Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ganin hawayenta .
" subuhanallahi ummita meke damunki haka ?
Kuka ta cigaba sosai batare da bata amsa ba "tashi ki faɗa min damuwarki matukar ina da maganin damuwarki zanyi miki mamana , ta soma kokarin kamota ta zaunar daita a bakin gado a lokacin da kukan nata ya d'an ragu sai sheshekar kuka " ki faɗa min meke damunki ?
Still shiru tayi tana kallon mama gaba-daya ta rasa abinda zata faɗa mata ..
yin duniya mama tayi da ummita ta sanar daita dalilin kukanta amman taki magana saboda ta batasan abinda zata cewa mata ba ....
mikewa mama tayi cike da damuwa "shikenan tunda ba zaki faɗa min damuwarki ba, daman kinfi son ganina cikin tashin hankali ta K'arasa maganar tana barin d'akin ..

Mama na fita ta sake fashewa da wani sabon kuka "karki yi fushi dani mama... , Allah ba wani abu bane kawai nima tsintar kaina nayi cikin wannan yanayi na zubda hawaye na rasa meke damun zuciyata duk inda na juya bana jin dadi ........
ta dade kwance akan gado tana sambatu kafin daga baya ta dawo parlourn kasa dan ta bawa mama hakuri ta kuma sanar mata da damuwarta ,amman mama ta katseta ta hanyar d'aga mata hannu "ki barshi kawai bana bukatar jin komai daga bakinki lokacin dana bukaci ji ya wuce, amman ina son ki san wani abu duk duniya nice mutun ta farko da zansa damuwarki kowani iri ne, "na sani mama kiyi hakuri zan faɗa miki "
"Ba yanzu ba ki barshi har zuwa sanda na sake nema ta wuceta ta nufi kitchen domin daura girki ta biyo kitchen din domin tayata aiki "kije ki na hutarta dake ...
A matukar tsorace ta dubi mama " fushi kikayi dani mama ?
Tayi maganar hawaye na ƙoƙarin gangaro mata "ko daya ta ya zanyi fushi da farincikina duniyata?
" ko nayi fushin ma baya wani tasiri kawai dai bana son ki wahalar da kanki har yanzu percent ce na yafe miki duniya da lahira Allah yayi rayuwarki albarka kin sha maganinki kuwa ?
Mama tayi mata tambayar tana tsareta da idanunta girgiza kai tayi alamun a'a "maza kije ki sha kinji diyar albarka ..
a hankali ta juya ta fito daga kitchen din ta K'arasa parlour ta zauna a bakin kujera shiru duk zuciyarta babu dadi duk minti sai qirjinta ya buga da matsanancin karfi ta kasa kunnuwanta ko zataji wani abu game da ma'aruf amman shiru ....

Abba ne ya shigo ya tarar daita cikin wannan halin , da sauri ta juyar da kanta gefe tana maida hawayen dake sake cccikowa a kwarnin idanunta dan kar ya fahimci halin da take ciki aikuwa ya fahimta., cike da tashin hankali Abba ya k'araso inda take zaune "ummita me ya sameki ?
"Waye ya 'bata miki rai ?
Juyowa tayi a hankali ta kalleshi zuciyarta na wani irin mahaukacin bugu , muryarta a tsarke tace " babu komai amman Abba ya hannun ya ma'aruf tun jiya har zuwa yanzu na kasa samun natsuwar zuciya ina son sanin halin da yake ciki ? Murmushi yayi yana kallonta
"Ki kwantar da hankali hannunsa yayi sauki sosai ,bai dade da fita zuwa police station ba akan case din yandaban mutanen da suka kawo miki farmaki ,basu san koni waye ba shiyasa sukayi amfani da kwarewar su suka shigo min gida , yanzu haka duk an samu nasarar kamosu duka ,sai mutun daya wanda shine ya kasance tawagar tafiyar, amman nasan da sannu za'a yi arangama dashi "
"Ki natsu ki kwantar min da hankalinki kinji ,idan ba haka zaki saka mamanki cikin fargaba ya karasa maganar yana shafa bayanta bari naga mamanki na fito .
lumshe masa fararen idanunta tayi tana sauke naunauyen ajiyar zuciya ko babu komai hankalinta ya kwanta ..
Sai dai wani abun daga hankali duk yadda ta motsa zuciyarta na makale da tunanin abinda ya faru tsakaninta da ma'aruf kwakwaluwarta ta kasa manta wannan gwagwarmayar da yayi da moment din daya gudana atsakaninsu runtse idanunta tayi sosai dan ta kawar da wannan tunanin acikin kwakwalwarta amman sai tsintar bakinsa tayi cikin nata hannunwansa duka rike da gefen fuskarta yana tsotsar bakinta da yadda ya kamkameta a jikinsa tamkar zai yi mata numfashi ,haka ta dinga feeling din abun tamkar a lokacin abun ke faruwa ,duk yadda taso tunanin ya bar kwakwaluwarta amman yaki buɗe idanunta tana kallon celling d'akinta kallonsa take lokacin daya tsurawa kwayar idanunta nashi idon yana faɗa mata bakaken kalamai da kyar ta samu bacci barowa ya ɗauke cike da tunaninsa da bai tsaya iya nan ba har mafarki tayi dashi yana kwakume daita tare da ƙoƙarin tsotsar bakinta bayan ya zuba mata manya idanunshi da kyar ta samu ta kwaci bakinta tana turo baki shi kuma yana ƙoƙarin cafko bakin ...
Tare da furta mata magana cikin rad'a acikin kunneta " kada ki hanani abinda nafi bukata arayuwata ina son shan baki ki barni na sha har sai ya isheni idan kina son zaman lafiya ki bani baki wallahi zan iya karar da rayuwata zanyi nisa da kowa akansu ya karasa maganar yana haɗe fuskarsu waje daya haɗe da cafko bakin cikin zafin nama Kiran sallahr matsalacin unguwar ne ya farkar daita ta mike cikin zafin nama sharkaf da gumi tana fidda numfashi jikinta na kyarma ....
Sosai taji jikinta ya sauya abinda bata taɓa ji kenan tun ta sowarta wannan shine karo na farko datayi mafarkin namiji a rayuwarta lalluben makunin wuta ta soma yi ta kunna tana duban jikinta duk jikinta yayi sanyi sannan pent dinta ya jike ..
ta dauki remut din ac ta kara karfinsa sannan ta ziro kafafunta kasa ta sanya silifas ta shiga zagaye dakin zuciyarta na harbawa "me zanyi ni subai'a?
"Wannan wani irin tashin hankali ne ke shirin shigo rayuwata ?
"Me ye hadina da tunanin ma'aruf har ma da mafarkins tayi shiru tare da jingina bayanta da bangon dakin numfashi take saukewa kamar wacce tayi gudun ceton rai kanta ta shiga girgizawa kafin daga baya ta nufi bathorrom tana jin wani irin feeling a gabad'aya sansar jikinta komai nata ya sake hatta yanayinta ya canza wanda hakan ke tabbatar mata da dole sai tayi wanka tsarki wanka tayi haɗe da alwala ta fito tana takaicin kanta "meye abun mafarki ?
",A ganinta bata ga abin mafarkinsa ba amma dole ne nayi gaugawan cire wannan banzar shirmen tunanin nasa acikin brain dinna , taja dogon tsaki sannan ta karasa gurin inda jallabiyar sallarta da hijabi dinta suke ta saka tare da cire towel ta mayar dashi jikin kofa sannan ta dawo ta sanya zumbulelen hijab dinta har kasa ta tada sallah ..
Bayan ta idar ma damuwa da rashin sanin madafar dafawa tayi amman ta kudire aranta dole ne ta cire wannan banzar tunani , Allah kuwa ya taimaketa tun daga lokacin bata sake dogon damuwa akan shi ba, sai dai bata jin tsanarsa kamar da sai dai fa tunanisa na nan a cikin zuciyarya ya samu babban matsuguni ..
Yan daba an samu nasarar mikasu kotu inda suka bada bayanai masu inganci da abinda ya shigar dasu gida ba wai sata zasuyi ba sunje ne da niyyar rape amman suna neman adalci agurin kotu ta sausauta musu hukunci ,kotu ta yanke musu zaman gida yari na shekara bisa batare da wani aiki mai tsanani ba saboda basu wahalar da Shari'a gurin bayar da hadin kai ba ..

bangaren ma'aruf kuwa tuni ya manta abinda ya faru hannunsa ya warke sai soyayyarsa kawai yake sha da masoyiyarsa suhaima,
ya manta da wani zance wata ummita da sakina arayuwarsa duk shima yanzu ba wai yana jin kiyayyarta ba daman kuma kiyayyar tana dalili yanzu kuma tan yiwa mama yadda ya kamata bata bata mata rai sannan tana mata aiki har sai tace taje ta huta ...
Sakina kuwa tana kan bakanta domin ta damu zuciyarta da tunanin mutumin da bai san zamanta ba arayuwarsa sau tari ko tazo gidan nemansa baya yarda ta ganshi ,haka zaliki ko kiranshi tayi a waya baya daga wayarta tunda aka saka ranar aurensu bai taba tunanin neman inda take ba, ta lumshe idanunta a zaunen da take a bakin gadonta kwakwaluwarta na tunanin neman mafuta dan dole tasan abun yi ko yin aure ko barinsa ...
Mikewa tayi ta soma zagaye dakin kafin tasoma magana ita daya "dan dole ki nemawa kanki mafita to me yakamata nayi ?
Shiru tayi tare da koma saman katifarta can ta lalubo wayarta ta soma neman layin jiddah kira daya ta ɗauka sukayi maganar minti biyu ta mike tsaye ta sauya kaya cikin rawar jiki ta fito da niyyar zuwa gidansu ma'aruf ..
Kai tsaye ɓangaren mama ..

Kwance ta ganshi akan doguwar kujera mai zaman mutun uku idanunsa a lumshe tamkar mai jin bacci amman ba bacci yake ba tunani ne kawai yake yawo cikin ƙwaƙwalwarsa na zakulo kamalan da fadawa masoyiyarsa , kunnenshi manne yake da waya yana motsa labbansa a hankali, matukar mutun ba kusa yayi da shi yake ba zai taba jin abinda yake faɗa ba, nan kuwa daddana kalaman soyayya masu dadi da tsuma zuciya yake zakulowa yana furtawa sahibarsa.. sakina ta shigo parlourn batare da tayi sallama a bayyane ba , ta la'be a bayan labulen parlourn tare da kasa kunneta duk zanttukansa da yake fadawa suhaima a hankali suke shiga kunnuwanta ,wani irin d'aci taji yana kaiwa zuciyarta ziyara tare da tuttukin bakincikin mara misaltuwa duk wani annuri dake fuskanta ya bace a saman fuskarta sai zallar bacin rai ne ya maye gurbin tare da yi mata diran makiya ... maganasar ta daki zuciyarta sannan ta wuce har cikin tsokar dake makale da zuciyarta ,take numfashinta ya soma barazanar d'aukewa sakamakon abinda kunnuwanta suke jiyo kasancewarta mai jiyo magana a duk inda akayi a hankali hawaye suka fara cicciko a idanunta "me yasa ma'aruf ya tsane ni ?
"Me yi aibuna da bazai soni ba? Tayi wa kanta tambayar hawaye na gangaro mata bisa kunci ,duk yadda taso ta danne hawayenta amman tuni ya fara zuba kan kuncinta , a hankali take fidda numfashi , shi kuwa yana sane da shigowarta hakan
ne ma yasa ya ƙara sautin muryarsa tare da canza salon hira ...tana tsaye a gun har sanda ummita ta sauko daga sama tana rausaya cikin takunta na isa da yanga da daukar hankali duk wanda ya kalleta sanye take cikin jallabiya baka har kasa da jerin stone tun daga samanta har kasa sai kyali take kanta sanye da jar hula mai flower a geffenta duk da ba wata kwalliya tayi ba hakan bai hanata kyau ba , sosai jabbaliya tabi da shape din jikinta tana gama saukowa ta tsaya jimmmmmmmm tana kallon inda yake yana jiniya yatsun kafafunsa komai nashi mai kyau uwa uba tsafta ,yana da mugun tsafta na gubawa ajarida gefen kagarshi kaɗai idan mutun ya kalla dole yaji ta burgeshi kuma dole ka yarda da tsaftarshi tana kallonsa ya lumshe da sexy eyes d'insa Yana cizan gefen lip's d'insa na sama , ta jima tsaye akanshi tana kare masa kallo wani abu na mintsini zuciyarta yayinda gefe daya kirjinta ke dokawa da sauri , shima tun saukowarta kamshin turarenta ya kaiwa hancinsa da zuciyarsa ziyara,haka nan kirjinsa ke kuguden bugawa da matsanancin karfin gaske har yana jin kamar zuciyarsa zai fito waje gaba-daya hankalinsa ya bar gurin suhaima ya koma gareta batare da tasan da hakan ba ,yana jin yadda ta kafe shi da idanunta amman yaki bude idanunshi ya cigaba da motsa bakinsa, second biyu idanunta suka dauka akanshi tana kallonsa cike da jin faduwar gaba mai tsanani ta lumshe idanunta batare da tasan tayi hakan ba sannan ta dauke Idanunta da niyyar daukar abinda ya kawo parlourn kawai idanunta ya kai ga labale shiru tayi na second biyu sannan ta karasa a hankali tare da kai hannunta ta yaye labulen sakina tagani tsaye kumcin kwance da ruwan hawaye .......
Murmushi yake ta sakar mata da sauri sakina ta goge fuskarta tana hura hancinta da bakinta "haba aunty sakina sai ki tsaya anan bazaki shigo ba tayi maganar tana riko hannunta cikin nata tamkar babu abinda ya shiga tsakaninsu duk da tasan shirinsu akan a tun ranar meenal ta fada mata komai bata saki hannunta ba sai datayi mata mazauni a kusa da kujerar da ma'aruf yake zaune "ga mazaunin ki aunty sakina bari na kawo miki ruwa " ki barshi yanzu zan wuce yanzu kuma ?
Tayi maganar tana kallon da ma'aruf yake kwance wanda yayi tamkar bai san da zaman mutane agurin ba "gaskiya ba zaki tafi yanzu batare da kin sha wani abu ba ,sakina ta yatsina fuska tana danne abinda take ji a ranta ...
Ummita ta nufi kitchen tana shiga ya mike tsam zuciyarsa na matukar zafi yana ƙoƙarin fita ta kira sunanta cikin damuwa "ma'aruf gurinka fa nazo"
Batare daya juyo ba yace "na miki me ?
Ta mike tsam ta karaso inda yake tsaye "kasan abinda zaka min ai , tayi maganar muryata na rawa.
"kasan abinda ya kawo "me gareka me yasa kake guduna fi sabilillah ?
"baka ɗaukar kirana baka zuwa gareni yau tsawon wata uku kenan da sanya ranar aurenmu amman ko sau daya baka taɓa ƙoƙarin kawo min ziyara a matsayina na matar da zaka aura ba ..
Ummita data ɗauki cikakken minti uku a kitchen ta soma k'ok'arin fitowa cak ta tsaya zuciyarta na harbawa da sansar jikinta, rike take da tire dake dauke da cup biyu da kwalin fivealive ..
"Ki daina 'batawa kanki lokaci sakina saboda zuciyar ma'aruf bata tare dake tana ga wata daban, tun farko kinsan bana da muradinki arayuwata, da zuciyata na kaunarki tun farko da bata gayyoto wani ruhin kusa daita ba, a halin yanzu kin zamo wa zuciyata annoba , idan kika nacewa aurena zaki haɗu da cuttuka zamani daban daban , zuciyarki zata buga saboda har ga Allah bana sonki ban kuma shiryawa kaina rayuwa dake ba ,ama cire batun girman dake tsakaninmu haka nan nake jin bana miki soyayya irinta aure ya juyo tare da kafeta da manya idanunshi da suka soma kadawa " idan ina sonki ,ko shekarunki sun ninka nawa zan aureki kuma nayi rayuwa dake amman bana sonki ,zan dai aureki ne saboda bazan bujerewa umarnin iyayena ba ,kisawa ranki sakina aurenki auren biyayya ne ,auren suhaimah kuma auren so ne .....
yana gama fadar hak ya furza da iska mai zafi daga bakinsa sannan ya d'aga labulen ya bar dakin itama tabi bayansa a dai-dai lokacin da ummita tayi kundinbalan fitowa daga kitchen jikinta kyarma sai dai taga wayam ba ma'aruf ba aunyi sakina, tayi shiru jikinta na ci-gaba da rawar data rasa dalili runtse idanunta tayi naganarsa na dawo mata haka nan ta tsinci zuciyar ciki abu biyu dadi da kuma haushi ,"ki sawa ranki sakina aunki aure biyayya shine abinda yayi mata dadi sosai , magana akan suhaima ne dai ya dagula mata lissafi har taji zuciyarta na barazanar d'aukewa a hankali ta juya cike da sanyi jiki ta koma kitchen ta ajiye tiren, ta maida driks cikin frigde ta dawo parlourn ta kunna kallo zauna still gabanta na faduwa fiyye da koda yaushe , sosai ta dinga jin zuciyarta na bugawa ..
Kallon take amman zuciyarta da hankalin bai kan kallon yana waje inda tafi tunanin ma'aruf da aunty sakina suke, a hankali ta mike da niyyar fita taga wainar da suke toyawa a wajen ,tana kokarin bude kofar shi kuma sai gashi ya bude da karfi tare da sanyo kai cikin rashi ya buge mata karfa ta dama kara ta saki mara sauti tayo jikinsa suka yi karo da juna batare da saninta ba , kugunta yayi saurin rikewa sannan ya tsura mata idanunshi kafin daga bisa ya runtse idanunshi da sauri saboda jin yadda tsayayyun dukiyar fulaninta suka doki kirjinshi ya rasa me zai ce mata , ita kuwa jikinta ne ya dauki rawa kamar mazari ga kuma azabar ciwon da kafarta keyi ,naunauyen ajiyar zuciya ya sauke yana buɗe idanunshi tar akanta Yana jin wani irin yanayi a jikinsa gaba-daya tsigar jikinsa sun tashi ya rasa wannan bala'i da duk sanda jikinsu zai hade sai yanayinsa ya sauya, yadda ya tsura mata ido yasa jikinta ya kama rawa tana jin tamkar ta zura aguje ne amman babu dama aikata hakan ta soma yin kasa daga jikinsa , tana jijiga kafarta shima ya biyota ya durkusa a gabanta batare da yace mata komai ba, kallonta ya sake yi a karo na sau babu adadi sannan ya kai hannunsa ya shafa kafarta inda yafi tunani ta buge, a hankali yake shafawa yana lumshe manya idanunshi yana sauke numfashi da wani irin sauri ,ita kuwa ji ta dinga yi tamkar ana zarar ranta bata ankara ba taji saukar muryarsa cikin doki dodon kunneta "me yasa baki yin komai a natse ?





TWO FRIEND'S (BSBS)

💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~TRUE LIFE STORY~

FREE NOVEL NOT FOR SELL


AL'QALUMAN



*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*


~DEDICATED TO~
*HASAN & HUSEEN ATK I REALLY APPRECIATE THE LOVE , ESPECIALLY HASAN ATK THANKS FOR YOUR CONCERN*



WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim


PAGE 26

.......jin abinda ya faɗa hankali ta d'ago idanunta zuciyarta na wani irin dokawa da sauri a daidai lokacin shima ya d'ago kanshi idanunsu suka tsarke cikin juna , wani irin abu ne ya bakunci tsokar dake makale da qirjinsu take zuciyoyinsu
suka buga a lokaci ɗaya .
Yayinda ko wani bagare na jikinsu ke sake bud'ewa da karɓar wani sako na musamman a cikin zukantansu da gangar jikinsu , ta shagwa'be masa fuskarta kamar zatayi kuka Muryarta a raunane tace "nice ma bana komai a natse ?
Tayi maganar tana rausayar da idanunta cikin nashi .
Ya d'age mata girarsa daya batare da ya sake yin magana ba, take taji wani abu ya soma d'awainiyya da ruhinta da gangar jikinta saboda har lokacin hannunsa na kan gwaiwar kafarta wanda bai tsaya iya nan ba har tafin kafarta take jin saukar hannunsa , shima wani irin sanyi ya dinga jin yana bin sansar jikinsa , gaba-daya ya rasa me yasa yake biye mata , gashi dai zuciyarsa so take ya barta ya ɗauki abinda ya dawo dashi parlour'n amman ya kasa barinta , da kyar ummita ta samu ta janye kafarta daga garesa dan har lokacin shafa gurin yake gashi ita bazata iya jurarar abinda take jin yana mata yawo a sansar jikinta ba ..

A hankali ta soma dingisa kafarta tana tafiya cike da jin haushi , muryarta raunane tace "ban san ranar da zaka fadi wani abun alkhairi akaina ba , kullun ni mai laifi ce agurinka alhalin yanzu na daina komai ta k'arasa maganar kwalla na shirin zubo mata ..
tsirawa bayanta manya idanunshi yayi yana kallonta duk da bai kalli fuskarta ba yasan hawayenta ne ke shirin tsiyoyo kufce mata .
cike da shaukin da yayi wa zuciyarsa tsinka ya mike yana girgiza mata kai " babu wannan ranar ya faɗa tare da d'aga zara zaran yatsun kafafunsa ya nufi hanyar sama ,ta samu guri ta zauna akan kujerar mutun ɗaya tana danne zuciyarta haɗe da maida hawayenta , dan tasan ko kukan jini zatayi bazai yi abinda take buƙata daga gareshi ba hasalima bashi da lokacinta bare lokacin wani kukanta , tana zaune tana cika tana batsewa da hura hanci ya dawo parlour'n hannunsa rike da kwalban man aboniki ya isa gabanta ya durkusa a daidai kafafunta , shiru yayi tare da tsurawa yatsun kafafunta ido masu matukar kyar sannan ajere da juna

2 Comments On WANNAN CE QADDARARMU
avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment