Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jin abinda zatace
har ya shiga ,bai fi second biyu ba ya fito "ke kawo min ruwa mara sanyi , ta juya da sauri shi kuma ya koma .

ya karaso ya hawo saman gadon da take kwance ruf da ciki ya kai hannu ya birkitota gabadaya ta zube ajikinshi tana sheshekar kuka , yayi shiru hade da tsareta da idanunshi yana kallon yadda zuciyarta ke bugawa ga kuma zafin da jikinta yayi kamar garwashin wuta a hankali menal ta shigo ta ajiye ruwa , ta juya da sauri ta bar dakin tana mai tsananin jin farinciki acikin ranta saboda lura da tayi gabadayansu suna cikin matsanamcin soyayyar juna "Allah ka tabbatar da wannan al'amarin .. ....

Magani ya ballo ya rike a tafin hannunsa ya janyo robar ruwan ya bude "menene abun kuka salon ki sake rud'a jikinki kisa mutane aiki ?"oya buɗe bakinki ki sha magani "bazan iya ba idan na sha amai zanyi bai sake cewa komai ba ya zuba maganin daya ballo gabadaya cikin bakinshi ya tautauna batare da yayi kuskuren had'iyewa ba , ya dan tsiyaya ruwa bakinsa ya duko daidai fuskarta tayi saurin runtse idanunta numfashinta na sama sama kirjinshi na dokawa ya matsota sosai ya kamo fuskarta ya kai bakinsa kan lip's dinta ya bude da labbansa na kasa ya shiga tsiyaya mata maganin da fari cije hakoranta tayi amman jin ya toshe mata hanci da hancinsa babu yadda zata fitar da numfashi , ta bude bakinta babu shiri , ko ɗaya gama tsiyaya mata maganin bai zare bakinsa ba , cigaba tsotsan bakinta yayi , ya tara miyon bakinsa dake haɗe da magani ya shiga tsiyaya mata sai daya tabbatar da babu sauran magani a bakinsa sannan ya zare bakinsa.

"jikinki yayi zafi sosai ko na rage miki zafin ?
Tana jinsa tayi shiru kwantar daita yayi ya janyo blanket dinta ya lulkubeta ta runtse idanunta a tunaninta iya nan abun zai tsaya amman sai taji motsinsa, kusa daita ya dawo ya bude bargon daya lullu'beta dashi ya shige tare da janyota jikinshi ya manna bayanta da kirjinshi matsawa tayi tana sauke numfashi ,ya sake matsota ya manneta da jikinshi "malama ki tsaya taimaka miki fa zanyi ban son salo idan wani abu nake bukata nasan inda zani tunda ina matar da zata iya min komai ba sai na wahalar da kaina ba "to..to ni dai banason kana haɗa jikinka da nawa ...

" tsawa ya buga mata bata san lokacin data juyo a firgice tana fuskantar shi ba qirjinta na sama da kasa "very stupid idan abinda kike tunani kenan idan naso zanyi dake ko zaki hana ne ?
Har za tace " eh sai kuma tace "a'a jikinta na rawa , tsaki ya ja "close ur eyes and I don't want to see your ties ko wannan sheshekar ya k'arasa magana yana zare doguwar rigar jikinta yana gama cirewa yayi flinging da rigar ta saura daga ita sai pent dama bata saka bra ba , rigarsa ya cire ya da farar singlet dinsa kana ya haɗe jikinsu guri ɗaya ya rungumeta "hug me too ........
da sauri ta kamkameshi ajikinta tana sauke ajiyar zuciya, a hankali ya dinga move da hannunsa a sansar jikinta yana taimaka mata da dumin jikinshi tun tana jin tsoro ko zai mata wani abu har ta ɗan saki jikinta cikin awa ɗaya jikinta yayi normal dan haka ya maida mata rigarta shima ya maida nashi ya sauko ya lullu'beta har dare yana tare daita ya kasa barinta sai wurin 10 ya barta tare da hajiya ummah da meenal ranar kwana tayi tunani iri iri babu abinda zuciyarta bata fahimtar daita akan son shi take ba amman taki yarda, dan bata ga ta inda hakan zai faru a tsakaninsu .
Cikin ikon washegari ta tashi jikinta yayi sauki tamkar ba ita ta wuni kwance jiy ba ..


TWO FRIENDS BSBD


💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~TRUE LIFE STORY~

FREE NOVEL


AL'QALUMAN



*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*


~DEDICATED TO~
*MARYAM TIJJANI ADAM*


WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim


PAGE 44


A tsanake mah'ruf ya fito daga bathroom kugunsa d'aure da white towel yayinda hannunsa ke rike da wani ƙaramin towel pinky colour yana goge jikinsa yana tunanin ummita da baby'nsa ..

suhaima ta shigo d'akin bakinta ɗauke da sallama cikin riga da siket wadanda suka kama jikinta sosai da kyar take iya numfashi ,tana ganinsa tsaye ta k'araso garesa da sauri kamar zata shige jikinsa tana rausaya ta amshi towel din hannunsa ta cigaba da goge masa jiki ,bai ce mata komai ba ya tsurawa mirrow idanu yana kallon sansar jikinsa , yadda yake kallon kanshi ta madubi yana gyara suman Kanshi haka itama take masa wani mayataccen kallo kamar zata cinyeshi tana cigaba da goge masa sansar jikinsa "kallon fa na menene ?
Ya tambayeta yana matsa body lotion a tafukan hannunsa ta kai hannu ta shafa qirjinsa zuwa nipple's dinsa tana lumshe idanunta "dole na kalli mijina abun sona dan ni kaɗai nasan yadda nake ji akansa ta kare maganar ta soma bin jikinsa da body lotion "habibi ....
Ta Kira sunanshi tana narke murya , ya kalleta ta cikin mirrow batare daya amsa mata ba , bata damu da rashin amsawarsa ba saboda tasan halinsa .

"na matsu na ganni ɗauke da cikinka , wallahi har abun ya fara damuna kullun cikin sa rai nake amman shiru har yanzu , idanunshi na kanta har ta gama magana , ta gama shafa masa mai ta soma shiryashi cikin wani had'ad'd'en suit kalar ash colour mai kyau wanda ya fito da ainihin kyawunsa ...

"Komai ne zaki min bakya gajiya baby yayi magana yana furzar da iska ? "Komai zan maka habibi , kai ne komai nawa ,rayuwata duniyata , komai nice zan maka muddin ina raye , ina matukar sonka habibinah shiyasa nake son na haifi baby mai kama da kai sak .

shiru ya sake yi yana sauraronta tana shiryasa yana gyara inda bai mishi ba "nayi maganar baby baka ce komai ba habibi ko baka son na haifa maka baby ne ?
"Ina so mana yayi maganar atakaice, dariya tayi sosai Allah ya bamu masu albarka ya sake cewa" ameen turare ta ɗauko ta fesa masa kadan dan tasan baya son turare yayi masa yawa ya soma ƙoƙarin ɗaukar agogonsa , nan ma tayi saurin ta amsa ta d'aura masa ,ta k'arasa inda jerin takalmansa suke ta dauko masa wanda zai bi da kayansa ta dawo ta durkusa gabansa ta saka masa "na gode baby Allah yayi miki albarka "ameen habibi Allah ya bamu kyawawan baby's masu matukar kama da kai yayi murumushi wanda ya bayyana dimples d'insa "yau dai da maganar baby kika tashi well karki damu kin kusan samu ,cike da jin dadi ta manna masa kiss a lips d'insa .

"baka ta'ba faɗa min abinda ya sani farinciki naji dadi kamar wannan ba , ta ɗauki jakarsa "muje kayi break tana biye dashi abaya har dining table taja masa kujera ya zauna ta soma haɗa masa tea mai kauri ta bude plet wanda ke ɗauke da soyayyen cheaps wanda da soyayyen kwai da plantain , alhankali ta ajiye cup a gabansa ya ɗauka ya soma kur'ban tea yana kunshe ido ,tana daukar cheaps tana saka masa abaki tana jin babu abinda bazata masa ba dan yaji dadi , da anawa mutu numfashi da sujjada to wallahi da zata iya yiwa mah'ruf ...
duk wannan abinda take masa hankalinsa baya gareta ,dan Allah Allah yake ya bar gidan
ya da'ura idanunshi akan fatlion dinsa yaga yadda jikinta yayi ..

Mikewa yayi yana goge bakinsa da tissu ta dauki hijab dinta ta saka ta biyosa "Habibi ka kular min da kanka duk wacce ta kalleka ka maka mata harareta haɗe da warning dinta , "naki wayon duk wacce ta kalleni kallonta zanyi , ta 'bata rai sosai tana harararsa "ai zan ji duk wani motsinka dama duk wacce zakayi muamula ajikina saboda ina sonka fiyye da kowa ta k'arasa maganar a daidai lokacin da suka karasa jikin motarsa yana duba agogonsa yayi kyau sosai dole idan kaganshi kaji ya burgeka yace "thanks my baby with the love you have for me amman karki manta ku biyu ne a halin yanzu ta uku ma tana nan zuwa dan haka ki rage wannan son , Kai ta girgiza masa ,"babu wani son da zan rage sai ma abinda zai qaru kuma bana son Karin kowa ,in dan ma son zuciyata ne nafi son ni kadai, dan bazan iya sharing dinka da kowace mace ba , yayi murmushi tare da danna key din motar , "banda fatlion dole kiyi sharing dina daita ko ba haka ba ?
ta sake hade rai sosai a zuciyarta tace "itama an kusan rufe babinta amman zahiri cewa tayi "wannan ai kanwata ce kuma uwar gidan habibina bani da tacewa akanta ya bude mota ya shiga ya zauna ta zagaya ta ajiye masa jakarsa ta manna masa key "ka kular min da kanka plz " yayi ƙoƙarin ficewa ..

a gaugauce ya shigo haraban gidan bayan mai gadi ya bude masa tangamemen get din gidan daidai doguwar barandar da zata kai shi bangaren mama ya haɗu da hajiya inna tana ganinsa ta haɗe rai " babana kai ne da sassafe haka ?
Ya furzar da iska mai zafi daga bakinsa yana daure fuska tamkar wanda aka aikowa da sakon mutuwa yace "yanzu ne sassafe ki koma ki duba lokaci ki gani kafin kizo ki tsareni nifa banason sa ido da damuwa komai mutun zai yi idanunki na kai ya sa kai zai wuceta.

"kai dawo nan banson shakiyanci ,karya uwar me nayi karfe nawa yanzu da baza kirata da sassafe ba ? wallahi babana ka fita daga idanuna na rufe ina d'aga maka kafa ne kawai dan darajar mai sunanka ,
duk kwanakin nan fa ina lura da kai gabad'aya rawar kafafunka sunyi yawa a wancan bangaren , mai d'aki bata nan uwar me kake wa sintiri ?
"ban gane nufinki ba dan me d'aki bata nan sai kar na shiga nayi abinda zanyi ?
"Bafa nason abinda kike min ta ya zaki samun ido ...?

"an sa maka ido kayi uwar da zaka yi mara kunya kawai kuma wallahi kar na sake ganin waɗan nan tsilla tsillan kafafunka a wancan bangaren har sai mairo ta dawo daga wancan garin agumawan ..

a hankali ya ɗauke idanunshi akanta ya maida bisa hanyarsa ya bar ta nan tsaye tana 'ba'batu iri iri bai tsaya ba , bare saurarenta ko yunkuri dakatar daita daga maganganu da take ya ci-gaba da d'aga kafafunsa ..

Zuciyar mahruf a cunkushe da haushi haɗe da takaicin Inna ya shigo bangaren mama kai tsaye ya haye step ko taku uku bai yi ba sai ga hajiya inna ta shigo a hargitse "kai dakata zo ka wuce dan wallahi bazan bari ka hau saman nan ba kaji na rantse .
ya juyo a tsanake ya tsura mata idanunshi yana kallonta yana tunanin irin wulakacin da zai mata ,wani irin mugun kallo ya dinga mata mai haɗe da harara wanda yasa ita kanta hajiya inna dake tsaye jin faduwar gaba da takaicin shishigewar da yake wa mairo da
Bangarenta .
cike da jin haushi tace "daina kallona da waɗan mugayen idanun naka, hawa ne dai wallahi bazakayi ba sai idan mai d'akin ta dawo ,ganin yadda ta ɗauki zafi idan shima ya dauki zafi komai zai lalace daga ransu abba yazo ya ɓaci dan haka ya sauko daga nashi fushin , jikinsa a sanyaye ya k'araso gareta ya riko tsintsiyar hannunta ya nufi kujera daita ,ya zaunar daita shima ya ɗan dosana yana dubanta tare da riko duka hannuwanta cikin nashi "haba hajiya inna me kike tunani akaina ?
"Dan Allah zuciyarki ta daina kawo miki bad thinking akaina hakan bashi da kyau kuma bana jin dadi , sannan tsufa kike , ba'a son mutun na tsufa yana irin abubuwan da kike yi ,dan a tsufan mutun ake fahimtar kuruciyarsa ,dan girman Allah ki daina irin wadannan abubuwan kada mutane su dinga yi miki mummunar fassara, ina son ki koma ga mahalincinki zukatan mutane na cike da tsantsar kewarki da kewarki , ba ki mutu mutane na murna da jin dadi ba ....
Cike da sanyi murya da rarrashi ya kwantar da kai yana faɗa mata maganganu masu sanyi ..

"Duk na ji bayaninka , shigowar ka ne bana so dan mace da namiji idan suka hadu sai wani Allah , kar azo a yaudare min kai da salo , yadda nake jin sonka idan wani abu ya sameka zan iya mutuwa , sarai ya fahimci abinda take nufi, yayi murmushi "kai hajiya inna rikici duniya , wallahi ke hukuma ce sai da rarrashi , to ki kwantar da hankalinki babu abinda zai haɗa mahruf dinki da wannan kucakar yarinya ........
"kucaka fa kace bayan da bakinka kace kana sonta ?
"Kai haba ni fa da wasa nake miki dan kawai na baki haushi ranar , tayi murmushin jin dadi "jairi yaro kawai bani zaka bawa haushi kanka da iyayenka zaka bawa haushi "duk naji koma menene amman dan Allah ki cire wannan tunani babu abinda zai had'ani daita da kikace baki yarda ta tare ba kinji na sake magana ?
Ta girgiza masa kai " baka sake magana ba amman yanzu kayi min alkwarin babu abinda zai shiga tsakaninka daita ?
Ya lumshe mata idanunshi yana jin qirjinsa na dokawa da karfi "kayi shiru ka bude baki kamin magana kamar yadda nake maka "nayi ya faɗa atakaice . "da wa kayi alqawari "da.........
takun saukowar ummita ne ya dakatar dasu , suka maida hankalinsu gabadayan zuwa kan step , a hankali take saukowa ilahirin jikinta na kad'awa tamkar wata bishiya sanye cikin shigarta ta kullum wato doguwar riga har kasa mai zanen fulawa pich colour daga sama , a hankali qirjinta da jikinta ke kad'awa , tayi wani azaɓaɓɓen kyau farinta ya sake fitowa , ba wani kwaliya tayi ba amman idan kaganta zaka ji kamar ka sureta ka gudu ,tunda ya daura idanunshi akanta ya kasa ɗaukewa sai hadiyar miyo yake , haka ma hajiya inna dake mata wani irin kallon zuciyar na kai kawo , gabadayansu bata kalli inda suke zaune ba bare ta gaishesu ,hakan kuwa yayiwa mah'ruf dadi dan hankalin hajiya inna zai kwanta da ganin yadda tayi , yayi saurin sauke wata boyayyar ajiyar zuciya yana dauke kanshi kar ta kamashi yana kallonta "yar banza yarinya kullum ita kenan cikin bakin rai da bakin kaya kamar na mutanen farko ......
bata rufe baki ba taji sautin muryarsa a hankali cikin dodon kunnenta "to ai irin halinki gareta .
"kai babana ta fadi haka tana zaro ido waje "aikuwa dana shiga uku idan irin halin wannan yarinyar gareni .
"karki ji da wasa halinku daya daita bambancin kadan ne .
Ta ja dogon tsaki wallahi ka cuceni kuma ka 'bata min rai ,bari ma na tashi na wuce dan maganarka zata iya haddasa min ciwon kai mai tsanani a karshe hawan jini ya kamani ,ta soma ƙoƙarin mikewa ta zata fice "ya kuma zaki tafi ki barni rantsuwan fa ?
"Tana nan ban ɗauke ba idan kafi ka saneni mu karasa maganarmu ta karasa ficewa daga parloun ,yayi murmushi "hajiya inna jidalin duniya babu mai iyawa dake sai Allah daya halicceki , ya mike yabi bayan ummita daya ga shigarta kitchen ..

A bakin kitchen din yaja ya tsaya tare da rungume hannuwansa duka a kirji yayi crossing leg's dinta yana kare mata kallo yana jin wani sauyi ajikinsa , tayi kamar bata san da tsayuwarsa ba ta ɗauki abun kunna gas ta rike a hannunta tana jujjuyawa domin rasa abinda zatayi dashi , a hankali sautin muryarsa ya fito "me zakiyi bakiji abinda na faɗa miki jiya bane ?
Sai lokacin ta waigo ta dubesa zuciyarta na harbawa "me kace dan gaskiya ni na manta ta fadi tana sake ɗauke kanta , bai ce mata koma ba ya tako har inda take tsaye ya riko tsintsiyar hannunta ya fito daita ya zaunar daita " zauna na sake maimaita miki duk da nasan kina sane "likita ya hanaki aikin wahala da duk wani aiki sai dai ki zauna a girka miki kici ..

"Yanzu ki faɗa min idan wani abu kike so , ko abincin da hajiya ta kawo miki bai miki ba ?
Ta zare hannunta cikin nashi tana yatsina fuska " an ce maka wani abu zan girka , part din umma zani sai kuma naji wacan tsohuwar na sakin layi shine na ......tayi shiru ta kasa k'arasa maganar ,maganarta ta daki zuciyarsa sosai sai yaji tamkar ta kunno masa fellling's dinta ne yayi kokarin dannewa yace "shine da kika fito kikaji rana sakin layi sai kika rasa yadda zakiyi kiji gulmar sosai sai kika shiga kitchen ba ?
"An gaishe da uwar gulma , ta girgiza masa kai "Ni ..ni fa ba "shiiiiiiiiiii banason jin komai kinci abinci ko kuwa ?
"Naci tayi magana a yangance tana rausayar masa da

2 Comments On WANNAN CE QADDARARMU
avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment