Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

, aunty Aysha ta kalli ummita tace "kema fa da kin tare da za'a iya cewa kina da ciki dan gbdy yanayinki ya sauya "ummita tayi murmushi "kai aunty cikin lafiya wallahi zazzabin dare ne yasani gaba zata sake yin magana hajiya inna ta buɗe kofa da karfi ta shigo sai da suka firgita tare da canza hira zuwa wata , ta kallesu shekeke "ina fatima ?
"Ta tafi koyon sallama... Ummita ta bata amsa da haka tana kallon wani bangaren cike da jin haushi sam ba zaka ce maganar daga bakinta ta fito ba .

"a gidan uwarki da ubanki zanje koyon sallama shegiya mara kunya kawai duk nan ba mutane bane , basu da baki sai ke tattaciyar mara kunya ta kai hannu zata bugewa ummita baki ,ta kawar da fuskarta "ki daina zagin iyayena dan iyaye basu fi iyaye ba ,kika sake zagina zan rama ta karasa maganar tana hura hanci .....

"An zagi Iyayen naki sunci uwarsu da ubansu ki rama idan kin isa tattaciya yau kiga yadda zan sa babana ya ci min kaniyarki , ummita ta bude baki zata sake magana aunty Aysha ta take mata kafa alamun karta yi ,tayi shiru zuciyarta na tuttukin bakincikin hanata magana da aunty Aysha tayi , cikin haka mah'ruf ya shigo bakinsa ɗauke da sallama .

Gaba-daya suka haɗa baki gurin amsawa ban da ummita data amsa a ciki batare data kalli inda yake ba ya ɗan saci kallonta sannan ya maida hankalinsa ga hajiya inna dake cewa " yauwa babana naji dadin zuwanka taimaka ka gyara min zaman yarinyar nan "
"Akan wani dalili kenan zaki zo da rigimarki na rashin gaskiya "babu wani rashin gaskiya agaban takwara akayi komai ko karya ne bata zageni ba? tayi maganar tana kallon aunty Aysha dake zaune , da sauri ta girgiza kai can kuma ta kada kai ganin hajiya inna ta zaro mata ido "to kaji gaskiya yar albarka bata karya, amman ai ke karya kika yi aunty Aysha ta fadi haka a zuciyarta.

Ganin mah'ruf yaki cewa komai yasa hajiya inna ta fara zuba sambatu da zage zage , sai dai jin maganarta yake kamar shirmen saboda rashin ɗaukarsa da mahimmanci hajiya ummah dake sallah tayi sauri ta idar ta fito "menene hajiya ke dawa? me aka miki ? "Ni da wannan shugaban marasa kunyar ce, nace a mata hukunci an yi banza dani.

"kiyi hakuri su waye suka yi banza dake "waye banda wannan mai busheshen jikin shima mara mutunci dan uwanta ta nuna inda mah'ruf yake ya ɗan kalleta ta kasan idanunsa yana jan tsaki ,hajiya umma tace "Allah ya bawa mammamu hakuri zan sa ya hukunta miki ita da kaina idan ta sake "dakata ban son dogon turanci shiga ki amso min eirpiece dina da wacan bakar munafukar ta ɗauke min ,ko kuma kira min ita idan tana ciki , Hajiya umma ta kwallawa menal kira ta fito da sauri "ina eirpiece din hajiya ? Menal ta kalli hajiya inna "shine kika biyoni saboda eirpiece to ban gama amfani dashi ba idan na gama zan kawo miki..
"Kinsan Allah yanzu zaki bani dan lokacin kukan kurya ya kusa ..

mahruf ya d'ago ya watsa mata wani kallo mai haɗe da harara, da sauri ta koma ta dauko ta mika mata "gashi shikenan ko da wani abu ?"tambayi uwarki ta juya ta fice daga d'akin gaba-dayansu babu wanda bai sauke ajiyar zuciya ba ..

Ummita ta mike akan doguwar kujera ta kwanta tana jan tsaki sannu a hankali bacci yayi awon gaba daita har aunty Aysha ta wuce bata sani ba ,har gurin karfe hudu tana kwance mahruf yaje yayi Sallah ya dawa tana kwance lokacin babu kowa a parlou'n ya karasa inda take ya tsaya akanta yana kallonta yana cewa "iya rigima idan bakiyi tsokana ba bakya jin dadi ,ya ɗan rankwafo ya shafa fuskarta wani irin zafi ya ratsa tafin hannunsa yayi shiru "daman bata da lafiya ne ?yayiwa kansa tambayar idanunshi na kanta bakinsa ya kai cikin kunneta ya soma busa iska a ciki yana shafa gashin kanta daya bayyana adalilin zamewa da dankwalinta yayi .

hankali ta bude kyawawan idanunta tsigar jikinta na mikewa yrrrrrrrrrrrrr ganin ta bude idanunta ya motsa bakinsa "ki tashi lokacin sallah yayi ta mike zaune da kyar tana yatsina fuska "baki da lafiya ne naji jikinki yayi zafi ?"lafiyata lau haka temperature din jikina yake ,"tunda yau na saba jin dumin jikinki da zaki faɗa min haka ?tayi masa wani irin kallo mai tsayawa arai "kije kiyi sallah an jima doctor husain zai zo ya dubaki ...

Da misalin karfe takwas na dare doctor husain yazo tare suka shiga d'akinta da mah'ruf ya duba jikinta ya d'ago yana yiwa mah'ruf dake tsaye rungume da hannunsa magana " "lafiyarta lau tana dai bukatar hutu ne, babu abinda ke damunta da cikin jikinta da zarar anyi mata allura ta sha magunguna zata dawo daidai "cikin jikin wa ....?
"shiiiiiiiiiii ki kwanta ki huta docto yi mata allura doctor husain yayi mata allura ya rubuta magani mah'ruf yace " muje ko ,doctor husain ya mike zuciyarsa cike da wasi wasi "me tambayar ummita yake nufi ?"batasan tana dauke da ciki bane ko me ? mahruf ya mika masa hannu a daidai bakin kofar fita parloun suka yi sallama ya dawo d'akinta har lokacin fuskarta kunshe da mamaki "dazu aunty Aysha tace gabad'aya yanayinta ya sauya yanzu kuma ga abinda likita yace ,"to meye gaskiyar lamari ?
Ya d'auko kujera ya zauna tare da haɗe hannuwansa guri daya yana dubanta "menene duk kika wani firgice ?

Muryarta na rawa tace " naji doctor yayi batun ciki shine.... "ki share kuskure ne ,cikin jidda yake son fada dan dazu taje gurinsa ko baki san tana da ciki bane kike wa mutane wani kallo ?
tayi shiru tana daga kai "kin ci abinci ta daga masa kawai yana nan zaune har kusan awa guda , lokacin tuni bacci ya d'auketa ya mike ya daga rigarta ya sum'baci cikinta sannan ya lullu'beta da blanket ya wuce ..


a hankali aka soma shirye shiryen bikin meenal, kullum meenal sai taja ummita da maryarm rakiya tsiyayya batare da sanin Mah'ruf ba aganinta ko ya sani bazai hana ba tunda yasan hidimar bikinta ne , itama ummita batayi ƙoƙarin sanar masa ba , mutumin da ya furta baya sonka da rashin ɗaukar aurenka ba abakin komai ba hakan shine daidai dashi itama bazata damu da sai ta faɗa masa ba idan yaji haushi ya ɗauki mataki .

abinda bata sani ba abun na bala'in taba zuciyarsa duk sanda ya shigo bangaren mama bai ganta ba ko yaji ance sun fita , wanda yake da tabbacin duk waɗan da suke fita tare babu wacce ta kaita komai sai yaji kmr ya kashe kansa .

a yammacin ranar Litinin wanda yayi daidai da sauran sati daya bikin meenal ya rutsata a d'akinta dawowarsu kenan daga oshodi market tana daure da farin towel tana kokarin shiga wanka, tana ganinsa gabanta ya fadi saboda yadda ya haɗe fuska murtik ,sai dai taki nuna masa ta tsorata da ganinsa ta nufi bayi tana shiga ya biyo bayanta a fusace "dan wulakanci shine zaki shige bathroom ki barni bayan kinsan gurinki nazo ?
ta kallashe na second biyu sannan tace "muje to ka faɗa min abinda zan maka ta nufi kofar fita hannuta daya dafe da towel .

ya riko damtsen hannunta ya dawo daita gabanshi jikinta na taɓa bangon bayin yayinda towel din ke kokarin fad'uwa ta sake damkeshi da kyau "baki isa ba tunda kika bari na shigo nan, anan zanyi maganar ,numfashi ta sauke tana dubansa ya soma magana cikin zafi rai "da alamun kina son ganin fushina da baki taɓa gani irinsa ba ?
" ke ko ba kiji islamiyya ba dakikkiyar kwakwaluwarki ba zata fahimtar dake meye aure ba, yayi magana yana matsota sosai yana taɓa tsaitin brain d'insa tayi saurin ja da baya tana kamkame towel kirjinta na bugawa.

ya sake matsota sosai yana busa mata numfashinsa " duk abinda za'a yi a bikin nan karki kuskura na ga kafarki kinje ko'ina koda kuwa kofar gidan nan ne, ke har dinner kad'a naga kafarki , "karka min haka meenal baza taji dadi ba kasan matsayinta gareni bikinta guda ka hanani zuwa impossible zani ,saboda shi auren naka da kake takama dashi ,shi da babu duk daya ne agurina "okya bari kiga .... ya Kai hannunshi jikin towel din jikinta ta zaro ido waje tana sake rikewa a gigice "wai meye haka ?

"nuna miki mahaimacinsa
zanyi ya ja towel din kasa take saman dukiyar fulaninta suka bayyana , ta sake rikewa jikinta na rawa fixga daya yayiwa towel din sai ga towel din a hannusa sai ga boobs dinta dake tsaye sun bayyana saurin durkushewa kasa tayi agurin ta fashe masa da wani matsanancin kuka yayi tsaki a zuciyarsa yace " me ye sabo agurina na sha ganinsu har ma da ajiyata ?

Mikar daita tsaye yayi taki tsayawa bisa kafafunta tana ƙoƙarin boye jikinta ajikinshi wata irin razananniyar tsawa ya buga mata "ke ki tsaya mana ,take ta makale da bango jikinta na rawa tare da runtse idanunta gam , ya tsura mata ido na second biyu sannan ya kai hannunsa kan dukiyar fulaninta ya dinga zagaye nipples dinta da fingers d'insa "haka kike so ko ?
Tayi saurin girgiza masa kanta ,numfashinta na fita da kyar " karya kike abinda kika dade kina kwad'ayi kenan shiyasa kike jin haushin matata dan kinga ita kullun muna tare "
Ta buge masa hannun "I don't like what you doing to me "you must like it fatlion dan abinda nake hangowa atattare dake kenan ya cigaba da wasa da dukiyar fulaninta numfashi take fitarwa da kyar tana amsar sakoninsa masu wuyar misaltuwa jikinta na rawa "stop it plz zan mutu tayi maganar muryata na fitowa sosai yayi saurin toshe mata baki "ke meye haka kina hauka ne kike daga murya ?
Ta buge masa hannun ta kama handile din kofa zata fita ya janyota jikinshi "haka zaki fita dan baki da hankali ?
"To ka bani towel ka kama gabaka bazani koina ba ...
"Gud kin taimaki kanki ya duka ya dauko towel ya yafa mata aiko ta damke sosai ajikinta wani abu na ratsa sansar jikinta da zuciyarta ..

Tana jin motsin fitarshi ta dannawa kofar key shiru tayi tsaye tana kallon yatsun kafafunta komai nashi na daban ne tunda ya soma daura hannunsa ajikinta take jin sauyi daban daban amman na yau yafi na ko wani lokaci duk abinda zaiyi cike da jarumta yake yin shi ,har gurin sarrafa mace ba'a barshi abaya ba ,kullun sake kusanci yake samu da zuciyarta ,tunaninsa moment din da suke gudanarwa a duk lokacin da sautsayi ya gitta, nuna tsananin kishinta har zuwa abinda ya faru yanzu kasa ta soma yi tana sake damke towel " duk wannan abinda yake yi min amman yace ba so bane ?
"Idan ba so bane menene ?
Ta karasa zubewa kasa "to me yasa bazai soni ba , ko kuwa ban kai macen da zai so a duniya bane ?
"Yaso suhaima ma bare ni da nake da tabbacin nafi suhaima komai da komai , da kyar ta samu ta mike tsaye tayi wanka ta fito ta shirya ta zauna a gefen gado zuciyarta na tsananta tunaninsa da duk abubuwan daya sha shiga tsakaninsu ..

Washegari meenal ta shigo part dinsu saboda ummita zata rakata amso dinkunanta agurin manu saira , kwance ta sameta sai dai idanunta biyu tunanin Mah'ruf take , meenal ta kalleta "ya na ganki kwance baki shirya ba ko kin manta da zamuje shigon manu saira amso dinkunamu?
"Ban manta ba but kije kawai ko ki biya Maryam ta rakaki dan ni ya mah'ruf ya hanani fita ko'ina "
"Ya hanaki fita ko'ina fa kika ce ?
Ta daga mata kai "ke kuma sai kika biye masa ke da zaki tsokanoshi ta haka ne zaki dinga fahimtar felling d'insa akanki,tunda dai yace bai sonki .
"kar na farantawa na kuntata masa kinsan halinsa ke dai kawai gara nayi abinda yake so " da kyau kam gara ki dinga biye masa, shi yana can kullun makale da matasar bai ma san da rayuwarki ba shine har zaki fara bin dokarsa.
Ummita tayi shiru tare da mikewa ta zauna sosai "to yaya kike son nayi meenal har fa dinner yace Kar naje "ai kuwa rashin zuwanki dinner ni zai shafa domin ana mutane zasu fahimci rashin daukata da daraja da bakiyi ba kuma.......

"karki ce haka meenal kinsan ina sonki amman ki duba lamarin kar naje shima zaije da matarsa ya disgani cikin mutane ta k'arasa maganar kmr zatayi kuka "na yarda da batunki nasan zai aikata amma dan Allah ki taimaka kije zuwan naki ma yana da mahimmanci kawo kunnenki kiji ta mika mata tayi mata magana , a matukar firgice ummita take kallonta "kai meenal ki rufa min asiri karki sa yayi min wulakanci "dan Allah kiyi abinda nace dan so nake ki tsokanoshi , ki tsokono feeling's d'insa akanki , dan mugunta shi zaije da matarsa ke sai ya hanaki wallahi sai kinje kima shirya zuwa idan ya hanaki fita ko'ina banda dinner din bikina tana gama maganar ta mike ta bar d'akin ..

An daura auren meenal da abdulshakur lafiya aka zarce da biki
yayinda mah'ruf ke d'akinsa na gida da matarsa tun bayan dawowarsa daga daurin auren abinda ya sake sanyaya zuciyar suhaima kenan domin dinner din ma cewa yayi bazashi ba ,can ta kalleshi a firgice jin itama ya hanata zuwa, ta soma rarrashin cikin haka kiran hajiya ummah ya shigo wayarsa yana ɗauka ta rufeshi da bala'i ta inda take shiga bata nan take fita ba " ka bar yarinyar mutane tayi farinciki cikin yanuwata ka kirata yanzu ka bata umarnin zuwa idan ma baka bata izinin ba ni zan bata, idan taje dan Allah ka yankata , shasha kawai da bai san mutunci ba, ka dai cigaba da wasa da damar da Allah ya baka kaji "

Ranshi ya ɓaci sosai saboda yasan ummita ce ta had'ashi da Hajiya suhaima ta bugaci yayi mata karin bayani domin taso taji fadan hajiya dan yana kusa daita yayi mata banza , tsowon lokaci yana zaune yana juya wayar hannunsa "ka gani ko ,bansan me yasa zaka hanamu zuwa gurin dinner din nan ba , yanzu dai sai ka fara bin umarnin hajiya ta fadi haka tana kama bakinta dan kar tayi subul da baka ,mah'ruf ya kalleta yace"tashi muje gida ki shirya daga can sai mu wuce "ummita fa ?
"Tabi su suje taji dadi maganarsa sai wani shishige masa take suna zuwa gida tare suka faɗa wanka duk ransa babu dadi ita kuwa murna kamar me suna fitowa, shi ta soma shiryawa tana masa kallon soyayya sai da suka gama shirinsu tsaf sannan ya kira ummita ta ɗauka gabanta na faduwa "ki shirya kije , zaro ido tayi da saurin tana girgiza kai kamar bataji dadi abinda yace ba "wannan maganar ai mun ga mata kai ne fa kace babu inda zani ,ya fito yana waya suhaima na binshi abaya "ke ban son iskanci bayan kin fad'awa hajiya shine zakiyi wani pretending "nifa babu inda zani ku dai kuje kawai amman ni na hakura .

"kinsan Allah idan baki shirya kinje ba zaki ga rashin mutuncin da zan miki , ta sake zaro ido cikin mamaki meenal dake kusa daita ana mata daurin d'ankwali ta tambayeta da hannuta da hannu tayi mata alamar tana zuwa "kiyi shigar mutunci ba anyhow ba ki saka hijab sauran kizo yadda kika ga dama yana gama fadar haka ya kashe kiran tayi wani irin tsalle "yeeeeeeee ya yarda meenal ,Allah ya amince naje suka sa dariya har maryam da aslamiyya "ke ba dole ba ai hajiya na fad'awa suka sake sa dariya a gurguje taje tayi wanka ta fito akayi mata make up ta dauko anko dinta zata saka meenal tace "tsaya uwar gidan miskilili wani purple les mai shegen kyau ta dauko mata "wannan zaki saka ai bazaki saka kaya irin na wancar matar tasa ba ,dan shishigi itama anko family tayi kisa wannan ta rungume meenal ajikinta tana farincikin ta sanya kayan tasa English gold hannu da wuya tayi kyau sosai kowa a dakin kallonta yake takalmin ta da jakar kalar less din jikinta ne ta d'auko mayafi zata yafa meenal tace "no haka zaki zai gane kurensa ki saki jikinki kada kiji tsoronsa dan naga a dan watanin kin dawo matsoraciya ki sake ki zage ki shiga mutane kar ma ki nuna kina da aure akwai abinda nake son gani kece zaki riki hannuna zuwa mota idan muje holl still Kece zaki kai ni mazaunina , ta damka hannunta cikin nata suka fito kawayen amarya na biye dasu abaya kai tsaye harabar gidan suka nufa inda motar da zata dauki amarya take ummita tayi shiru tana wasa da yatsun hannunta ita kadai tasan yadda zuciyarta ke dokawa gabadaya wani irin tsoro ne ke tattare da zuciyarta har ma da gangar jikinta ....
Koda suka isa harabar the orange gurin ya cika da jama'a .....



TWO FRIENDS BSBD

💗💗💗💗💗💗
     WANNAN CE
   QADDARARMU
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~TRUE LIFE STORY~

FREE NOVEL NOT FOR SELL
            
      
AL'QALUMAN


*AYSHA  A BAGUDO*           
*FAIZA  HAMMADU*

~DEDICATED TO~
*AUNTY BILKISU*

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

PAGE 50

....tun  da  suka shigo  harabar   the orenge  palace    qirjin  ummita  ke   dokawa  da matsanancin  karfin gaske  meenal  dake tsaye    kusa da Abdulshakur    ta waigo  inda   take   tsaye  a bayanta   ,  kallo   ɗaya   tayi  mata ta  fahimci  halin  damuwar  da take ciki,  ta   ɗan  matso kusa  daita  sosai   ta kai bakinta  daidai  saitin  kunnenta  saboda  qarar sautin  daya  karad'e harabar  gurin    tace  "ki saki  jikinki  plz  yanayinki zai  fahimtar  da mutane tarin  damuwar  da  kike ciki ,  gashi  idan baki manta  ba  kece wacce zata  bada cikakken  tarihin  amarya,  ki karfafa  zuciyarki dan Allah   kada  ki  bari tsoron ya  mah'ruf  yayi tasiri  a zuciyarki ,kiyi kokari  kiyi  abinda zai hauka  zuciyar ya mah'ruf  dan ki   fahimci tasirinki gareshi  ,  na sanki  nasan  you can  do more than that  ,  ke din  ta daban ce acikin mata ,  matar   nuna  wa ce  sannan  ta  fita tsara   ..

   Tunda  meenal  ta soma magana  jikin ummita  ke kad'awa  kamar mazari qirjinta na cigaba da dokawar da take  tun farko   "bazan  iya  ba meenal  shi  yasa tun farko   nace karki  zabeni  amatsayin  wacce  zata  bada tarihinki"
"Idan  ban  za'beki ba  wa kike  expecting  na zaba ?
Ummita tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya ,
"kece  mafi kusanci da rayuwata , kece  kika san menal  fiyye da kowa a duniya   ,kuma  nasan zakiyi  active  mai kyau shiyasa, sannan ina son kiyi active din da zai wargaza zuciyarsa da tunaninsa.
"  ummita ...............
ta  kira sunanta  cike da kulawa  ina sonki da ya mah'ruf   bana  son  kina nisanta kanki  da shi domin shima    mijin nunawa sa'a  ne  wanda  da ana likawa  a  goshi zaki  iya likashi   karewar zuciyarki , mijinki mijin  da  zaki  yi  tinkaho dashi ne   bayan jini na yan'uwantaka  kun dace da  juna sosai   fiyye da sauran  ma'auratan  duniya  ,dukkaninku kuna wasa  da zuciyoyinku ne amman batu na soyayya  tuni    kun kamu da  matsanancin  son juna  babu wanda zai ganku  bazai fahimci haka ba  .

"wayyo  menal ba zaki fahimta  ba  amman babu wata  soyayyarsa  a ciki  zu.......
" Karki  ce   haka  a ta wannan  bangaren ,ko zaki  boyewa  kowa , bani  ya kamata  ki  boyewa ba  sannan ko rantsuwa   nayi  ba  zanyi kaffara ba akan  kuna  tsananin son  juna  ke  da ya mah'ruf  irin taku kalar soyayyar kenan , Ki d'aure  yanzu   second   game  zamu  fara  karki  sanya  ke  ko  magana wani yayi miki agurin dinner din nan  kiyi  masa  muga yadda  zai  nuna  feelings dinsa  ..
ummita  ta buɗe bakinta  da  niyyar  sake yin  magana  taji  an  bawa  ango  da  amarya umarni shiga   cikin  hall dole ta tsuke bakinta .

  a  hankali  suka jero   ango  sanye  da  wata  dakakkiyar  shadda gezner   mai   ruwan kasa , shaddar  ta sha aiki    zubi   mai  kyau  har ajikin  babbar riga, kanshi  sanye  da hula  wanda   ya  dace da kayan  jikinshi , kafarshi sanye  cikin  wani had'ad'd'en  black shoe sai  kyalli  yake ,  haka itama  amarya kalar kayan  dake jikin  ango take  sanye  dashi har kasa   sai  dai nata material  ne hannunsu sarkefe  cikin  juna  suke  ta kowa   ahankali  domin  shigowa  inda tarin  mutane  suke  zaune  , nan  take  hankali  masu  video  da   masu  ɗaukar hoto  ya karkata  garesu   a tsanake    suka shiga  d'aukarsu  , yayinda   kawayen  amarya  na   biye  dasu  abayansu   har  cikin hall  inda sautin kida  ke  tashi  nan take ango  ya  soma  rawa tare  da   amaryarsa
Masu  ɗaukar   hoto nayi  masu  video  nayi haka kawayen   amarya da abokan  ango  na d'aukarsu   a wayoyinsu da  ipad  saboda kyawun da  sukayi  mutane basu bar wayoyinsu  sun  huta daga  ɗaukar  amarya da angonta  hotuna  da video  ba har  sai da suka zauna  a mazaunin da'aka tanada domin su .

Aka  fara  bude  taro da addu'a  sannan  MC ya bukaci  abbas  babban   abokin   ango,  ya fito a  tsanake    ya soma  karanto  tarihin abdulshakur  ,makarantar da  yayi  tun daga kan kuruciyarsa  ta primary da  secondary  ,har zuwa matakin  jami'a daya kammala  a  ɗan fodio  sannan  ya  da'ura daga inda  had'uwar menal da abdulshakur  ta samo asali  ,abbas na kai wa nan  ya  juya  ya kalli abdulshakur   yace  "ya  naga  kayi  shiru  kai da amaryarka  me kuka tuna haka ?
"okay  kun  tuna ranar had'uwarku  farko ko ? "kana  tunanin  irin harara da  tsiwar  daka sha agurin yayarta ko  ? aka sa dariya ana tafi " ya sake juyowa ya fuskanci tarin jama'ar dake zaune suna kallonsa
" to  muna   murna  muna godiya  muna muku fatan alkhairi  da kuka halarci wannan biki na babban  aminina  ..

Mc  ya  amshi  lasifika a hannunsa  yana barkwanci   kana ya  soma  neman babbar kawar  amarya , tunda sautin  sunanta  ya karad'e  hall  din zuciyarta  ke rawa  hankalinta ke kara tashi ita kaɗai tasan halin da take ciki a lokaci  amman cikin  taimakon  Allah ta sanyawa  jikinta jarumta tare  da  cijewa  ta fito, a hankali  take  bada step  zuciyarta  na 

2 Comments On WANNAN CE QADDARARMU
avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment