Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haka nan taji zata iya kula Ibrahim saboda kamewar dake tattare dashi , cikin sa'a bai sha wata wahala ba ta amince da soyayyarsa .

bayan ya dawo gida yake sheidawa d'an'uwansa shuaib komai akan mairo ,kuma ita yake da burin ta zamo abokiyar rayuwarsa , shuiab ya jinjina girman al'amarin "lallai kace rabon amarya ne ya kai ka kwatano ina cewa kaje kana kin zuwa , Ibrahim yayi murmushi "wallahi yaya da farko ma ban so zuwa ba sai daka matsa a she akwai abinda Allah ya boye har yasanya min son tafiyar "to Allah ya tabbatar mana da alkhairi amman bahaushiya ce ko ?
"Eh to hausawa ne amman zaunanun garin ne ,dan acan aka haife iyayenta da kamaninta sai dai ta sheida min asalinsu 'yan auyo ne dake karkashin jahar jigawa zama ne ya kawo kakanninkakaninta ......

"Shikennan zan yiwa hajiya inna magana , shuiab bai yi jinkirin sheida wa mahaifiyarsu ba , tashin farko Hajiya inna ta hau bala'i " bata yarda a auro mata diyar agumawa jikar agumawa masu tallan kifi ba ,dangin matsiyata waɗan a kamun kifi zasu kare ...

Shuaib yayi kokarin yi mata bayani akan tushen yarinya kamar yadda dan uwansa yayi bayani amman fur taki tsayawa ta sauraresa , abu kamar wasa Hajiya inna taki auren Ibrahim da mairo, juyin duniya shaiab yayi daita tace" sam bata yarda ba , yayita bata hakuri da rarrashi saboda baya son dan uwansa ya shiga damuwa amman taki ....tace " tafi son ya auri real hausa babu jagwalgwalo ..

a lokaci tuni Ibrahim da mairo sunyi nisa a duniyar soyayyar da suke jin duk duniya babu wanda ya isa ya rabasu, wasa wasa hajiya inna taki amincewa har sai da magana ta kai gurin baba sarki wanda ya kasance kani ga mai gidan ita hjy inna wato kanin mahaifinsu Ibrahim , nan fa ya shiga yi mata nasiha da wa'azi ,tunda dai yarinyar muslimai ce ai aurenta ba zai zama da wani aibu ba , tayi hakuri ayi tunda shi Ibrahim din yana son yarinya , ta ɗauka wannan auren kaddara ce , da kyar dai sarki aminu wanda kudinsa ne ya bashi sarauta kamar yadda sarautar zamani ta gada ya shawo kanta ta yarda , a lokacin an haifi Abdurrahaman har ya kai shekara uku ..


batare da wani bata lokaci ba baba sarki ya taka har kasar kwatono domin nemawa Ibrahim auren mairo ,sai dai cikin rashin Sa'a suma iyayen mairo suka ki batun auren ,a cewar su bazasu bada diyarsu tillo mace ba , dan mairo ita kadai ce mace acikin family dinsu gabad'aya , duk maza ake haifa mazan ba wasu masu yawa ba duk daki bai fi ayi haihuwa maza biyu ba ,kamar yadda suke a d'akinsu maza biyu sai ita , shiyasa suka dauki son duniya suka daura mata basa son abinda zai nesanta ta dasu ,
sai da aka kai ruwa rana sannan suka ce zasuyi shawara a tsakaninsu , a wani zuwa da baba sarki yayi wanda shine zuwansa na biyar....

A lokacin tuni mairo ta daga hankalinta akan lallai ita Ibrahim take so, muddin basu bashi aureta ba ba zata taɓa aure ba , koma zata gudu ta barsu bazasu sake ganinta ba ,nan fa hankalin danginta yayi mugun tashi ,dan Allah yayi agumawa da son ya'ya barin ita tilo ,sannan suna kokarin suga sun bawa ƴaƴansu abinda suke ,sun amince
da zumar sai sun tura wani daga cikinsu zuwa kasar nigeria domin sanin inda dangin Ibrahim suke, hakan ce ta kasance musamman suka haɗa baba sarki da wakilinsu, ai kuwa wannan abu ya sake tsayawa hajiya inna rai, taji kamar ta mutu dan bakinciki , kwata kwata taji bata son mairo a ranta ,ta dinga bala'i "dan me za'a ce baza'a bawa Ibrahim dinta aure ba ,me aka fishi ?
" gata ko dangi diyar tasu fin shi tayi , ko diyarsu zinari ce ko me ?

"ko ma dai menene gashi kingani ,baza ziniri bace agurinki amman tafi zinari agurin danginta , dan da kinga bakar wahalar da muka sha da shuiab akan wannan yarinya ,da kanki zaki kirata da lulu'u karewar zinari saboda sanin darajarta , dan har ruwa muka tsallaka zuwa wani yankinsu ,kuma ita yarinyar nan ita Ibrahim ɗinkin ya gani yace yana so ,ya tsallake tarin yammata yan'uwa dana ƙasar shi, yaje wata kasar , ke dai abinda nake so dake addu'a Allah yasa alkhairi ce a tare dashi ....

A tsakanksnin wannan lokacin akayi auren mairo da Ibrahim bayan tarin dukiyar da iyayenta suka amsa bisa al'adar su ta agumawa , nan hajiya inna ta sake yarda da lallai mairo daban take acikin mata , amman da yake tsanar yarinyar ta rufe mata ido ta dinga zaginta tun kafin a kawota , duk wanda yazo mata Allah yasanya alkhairi ,"sai tace " kun taya ni dai da addu'a dan Ibrahim ya daukowa kansa bala'i da kanshi ,kunga abinda aka kashe ?
"An kai musu kudin kimanin miliyan ɗaya, bayan motar doya dasu manja komai dai na kayan abinci tamkar wasu dangin mayu , har da kwalekwale jirginsu su din kama kifi sai daya siya , ga kayan sakawa wai da kayan mijin ake fitar biki , Allah bai yi musu arzikin siya mata kayan fita biki ,wannan bala'i tsiyar da me yayi kama ?
Wasu su bata hakuri suce tayi addu'a ,yayinda wasu su ke zugata ..

Ibrahim ya gina gidansa da zasu zauna da amaryar amman inna tace sam bata yarda ba sai dai akawota nan gidan bangarensa , tun da mairo ta tare a gidan bisa umarnin hajiya inna , ta fuskanci akwai matsala domin ta lura da inna bata sonta domin kiri kiri take nuna mata kiyayya ..

Mairo ta ɗauki damarar hakurin zama daita da halinta ,dan bata da yadda zatayi ,ko babu komai uwar mijinta ce ,uwar miji kuma ba'abar wasa bace ,itace mafi girmamawa arayuwarta , tunda itace matar da ta haifa mata miji bare miji irin Ibrahim, ai dai komai zatayi tayi amman ta barta tayi rayuwa dashi ...

Iyayen mairo basu kawo mata komai ba ,daga sai wasu mata guda biyu suka kawota kuma sunan basu tafi ba suna jiran sauran yan'uwansu k'araso , sunyi kokari gurin kayan daki dan basu tsiya komai a kasar ba ,sai da suka zo Nigeria ,duk abinda ake na al'adar ƙasar shi suka saka mata a daki, tun nan inna ta raina kanta ta fahimci ba wai talauci da tsiya yasa aka amshi tarin dukiya daga hannun Ibrahim ba ,dan abinda aka saka mata a d'akinta ya haura miliyan uku , kudi na gugan kudi million biyar mahaifin mairo yasa aka damkawa Ibrahim check a hannunsa domin ya kara jari acewa, sannan yace su shirya shi da yan'uwansa da mahaifiyarsa zuwa kasa mai tsarki , suma tsaye inna tayi a lokacin da taji labarin bakin zagi ya mutu murussss ita da masu zagin ba'a kawowa amarya komai ba ..
Duk da wannan hidimar da akayi hakan bai sa inna taji kaunar mairo acikin ranta ba asalima sai kushe arzikin take ...

*******
Yan'uwa mairo sun sake damka amanarta a hannun hjy inna da fatima ,ita dai fatima ta amsa amana da zuciya daya habiya inna kuwa acikin zuciyarta take furta ban amsa ba dan bazan rike wata amanar diyar agumawa ba ...
Tun sanda mairo tasoma girki zata kawowa hajiya inna amman bata amsa tace" ita bata ce kayan karni ...
haka mairo zata juya da abincinta ,bai hana gobe idan tayi ta sake kawo mata ..
A sheakarar suka sauke farali amman banda Hajiya Inna da tace bazata , dan maka ita ba bakuwa bace taje, tayi maimaici har bazata kirga zuwanta ba , ita yanzu sai dai akirata da hajijiya ba hajiya ba....
dole aka maye gurbin kujerarta da hajiya Fatima ....

Bayan sun dawo aikin haji Ibrahim yaso mairo ta cigaba da karatun ta amman Hajiya inna tace sam ai tagama karatu ,su a daginsu matar aure bata zuwa karatu ta zabi ko aure ko karatu ,i dan kuma yawon tazubar za'a tafi na halin agumawa to a faɗa mata tasani , duk yadda Ibrahim yaso ya fahimtar da Inna Amman taki yayi shiru yana sauraronta inna ta hana mairo karasa karatunta amman ita tata diyar tana can jami'ar Ahmadu Bello University , to shi daman Ibrahim mutun ne nagartacce ga al'ummar unguwa ma sun san da biyyayarsa da dadin mu'amula bare akan mahaifiyarsa haka ya kau da idanunsa domin yiwa mahaifiyarsa biyayya ...

Bayan shekara daya shiru mairo ko batan wata batayi ba, nan hajiya inna ta sake ɗaukar karan tsana ta daura mata duk abinda tayi sai tace bata iya ba ko tace za'ayi musu halin agumanci "bata da aiki sai kiranta da juya dangin agumawa masu tallar kifi ,kaje ka dauko marasa irin haihuwa ,
kalmar dai tsiya da talauci babu ita dan idanunta sun gane mata zahirin wacece mairo , har zuwa lokacin da injiniya ya auri saudat diyar baba sarki inna bata canzawa mairo ba ,da auren ma babu abinda batace ba,"wannan shine auren da take so kuma take alfahari dashi ,Hausa da Hausa ba wake da shinkafa ba , auren saudat babu jimawa ta samu ciki ,wata tara cif ta haifo dan namiji yaci sunan malik .

Bayan wani lokaci ta sake yin wani ciki ,nan fa salo iri iri ya tashi gabad'aya ta koma gidan Inna ,tare suke zaman zagin mairo,sam inna bata son laifinta har manufuka Tasha Kiran Hajiya ummah wai saboda taga arziki shi yasa take shigewa mairo, a daidai wannan lokacin hajiya ummah itama ta samu cikin Ma'aruf nan damuwa ya taru yayiwa mairo yawa ,haka zata zauna ta dinga kuma tana kaiwa Allah kukanta, tunda har asibitin kasarta taje likitoci sun tabbatar mata da lafiya lau mahaifarta take , at any time zata iya samun ciki ,suka ce tazo da mijinta a duba ko daga garesa ne , shima koda aka gwada shi lafiyarsa lau kwayakwansa na move shima mai haihuwa ne, dan haka suka mika lamarinsu ga Allah tare da bautawa yaran yan'uwa duk dan da mairo tagani ta makale saboda Allah yayita da son yara ....

Saudat ta riga hajiya umma samun ciki amman cikin ikon Allah Hajiya umma ta rigata haihuwa ...
tsiransu kwana uku,
Dan haka aka haɗa suna, ranar suna dan hajiya umma yaci Ma'aruf sunan mahsifinsu ,yayinda dan saudat yaci sunan Aminu sunan baba sarki , tun da aka haifi Ma'aruf hajiya Inna ta ɗauki soyayyar duniya ta ɗaura masa, haka mairo itama tana son yaran duka itace ke d'awainiyya dasu barin Ma'aruf wanda tun da aka haifeshi uwarsa take cewa "mairo kinyi da ,ki shirya wannan d'anki ne halak malak dul sanda taji haka sai mairo tayi kuka dan murna "na gode yaya da karamanci wallahi koda baki mallaka min mai sunan baba ba naji dadin da wannan mutuntaka Allah ya raya mana shi .."ki daina kuka kema zaki haifi naki ,sai kin rike naki da hannunki lokaci ne , kowa da lokacin da Allah ya gaddaro masa ki daina sanya damuwa aranki ..
Da waɗan kalaman take jin sauki acikin ranta ..

Ita kuwa saudat bata son mairo na daukar mata yaro , sakamakon tana bayan inna yayinda ita hajiya ummah bata yarda da hakan ba ,suna shiri da mairo sosai saboda tana da saukin kai ,hakuri da sanin yakamata uwa uba kawaici akan komai idan ba'a an faɗa maka asalinta ba bazakace agumawa bace , Hajiya inna da saudat kullun cikin zagin mairo suke lura da hakan yasa injiniya ya hauta da bala'i yace idan batayi hankali ba zai iya sakinta akan mairo hakan yasa ta ɗan saduda ta rage shiga ɓangaren inna ..

Ma'aruf ya shaku sosai da mairo domin shine ya rada mata sunan mama har mama ya bita ,duk inda tayi yana biye daita ,itace koman shi, kashinsa fitsarinsa wankasa
lokacin da ya isa yaye Hajiya ummah ta damkawa mairo shi amatsayin na wacce zata yayesa ,hakan ko yayiwa inna ciwo dan duk cikin jikokinta tafi son ma'aruf saboda sunan mijinta da akasa masa babu bala'i da batayi a karshe ta dauko shi ta dawo dashi gurinta "idan fitsari abun yi ne kaza tayi ,aiko ranar bata runtsa ba ,yadda taga rana haka taga dare ,dole ta lallaba ta dawo dashi ba dan taso ba ......

A wani zuwa da yayan hajiya mama yazo da matarsa kawo mata ziyara, yaga irin wulakanci da'ake mata akan yara ,shine yayi mata alkwarin ida zai dawo zai kawo mata dansa usman .....

Wata rana mama na zaune tana kukan bakinciki abinda hajiya inna take mata da saudat , hajiya umma tashigo dakin hannunta rike da jakar kayan Ma'aruf , ta risketa cikin wannan hali tayi saurin ajiye jakar hannunta, ta karaso gareta tana dafa kafad'arta "menene mairo mai ya sameki ?
Gaba-daya ta rud'e kamar ba kishin sauri ba "ta d'ago kanta ta goge hawayen fuskarta "babu komai "matsalar haihuwa ke saki zubda hawaye ?
Hjy mama tayi shiru ta kasa magana "nasan itace kiyi hakuri wallahi idan da rabo zaki haihu idan kuma baki da rabo haka zamu hakura mu ɗauki hakan a matsayin *WANNAN CE QADDARARMU* amman ina muku fatan samu naku keda ibrahim ,kuma inshaallahu zaku samu "na gode sosai "karki min godiya ban daukeki matsayin kishin sauri ba matsayin kanwa na daukeki ,Ibrahim dan uwana ne iyayenmu uwa daya uba daya ko babu aure tsakanina da d'an'uwansa, ke din matar d'an'uwana ce ki kwantar da hankalinki ina matukar sonki har cikin raina , ga kayan baba can na kawo miki , ta nuna mata inda jakar kaya yake ,mun mallaka miki shi halak malak, nasan zai samu riko na mutunci da kyautatawa daga gareki tana gama faɗar haka ta mike ta bar d'akin ..


Wannan kyauta da Hajiya umma tayi mata ta faranta mata rai matuka, sai dai bata daura ranta da zuciyarta ba tunda tasan yadda Hajiya inna ke mahaukacin son shi ..
Hasashen Hajiya umma ya tabbata domin hjy mama ta maye gurbinta agurin Ma'aruf ....cikin haka aka kawo mata Usman ,tayi murna tayi farinciki ko yanzu an sake wanke mata zuciya ..
Ma'aruf da sauran yaran gidan duk suka dawo dakin mairo,anan suka taso tare da usman har zuwa sanda aka haifi jiddah ..

Shekarar jiddah biyar mijin hajiya umma ya rasu, mutuwa ta gigirsu sosai dan har sai da Ibrahim ya kwanta zazzaɓi ,
bayan Hajiya ummah ta gama takaba Hajiya inna tabawa Ibrahim umarni ya auri hajiya ummah .
"ka auri Fatima tunda ita wancan taki haihuwa sai wahalar da kanta take akan ya'yan mutane ,sai kuma ci take tana zuba kashi , babu abinda hajiya inna bata faɗa ba ..
Babu yadda Ibrahim ya iya da rayuwarsa haka ya auri hjy umma bisa umarnin mahsifiyarsa da kuma goyon bayan da mairo ta bashi ita kanta hajiya ummah bata so wannan hadin ba tayi ƙoƙarin kauce masa amman yadda mairo ta dinga rokonta tana kuka "yaya ki maimakeni , nasan halinki kinsan nawa ,na kuma san kina sona bil hakki da gaskiya, nasan ba zaki cutar dani ba ,da Ibrahim yaje ya auro wata gara ya aureki tunda nasan halinki kuma a karshe dole zai kara aure saboda bana haihuwa ,ki taimakeni ki amince da auren nan .....
Wannan aure shi ya dan sausauta wani tashin hankali a gidan, tsana da tsamgwama ya ɗan ragu
komai tare suke da Hajiya umma , bama zaka gane kishiyoyi bane babu abinda yake bambamtasu.
A wannan lokacin ummasalma diyar hajiya inna takare University kuma a shekarar tayi aure ,cikin ikon Allah ya albarkaceta da samun haihuwa da namiji wanda yaci suna kabir sunan mahaifin mijinta .. bayanshi ta haifi aysha lokacin da zata yi haihuwa ta uku ne Hajiya umma ta samu ciki murna agurin wannan family ba'a faɗa hajiya inna har da rawa tana cewa "Baga shi ba, ai na faɗa maka dangin juya ka auro ga masu irin haihuwa nan ka aura yanzu za'a soma cika maka gida da ya'ya, wallahi har kunya hajiya umma take ji , a zahirin gaskiya ba ita taso wa wannan cikin ba hjy mama tasowa wannan ciki amman babu yadda zatayi, al'amari Allah ne, bawa kuma bai isa yayi wa Allah shishigi ba, da dai tana da hali da ta cire cikin ta bata ko itama ta zama uwa rayuwarta ....


Two friend's (bsbs)
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~TRUE LIFE STORY~

FREE NOVEL NOT FOR SELL


AL'QALUMAN



*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*

~DEDICATED TO~
*UMMIN KADUNA INA ALFAHARI DAKE*

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim


PAGE 15

.....samun cikin hajiya ummah yasa gabad'aya hankalin alhaji Ibrahim wanda ya koma Abba bisa koyarwa hajiya mama ,ya kartata gurin hajiya Ummu , wannan abu ya damu hajiya mama matukar kuma abun ya tsaya mata a rai amman ta share taki nuna hakan ko a saman labbenta ta kawo ido ta saka ta sake nisanta kanta dasu tunda daman inna bata son kusancinsu da umma ,a bangaren hajiya umma kuwa babu wani sauyi tana nan kamar yadda suke ada , domin lokacin data lura hajiya mama ta d'auke kafafunta daga bangarenta ,ita bata yi hakan ba ,musamman take zuwa bangarenta su sha hira, ita kam tana tausaya mata sosai " da me zataji da rashin haihuwa ko kuma da damuwar hajiya inna da saudat?
Lokacin da hajiya inna ta lura da shige da ficen hajiya umma yayi yawa bangaren mama, ta dirke sabon bala'i iri iri "tana gudunki dan bakinciki amman kina shishige mata , bari garin neman suna kije ɗan cikin da kika samu a bar miki dashi , agumawa da asiri da bakin kishin tsiya babu abinda baza su iya yi akan kishiya , ke mutun nawa kika ga anyiwa kishiya acikin agumawa an zauna lafiya?
" mutanen da har tsafi suke akan abun duniya ,mutanen duk muslincinsu babu Allah aransu ke ......
"haba inna ki daina furta haka a gabanta babu dadi , wallahi bana jin dadi haka har acikin raina babu wanda ya isa ya baka ko ya kwace maka sai Allah.
"eh lallai wuyanki ya isa yanka fatimatu yau ni nake faɗa kina faɗa akan wannan diyar masu yin su.....?

"Koda yake ba laifinki bane ruwan azirki da kinibibi kika gani ,tunda ke naki uban talaka ne futik ,nan kuma kullum ana kawo miki toshiyar baki da siye miki zuciya daga wancan garin nasu ana baki duk abinda aka kawo mata ai dole ki dinga ganina a matsayin mahaukaciya " ko saudat da ban rike a hannunsa ba , ban ci wahalarta ta sisin kwabo ba , tana bin umarnina tana son abinda nake so ,ai kuwa sai Allah yayi mata albarka ita da ya'yanta .

"kiyi hakuri inna bana nufi na bata miki rai "ki min shiru idan na sake ganin kin tako waɗan tsilla tsillan kafafunki d'akinta sai na tsine miki albarka , ko da ban haifeki ba , naci kashinki kuma sai tsinuwata tayi tasiri akanki maza ki wuce bangarenki shasha da bata san ciwon kanta ba .....
sumi sumi hajiya umma ta fice daga d'akin zuciyarta tattare da bakinciki jikinta har

2 Comments On WANNAN CE QADDARARMU
avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment