixge hannuwanta   da karfi tana  kuka  ,cikin   bala'i da  matsanancin  tashin hankali  yace "kina hauka ne  fatlion   me yasa kika fito   haka ?
"Kalli  yadda  idanun mutane  ke  kanki kowa fa anan  ke  yake  kallo  oh  my goodness  ? ya dafe goshinsa .

"Ina  ruwanka   da fitowata  haka ?
kowa  ma ya kalleni ,baka da  case dani  tunda  baka  sona   baka kaunar kasancewa  dani, to ka bar  masu sona su kalleni  ,ni  wallahi na ma fi  son  suyita kallona dan bana  jin haushi bare naga     laifinsu sai  ma dadi da  nake ji idan suna kallona .

Ya  sake  kai hannunsa jikinta   hankalinsa a matukar  tashe  ta buge masa  hannu ,  ta mike tsaye   har  dankwalinta na  ƙoƙarin  zamewa yayi saurin   janyo  mayafin abayarta   yana  gyara mata    "dan  Allah ka rabu  dani meye matsalarka dani  ne  live me   alone   ta buge masa hannu  ya sake matsota da sauri   "ke bana  son  hauka fa ya kike  wasa da matsayinki ......

   "ga ƙatuwar mahaukaciya  can  acikin motarka   ka baro amman ni  bana tare da hauka ,   batun  matsayi kuma   kai  kasashin dan ni  ban san shi ba  ,ni  dai ka  biya  mai mashin kudin  aikinsa sannan muyi  abinda ya kawo ni .

"idan  naki  biya ba fa ?

"Zaka  sha  mamaki kuwa dan  zanyi abinda sai ka  tsaneni  gabadaya ,mai machin  yaga  maganarsu 
taki  ci taki karewa   gashi  ba wai yana  jin abinda  suke faɗa bane  bayan  ka  biyashi  kudin aikinsa  kawai  yake iya jiyowa , hakan  yasa ya  karaso  sosai   inda suke   "hajiya  kina 'bata min lokaci   fa gashi yamma   nayi ,kuma wannan  shine  lokacin  neman   na  abinci.

"kaji  ko ka   biyashi kudinsa  ya wuce  ko kuma  ka sauwake min  aurenka anan  na  bishi   a matukar fusace yace  "bazan biya  ba , kifa kiyayeni  fatlion  ,  ba fa  ke kadai  kika iya   zafin kai   da  zuciya ba ,  ya kai hannu zai  shako  wuyanta  saboda bakinciki  ganin   mutane sun fara  taruwa  akansu  har  suhaima ta fito daga cikin  motar  ta tsaya tana kallonsu  tayi saurin gocewa tana hura masa hanci  .

mai  mashin ya  rasa yadda  zaiyi   ya amshi kudinsa   ya kara gaba, cikin haka  wani mai tireda    ya  tsallako  daga d'ayan  bangaren ganin hausawa  ne  " ki  bishi   tunda  iskanci kike  ji  dan kosisi bazan biyasa ba, dan ban aikeki daukosa  ba kuma wallahi  sai kin gane kurenki  stupid Kawai  ya juya  "suhaima shiga mota  mu wuce  .

"kasan  Allah  idan kaga ka  bar gurin nan   abu daya  kayi  min  cikin uku , sakina  ko  kuma biyan  mai  mashin ko  sanin   yadda  zakayi  dani  ban cin  haka  wallahi   babu inda   zani      kai ma babu inda zaka ta   k'arasa maganar  cikin kuka  tana zubewa ajikinshi "Allah  ni sai    ka  sakeni  wallahi na gaji da auranka .......

  "Hajiya  wai  me  ke  faruwa  ne  ? Mai tireda ya  tambayeta
Ta  d'ago daga jikin Mah'ruf   hawaye  Shabe Shabe a fuskarta kamar wacce  akayiwa dukan mutuwa , ta nuna  kanta da  ɗan yatsanta tana kallon  mutumin "ni matarsa  ce ta sunah  wannan  kuma karuwarsa ce   ya d'aukota  acikin  motarsa  ban  san  inda zasu ba  ta karasa  maganar  tana  sake  rushewa da wani kukan  wallahi bazan yarda  ka dinga   wulakantani  saboda wannan   karuwar ba ....

"inna  lillahi wa ina ilaihi rajiun   ya shiga furtawa a fili  ,a matukar tsorace mah'ruf da suhaima  suke  kallonta  fuskokinsu  ɗauke da matsanancin  mamakinta " take gumi ya  shiga tsatsafo masa ya  dinga kallonta kamar wata sabuwar halitta a gabansa ,  ta sake maida  idanunta  da hankalinta ga  mutanen dake tsaye agurin   "wallahi mijina ne  ita kuma  wannan ka.....
Yayi  saurin toshe mata baki "zan fa miki rashin mutunci  kika sake furtawa  suhaima wannan kalmar , ta buge hannunsa  tana kallon cikin  kwayar idanunshi  hawaye na tsiyaya  daga cikinsu "  wallahi  kasan yadda  zakayi  dani , kana  kallona  Kamar nayi maka  karya ita din  wannan  matar wacece agurinka  ?
"wacece  fa kika ce ?
ta rausayar  idanunta cikin  nashi batare da tace  komai ba yayinda
suhaima  tayi shiru zuciyarta  da  jikinta na wani  irin rawa  yau taga bala'in  daya  fi karfinta  ita ake kira da karuwa alhalin  da aurenta  ?

mai  tireda yace "Alhaji ka d'auketa  ku tafi gida tunda   matarka ce in yaso idan kunje gida kwa sasanta  ,naunayen ajiyar  zuciya   mah'ruf  ya sauke   ya janyo hannuta "kin san  Allah sai na  shuka  miki rashin mutunci idan ban jefaki cikin   guater din  can ba  zaki  sani ne  .
  "ni  dai kome  zakayi kayi amman   kasan  yadda  zakayi dani tana k'ok'arin  fizge hannunta ya  sureta  gabad'aya  yayi  sama daita ta saki ƙara  mai  sauti  tana kiran "  ka saukeni  tare  ta runtse idanunta, tana jiran  ta  jita  cikin quater  kamar  yadda ya ambata kawai   taji  ya  buɗe gidan  baya  ya ajiyeta a hankali  zuciyarsa na wani  irin dokawa da karfin gaske ,ya matso kusa  daita ya kamo hannuwanta  gabadaya ya  rike cikin nashi tare da  tsura  mata idanunshi   "ki zauna karki kuskura ki fito ,  idan  kika  fito sai  na  shakeki  kin mutu na huta   zaki  gane baki da wayo ,  ki fito idan kin isa ya  dawo gurin mutane  yana  huci  kamar zaki ya biya mai  mashin kudinsa sannan  ya kamo hannun suhaima  data dawo tamkar wata mutun mutumi  a tsaye zuciyarta  da kwalkwarta na  wani  guri  ,ya kalli  mutane  dake gurin yace  "wallahi  itama wannan  matata  ce  ta sunah, dukkanisu  matana ne ,take  mai tireda da sauran  mutane sukayi murmushi   domin sun fahimci  kishi  ke damun ummita ...

a hankali  ya  soma tafiya  da suhaima  data dawo  kamar  wata matacciya , yana buɗe gaban  mota yaga ummita  zaune ta hakince  tana cika tana batsewa  " ki  fito ki koma    baya    bana ce karki  fito  ba  saboda kin rainani  shine kika dawo nan ?
"to  ni  me nayi ita ta koma  baya  mana   dan nan  ne mazauninta  yayi shiru yana kallonta .
"Ya  mah'ruf.........
ta  kira  sunanshi tana tsareshi  da  idanunta  na tambayeka  mana " auren wa  aka soma d'aurawa tsakanin   ni da wannan matartaka?

"Ban  sani ba  idan kika sake  min irin wannan banzar   tambayar zan tattakaki  agurin nan  .
  "a zuciyarta tace  kada Allah yasa ka sani ,   azahiri  kuwa    cigaba da maganarta tayi   ba tare da ta damu da gargadinsa ba  "aurena  aka soma d'aurawa sannan na riga wannan matartaka   tarewa gidanka  amman tsabar makirci   yasa aka dawo dani   gida a daren farkona , ni bama dawowata  gida ne  yafi damuna    da min ciwo ba  kamar aurenka dake kaina ,ya  kai hannu zai ciccibota  "sai kuwa  kin mutu  dashi ba  dan bazan taɓa sakin ba ..

   "kasan  Allah  wallahi kana   ta'bani  ka taɓa aurenka ,dan  fitowa zanyi na faɗawa duniya ka  sakeni  saki uku ,na fito  nayi  zawarcina son raina  na kula  duk uban da yayi magana idan ma takama  nayi aure akan aure   .......
  "Zan fito dake kuma bazan  sakeki ba  Allah ya  tsinewa wanda ya fasa  yin zawarci  ki fito da kafafunki tun raina bai gama  ɓaci  ba ya k'arasa maganar  yana huci, suhaima ta karaso garesa  ta dafa shi "rabu  daita  habibi  ni na zauna a baya shiga muje  kawai idanun  mutane na kanmu .

Ummita    taja  tsaki  "aikin    banza   kawai ni za'a  kawowa    makirci da bariki    da ......
  "karki  sake ki zagar min mata dan  basa'arki bace ,idan ke ba  kya  ganin mutuncinta  ni ina gani .

"ta juya masa keya  tana zabgawa suhaima  harara    "to kayi   mata magana  ko kaja mata kunne  idan  ina magana da  mijina  ta  daina saka min wannan banzar rubabben   bakinta   shine zaman  lafiyar dani  dan banason  shishigi da neman  suna ta karasa maganar tana juyowa  ...

Ya d'aga  hannu zai buge mata baki  suhaima  tayi saurin  rikeshi "haba habibi ka daina biye mata yarinya ce fa ,ummita ta kalleta cike da takaicin  kalmar tana jin kamar tace uwarta yarinya  ba ita ba  amman ta share  ....
Mah'ruf ya furzar da iska mai zafi  daga bakinsa "wallahi  kin ci darajarta suhaima  da abinda zan miki yau  yayi shiru yana jan tsaki ....
ta yatsina fuska aranta tace" babu abinda zakayi da ya wuce mari ,shi kuwa idan da sabo na saba har ya zame min  man shafawa ,  yau dai sai kun gane kuranku daga kai har ita  .

Tana kallo suhaima  ta bude  gidan baya jikinta a sanyaye  ta shiga ta zauna  zuciyarta  tamkar ta buga  yaja motar da karfi  ya wuce  ya bar mutane  suna fadar albarkacin bakinsu .

"Ni matarsa ce  ita kuma wannan   karuwarsa ce kalmar ta dinga yawo acikin  'kwa'kwalwar suhaima , sosai ta shiga matsanancin  tunanin  yadda  zatayi da rayuwar  ummi .

Tafiya kaɗan  yayi  taga mai siyar da  agwaluma a bakin titi  tayi saurin kai hannunta   jikinshi   "a tsaya  zan  sha  agwaluma , har zai buga mata tsawa ya fasa yaja ya tsaya yayi kasa da glass din motar  ya  kira mai siyar da agwaluma, ta k'araso "nawa ne wancan karamin kwando ?
"5k  ne  "okay juyo shi  a leda  "nifa duka  yayi min yawa guda biyar ma ya isa tayi magana a shagwa'be cikin zazzakar  muryarta "tafi ki kawo yadda nace miki?
ya fad'awa matar yana ciro wallet dinsa ,ta mika masa bakar leda ya amsa haɗe da mika mata kudi ya ajiye mata a saman cinyarta ya ja mota ,ta  buɗe  ledar ta ɗauki   agwaluma  ɗaya zata  kai  bakinta , ya rike hannunta da sauri "no ki bari sai  an wanke  "ni dai kabarni na sha kayana haka dan wallahi miyona ya tsinke idan ban sha komai zai  iya  faruwa  dani  , dole ya sake tsayawa ya siya ruwan roba ya dibo agwaluma guda biyar ya wanke mata ya mika mata   jikinta na rawa  ta soma sha tana lumshe  idanunta.

motar tayi shiru har  suka kawo  gidan  babu wanda ya sake cewa  komai ita kuwa sai shan agwalumarta take tana yatsina fuska  ,yayi parking a harabar  gidan ,suhaima  ce ta soma  ƙoƙarin  fitowa shima ya yunkura  zai fito ummita  tayi saurin  riko hannunsa cikin nata tana murzawa a hankali  haɗe da   kafeshi da idanunta  da   ruwan  hawaye ya kodar dasu , ita kuwa suhaima ganin haka  yasa ta  dawo  cikin motar  ta zauna tana kallonsu zuciyarta kamar zata buga .

  a hankali ummita  ta soma  hura masa iskan bakinta  a fuskarshi da hucin numfashnta , da sauri ya kawar da fuskarshi  yana jin wani iri a gabad'aya  ilahirin jikinshi ya yunkura  cikin sauri  zai fita  ta  sake rikoshi da  hannuwanta duka  "dawo ka zauna magana zamuyi  mai mahaimaci  ya  dawo ya zauna  yana  kallonta  wani irin kwarjini tayi masa "uhmmmm ina jinki?
cikin  wani salo da yin kasa da muryata  tace " ya mahruf  ........
A yarda  ta kira sunanshi bakaramin  rud'ashi tayi ba ,cikin Sa'a ta janye  hannunta cikin nashi ta d'aura  a sama fad'ad'd'en  qirjinshi  take bugun zuciyarsa ta karu dan har tana jin yadda take bugawa  tayi  wani murmushi "ka tsaida zuciyarka sosai sannan ka tambayeta menene matsayin subai'a  acikinta ,kana ikirarin baka sona amman a zahiri ake gane zallar kishinka akaina ,tsaki yaja  yana sauke  wani wahalallen numfashi  tare da cire hannuwanta "daman wannan banzar tambayar zaki min ?

" Kai kake masa kallon banza , amman ni agurina ba banza bane, yakamata dai  ka sauke nauyin  dake kanka ka bawa  wasu  dama  ko kuma ka  inganta aurenka  ,yana sauraronta yana  jin  kamar ana janyoshi gareta  da wasu mahimman farinciki  amman  bazai iya bayyana  su ba ,gara su kare rayuwarsu haka . "tun  da bazaka iya inganta damar da Allah ya  baka ba ka lamuncewa masu so  domin su amfana dashi ....
zuciyarsa   tacigaba   da dokawa   kamar  zata tarwatse  saboda fahimtar inda maganarta ta dosa  , cikin rad'a ta cigaba  da maganar da zaka ɗauka kalaman soyayya  take  faɗa masa  nan  kuwa bukatar saki  take   daga garesa.

  "why  fatlion iyayenmu bazasuyi  farinciki ba most especially mama  ya kai bakinsa cikin  kunneta "zan rayu dake koda bana sonki , janye kunnenta tayi ta zuba masa idanunta  tana jin zallar 'bacin rai na ratsata take hawaye ya soma bin kuncinta ji take duk duniya babu mutumin  da yake mata tozarci   kamarsa  , furta kalmar   bai sonta akoina baya  masa  wahala kuma  ko  agaban  waye ,take  kanta  ya soma  sarawa ta kalleshi  ta  sake  rushewa da wani kuka  tace  "nima ai bana  sonka dan baka dace  dani  ba hasalima baka kai matsayin wanda zan so ba  ,idan bazaka rabu  dani  ba zanyi komai  na rabu da kai wallahi ya bud'e  baki zai yi  magana  tayi saurin rufe masa baki da hannunta  tana girgiza masa kai alamun kar yace  komai dan tasan duk  abinda zai fito bakinsa a lokacin  ba alkhairi  zai faɗa ba.

a hankali  tayi kasa da hannunta tana shafa  qirjinshi  tana  magana muryata can kasa .,.
Jikin  suhaima na rawa ta bude motar da karfi  ta fita tana bugo kofar da karfi  sai lokacin ya tuna tana  cikin motar "oh my god  ya  furta " sai kinga yadda  zanyi dake  yau ya fixge  jikinsa ya fito tayi murmushi   "kaɗan  kuka gani sai na addabe rayuwarku  sai na hanaku  zaman  lafiya ,ta  fito  da sauri  itama "ai baku ga komai  ba  ,  yadda suhaima  ke d'aga kafafunta  da sauri haka shi da ummita ke d'agawa .

Ko taku biyu bata yi da  shigowa  parlourn ba    ,ya  risketa da  sauri    ya nufota haɗe da cewa "dan  girman Allah baby  kiyi  hakuri  nasan  fatlion bata kyauta ba furucinta sunyi  tsauri dayawa  ya faɗa yana ƙoƙarin rungumeta  ajikinshi sai ganin  ummita yayi ta shiga  tsakaninsu tana duban suhaima  "haba malama   yau fa  ranata ce a gigice ta kalleta zuciyarta  cike da tsoro da firgici  "yes  na faɗa yau  rana ta ce kuma banga uban daya isa ya hanani morar wannan ranar  ba ,   wata nawa da d'aura  auranmu  amman kullun   kuna  tare dashi , kin  like masa kamar chungum  kin hanashi sukuni   amman hakan bai    hana mu  had'uwa  boye  ba  , yau kuwa  na rantse  da girman  Allah ko sama da kasa zata haɗe  sai ya kasance tare  dani  a bayyane sai dai idan  mutuwa zakiyi ki mutu ......

Tsawar daya buga mata ne yasa gabadaya ta rude  ta juyo a gigice ta rungumeshi  ajikinta tana fashewa  da kuka cikin damuwa  yake  sauke numfashi kamar zai yi kuka  hannu  suhaima ta kai ta fizgota da karfi ta  wanketa da mari  .
"duk iskancin da kikayi a titi  bai  isheki ba  sai kin yi  a gida  bari kiji na faɗa miki.......
tasssss  tasssss kake ji itama ta sauke mata biyu ajere   "how  dare you slap me?
"wannan ne kawai zai iya marina na kyaleshi shima  darajar aure ne , amman  irinki  dari suka d'aga hannunsu akaina sai na rama double dinsa,  mah'ruf ya riko hannu suhaima yana rarrashita  ..

Ummita  ta matso kamar zata shige  jikinsa  "ya Mahruf  ta kira sunanshi cikin wani salon murya da ita kanta bata san tana dashi ba   ....
Yayi mata banza tamkar ba da shi take magana  ba   fuskarshi da alamun damuwa ,hannu ta kai jikinsa tana mai  tsura masa ido "am talking to you my husband ..
"what the fuck do you want me to do  ya fada a zafafe Yana juyowa ? matsoshi tayi sosai ta had'e qirjinshi da nata  tana busa masa numfashi  " just  kill me  ta fada atakaice.
" well  I have already hate you  before so it's normal if I wishi to kill stupid lion like you ya k'arasa maganar  yana sake kamo hannu suhaima ya nufi d'akinta  ya zaunar daita yana fuskantartata  "am sorry  suhaima zan san abun yi zan ɗauki mataki sosai akanta ...

"no ka barta plz   nima nayi nadamar  kulata danayi amman  ka barta kawai babu  komai na yafe mata  ,ya rungumeta ajikinshi "baki taɓa faranta  min ba kamar yau, na gode  Allah yayi miki  albarka baby nah  ina alfahari da kasamcewarki matata  tace "ameen  zuciyarta cunkushe  da bakinciki ," ki kwantar da hankalinki bari naje nayi maganinta  "nace ka barta  dan Allah komai ya wuce  "amman da gaske kuna had'uwa a boye  daita ?
ya kamo goshinta ya manna mata   miss  " rabu  daita wannan ba gaskiya  ta faɗa ba , ko alqurani zaki  bata bazata  rantse miki  akan haka ba ,  ni dai kiyi hakuri  ina zuwa   bani minti biyar  yanzu zan dawo gareki  ya fita, yana fita  taja tsaki  a ranta  tace " zaki  san kinyi  dani wallahi sai na daydayta  rayuwarki  sai kinga  kashi kince kudi ne ...

Yana  dawowa parlourn ta  matso kusa dashi  kamar  zata  shige jikinshi  saurin  dakatar daita yayi a fusace yace "look  fatlion  kina son tarwatsa min faricikin gidana ko ?
  Ta yatsina fuska  ," ba magana  nake miki ba kika min banza ?   ta cigaba  da kallonsa batare da tayi magana ba  "kinsan Allah ko me zakiyi sai dai kiyi amman bazaki taɓa samu matsuguni  acikin  zuciyata  ba, muje na kaiki part dinki tunda kin kawo  kanki   ya ja hannuta  ta soma turtujewa  tana kuka "ni wallahi  bazan shiga ba gida  zan koma kuma ai nima  ba sonka nake ba ,kai ne kake  sona tunda  gashi   kaki  rabuwa  dani   ta fixge hannuta da karfi zata kwasa aguje  da sauri ya  cafkota  jikinsa "inna lillahi wa ina ilaihi rajiun "wani irin wulakanci ne haka  ?
"kinga   natsu  plz ki daina  wannan gudun ba'a son masu irin   ciwonki  na  gudu  haka fa ,"to kace wasa kake min , tayi  maganar a shagwa'be  "bazan ce ba  kin dawo kenan ta sake ƙoƙarin fixgewa ya matseta  gam  ajikinshi cikin kuka tace "bayan baka  sona kake rungumeni  "eh ba'a sonki kuma baza'a soki ba baza'a  daina rungumarki ba .

Tasa masa kuka" Allah  ka daina fad'awa wacan  matartaka  cewar baka sona  idan  ma ya zama dole sai ka faɗa ni ka dinga   faɗa  min tayi maganar  

2 Comments On WANNAN CE QADDARARMU
avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment