Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

matukar kyau da sheki tamkar wanda ake fashawa madara , yayi saurin mikewa tsaye yana ƙoƙarin barin gurin bayan ya kawar da fuskarshi akan dukiyar fulaninta ,tayi saurin riko laulausan tafin hannunsa cikin nata , gabadaya ya juyo zai harxuko mata cikin fushi ganin tana kokarin kawo masa hauka dole tasa ya kasa aiwatar da komai , jin tafin hannunta saman fad'ad'd'en qirjishi tana shafa gashin dake kwamce a qirjinshi ..
wani irin yrrrrrrrrrr yaji a ilahirin jikinsa take wani bakinciki ya mamaye shi, kafin yayi wani abu ta shige jikinsa ta kamkameshi ajikinta haɗe da narke masa "plz marry me mar'shub I really love you ka aureni dan Allah ina sonka ba zan iya rayuwa babu kai ba marry me plz .......
"stop this nonsense bazan ta'ba iya aurenki ba wai ni sa'anki ne da zaki zo kice na aureki ...?
Ta d'ago kanta daga kirjinshi sannan ta shiga yawo da hannunta a sansar jikinshi ta jawo hannunwansa duka tana tafiya , shi kuwa tuni jikinsa ya mutu ya shiga binta har suka kawo bakin gado ta faɗa tare dashi , yayi mata runfa suna fuskantar juna ,ya bala'in tsura mata ido itama shi din take kallo hannuwanta duka a gefe da gefen fuskarshi tana shafa sumar dake kwance agurin ,a hankali ta matso da fuskarshi daidai nata har yana iya jiyo tudun dukiyar fulaninta still tana cigaba da yawo da zaran yatsun hannunta a gadon bayansa zuwa wuyansa shiru yayi yana amsar sakoninta jikinsa na wani irin tsuma ta daura lip's dinta kan lip's d'insa lumshe idanunshi yayi yana jin dadi a sansar jikinshi ....
Jin zata haɗe bakinsu yayi saurin mikewa a matukar firgice "no no I can't tunda bana sonki bazan.....
"Dan Allah ina da komai da kake sosai , da kai kadai na dace " ki daina rokon na aureki dan banzan taba aurenki ba .......
"Mah'ruf ! Mah'ruf!! Mah'ruf !!! Tashi tashi !! Wace ce take rokon ka aureta?
a matukar gigice ya farka daga dogon mafarkinsa bayan ya haɗa uwar gumi sharkaf yana fidda numfashi da kyar ,shiru yayi a matukar tsoroce yana kallon rayhan cike da mamaki fuskarsa da alamar tambaya .
"mafarki kayi Mah'ruf wacece ...?
Naunauyen ajiyar zuciya ya sauke "ni mafarki ya furta yana nuna qirjinshi?
"Yes of course mafarki kayi mai kunshe da soyayya ..
"gaskiya ni babu wani mafarki da nayi ya takaita magana jin reaction din jikinsa na sake sauyawa jijiyarsa ce ke sake shiga wani yanayin da bai taɓa experience din haka ba, ya mike tsaye ya sauko daga saman katifa yana gayara zaman boxcer dinsa sannan ya d'auki jallabiyarsa ya zira ya shiga bathorrom rayhan ya bishi da kallo ..

ya dade a cikin bayi yana saka da warwara tabbas mafarki yayi da yarinyar daya rasa tantanceta matsayinta acikin zuciyarsa ,"ya Allah ya furta a kasan zuciyarsa meke shirin faruwa dani ? "Ya Allah idan zaka jarabeni ka jarabeni gwargwadon imanina Allah karka barni haka ,karka bari yarinyar nan tayi galaba akaina
Yayi shiru yana jira daga zuciyarsa shi dai yasan ba sonta yake ba to me yasa tunaninta zai addabi rayuwarsa gashi har da dogon mafarki ,ya lumshe idanunshi " a hankali ya furta " ba komai bane dan na kwanta zuciyata da tunaninta ne ....
ya ajiye hakan a wannan muhalli dan bai son cigaba da tunaninta ..

Washe gari ya kasa fita ko'ina yana zaune akan dining table shigo da sanda hannunta rike da basket dan har lokacin a tsorace take dashi , shima kuma a kallon maci amanar yake mata ,ita abinda ke bata haushi ya rayhan bai nuna jin haushinsa dan ya ganta da hafiz ba sai shi dan shishigi .

yana lura daita a hankali take komai ,yayinda take zuciyarsa ta shiga dawo masa da abinda ya faru a mafarkinsa tun daga lokacin data zira harshenta cikin kunnenshi har zuwa sanda ta furta ya aureta i love you mar'shub tana hura masa iskan bakinta ya kasa manta moment din duk da ba wani gudunmuwa ya bata ba .
Yana kallonta ta kasan idanunshi ta ajiye basket din data shigo dashi ,har ta juya taji ya ja tsaki tasan shine da haukansa dan haka taki juyowa sai dai zuciyarta ta cika da bakinciki "fat lion ya kira sunanta cike da isa .
Tsayawa tayi cak batare data juyo ba tana sake jan tsaki a fili kamar walkiya ta ganshi agabanta sai da qirjinta yayi wani mahaukacin bugu da karfin gaske " baki isa ki amsa kiran da nayi miki bane ko me kike nufi?
Yayi maganar cikin zafin rai "gashi kuwa idanunka sun gane maka har ma da nasarar tako kafafunka zuwa inda nike da magana ne ka tsaidani?


Shiru yana dubanta tamkar ranar ya soma ganinta "tabbas mafarki ba gaskiya bane ya dade da sani ko duniya da abinda ke cikinta za'a daura mata yasan bazata taɓa cewa tana soshi ba bare ta furta masa wannan kalmar aure wani abu sai sharrin mafarki.
"Ke nan wai wani abu kikaji aranki har da wani gadarar an tako zuwa inda kike ?
"Sosai kuwa tunda har ka tako angama dan kasan bazan zo ba ,"ba laifinki bane , dana bari waɗan can ya iskan sunyi fata fata dake da baki samu bakin magana ba "ai tun lokacin nace ka mika ni garesu ko ba'ayi haka ba ?
Tayi maganar tana kallon cikin kwayar idanunshi, kallonta yake cike da takaici da bakinciki tun data tsurawa kwayar idanunta nashi idonunta jikinta ya soma bari.

rayhan dake bayi ya soma jin sautinsu yasan idan bai yi wani abu ba komai zai iya fara ya daura towel ya fito da sauri ya shiga tsakaninsu a daidai lokacin da Mahruf ya cafki tsintsiyar hannunta zai murd'e "daman kamar na sani na fito dan nasan sai ka saka min ita kuka ya kwace hannunta cikin nashi yi tafiyarki my princess ta nufi kofar fita tana jan tsaki a ranta dan bata isa ta sake yi a fili ba ..
"Kaje ka cigaba da aikinka dan Allah ka dinga hakuri Mah'ruf me ma tayi maka yanzu?
"Haushin iskancin da take maka wallahi har na fika jin haushin ganinta da wancan dan iskan dan giya , yarinyar daga wannan sai wannan kamar ....
sai bayan da yayi maganar ya fahimci yayi subul da baka saboda irin kallon da rayhan yake mishi ya shafa sumar kanshi zai koma inda ya taso yaji rayhan ya riko hannunsa "ina jin kamar ...
"Kamar me shima ya katse shi dan Allah karka k"arawa kanka damuwa dan bana son naji kana shiga damuwa da tashin hankali shine ma dalilin dayasa na kasa yin nisa da kai lafiyarka da rayuwarka ya fiyye min komai mahimmanci arayuwata ,wallahi rayhan ban san ina sonka ba sai lokacin dana ga kana ƙoƙarin barin mu plz ka daina damuwa da damuwar yarinyar nan idan ma ya zama dole sai ka damu ka barni ni nayi maka plz bana son na rasaka ya karasa maganar kamar zai yi kuka shiru rayhan yayi yana kallonsa hakan zuciyarsa ta kasa gasganta maganarsa ganin irin kallon da rayhan din yake masa yasa ya karasa gurin maganinsa ya ballo ya mika masa "sha maganinka "sau nawa zan sha ?
"Yanzu fa kabani na sha kafin na shiga bayi "my goodness am so confused "okay kaje kayi wanka ni zan karasa tura sakonin ya wuce shi ya maida magani cikin farin roba ya matso da system gabanshi ..
Zuciyar rayhan bata amince dashi ba amman haka ya koma bayi yana sake sake a ranshi ..
*****
Yau wata guda kenan da fara sitirin hafiz almustapha zuwa ga ummita da ƙoƙarin shawo hankalinta da kuma shawo hankalin iyayensa da su shige masa gaba ya auri ummita da ciwon sonta ya zame masa shamaki da dukkanin farimcikinsa ,
yayi kuka da hawayensa gwiwowinsa a kasa yana rokon mahaifinsa tare da alkwarin zai yi duk abinda suka bukace shi, akwai ranar da mahaifinsa ya sharara masa mari har guda uku bai motsa ba, ya maresa ne akan ya tashi agabansa amman ko gezau bai yi ba ya kudurce a ransa gara ya rasa ranshi a gabansu daya tafi titi ciwon son ummita ya kasheshi ..
anan iyayensa suka barshi yana surutai ..

Ta bangaren ummita babu sausauci domin ko yaje baya samun ganinta sai daya yi tsawon wata guda yana zariya babu wani cigaba daya samu akan hanyarsa ta dawowa gida hawaye bai yanke a idanunshi ba ...bai daddara ba ya sake dawowa mahaifinsa "dady ka bawa hajiya hakuri "tace kyale mara kunya zuwa yayi ya nuna min ban isa da shi ba kasan Allah ko zaka mutu mahfuza zaka aura da wannan halin naka wa zai baka auren diyarsa ?
"Soyayyar yarinyar ce ya jawo silar komai hajiya wallahi akan sonta na fara shaye shaye saboda ta hanani kusantar inda take amman Wallahi nayi alkwarin daga ranar da aka mallaka min ita a matsayin matata zan daina shan komai na dawo kamar yadda kuke bukata ......
Basu ce masa komai ba suka zuba masa ido kawai ..

*****

Misalin qarfe tara na dare Abba da mama suna zaune a parlour'nsa suna ɗan tattauna wa cike da damuwa ,Abba ya dan waiga ya kalli mama yana cewa " Mah'ruf fa kwana uku kenan ban ganshi ba sai dai yana kirani a waya da zarar mun gaisa zai katse abun fa na damuna sosai ya qarasa mgnar cikin damuwa .

Mama ta sauke naunayen ajiyar zuciya cikin sanyi tace "wlh ni ma yau kwana biyu kenan ban sanyashi a idanuna ba sai dai kullum zai kirani mu gaisa nima .
Haka shima rayhan bai shigo ba kuma dukkansu ko abinci yadda aka kai musu haka za,a d'auko ..
Abba ya jinjina Kanshi ya zaro wayarsa number dan gaban goshinsa ya soma kira yana d'agawa ko gaisuwarsa bai tsaya amsabawa ba yace "idan kana gidan kuzo yanzu kai da rayhan ,mahruf ya amsa da sauri tare da katse kiran .

Ya kalli rayhan da suke tare amman shi yana zaune akan daddumar sallah ya jingina bayanshi da bango daki rike da Alqur'ani mai girma yana karatu sai dai kuma idonsa a lumshe yana ta rera karatun cikin zakakkiyar sautin da Allah ya hore masa murya mai dadi sauraro ,ya iya bawa baki hakinsa wanda haka abinda mah'ruf ya lura dashi tun bayyanar ciwonsa ya sake kasance wa shiru da yawonsa son ibada sai ya kwana ya yini akan abu daya saɓanin da ..
Ahankali yayi masa magana sai dai bai jiba saboda zurfin da yayi ciki karatu sai da ya qarasa
In da yake ..
"Abba fa na kiranmu , saurin bude idanunshi yayi yana duban Mah'ruf cikin wani iri. yanayin na tuhuma da fargaba"lafiya dai ko ?
ganin yadda ya koma a lokaci daya yasa cikin qarfin hali mah'ruf ya dan murmusa yace "kai bafa komai lfy ya fada a lokacin da ya mike tsaye ba dan ya yarda ba yace" toh shikenan Allah yasa lfy.
Tare suka fito Suna tafiya a hankali cikin natsuwa suka yi sallama tare da shigowa cikin girmamawa .
Abba ya d'ago bayan ya amsa sallamarsu suka zauna inda Abba ya nuna masu kusa dashi a kan carpet yayinda abba har lokacin yana zaune kan kujera, shiru sukayi tare da zubawa abba ido kowanensu zuciyarsa na dokawa mama ce ta fara mgn cikin kaduwa tace" " rayhan ba dai jikin bane naganka wani iri ?
"a,a Mama naji sauki sosai babu abinda ke damuna Ya bata amsa ..
Cikin damuwa tace "ni dai kayiwa Allah kabi dokokin doctor husain , "abba kalli yadda yaron nan ya zama an yi magana yace lafiyarsa baya damuwa yanzu wa zai kalleshi yace baya cikin damuwa ? Kai baba kana kula dashi da shan maganinsa kuwa ?
"Sosai mama yana shan maganinsa yadda likita ya tsara "to me yasa idan an aiko muku da abinci bakwaci yadda aka kai haka ake dawo wa dashi ?
"Abinda yasa shi rayhan ba komai likitoci suka yarda yaci ba amman ina kokarin samo masa abinda ake son ya dinga ci, ni kuma azumi nayi shekaranjiya Monday ,
sauran kwanaki kuma a gidansu jafar nake cin abinci ..
Abba ya zuba musu ido tare da dafa kan rayhan dan shine abun tausayi a yanzu Yace" rayhan ka tausayawa mana ina jin babu dadi a tun sanda nasan matsalarka sannan kullun cikin tunanin nake me ye matsalarka ?
"Ka faɗa min wallahi matsawar ina da halinshi zan maka ko mah'ruf kasan danuwarshi ?
Yayi saurin girgiza kai ",ai Abba idan ma yana da damuwa damuwar ai ta kau "kenan dai kasan damuwarsa ?
Mah'ruf ya shafa kwyarsa yana son yin magana rayhan ya katse shi "Abba babu wata damuwa idan kuma ina daita a halin yanzu na rantsewa wanda ke busa min numfashi kai zan fara nasarwa saboda kai ne mahaifina ....
Abba ya jinjina kai yana kallonsu sannan yace "Allah yasa kai fa Mah'ruf meye damuwarka da kayi dan wuya cikin razana da buguwar zuciyar ya sake d'agowa yana duban Abba "wa ni ?
"Um amm babu komai Abba babu abinda ke damuna "ya ga damuwa ina hangowa atattare da kai amman kuna son boye min, a hankali zuciyarsa ta tsananta dokawa zufa ya fara keto masa har cikin tsokar dake makale da zuciyarsa "kayi shiru kana kallona tambayarka nayi ba kallona nace kayi ba ,jarumta ya sanyawa jikinsa cike da karfin hali ya dubi mama shima Abba mama ya kalla da tayi shiru tana dubansa "ko kinsa abinda ke damunsa ne ?
"Uhnmmm mama ta sauke ajiyar zuciya ina na sani ,in da na sani ai da tuni nayi maganin abun kafin ka fargaba ,oho ta saurin katse maganarta kana tace " damuwarsa daya ce nasani na batun aurensa daya fadamin cewar shi fa idan an kara lokaci zai fasa ko ba haka kace ba ..?
Zufa ta sake keto masa ya dinga jin wani abu har cikin ƙwaƙwalwarsa
Abba yayi murmushin irin nasu na manya sannan ya cigaba da nazarinsa kafin daga baya ya cigaba da magana "ai kuwa dole za'a kara lokaci dan tuni mahaifinta ya kira ya nemi alfarma ,alfarma kuwa ko alahiri wani nacin na wani ...
Wata matsananciyar kunya ce ta kamashi ya sunkuyar da kanshi "shifa ba da wata manufa ya fadi haka ba ,gashi babu halin da zai karyata maganar mama tunda yasan ya faɗa, ko ma bai faɗa ba mama tace ai dole ya amsa ya faɗa ...
"Magana Abba ya cigaba da yi mai shiga jiki daga karshe ya dubi rayhan "yanzu tunda bikinka dana malik za'a yi sai ku tautauna duk abinda kuke so kuyi min magana gurin zama tuni an kammala kuje ku gani har kai baba duk abinda bai yi muku ba ku faɗa kuje Allah yayi muku albarka "ameen Abba suka amsa tare da mikewa suka fice daga parlour'n ..

***
Lamarin hafiz ya soma zama tamkar hauka dan yadda Abba ya sanarwa muhd Sa'id haka ya fito suka gana dashi ya kuma yi masa bayanin komai ,ko Muhd Sa'id daya samu labarin yayi matukar gigita haɗe da tausaya masa ,sai ma yaga shi ba son ummita yayi ba ga wanda yafi shi hauka akanta tunda zai iya kashe tsawon lokaci yana zaune a kofar gidansu tun safe idan yazo baya wucewa sai dare yake tafiya ganin haka yasa kanin mahaifinsa yazo gurin mahaifinsa cikin hikimar da Allah ya hore masa ya fara tunatar dashi yadda manzon Allah ya zauna da sahaibansa ya muamulantu dasu da kyakkyawar muamula har yahudawa da kiristoci ya kyautata musu ya jawosu gareshi ta hanyar tausayi da rashin kyama baya danne halin kowa bai yarda a danne hakin wani ba ya nuna dimbin tausayi akan alarinsu hakan yasa Muslunci daukaka.
komai yana son siyasa da siyasa Annabi ya yaki kafirai ina ma ace zamuyi koyi dashi mu daina kyamarmu dawo dasu bisa hanya mu jawosu jikinmu da muci ribar hadisin da Manzon Allah yace "ka shiryar da mutun daya yafi kaba da kyautar rakuma dari a Muslunci bayan gana dogon sharhin daya daure jijiyoyin jikin Alhaji almustapha ya gabatar da bukatar hafiz ta son auren ummita ,yarinyar ba kyamata bace abar son haɗa zuria ce ko wani kyakkyawan halakata da yaronmu hafiz ,kai ni mahaifiyarsa mun san yana da boyayyen halin dayasa dole za'a kyamacesa idan su iyayen yarinyar basu kyamacesa ba ku me zai sa kuke shige masa gaba a wakilla aurenta ya zamo shiriyar komai agaremu ..

naunauyen ajiyar zuciya Alhaji almustapha ya sauke "daman ba daga ni bane daga mahaifiyarsa ce tun farko tayi masa mata sannan ga yanayinsa wa zai bashi aure da wannan halin ..?
"Karka ce haka yaya mu gwada sa'ar mu shi kanshi yaron zai fahimci kokarinmu akan lamarinsa sannan zai iya haɗawa da mahfuza ya aurensu duka .

"Shikenan mu'azzam tun da kana ganin babu wata matsala duk wannan bazai gagara ba sai aura masa duka ,zamu koda ba zasu bashi ba gara yasan laifin daga gare su ne nan suka saka ranar da zasu ga iyayen ummita
Fuskokinsu cike da annuri suka rabu da kaunar juna, tun daga kasan zuciyarsa wani haske da sanyi ya taso masa har zuwa fuskarshi murnarshi ta kasa boyuwa "na gode na gode sosai Abba "bana bukatar godiyarka ka sani darajar d'an'uwana kaci kuma zan yi komai domin Allah duk inda mutun yake halinsa na gari shine jagoransa ba lallai ace basu san halinka ba shiyasa ma kaga mun dage akan ka auri mahfuza saboda ita ba za'a tsaya duba wata nasaba ko halaiyenka ba tashi kaje kayi addu'ar samun nasara ..

"Yau rana ta za me masa farar rana domin cikin Sa'a a bude ya samu get din gidan batare da wani fargaba ba ko tunanin wani abu ba ya tura hancin motarsa cikin gidan yana yin parking da meenal yaci soma cin karo ya isa har inda take tsaye tare da saurayinta abdulshakur shigowarsa ne ya dakatar da hirar da suke "Assalamu alaikum hafiz ya faɗa yana mikawa Abdul hannu sukayi musabaha sannan ya mai da kallonsa ga meenal wacce ta haɗe rai tana kallonsa cike da mamakin girman nacinsa, kwata kwata kamar mara zuciya ,tundaga sakoninsa dayake aiko mata daga wáta uwa duniya da irin tarbar da akayi masa ya kamata ya fahimci ba'a sonshi amman dan naci ya nace "Barka da War haka ameena ,"kamar ganina yasa kin kasa magana kina mamakin shigowata ko ?
Ta ta'be baki "gaskiya kam ina mamakin naci irin naka da rashin aikin yi ,"ke ni duk ajin da kika sakani zan iya shiga matukar akan subai'a ne sai lokacin Abdul ya ɗan saki ranshi dan a tunaninsa ko gurinta yazo ..
"Ina masoyiyarta ?
"Tana nan lafiya sai dai a halin yanzu bata da lokacin kowa sai na mijin da zata aura ..ya ji tamkar ya makure mata wuya amman tunanin da yayi a gidansu yake ya share yace "da dai zaki taimaka kiyi min afuwa ki kira min ita ko ganinta ne nayi na samu natsuwa, ko kuwa abokina?
ya kalli Abdul wanda shima su yake kallo "haka ne meenal ki agaji abokina a kira masa anty ko ya samu ishashen natsuwa ..
"Bafa zata fito ba ku bama ta nan bata gidan gbdy , suka bi idanu suna kallonta "karya biyu alokaci daya ?
",Uhnmmm kuna kallona da tuhumar nayi kariyar ? tayi maganar tana shirin barin gurin a zuciye sai ga ummita ta fito ta karaso har inda meenal take saboda bata lura da wanda yake tsaye kusa da Abdul ba tunaninta ko abokinsa ne ya rakosa har tazo daf dasu Abdul ne ya soma magana "sannu da fitowa auntynmu ...
" sannuku kanina ta ɗauke kanta dan gane wanda suke tare ta wuce da sauri hafiz ya sha gabanta shima Abdul ya mike "antinmu irin haka bai dace ba Kinga meenal taso mu basu guri ,jiki a mace ta bishi da tayi niyyar tayi wucewarta sai kuma ta fasa ta tuna wani abu hakan yasa ta tsaya fuskar hafiz washe yaji sanyi har cikin zuciyarsa rabon da yaji dadin zuciyarsa tun sanda ya duro kasar haka nan rabon shi da abinci mai nauyi tunda da ita da mahaifinta suka sanar masa bazai sameta ba ",abar Sona sannu da zuwa ta daga masa hannu fuskarta cike da biyayya saboda darajar koyar daita da yayi "dan Allah malam kayi hakuri ziyarar ta kare daga yau dan lokacinka kake batawa ...
Soyayya halitta ce hafiz,tun farkon tafiyar nayi tunanin ka fahimci haka ,hafiz bana so...
Yayi saurin rufe mata baki da hannunsa "Ni kuma ina sonki fiyye da yadda nake son kaina cikin fushi ta buge hannunsa ta wuce ta barshi ..
Sun fi sati daga Mah'ruf har ummita da mama da meenal istahara suke ta neman zabin Allah game da al'amarin da ya zame musu tamkar gobara daga teku .
Sosai suka tsananta addu'a dan neman zabin Allah..

Mahaifin hafiz da kanin mahaifinsa mu'azzam sunje ga iyayen ummita anyi musu tabar mutunci sai dai sunce a daka an rigada anyiwa ita yarinyar miji ,wanda ikon Allah ne kawai zai iya juyar da al'amarin, tashin hankali wanda ba'a saka masa rana haka suka taso kamar waɗan da kwai ya fashewa a ciki ,jikin mahaifin hafiz yayi sanyi a lokacin da zasu wuce suka hadu da ummita ta dawo daga islamiyya kamalar yarinyar da natsuwar uwa uba kokarinta ta cancanci ayi komai

2 Comments On WANNAN CE QADDARARMU
avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment