Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mahimmancinki abinda ya faru ba laifi bane , sannan babu yadda zanyi da rayuwata da hakan bai kasance ba a wancan ranar ta ya samuwar wannan cikin jikinki zai kasance ?
"Ki fahimceni wallahi ban cutar dake ba , ta dubeshi cike da sarewa zuciyarta na tsalle abu biyu sun haɗe mata a lokaci daya farincikin jin kalmar da tafi bukata agareshi da bala'in hajiya inna , idanunta na zubar da hawayen farinciki da bakinciki ta juya tana kuka , yayi saurin fizgota ta faɗa fad'ad'd'en qirjinshi suna kallon kwayar idanun juna "me yasa zaki wuce ki barni ? "Ina zaki ki barni yayi maganar a fusace take jikinta ya kama rawa tana son barin wajen ne saboda idanun inna dan tasan abinda mah'ruf yake bakaramin kona mata zuciya yake ba , hakan kuma zai sa taji haushin mama fiyye dashi mah'ruf din .

"tambayarki nake ina zaki ki barni ? nasan nayi kuskure , duk yadda nake ƙaryata gaskiyar dake zuciyata yau gashi ta bayyana kanta a idanun shakikaina wand'a duk duniya su nafi jin kunya fiye da komai ,na soki tun ban san sonki nake ba, na shiga tashin hankali iri iri a kanki , zuciyata ta shiga rud'ani da tashin hankali akanki , idanuna sun sha kwana a buɗe saboda tunaninki ,
ban taɓa sanin mahimmancinki ya yiwa zuciyata tasirin da ni kaina bazan iya magance matsalar ba sai lokacin da zaki auri rayhan wanda nasan aurensa daidai yake da rasaki da zanyi gabadayan ,na shiga damuwa da tashin hankali mara misaltuwa akanki , duk abubuwan da suka faru ban yi dan tuntata miki ba , a yanzu da nake jin kalmar rasaki na sake tabbatar da irin qaunar da nake miki ,ina sonki fiyye da komai da kowa dake cikin duniyar nan .....
" kin amince da irin soyayar da nake miki ?
Tayi saurin girgiza kanta alamun a'a "me yasa ?"why fatlion ? ya faɗa a tare ..

Ta cire hannunsa dake kafad'arta "dan Allah fatlion ki fahimceni karki min haka don't do this to me, ki fahimci yadda nake sonki dan Allah karki barni , karki bar magangun hajiya inna su yi tasiri arayuwamu alhalin muna tsananin son juna.....
gaba-daya maganarsa sake Kunno mata emotion din soyayyarsa suke da take ƙoƙarin dannewa a cikin zuciyarta, a hankali take cigaba da rera kukan farinciki da bakinciki "Allah na gode maka da kawo wannan ranar ina cikin koshin lafiya a gaban kowa mahruf ke nacin yana sona ya kamo yatsun hannunta cikin nashi yana muzwa yana kallon cikin idanunta yana girgiza mata kai alamun ta daina kuma ya fixgo numfashi da kyar "ina fatan ki fahimceni ki ajiye maganar hajiya inna agefe is normal thing ...


"A yanzu ne kake son na fahimceka ? "tayi masa tambayar tana tsareshi da raunannun idanunta , shiru yayi qirjinsa na bugawa da matsanancin karfi idanunshi da suke cike da tashin hankali ya sake zuba cikin nata yana kallon kwayar idanunta "ka manta lokacin da ka dinga ikirari kana fad'awa duniya cewar baka sona me zakayi da subai'a ?"Idan kai ka manta ni ban manta ba yana cikin kwakwaluwata sannan yanzu kace you're in love with me ta ya kake son na fahimceka ?
kai kullun tunanin kanka kake da muradin bawa zuciyarka abinda take so , as you wish it happen today ,fellings dinka kawai ka sani you don't care about my feelings batun hajiya inna kuma wannan ya rage gareka dan nima babu ruwana kuma ba matsalar subai'a bane , da ka sakeni , ko ka cigaba da rayuwa dani am not care , am nat scared dan ita kalmar ma da kake magana akanta ban santa ba bare zuciyata ta amince min da ita , tana gama fadar haka ta juya.

"fatlion Ki tsaya kiji ya dawo daita gareshi jikinsa na rawa ya talla'bo fuskarta da hannuwansa duka "dan Allah ki fahimceni "I know I hurt you tare da yi miki abubuwan da basu dace ba amman ba wai dan bana sonki bane hasalima soyayya ce amman daga yanzu komai zai kasance miki yadda kike so ,mah'ruf zai zame miki yadda kike bukata ,ki kalli cikin kwayar idanuna zaki fahimci gaskiyar dake cikinsu "oh my goodness ta furta tana runtse idanunta wasu tsiraran hawaye masu zafi suka zubo mata "ni yanzu me kake son nayi maka bayan ga abinda hajiya inna tace ?" Is to late now plz ko ina sonka son bashi da wani amfani "is not too late fatlion I said that I love you with all my heart ya faɗa yana bin iyayensa da kallo wand'a suka dawo tamkar poster tsaye suna kallon ikon Allah ,hajiya umma kuwa tafi kowa murnar faruwa wannan abu ,taji dadi yadda ya furta yana son matarsa a gaban hajiya inna , kuma duk runtse duk wuya bazata yarda ya saki ummita ba ,sai dai duk abinda za'a faru ya faru amman baza ta yarda ba ..


Kallonshi kawai ummita take bata ko iya kiftawa idanunta a hankali ya hura mata iskan bakinsa da sauri ta lumshe idanunta , wata kalar kunya ce ta rufe a lokaci daya , gabadaya jikinta rawa yake ta juya zata wuce ya riko hannunwanta duka cikin nashi dole tayi kasa da kanta ta kasa kallonsa "kasa d'agowa tayi , cikin wani salon magana yace " ki fahimceni babu wanda ya isa ya raba aurenmu zamu rayu tare ...
" no ya mahruf this no possible "me yasa ba zai yiwu ba ?
ta sake juya ya rikota cikin zafin nama " Ki tsaya ki fahimceni mana plz fatlion don't do this , don't do this to me , ki fahimci iri zafi da rad'ad'in da zuciyata take ciki a yanzu , plz don't do this , hajiya umma ta k'araso garesa cike da tausawa halin da yake ciki ta dafa kafad'arsa "ka barta tukunna a gama da wannan matsalar "no hajiya Ki bari na sake fahimtar daita dole ta fahimceni ,ni wannan itace babbar matsalata ba wancan damuwar ba, dole hajiya umma tayi shiru tana runtse idanunta "uhm ina jinki ? ta tsura masa idanunta " dan girman Allah ka rabu dani , da kace ba zaka taɓa sona ba yanzu kuma kazo kana min nacin magana ɗaya ,a gaskiya ka daina min naci dan bana sonka , kuma bazan taba son mah'ruf ba , idan ma kana tunanin subai'a zata soka ka cire hakan a cikin zuciyarka dan subai'a bazata so mah'ruf ba ,"dan girman Allah ki fahimceni "wai me zai na fahimta idan dai son da ka furta ne gaskiya bazan fahimta ba , "ya mahruf zan so ka tuna wani abu saboda Allah da saboda kai da ni ,ya tsuke bakinsa cikin zafin rai yana kallonta ," ina son rayuwar farinciki wa kaina banason abinda zai dangwamar dani cikin tashin hankali da damuwa , zai fi kyau ka nisanta kanka dani tunda ba'a sonka dani nima kuma bana sonka , bazan iya irin rayuwar auren da mahaifiyata tayi ba " amman ni ina sonki ,kuma mahaifiyata tana son aurena dake meye damuwarki da wata hajiya inna ?
"ni hajiya inna ba damuwata bace tunda ba itace ta kawoni duniya ba ,ina dai kyautata mata ne darajan su abba , ba zata zama matsala a rayuwata dake ba, abinda zai daga min hankali shine rashin sona da kika furta bakya yi a yanzu shine damuwata kuma shine matsala ..


Bangaren suhaima kuwa tunda ta bar gidan hankalinta yaki kwanciya, ta kira gidansu mah'ruf yafi sau goma ,amman magana ɗaya dai ake faɗa mata wacce kwakwaluwarta ta kasa ɗauka a karo na karshe ne aka faɗa mata abinda yafi komai daga mata hankali "suhaima subai'a ta rigada ta kwace miki miji ,ta ɗauke miki hankali miji ,bayan cikin da yayi mata har da nasaran sace zuciyarsa tayi , wannan gobarar tafi karfinki ba zaki iya kasheta ba sai wani ikon Allah ta runtse idanunta tana furta " wayyohlly zan iya kashe kowace irin gobara ce muddin akan mah'ruf "to sai kinji duk abinda ake ciki zan sanar miki sai ki san matakin da zaki ɗauki amman wannan yarinyar tayi nisa acikin zuciyarsa tana gama fadar haka kira ta kashe wayarta suhaima ta mike daga zaunen da take ta soma Zariya tana furzar da iska "cikin mah'ruf ai tunda ban dauki cikinsa babu shegiyar da zata haifa masa ta shige dakinta da sauri kamar zata kifa ...


A parlou'n mama kuwa tunda mah'ruf ya soma dramar soyayyarsa idanun hajiya inna ke kanshi ta kasa ɗaukewa ta tsura musu ido tana kallonsa ta a jin zallar 'bacin rai na ratsa kowa ni sashi na jikinta ,ji tayi duk duniya babu mahalukin daya taɓa 'bata mata rai kamar mah'ruf ya gama wulakanta kanshi daita kanta , data san haka zai dawo akan mace da tun farkon tafiyar bata bari an saka mata sunan mahaifinta da mijinta ba bare ta dauki soyayyar duniya ta 6daura masa, ranta a matukar 'bace tace "yanzu na sake tabbatar da cewar ba'a barka haka ba akwai wani kulli a karkashin kasa da aka kulla ,Kiri kiri yarinya tace ka saketa ba tayin aurenka bata sonka amman dan naci irin na asiri sai wani rawar jiki kake kana furta ta fahimceka, fahimtar uwarka da ubanka zata maka illa ka dankarawa shegiya saki uku rasssss ka huta ,ka zauna da matarka mai kaunarka ,kasan Allah ko mutuwa zaka yi sai ka rabu da kwallon mangoro ka huta ,kai yanzu nan burgewa kayi ka tsaya kana wannan shirmen a gaban mace kai dole da ayar tambaya cikin wannan lamari tabbas biri yayi kama da mutun asirin agumawa yayi tasiri amman kasan Allah wannan asirin bazai tasiri akan ba sai na karya shi yau dan muddin ina raye sai na rabaka da wannan abar sai na karya asirin da aka maka ta karasa maganar tana nuna sa da yatsanta ,a natse ya d'ago da idanunshi ya zuba mata su "wato dai ita hajiya inna tayi nisa bata jin kira mugun halinta dashi zata mutu ,duk yadda ya'yanta dasu kansu ke kokarin daurata akan hanya taki canzawa, bazata taba canzawa ba ,bazata taɓa fahimta ba duk abinda suke faɗa mata banza ne 'bata bakinsu kawai suke ,kai jama'a ko mutuwar rayhan babba aya ce gareta amman saboda daurin kai taki saduda ya k'arasa zance zuci yana jan katuwar tsaki ,itama hajiya inna tsaki taja tana Allah wadai da shi ....

Aunty jikinta na rawa ta matso gurin hajiya inna tana bata hakuri da kokarin shawo kanta" baba babba kazo ka bawa inna hakuri "sau nawa zan bata hakuri yayi maganar a zuciye jikinsa na rawa ?
na rigada na bata iya hakurin da zan iya bata, ku dai ku cigaba da bata hakuri zata hakura amman wallahi duk abinda zatace tace amman bazan iya sakin matata ba tunda ina sonta itama kuma nasan tana sona kawai dai bata son faɗa ne a gabanku ni babu ruwana da fada da karta faɗa ba damuwata bace as far as ina sonta ,soyayyata da nake mata ya isa ba sai ta soni ba ..

Ya dawo gurin ummita ya rike hannunwanta duka cikin nashi "Kina jina ki kwantar min da hankalinki zan killace ke da mama bazan taɓa barin ku dangwama cikin wahala da kuncin rayuwa ba ,ina son mama fiyye da tunaninki " taho muje ya riko tafin hannunta Kema mama taso muje , abba idan zaka biyomu kai ma bimillah kai duk ma wanda yaga zai iya biyo yazo muje mu bar mata gidan tayi rayuwarta ita kaɗai , babu mutsu mama ta biyo bayansa itama hajiya umma ta biyo bayansu abba kam kasa tashi yayi duk abinda yake son yi kenan amman rawan da jikinsa yake yasa ya kasa aiwatar da haka .
suna fita ko minti goma basu yi ba sai ga baba sarki ya shigo a daidai lokacin da numfashin abba ya soma ƙoƙarin d'aukewa....



TWO FRIEND'S BSBS

💗💗💗💗💗💗
     WANNAN CE
   QADDARARMU
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~TRUE LIFE STORY~

FREE NOVEL
            
      
AL'QALUMAN


*AYSHA  A BAGUDO*           
*FAIZA  HAMMADU*

~DEDICATED TO~
*AMEENA AUTAR HAJIYA*

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

PAGE 55

  
  gaba-daya  hankalin sauran mutane dake gurin ƙara   tashi  har hajiya Inna ,  suka yi kan  abba  hajiya inna na  kiran sunanshi  "Ibrahim!  Ibrahim  !! aunty ta fashe da  kuka haɗe cewa  "hajiya  kinga  abinda kika  haifar  ko , ya Ibrahim  na iyakacin kokarinsa   gurin  miki biyayya  ,yana  gudun ɓacin  ranki   idan  ya rasa  ranshi  ke  zakiyi hasara  saboda  bazaki sake  samun  kamar shi ba, dan  Allah ki hakura ki barshi  ya  k'arasa rayuwarsa  da  'yarsa da matarsa  ta  k'arasa maganar  tana sake rushewa da  wani  kuka .

"Ibrahim ka buɗe idanunka  ni ne  babu abinda  zai  faru ba zaka rasa  matarka  da yarka ba, a gaugauce injiniya ya  dibo  ruwa ya kawo ya soma  shafa masa a fuskarshi  zuwa  qirjinsa amman  shiru  bai motsa ba  , kallonsa  kawai  hajiya Inna  take  bata ko kifta  idanunta  ga wani kalar tashin  hankali daya bayyana akan fuskarta gabad'aya  jikinta  rawa yake  daga  karshe ta soma   furta kalmar data ji ta karad'e parloun'n wato " Inna  lillahi wa Inna ilaihi  rajiun tana cigaba  da  kallonsa tana jin sabon  tashin hankali ganin  tsayuwa na neman gagararta yasa  ta zube kasan tayis ta rushe da matsanancin kuka  "shikenan  na  rasa d'ana , Ibrahim  dina  ya mutu ya barni  jikinta  ba ƙaramin mutuwa   yayi  ba, ta sake  fashewa  da wani  gigitaccen kuka "shikenan  na cuci kaina  na kashe d'ana da kaina da gaske mutuwa zaka yi ka barni ?  Inna lillahi wa inna ilaihi  rajiun  Ibrahim karka mutu ka barni haka ta  dinga furta kalmar  tana maimatawa a zahiri da badini  tana jin jikinta kamar ba nata ba ,  kuka take sosai tana  jan gindi domin son Isa  inda yake .

Cike  da  tsananin  tashin hankali  injiniya  ya  kira layin  doctor  husai  yana ɗauka ya  sheida masa abinda  ya  faru  ko cikakken minti goma doctor husain  bai  ɗauka ba  ya  k'araso . gabadayan  suna tsaye akan abba sun kasa motsawa  jikinsu na rawa hatta  hajiya saudat ta shiga tashin hankali ganin  halin da abba yake ciki  ,likita ya ɗauki  minti goma  yana  duba abba  sannan  ya d'ago ya tabbatar musu da  "damuwa ce tayi masa yawa, zuciyarsa na daf da tsayawa  a ko wani hali matukar bata samu hutun da take buƙata ba  , amman a yanzu  inshaallahu  da  zarar anyi  masa allura ya samu  hutu  na wani lokaci zai  dawo daidai jakar aikinsa ya d'auko ya soma yi masa allura , gabad'aya suka tsura masa  ido  fuskarsa sharr sai dai da gani yana cikin damuwa da tashin  hankali , hannunsa injiniya ya riko yana mai tsananin tausayawa d'an'uwansa , gabad'aya kana kallonsa zaka san damuwa tai masa mummunar kamu shi kanshi wani irin zazzaɓi ne ya rufeshi kusan minti biyar yana rike da hannun abba yana zubar da hawaye ,hawayensa dake diga saman hannun abba ne ya farkar dashi ya bude idanunshi kaɗan yana sauke numfashi take ya furta kalmar alhamdullahi "sannu yaya  bai iya furta komai ba yayi shiru yana kallon injiniya idanunshi cike da kwalla numfashinsa na sama da kasa   ..

Alhamdullahi  hajiya inna taji  suna  furtawa a hankali, ba tasan sanda tayi  wata  irin zabura  ta k'araso  inda  suke  "yana raye  bai mutu ba  inji cewar  baba sarki ,"alhamdullahi  Allah na gode maka ta furta tana share hawaye jikinta na rawa .

Da  kyar  aka samun numfashin Abba ya daidaitu , a hankali  yake  bin  mutanen  dake gurin da kallo, shiru parloun'n yayi  baka jin motsin komai sai na saukar numfashin mutanen dake zaune a cikinsa .

"a soma kira min  ma'hruf tukunna  tunda an samu Ibrahim  din ya farfaɗo sautin  muryar baba sarki ta ratsa kunnuwansu  sannan ya maida hankalinsa  gurin  hajiya inna  wacce tayi tsuru tsuru cikinta na kad'awa a kan yanayin  Abba bata son rasa d'anta  duk duniya babu abinda take so da kauna kamar shi  tafi son shi fiyye da sauran  d'anta bujerewa umarninta yasa take nuna ko'in kula akansa  ..

    "Kinyi  shiru  hajiya     kamar bakece silar faruwan  komai   ba  ? injiniya ya buɗe  baki ya soma  magana "baba ka taimaka ka saka baki mairo  ta dawo  gidan nan  banason  ta bar rayuwar yaya  ,barinta rayuwarsa  ba karamin hasara  bane ..

"Ai sagiru al'amarin  mahaifiyar taku ne abun tsoro ,  shekara da shekaru  har yanzu ana kan abu daya , abu yaki ci yaki cinyewa  me take son ayi mata ?

"Wani irin hakuri ne ban  bata ba  Allah take son take son ya sauko daga sama ya bata hakuri ko me ?" kin shiga rayuwar d'akin  kuma kina son shiga rayuwar jikokinki dan  rashin imani  irin naki  ,ya k'arasa maganar yana takaicin  halinta .. adaidai lokacin da injiniya ya samu layin  ma'hruf .

"Ma'hruf na tsaka da tuki yaji  kira a karo na uku gefe  ɗaya  ga kukan da Ummita  ke damun kwakwaluwarsa  dashi ,a hankali  ya soma rage gudun  da  yake  tare da gangarawa  gefen  titi yayi  parking  ya bala'in had'e  ranshi  yana dubanta.

kwakwaluwarsa ce ta shiga tunani abinda ya kamata  yayi mata sai dai  yanayin  daya tsinci kanshi ciki adalilin kallonta da  yayi ya shafe komai  da yake ji , baya jin zai iya yi mata wani abu saɓanin rarrashi saboda  tsantsar soyayyarta  da yake jin yana bin dukkan sansar jikinshi , gaba-daya ya manta mama da umma  dake  cikin  motar ,ya  matso kusa daita ya riko laulausan tafin  hannunta  cikin  nashi  ya matse  gam  yana ci-gaba da kallonta "dan  Allah ki daina  kukan nan  yana ci min rai  yaya kike son nayi ?"nima Ina cikin tashin  hankali  fiyye da wanda kike ciki ,tabe bakinta tayi haɗe da fixge hannuta  "ina ruwana da tashin hankali da kake ciki kowa tashi ta  fisheshi ni abbana ka maidani ina son sanin halin da yake ciki nayi nadamar biyoka da nayi alhalin abbana na cikin wani hali ,  yayi shiru yana  kallonta  ta kawar da  kanta  gefen titi alamun  bata son ganin fuskarshi  ,yana  shirin magana   wani  kiran ya sake  shigowa wayarsa ya lumshe idanunsa ya buɗe  yana saukesu akan wayarsa  ya ɗauka domin ganin  mai damunsa da kira  da sauri ya  ɗauki   wayar  ya manna a kunnenshi  sakamakon ganin sunan wanda ya kira  "dady ..... ya kira sunan zuciyarsa cike da mummunar damuwa .
"kana ina ?
Yayi saurin katse shi da sauri na kusan karasawa gida  ,"maza ka dawo yanzu  yanzu  baba sarki yazo yana son  ganin mama da umma  ya fad'i haka ne  saboda yasan muddin  yace shi yake son gani  ba zai dawo ba, naunayen ajiyar zuciya ya  sauke  sai lokacin ya tuna suna tare da mama  ya  juya baya a hankali  inda  suke  zaune suna  karanto duk addu'ar data zo bakinsu  domin samun natsuwar zuciya ya  sauke wayar a kunneshi "lafiya baba ? mama  ta Kira sunanshi hankalinta a tashe  tana addu'ar  Allah yasa ba wani abu ne ya samu abba bayan fitowarsu ba .

"Wai baba sarki ne yazo yake  son ganinku   bari na  juya, ya soma ƙoƙarin juyawa haɗe da  cewa "ke kuma karki sake damuna,  dan  kukanki  yana  damun kwakwaluwata ya  cilla motarsa kan titi ya figa aguje    .

Minti goma sha biyar ne  ya kawo ma'hruf gida ,mama da  umma da ummita suka shigo ma'hruf na bayansu , Abba na ganinsu ya sauke naunayen ajiyar zuciya  ya gyara daga kwanciyar da yayi ya  zauna  yana kallonsu zuciyarsa na dokawa hawaye na sake  zubowa daga idanunsa ..

Guri suka samu suka zauna bisa ga  umarnin baba sarki  ,kallonsu
abba  yake  yana jin sanyi a ranshi su kaɗai suke sakashi  farinciki a duniya .

A hankali baba sarki ya cigaba da magana "Rayuwa dai duk yadda Allah ya rubuto    babu wanda  ya isa ya canza ta,  ita kaddara kuma tana kan kowa hajiya ki maida hankali ki,karki  bari ki mutu da hakin rayuka da yawa akanki kina  abu  tun da sauran kuruciya  har zuwa yanzu da  rai ya  kai   gargara kina  kan abu daya kamar addini .....
"   a yanzu dai  bazan sake  miki nasiha akan abubuwan  da  kike saboda  na  gaji  da halinki, na gaji da yi miki nasiha , sai dai Allah na ganin  komai  kuma shi zai hukuntaki bisa abinda kike  saboda baki dalili ko hujja na tsanar baiwar Allah  nan maryam , babu abinda tayi  miki  illa tsabar kabilanci dake damunki akanta , tana binki tana miki biyyar da ko hausa fulani da kike son Ibrahim ya aura albarka ,a irin biyayyar da take miki kina ganin da bahaushiya ce zata jura ?
" Sannan  yadda kike tunanin da iko da gadarar  kina da karfi da iko akan yaran nan haka nima nake dashi a matsayina na kanin mahaifinsu .

Baba sarki ya juya ya  dube Abba  cikin sarewa yace   "ban lamunce maka rabuwa da matarka maryam  ba har abada sai da mutuwa ta rabaku  haka   kaima ma'hruf  ka ɗauki matarka ka wuce daita , Kema mairo ki  koma  d'akinki  matsawar zaki  fahimceni  barinki  rayuwarmu ba ƙaramar hasara bace ..

A qalla baba Sarki ya ɗauki  kusan awa uku yana magana yayi da mama sannan   ya  juyo ya  dubi  hajiya Inna, sannan ya dubi sauran jamar  dake gurin a karshe ya mike tsaye duk mazan  suka mike Abba zai tashi  ya dakatar dashi "kayi zamanka Ibrahim na  yafe  Allah ya baka lafiya Allah yayi maka   albarka  , ka daina biyewa shirmen mahaifiyarka saboda  babu biyayya ga bawa a gurin sa'bon Allah , ita mahaifiyarka ce kayi mata biyyaya daidai yadda Allah yace amman gurin sakin aure babu wannan biyayyar ko ta tsine maka babu abinda tsinuwarta zata maka  gabadaya  suka   rufa masa  baya  har hajiya Inna  suka bar ummita da Abba da mama   .

Mama ta mike ta nufi d'akinta  tana kuka tana tausayawa kanta da  diyarta  a hankali shima  Abba  ya yunkura da kyar yabi  bayanta a bakin gado ya sameta tana zubar  da hawaye  ya zauna  kusa daita ya riko  hannunta  "ki  ƙara hakuri Maryam , nasan kina hakuri dani sai dai ina neman alfarma ki ƙara  hakurin ,  kuma hakurin nan naki ba zai

2 Comments On WANNAN CE QADDARARMU
avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment