Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yace "kiyi shiru fa ki daina kukan nan zasu iya jiyoki ....

Two friend's ( bsbs)

💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~TRUE LIFE STORY~

FREE NOVEL NOT FOR SELL


AL'QALUMAN



*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*


~DEDICATED TO~
FAIZA IBRAHIM (FAEEZATION) WANNAN SHAFI NAKI ,
KINA MATUKAR BURGENI TUN BAN SANKI BA HAR ZUWA YANZU DANA NASANKI ,NASAN DA TUN FARKO ANA SAMU READ'S IRINKI DA WRITER'S DA DAMA BASU MAYAR DA LITTAFFANSU NA KUDI BA ,SBD MAJORITY RASHIN CMMT NE YASA WRITER'S DA YAWA SUKA MAI DA LITATTAFANSU NA KUDI,KINA ƘOƘARIN SOSAI GURIN COMMET, KINA BAWA CMMT HAKKIN SHI YADDA YA KMT, ZANYI BOOK NA KUDI GUDA UKU BAYAN NA KAMMALA WANNAN CE QADDARARMU ,KINA ƊAYA DAGA CIKIN WAƊAN DA ZASU KARANTA BOOK DINA NA KUDI KYAUTA..........

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim


PAGE 23

...Jikinta na wani irin kyarma ta kamkameshi a jikinta , tsoro da matsanancin firgici ne ya sake bayyana a ilahirin jikinta, qirjinta ke dokawa da matsanancin sauri , yayinda wasu sabbin hawaye ke zubowa da daga kwarmin idanunta ,muryar ta can kasa wanda ke nuna tsoronta a fili tace "tsoro nake ji ya ... ........
sai kuma tayi shiru ta kasa cigaba da maganar , idanunshi ya tsura mata yana jiran yaji abinda zata ce "uhmmmm ina jinki what nonsense are you trying to say ?
Yayi maganar yana jan ƙaramin tsaki cikin yanayi na damuwa tace
"dan girman Allah ka daukeni daga gurin nan zuciyata tana daf da bugawa ta K'arasa maganar tana runtse idanunta tare da manne fuskarta da kirjinshi
fuskarta ya d'ago ya sanya kwayar idanunshi cikin nata yana kallon cikin kwayar idanunta, eye's to eye's suke kallon juna, kallo É—aya yayi mata ya fahimci tsantsar tsoron dake tattare da ita ,yayinda shi kuwa babu wata alamar tsoro ko fargaba a cikin kwayar idanunshi da gangar jikinsa .
wayar sa ce ta dauki sautin vibration sharewa yayi saboda yasan ba zai wuce suhaima bace , sake manne ta yayi a faffad'an qirjinsa dake kwance luf da gargasa haÉ—e da shafa suman kanta zuwa bayanta da zara zaran yatsun hannunsa dake kwance da gashi a saman kowane yatsa .
sake lafewa tayi a jikinsa wanda ya sake É—aukar kyarma a lokacin data soma jin takun mutanen data yiwa lakabi da mala'iku duniya "wayyoh Allah yaya gasu nan zuwa ta K'arasa fadar haka jikinta na rawa kamar mazari ,a gaugau ce ya toshe bakinta da hannunsa sannan yayi saurin juyo da ita ya koma da ita yadda take da farko da yi mata rumfa da faffadan kirjinshi har sanda mutum É—aya ya gilma su batare daya gansu ba ,mai gadi kuwa tun farko shigowarsu ya fahimci yan fashi ne ya tura kanshi a karkashin gadonsa yana kirma da kiran haiyalan salat da haiyalal falad ..

A qalla sun ɗauki kusan minti goma sha biyar tsaye a gurin ƙwaƙwalwar ma'aruf na tunanin abinda ya kamata yayi ,can kamar ance ya kalli inda ya ɗora kafar shi daya,
É—an hasken da yake gurin ya tabbatar masa da breaking tiles ne zube acikin buhuhunan bako, naunauyen ajiyar zuciya ya sauke da matsanancin karfin gaske sannan yace "ki tsaya anan babu abinda zai same ke
ki bari naji da wannan , yana gama fadar haka ya kai hannuwansa duka kan nata dake zagaye da qugunsa saurin riko hannunsa duka tayi tana girgiza masa kai alamun kada ya barta .

shiru ya sake yi haɗe da tsura mata idanunsa ,duk da hasken gurin bai wadatu sosai ba hakan bai hana shi fahimtar matsanancin tsoron dake tattare da ita ba muryarshi can kasa sosai yace "a she ke din ƙaramar rigimammiya ce ?
"Ina rashin kunyar da kike takama dashi yake ?
" Yau ina son ganin wannan jarumtar da kike takama da ita nuna min ina son gani," ina karfin hali da dakiyar zuciyarki ya tafi ?
"Ki dinga wasu abubuwa na gadara da jijji da kai kamar wata jinin saurata ko wata diyar governor ko wani mashahurin malami ki bani amsa ina sauraron ki ?
Tsit kake jin ummita babu bakin magana illa sake lafewa data yi hawayenta na tsiyaya a cikin gashin dake kwance a qirjinsa , idan kika sake rike ni zan
miqaki garesu suyi yadda suke so dake , dan da alamun gurin ki kaÉ—ai suka zo su kwashi gara, ya fad'i haka ne saboda wasu alamomin daya karanta tattare da mutanan da suka shigo da kuma kalma daya da ta fito daga bakin daya daga cikin mutanan wanda ya ji an kira shi da oga ya samu kyakkyawan mazauni a zuciyar sa "zaki ku tsaya a nan ni da damusa zamu haura saman mu sauko da ita, wannan kalmar da yaji itace tasa ya fahimci abinda ya kawo su gidan, ba sata ba, ba kuma wani abun ba , ita din ce dai silar zuwansu.
jin furincinsa dake shiga cikin kwakalwarta yasa ta sake shiga wani sabon tashin hankali, a hankali ta soma yin kasa daga jikin sa kaÉ—an ya rage bata zame kan tiles din da kafarshi daya ke kai ba yayi saurin taro ta jikinshi batare da yasan lokacin da yayi hakan ba, ya tsaya da ita bisa kafafunsa .....
Cikin daga murya ta soma magana tana tura kirjinsa da hannuwanta duka "Ka rabu dani ka mika ni garesu kawai suyi duk yadda suke so dani , daman na gaji da duniyar da abinda ke cikinta, gara kawai na mutu da rayuwar kuncin da zanyi gaba , idan ka mika ni garesu kace su kashe ni gaba-daya dan ..... .....
"shiiiiiiiiiii yayi saurin d'aura yatsan shi akan lip's dinta "ki yiwa mutane shiru ko kina hauka ne da kike É—aga wa mutane murya haka ?
"You better keep ur mouth short ance miki wadan nan mutanen irin mu ne da kika raina ?
"WaÉ—an nan zasuyi kaca kaca dake ne , su kuma barki bayan sun yi useless dake
as ending ki rayu cikin kunci ,dan haka ki rufewa mutane wannan banzar bakin naki ya K'arasa maganar tare da dukawa ya zaro breaking tiles guda biyu a haɗe ya cilla gefen hagunsa inda yaga wulgawar mutun tare da juyowa " wata irin razananniyar ƙara ya karad'e harabar gidan Zaki ya dafe kanshi jikinsa na bari " oga da alamun yarinyar tana wancan bangaren kuyi maza ku duba ...
muryar ma'aruf a dake sannan cike da dakiyar zuciya yace " ki tsaya anan idan kuma kika kuskurewa maganata duk abinda ya same ki ba zai zama damuwa ta ba ....
Yana magana ya sake zaro wasu breaking tiles batare daya kalli inda take ba ,ita kuwa jikinta ne ya kama rawar tayi saurin durkushewa agurin haÉ—e da kamkame jikinta guri É—aya .

shi kuwa Ma'aruf inda yaji sautin maganar su ya sake cilla tiles cikin Sa'a ya sake samun zaki a daidai saitin kirjin shi take yayi kasa luuuuuuuu ya zube warwars yana fidda numfashi da kyar , nan fa hankalin sauran yan daba yayi mugun tashi amman still zaki magana yake ....
damusa ya haska ƙatuwar tochlight din da suka zo dashi domin tabbatar da wanda ya cillo tiles din ,hasken ya bawa ma'aruf damar fahimtar inda suke ,oga ya daga muryarsa ya ce kuje ku daukota,
ma’aruf na jin haka ya janyo buhun breaking tiles gabadaya ya dinga cilla wa gun da ya ji magana...
har wannan lokacin ummita na duke agurin jikinta na rawa gaba-daya ta kasa kwakwaran motsi hatta numfashi da kyar take fitarwa tana karanta duk wata addu'ar neman tsari , ma'aruf babu tsoro ko fargaba yayi kansu da breaking tiles din yana jifansu dashi .
da suka ga jifan yayi yawa kuma hakan zai iya kawo musu matsala suka fara neman hanyar tserewa tare da ƙoƙarin jan zaki amma ina tuni jikin sa ya sake gashi kuma har lokacin ma'aruf bai daina musu ruwan tiles ba , kuma duk jifa sai yayi nasarar samun su nan take suka shiga bin bango batare da sun samu damar daukar zaki ba , ma'aruf yaji wa biyu mummunar ciwo , ya samu mutun ɗaya a hegemonies , daya kuma abayan wuya ....

ƙarar hayaniyar 'yan daba da saukar tiles din daya cika gidan yasa wasu daga cikin mutanen gidan suka farka kamar a mafarki , Abbah ya farka a matukar razane yana ƙoƙarin neman wayarsa domin neman yan sanda, mama kuwa tuni ta farka wata irin durowa tayi daga saman gadonta tsabar gigicewa kaɗan ya rage bata tintsira ba ,tayo hanyar parlourn a guje tana taka step bibiyu , tana gama k'arasowa taga kofar parlour abud'e ,take zuciyarta ta buga jikinta ya shiga karkarwa kamar mazari cike da tashin hankali ta kai idanunta kan kujeran da ummita take kwanciya, wayam ta gani bata ganta ba babu ita ba alamunta , shiru tayi tana zare idanuwa da waige waige bakinta na rawa, addu'a ta shiga yi acikin zuciyarta kafin daga baya hankalin ta ya kai kofar kitchen nan taga kofar da zata fitar da mutun harabar gidan shima a bude ,
Take mama ta sake shiga rud'ani da matsanancin tashin hankali , cikin wannan halin Abba da ummah suka shigo suka iske ta zaune ta zama wata mutun mutumi bakinta ne kawai ke motsi ta hanyar ambaton sunan Allah da ummita ilahirin jikinta na kyarma , kanta sukayo gaba-daya suna kiran sunanta ,Abba ya kai kunneshi daidai bakinta ta haka ne ya fahimci abinda take faÉ—a "subuhanallahi inna lillahi wa inna lillahi rajiun a lokacin su rayhan suka shigo ,"na shiga uku yau me zan gani barayi a cikin gidan nan kai maza maza kira jami'an tsaron ummah ta kamo hannun mama "ina ummita take?
Da kyar mama tace "ban Sani ba ku taimake ni bangan ta ba hawaye na gangaro mata a parlourn mama suka tarar da su rayhan tsaye jugun jugun kowane fuskar da alamun tambaya zaunar da mama ummah tayi "ki samu natsuwa babu abinda zai same ta tana cikin gidan nan bata gidan nan ko da na sauko kofar parlourn a bude take haka zalika kofar kitchen ku taimake ni don Allah kar wani abu ya same ta bansan yadda zanyi ba sai lokacin hankalin Hajiya inna ya sake tashi ganin ga kowa amman babu ma'aruf "kuna maganar ba'a ga ummita ba shi babana fa kun wani zo kuna maganar wannan jaira ? Kowa yayi shiru yana duban inna cike da faduwar gaba da mamaki namiji za'a a nema ko mace ,mama ta kalli inna Kawai tana girgiza kai shi kuwa rayhan tuni ya haura saman mama neman ummita ...


Cike da tashin hankali yan daban da suka haye saman Katanga domin tsiratar da rayuwar su suka yi nasarar dira,sai ogan su ne kaɗai ya tsaya akan katangar gida ransa a matukar bace yana jin wani irin tuttukin bakin ciki mara misaltuwa saboda zuciyar sa bata samu abinda ta ɗauki sama da watani biyu tana bibiya da bulayi akanta ba, cike da jin zafi ya haske haraban gidan da ƙatuwar tochlight din da dake rike da hannunsa yana haske haske domin gano wanda ya yiwa rayuwar sa katsanlandan batare da bata lokaci ba tochlight din ya sauka akan Ma'aruf dake tsaye yana ƙoƙarin komawa maboyar sa inda ummita take durkushe saurin kare fuskar shi yayi haɗe da juya bayan sa ya fixgo ummita cikin jikinsa domin sake bata kariya , take ogan yan daban ya fahimci ko waye ya rusa masa shirin sa akan ummita yarinyar da yake jin matsanan ciyar shaawar ta matsawar be dandani zumur ta ba a rayuwar sa ba zata tagyara, har zai haura yaji hannunsa rike da tiles din daya tare lokacin da Ma'aruf ke yi musu ruwan jifa , ai kuwa be tsaya wata wata ba ya saita daidai kafardar ma'aruf ya cilla masa sannan ya dire ..........

Saurin runtse ido Ma'aruf yayi saboda azaɓaɓɓen zafin daya ratsashi ,a hankali ya saki ummita dake rungume ajikinshi "ashiiiiiiiiiiii ya furta tare da kai hannunsa daidai inda yaji rad'ad'in danshi yaji a tafin hannunsa wanda ya bashi tabbaci jini ne .......
Idanunshi a runtse ya nufi hanyar bangaran sa , da sauri ummita ta mike tana kiran sunansa jikin ta na rawa dan har lokacin a matukartsora ce take, tafiya yake cikin zafin nama tana biye dashi ,kai tsaye dakin shi ya shiga tare da turo kofar yana ciza lip's d'insa na kasa yana shiga ya tsaya a tsakiyar parlournsa yana duba tafin hannunsa ya dafe kafadarsa da shi ,bai yi mamakin gani jini ba saboda yayi tunanin haka ,ya runtse idanun sa a daidai lokacin data shigo dakin a gigice still tana kiranshi " tsayawa tayi cak qirjinta na wani irin bugawa da karfi tamkar ana buga mata guduma da sauri ta karaso gareshi jikinta na kyarma " ya ....ya ma'aruf me ya sameka ?
"Wayyohlly Allah jini kalli yadda jini ke zuba tayi magana tare da kusantoshi har suna iya jiyo numfashin juna , matsawa yayi da sauri ya shige bedroom dinsa ya faɗa saman makeken katifarsa yayi ruf da ciki , itama tana karasa shigowa dakin ta hau saman gadon "ka tashi na d'aure maka gurin , jini ne fa ke zuba tana kallon ciwon hankalinta na sake tashi "barshi ki kama gaban ki yayi maganar muryar sa a dake sannan cike da jarumta yana furzar da iska ta bakinshi "ka taimake ni a lokacin da banyi tunani haka daga gare ka ba ya zama dole nima na taimaka maka please ka tashi ta kararsa maganar tana kai hannunta jikinshi haɗe da ƙoƙarin juyo dashi yana jin yatsun hannunta a jikin shi amman yaki tashi sai ma ƙara sakin duka karfinsa yayi akan katifar ta yadda ba zata iya komai ba ,ta sake kai hannunta adaidai lokacin daya juyo da niyyar zai balbaleta da masifa "what nonsense is this .... Gigicewa tayi bata san sanda ta faɗa saman faffadan kirjin shi ba, shima a rashin sani hannu wanta duka suka zagaye bayanta cak suka tsaya a tare suna kallon kwayar idanun juna , take zuciyoyinsu ya buga a lokaci daya dukkan nin su , babu wanda bai ji wani iri a sansar jikinsa ba, wani sabon bakon al'amari ya bakunce su tsokar dake makale da kirjin su ....
Shiru ya wanzu a tsakanin su suna kallon cikin kwayar idanun juna batare da kowanne daga cikin su ya furtawa d'an'uwansa komai ba, yadda yake kallon kwayar idanunta haka bugun zuciyarsa ke karuwa da bugawa da be taba jin irinta ba kuma bai san dalilin daya sa yaji haka ba a halin da yake ciki , kallon kwayar idanunta yake yana tambayar zuciyarsa shi dai yasan ko suhaima da yake da muradin ajiyeta a gidansa a matsayin matar da yake wa duniya ikirarin ita yake so be taba jin abinda yake ji a yanzu ba ,sai gashi yanzu yana jin most especial kamshin da jikinta ke fitarwa mai sanya natsuwa da kwantar da hankali , yadda qirjinsa ke lugude bugawa a karon farko ....
Itama hakan ce ya kasance a bangareta ....
Kasancewarsu haka komai ya sauya a gare su be fi da minti biyar ba sai ga Inna tashigo d'akin sakamakon sautin murya ummita da ta ji tana kiran sunan ma'aruf dan Allah yayi inna da jin Magana kamar me kunnan maciji nan ta shigo zanan ta a hannu tana kokarin gyara dauri , tana shigowa babban parlourn taji shiru kai tsaye tayi cikin bedroom d'insa inda idanunta suka hasko mata ummita da ma'aruf a saman gado suna kallon kwayar idanun juna ko kiftawa basa yi, saurin murza idanunta tayi domin ta sake tabbatar da abinda ta gani gaske ne ko kuwa gizo su ke mata nan ta murza idanun ta domin ta tabbatar da abinda ta ga ni dan ba ta tsamaci ganin su haka ba juyawa ta yi ta koma jikin ta na rawa kai; kai; kai;Abba daya san shi ake kira da haka ya nufo inda take jin sautin muryarta hankalinsa a tashe ,a daguwar barandar dakin ma'aruf suka kusan cin karo da Hajiya Inna yayinda umma ke bayansa da mamansu rayhan a tunaninsu ko wani abun ne ya sameta ita kuwa mama na parlourn batasan a wani hali take ciki ba "kai muje kaga ikon Allah muje kaga iskancin da wacan jairar yarinyar ke yi a d'akin babana a she duk neman da'ake wa yar iskar yarinyar nan tana can d'akinsa ta juya ta nufi dakin da sauri suma suka biyo bayanta gaba-daya babu wanda jikinsa baya rawa ....



TWO FRIEND'S (BSBS)



💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~TRUE LIFE STORY~

FREE NOVEL NOT FOR SELL


AL'QALUMAN



*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*


~DEDICATED TO~
*YAR MUTAN KAGARA INA YINKI KAWAR SIRRI KAWAR AMANA IYA WUYA DA DADI MUNA TARE BAZAN MISANYA MATSAYINKI NA BAWA WATA A ZUCIYATA BA , ALLAH KARKA KAWO ABINDA ZAI SHIGA TSAKANINMU HAR MA DA SAURAN KAWAYENMU DA MUKE MUA'AM,ULAR ARZIKI , ALLAH YA JIKAN ADAM DA MAHAIFIYARMU ALLAH YA KAI RAHMA MAKWANCINSU ALLAH YASA IDAN TAMU MUTUWAR TAZO MU CIKA DA KYAU DA IMANI AMEEN YA ALLAH*

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim


PAGE 24

......"Kunga abinda yar iska yarinyar nan take kokarin yi , ku kalli fa yadda take kokarin rungumarsa ajikinta saboda ita tattacciya ce mai mugun gado .....
Wannan furucin ne yasa ummita a matuƙar firgice ta dawo haiyacinta tare da 'boyewa a bayan ma'aruf tana furzar da hucin numfashi mai zafi wasu sabbin hawaye na gongarowa saman kuncinta .
Daga ummita har ma'aruf duban bangaren dasu inna suke tsaye suke zuciyoyinsu na dokawa da matsanancin karfin gaske , "ya Salam ma'aruf ya furta a kasan zuciyarsa , ya runtse idanunshi tare da sotsa keyarsa cike da matsananciyar kunya , tunda yake bai taɓa jin kunya irin na wannan lokacin ba, a hankali ya dafe kanshi daya ji ya soma sarawa . ....
ummita dake makale abayansa sai zaro idanu take tana zubar da hawaye "baza ki bar jikinsa ba almara , kinyiwa mutane narainarai da idanun gado kamar na maciji?


2 Comments On WANNAN CE QADDARARMU
avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment