Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lamo akan katifa zuciyarta cike da tunaninsa iri iri "ta rasa wannan bala'in, yana jin tsoron matarsa tasan yana gurinta "a'a ummita bai kamata ki yanke wannan hukuncin ba sau nawa yana ɗaukar a wayarta akan idanunki, dan yau bai ɗauka ba sai ki qalubalancesa?

"To ai ya kamata ya fahimtar daita yana gurinta , shine abinda yafi bukata bayan ta janyo hankalinsa tasan ya kasance daita , tayi shiru tana runtse idanunta tana tafiyar tafukan hannunsa a jikinta da cikinta zuwa mararta " wayyohlly Allah yasan yadda ake bawa zuciya farinciki ,bana sonka amman nasan kai ne farincikina
har kusan shabiyu bata samu damar runtsawa ba , ta mike ta d'auro alwala ta shiga gabatar da nafilfili bayan ta idar ta dade zaune tana canja carbi da rokon Allah ya mallakata shi ya karkato da hankalinsa gareta ta yadda zai yanta aurensu bata san tsawon lokacin data ɗauka agurin ba sai farkawa tayi tajita ajikin mutun saurin ware idanunta tayi tana kallonsa sanye yake da jallabiya sabanin kayan dazu da suka kasance na shan iska hannunta ta kai fuskarta ta mintsina domin tabbatar da mafarki ne ko gaske zafin da taji ya ratsata ya tabbatar mata mah'ruf dinta ne kwance a jikinta bata san lokacin data matso ta kai wa bakinsa kiss ba "ya Allah bana kin wannan bawa naka haka bana tsananin son shi sai dai a yanzu ina bukatar haka ka cusa mana soyayyar junanmu idan alkhairi ne a rayuwarmu da addininmu hannunsa mai ciwo ta kamo tana dubawa gurin ya ɗan kumbura kadan da shashin kwanciyar jini kasancewarsa fari ta tashi taje ta dauko man zafi na cream ta dawo ta zauna akan katifa tana kallonsa ta bude cream din ta lakata a yatsanta hannunta ɗaya ta soma ƙoƙarin shafawa masa cikin bacci yaji rad'ad'in zafi ya bude idanunshi kaɗan ganin itace ya fixge hannunsa ya juya mata baya kallonsa tayi ta koma ta inda fuskarsa take ta riko hannun "dan Allah ki barni bacci nake ji banason damuwa plz ban dawo dan ki bani kulawa ba na dawo ne dan ki tabbatar da nafi karfin gidana sannan kema baki isa ki bani umarni nabi ba saboda kin raina wa kanki hankali ni zaki bawa umarnin na tsaya sannan ki sake cewa na tafi .. ..
"Ya isa dare ne koma ka kwanta tsaki yaja ya gyara kwancinyarsa haka nan ta kasa nisanta kanta dashi ta shige jikinsa bai ce mata komai ba ..

Bangaren mama itama a wannan lokacin tana gaban Allah tana kai masa bukatunta" ya Allah na rokeka ka kawowa yarana zaman lafiya mai daurewa albarkacin fiyayyen halitta Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama , ka sanya musu natsuwar zuciya, ya Allah ka taimakeni da taimakonka ka daidaita komai a tsakaninsu su kaunaci junansu fiyye da yadda nake gani acikin kwayar idanunsu ,ka rabusu da sharrin aljan da mutun ya Allah ka kawo karshen matsalarmu su kasance acikin inuwa daya cikin farinciki ta dade hannunta a sama tana kai kukanta da matsalolinta gurin Allah ...

Kiran sallar asuba radau acikin kunnen mah'ruf ya ɗan bude idanunsa haɗe da yin sallati tare da janye jikinsa daga na ummita ya tashi zaune yana mike shiru yayi yana jin yadda jijiyarsa ta mike itama saukowa yayi yashiga bathroom dinta ya d'auro alwala har zai fito ya koma ya karasa jikin gadon ya zauna ya kai hannunsa yana shafa fuskarta a hankali ,a hankali ta bude idanunta akan kyakkyawar fuskarsa bai yi magana ba ya mike ya fita daga dakin "miskilili kawai komai sai yayi miskilanci ta mike ta sauko ta shiga bayi ..

Daga matsalacin gidansa ya wuce kai tsaye ya nufi d'akinsa akan gadonsa ya iske suhaima ta kwance duk tahargitse hade yin wata ƙatuwar rama tsakanin jiya da yau kallo ɗaya zaka mata ka tabbatar da bata cikin haiyacinta dauriya kawai take yatsun hannunta ya riko cikin nashi yana kallonta a firgice ta bude idanunta tana ganinsa ta rushe masa da kuka "why habibi me yasa yayi saurin rungumeta ajikinsa yana shafa bayansa da zara zaran yatsun hannunsa "ki rage takurawa zuciyarki kinsan kina da matsayi a zuciyata bana son kina tada hankalinki akan abinda bai kai ya kawo ba cikin Muryar kuka tace "da gaske agurin ummita ka kwana ?
Yayi shiru ya kasa magana yana mamakinta lokuta da dama tana nuna masa bata da matsala da ummita bata d'auketa a matsayin kishiya ba amman jiya dan ya faɗa mata zai kwana gidansu ta tada hankalinta tayita masa hauka tana kuka kar yaje su haɗe da ummita "dan Allah ka faɗa min gurinta ka kwana ko kuwa wani aiki kaje ?
Zareta yayi ajikinsa ta girgiza mata kai alamun "a'a kawai a wuce gurin ta sake rungumeshi ajikinta tana sauke ajiyar zuciya "tashi kije kiyi sallah lokaci na tafiya ya sake zareta ya kwanta ta mike ta nufi d'akinta .....
Bayan tayi sallah ta dawo d'akinsa ta kwanta ajikinsa ko cikakken minti goma batayi da kwanciyar bacci ya d'auketa ....



💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~TRUE LIFE STORY~

FREE NOVEL NOT FOR SELL


AL'QALUMAN



*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*


~DEDICATED TO~



WATTPAD @HAUESH

Page 49

.... A hankali ya juyo daita tana manne ajikinsa , ha'barsa na kan kafad'arta yana shinshina kwantaccen sumar kanta mai fitar da kamshn dake tsuma zuciya zuwa wuyanta ,
tsaye yayi a tsakiyar d'akin yana kare mata kallonta ta cikin mirrow yayinda kowani part na jikinsa ke sake bud'ewa da kar'barta a cikin zuciyarsa ..

jin shirun yayi yawa yasa ta d'ago Idanunta ta kalli cikin madubi domin ganin abinda yake , take idanuwansu suka sarke cikin juna , cigaba da kallon kwayar idanun juna suka yi qirjinsu na dokawa da matsanancin karfi ,ta kasa ɗauke Idanunta acikin nashi haka shima ya saka daina kallonta "a duk lokacin da zan kasance dake ina tsintar kaina cikin natsuwa mara misaltuwa ,ko fushi nake da zarar na kalli kyakkyawar fuskarki sai naji fushina ya kau , gabad'aya ji nake bana tattare da wata damuwar da zata dakushe farincikina muddin ina tare dake , sosai ya shagala yana zance zuci yana shafa cikinta zuwa kasan mararta , ta lumshe kyawawan idanunta tare da motsa ɗan ƙaramin bakinta "kana magana ne ? yayi saurin saisaita natsuwarsa ya kashe mata idonsa ɗaya yana cigaba da shafa cikinta da bashi da alamun tasawa "abinda faru d'azu sam banji dadinsa ba ya dakata yana nazarinta tayi shiru taki cewa komai tana cigaba da sauraransa "kinyi kuskure gurin wasa da abinda yake da mutunci da daraja arayuwarki karki sake irin wannan kuskuren da gangancin dan bazan dauki kalmar sorry ko rarrashi ba ...
"Zuciyata bazata jura ana tangaliliya da aurena kiyi respecting d'insa zan ji dadi tsaki taja acikin zuciyarta ..

a hankali ya k'araso bakin gado ya kwantar daita, ya soma ƙoƙarin cire agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunsa da wayoyinsa ya ajiye saman mirrow dinta kamar ya cire kayan jikinsa sai kuma fasa , ya kwanta ajikinta yana sakin numfashi da ajiyar zuciya wanda kusan a tare suka yi , matsowa yayi kusa daita sosai batare da yayi magana ba ya manneta a jikinsa , ya d'aura hannunta saman fad'ad'd'en qirjinshi ,
yayinda hannunsa mai ciwo ke kan sumar kanta yana shafawa yana lumshe ido , sun kusan minti talatin suna kwance haka kowanensu da abinda zuciyarsa ke sakawa .
wayarsa ce tayi ƙara sharewa yayi ya cigaba da shafa sumar kanta zuwa wuyanta da gadon bayanta yana jin wani irin qaunarta na fizgarsa , wanda yake jin zai iya komai akanta .

tayi shiru tana sauke numfashi yanayinta na sake ɗaukar sauyi na daban kiran ya katse, wani ya sake shigowa amman still yaki ɗauka ganin yaki ɗauka ta buɗe idanunta ,ta tashi daga jikinsa ta kai hannunta kan mirrow ta ɗauki wayar tana dubawa sunan suhaima ta gani yana yawo akan screen din wayar ,ta janyo numfashi da kyar ta sauke haɗe da cewa "matarka ce ka ɗauka mana "i cant ...
"I can't ta maimaita fadar haka a zuciyarta a zahiri kuwa cewa tayi " ya dai tabbata kana jin tsoronta kenan ?
ya ja dogon tsaki tare da ɗan mirgina gefe ya zuba mata manya idanunshi masu narkar mata da zuciya "me yasa kike min haka? yau kika sanni da zaki dinga dangantani da kalmar tsoro? "suhaima fa matata ce......"

" naji amman kai me yasa bazaka ɗauka ka tabbatar mata da inda kake ba ?
"Babu dalili kuma karki sake min .......
"Ko kaki ko kaso ya dai tabbata kana jin tsoronta ta karashe faɗa tana matsowa gareshi ta dora lip's dinta akan nashi haɗe da busa masa numfashi yayi saurin lumshe idanunsa "idan har ka tabbatar da baka jin tsoronta ka ɗauka .......

ya sake lumshe idanunshi jikinsa a
mace ya kamota jikinsa, ta shige masa sosai tana lumshe lulu eye's dinta da son dagula masa lissafi "pick up the call ....
wani irin hot kiss ya soma bata a fuskarta yana jin soyayyarta da sha'awarta na kawowa zuciyarsa farmaki "ya mahruf ...ta kira sunansa cikin wata irin kasalalliyar murya "kasan me ake kira da soyayya ?

Ya furzar da iska yana kallon kwayar idanunta "da alamun baka sani ba ,yayi shiru yana jin wani irin sauyi a gabobin jikinsa "a soyayya akwai sadaukarwa,kyautatawa ,
tattali kaffa kaffa , yiwa zuciya abinda take so, ita zuciya ba'a takura ta a soyayya sannan ba'a hanata ta hanu ,saboda shi kanshi so idan ya bunkasa da kanshi yake bayyana kanshi ...
Tun da ta soma magana yake sauraren yadda zuciyarsa ke tsalle da jin wani dadi na ratsa sansar jikinshi da zuciyarsa , ya sake matsowa jikinta yana jin kamar ya soma lasheta daga tsakiyar kanta zuwa yatsun kafafunta. "duk abinda na lissafa babu wanda baka wa subai'a ba ,ban taɓa maka irin taimakon da ka min ba ,ka yantoni daga makiya kashi da kashi sai dai .........
Ta tsinci kanta da kasa fadar abinda take son fada ta tsuke bakinta tana kallon cikin idanunshi " you still have time ya mah'ruf life is beautiful tana gama fad'ar haka ta mirgina ta sauko , yayi saurin riko yatsunta biyu ta tsaya batare data juyo ba .

yana rike da hannunta ya sauko ya mikar daita tsaye ya tsaya a gabanta yana kallonta "ban fahimci maganarki ba ki fito kiyi min bayani abinda kike nufi dani "nothing kana iya tafiyarka sai da safe daman nice na tsaida kai yanzu kuma na sallameka sai dai daga rana mai kamar ta yau karka sake zuwa inda nake ko magana ban yarda ba matsawar bakasan yadda zaka yi da aurenka dake kaina ba ,ba na matsu da kasancewa da kai bane"no no kamar yadda kace shi aure ba abun wasa bane abun mutuntawa ne , kana da ilimi daidai gwargwado an very proud of you yayana ta wannan bangaren amman ilimin naka ya zama na ......

Yayi saurin toshe mata baki ta hanyar d'aura nashi yana zaro mata ido kafin daga baya yace "okay dan Kinga na biye miki shine zaki nemi raina min hankali har da zagin aurena ? ya karasa fadar haka yana sake kai bakinsa kan lip's dinta bata ce masa komai ba ta cire bakin daga cikin bakinta sannan ta zare hannunta ta zagayeshi ta shige bayi haɗe da murda key ta jingina bayanta da kofa tana shafa fuskarta " haba wannan wahalar har ina bazan sake yarda na kusanci inda kake ba har sai na tabbatar da soyayyata ta gama bunkasa acikin zuciyarka , nayi wa kaina alkwarin nan kusa zaka furta da bakinka ...

Jikinsa na rawa ya matso jikin kofar bayi "fatlion ki buɗe min kofa "kayi min me idan na bude , ka tafi gurin firgitacciyar matarka da kake jin tsoronta "nace ki bude min yayi maganar a tsawace "bazan buɗe ba ya ja tsaki yana juyawa ya fuskanci kofar shigowa ,ya kai hannunsa ya dafe goshinsa tare da rike kugunsa ya soma zagaye d'akin can ya sake komawa jikin kofar "ki bude dan babu inda zani anan zan kwana , tayi masa banza har minti talatin ta wuce bata fito ba , wata minti talatin ta sake wuce amman tana ciki bayi taki fitowa ganin idan har bai fita daga dakin ba zata iya kwana acikin bayi yasa ya kwashi wayoyinsa ya buɗe kofar d'akin da karfi ya fita.

Tana jin motsin buga kofarsa ta fito tana sauke numfashi ,ta kwanta lamo akan katifa zuciyarta cike da tunaninsa iri iri "ta rasa wannan bala'in, yana jin tsoron matarsa tasan yana gurinta "a'a ummita bai kamata ki yanke wannan hukuncin ba sau nawa yana ɗaukar wayarta akan idanunki, dan yau bai ɗauka ba sai ki qalubalancesa?

"To ai ya kamata ya fahimtar daita yana gurinta , shine abinda yafi bukata bayan ta janyo hankalinsa tasan ya kasance daita , tayi shiru tana runtse idanunta tana tafiyar tafukan hannunsa a jikinta da cikinta zuwa mararta " wayyohlly Allah ya san yadda ake bawa zuciya farinciki ,bana sonka amman na tabbatar kai ne farincikina har kusan shabiyu bata samu damar runtsawa ba , ta mike ta d'auro alwala ta shiga gabatar da nafilfili bayan ta idar ta dade zaune tana jan carbi da rokon Allah ya mallakata shi ya karkato da hankalinsa gareta ta yadda zai yanta aurensu, bata san tsawon lokacin data ɗauka agurin ba sai farkawa tayi tajita ajikin mutum akan bed ,saurin ware idanunta tayi tana kallonsa sanye da jallabiya sa'banin kayan d'azu da suka kasance na shan iska hannunta ta kai fuskarta ta mintsina domin tabbatar da mafarki ne ko gaske, zafin da taji ya ratsata ya tabbatar mata da mah'ruf dinta ne kwance a jikinta bata san lokacin data matso jikinsa ta kai wa bakinsa kiss "ya Allah bana kin wannan bawa naka haka bana tsananin son shi sai dai a yanzu ina bukatar haka ka cusa mana soyayyar junanmu idan alkhairi ne a rayuwarmu da addininmu hannunsa mai ciwo ta kamo tana dubawa , gurin ya ɗan kumbura kaɗan da shashin kwanciyar jini kasancewarsa fari ta tashi taje ta dauko man zafi na cream ta dawo ta zauna akan katifa tana kallonsa ta buɗe cream din ta lakata a yatsan hannunta ɗaya ta soma ƙoƙarin shafa masa cikin bacci yaji rad'ad'in zafi ya bude idanunshi kaɗan ganin itace ya fixge hannunsa ya juya mata baya kallonsa tayi ta koma ta inda ya maida fuskarsa , ta riko hannun "dan Allah ki barni bacci nake ji banason damuwa plz , ban dawo dan ki bani kulawa ba na dawo ne dan ki tabbatar da nafi karfin gidana sannan kema baki isa ki bani umarni nabi ba, saboda kin raina wa kanki hankali ni zaki bawa umarnin na tsaya ,sannan ki sake cewa na tafi .. ..?
"Ya isa dare ne dan Allah koma ka kwanta tsaki yaja ya gyara kwancinyarsa haka nan ta kasa nisanta kanta dashi ta shige jikinsa bai ce mata komai ba ..

Bangaren mama itama a wannan lokacin tana gaban Allah tana kai masa bukatunta" ya Allah na rokeka ka kawowa yarana zaman lafiya mai daurewa albarkacin fiyayyen halitta Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama , ka sanya musu natsuwar zuciya, ya Allah ka taimakeni da taimakonka ka daidaita komai a tsakaninsu su kaunaci junansu fiyye da yadda nake gani acikin kwayar idanunsu ,ka rabasu da sharrin aljan da mutun ya Allah ka kawo karshen matsalarmu su kasance acikin inuwa daya cikin farinciki ta dade hannunta a sama tana kai kukanta da matsalolinta gurin Allah ...

Kiran sallar asuba radau acikin kunnen mah'ruf ya ɗan bude idanunsa haɗe da yin sallati tare da janye jikinsa daga na ummita ya tashi zaune yana mika , shiru yayi yana jin yadda jijiyarsa ta mike itama , saukowa yayi ya shiga bathroom dinta ya d'auro alwala har zai fito ya koma ya karasa jikin gadon ya zauna ya kai hannunsa yana shafa fuskarta a hankali ,a hankali ta bude idanunta akan kyakkyawar fuskarsa bai yi magana ba ya mike ya fita daga d'akin "miskilili kawai komai sai yayi miskilanci ta mike ta sauko ta shiga bayi ..

Daga matsalacin gidansa ya wuce kai tsaye ya nufi d'akinsa akan gadonsa ya iske suhaima kwance duk ta hargitse dakin fuskarta tayi wata ƙatuwar rama tsakanin jiya da yau kallo ɗaya zaka mata ka tabbatar da bata cikin haiyacinta dauriya kawai take yatsun hannunta ya riko cikin nashi yana kallonta a firgice ta bude idanunta tana ganinsa ta rushe masa da kuka "why habibi me yasa ? yayi saurin rungumeta ajikinsa yana shafa bayanta da zara zaran yatsun hannunsa "ki rage takurawa zuciyarki kinsan kina da matsayi a zuciyata bana son kina tada hankalinki akan abinda bai kai ya kawo ba ,cikin Muryar kuka tace "dan allah ka faɗa min gaskiya agurin ummita ka kwana kamar yadda kace ?
Yayi shiru ya kasa magana yana mamakinta , lokuta da dama tana nuna masa bata da matsala da ummita,sannan bata d'auketa a matsayin kishiya ba ,amman jiya dan ya faɗa mata zai kwana gurinta ta tada hankalinta tayita masa hauka tana kukan kar yaje "dan Allah ka faɗa min gurinta ka kwana ko kuwa wani aiki kaje yi ?
Zareta yayi ajikinsa ya girgiza mata kai alamun "a'a dan kawai a wuce gurin , ta sake rungumeshi ajikinta tana sauke ajiyar zuciya "tashi kije kiyi sallah lokaci na tafiya ya sake zareta ya kwanta.

ta mike ta nufi d'akinta bayan tayi sallah ta dawo d'akinsa ta kwanta ajikinsa ko cikakken minti goma batayi da kwanciyar bacci ya d'auketa ....
Tun daga lokacin mah'ruf ya rage shigewa ummita ko ta nemi ta shige masa sai ya taka mata burki dan yaji haushin abinda tayi masa ,hakan yasa itama ta kame kanta daga kokarin shawo kansa da take, ta mikawa Allah lamarinta tare da tsananta addu'a da jiran hukunci Allah ko zaman aure dashi ko rabuwarsu .

******
Bayan wata ɗaya wanda daidai lokacin bikin meenal jikin ummita yaki dadi kullun dare da ciwon kirji da baya take kwana amman da zarar gari ya waye zata dawo normal , gabadaya ta d'ashe tayi fari sosai duk wanda yasan mai shigar ciki kallo ɗaya zai mata ya fahimci ciki gareta sai dai wani ikon Allah , Allah ya kawar da hankullan kowa daga gareta, mutane dayawa sun ga cikin ajikinta amman Allah yaki basu damar magana sai mutun ɗaya , suna zaune a parlou'n hajiya umma suna hira bikin menal da addu'ar akan Allah ya sauki jidda lafiya su sha suna basa son haihuwarta ya had'e da bikin menal

2 Comments On WANNAN CE QADDARARMU
avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment