Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masu albarka  abun  yayiwa doctor Husain  Dadi ,dan yadda suhaima ta nuna damuwarta tayi matukar   burgeshi , da ana samun kishiyoyi irinta da wasu matan  basuyi bakinciki dan za'ayi musu  kishiya ba  .

tunda  doctor  da suhaima  suka fara magana   ya  zuba musu ido  kawai yana kallonsu jikinsa  na  rawa har suka gama  bai iya cewa komai  ba  domin bai san abinda  zai ce  ba, ko yace  ma  zai magana muryarsa  bazata  fito ba ya  lumshe  idanunshi hakan  ya  baiwa kwallar dake  cikin kwarnin  idanunshi  damar zubowa  "farkon  yayan  da  zai  samu  ya  rasa, shi  kaɗai  yasan  halin da  shi da mama  zasu shiga  akan rasa ya'yan nan  yana matukar  kaunar ciki  ko  yace Allah ya jarabeshi da cikin , a hankali  ya  furta ya Allah ka bani  wasu masu albarka  ....

Doctor  yace "ameen" muje  ka  kai ni naga yarana  yayi  maganar yana jin zafi  acikin ranshi  ,doctor  ya Mike shima  ya sauko daga kan gadon da kyar yake daga kafafunsa   suka fita  tare ..

Suna fita   suhaima  ta hau  tikar  warar shaku shaku  tana  jin farinciki mara misaltuwa, sai   da  tayi  rawar sosai sannan  ta kira number hajiya  rahma  "yayarmu albishirinki  ? a can bangaren  hajiya  rahma tace "goro  "ki tayani  murna  cikin  wannan   yar  iskan ya zube  ,a she ma yan biyu ne  ,shi kanshi bai sani ba  sai a yanzu "ke dai bari  yayarmu  yau  ina ciki  murna da farinciki mara misaltuwa  kamar an  sani a aljanna  haka nake  jina , can tayi shiru tana sauraron hajiya rahma  sannan ta sake kwashe  da  dariya tana rawa  da juyi "ke dai bari yayarmu  ni  dama an bar ma  zance zuwa gurin malamin nan  wannan makurcin  ma ya isa wallahi  "okya  shikenan maje  din  ai  zata sani ne  sai tayi nadamar zamowarta  kishiya agareni  tana  ji tana gani zata  bar min mijina ,shima ɗan iska wai  har da kuka  yayi  fa, ta  k'arasa maganar tana kwashewa da  wata dariya sannan tayi mata sallama  ta fito da sauri tana  neman inda suka shiga ..

Shiru  yayi  tsaye  yana duban  jariran ya'yansa waɗan  da  an gama  halintta  masu  komai masu  tsananin  kama dashi  sai  dai sunyi kankanta da yawa  , take wasu zafafan   hawayen   suka  zubo masa jikinsa na  rawa ya sake matsowa  garesu sosai  yana  dubansu ɗaya bayan ɗaya yana jin  soyayyarsu  na sake shigarsa  ,bai  ma san  yana tsabanin son baby's d'insa  ba sai daya rasasu   ,ya  yarda da kaddara  amman har da sakaci  ummita ....

doctor  husain  ya dafa shi "kaga yadda sukayi kankata ko ?
Ya kada masa kai batare da yace komai ba "wannan kankantar nasu nada halaka da rashin kusantarta da bakayi  da alamun tunda aka same su wani abu  bai sake shiga tsakaninku ba ,ya sake  yin shiru yana cigaba da kallon yaran yana hawaye  bai taɓa yiwa abu kuka ba duk tsananin abu ya kan daure amman ya rasa dalilin da yasa ya kasa daurewa wannan rashi da  yayi  doctor yace "kayi hakuri ba kai   ba  koni naji rashin dadin  komawarsu  Allah dai ya  bamu  wasu masu albarka .

Still bai ce masa komai ba  juya  ya  nufi d'akin  da aka kwantar da  Ummita doctor husain bai yi kokarin biyosa ba
ya   zuba  duka    hannuwansa  cikin  aljihun  wandonsa ya tsaya  a  tsakiyar  d'akin bayan ya shigo  yana kallonta  kwance  daga nesa tamkar wata  matacciya , alhankali  ya dinga  d'aga  kafafunshi har  ya  k'arasa  bakin gadon  ya tsaya yana cigaba  da kallonta da kyawawan  idanunshi da suka koma ja  yana  jin kamar ya tasheta  ya saka mata  kuka ....

suhaima  ce ta shigo ta tsaya  kusa dashi tana faɗa  masa kalaman  rarrashinta  na  karya kafin  daga  baya ta janyo masa  kujera "ka zauna habibi  kar juya ya debeka  bai  yi mata mutsu ba , ya zauna batare  daya ɗauke idanunshi  akan ummita ba , "ka  natsu dan Allah nan  da  wani lokaci zamu   sake samun  wasu ka sani ma  ko nice zan kawo maka kyawawan baby's   tayi  maganar   tana  satar  kallonsa  domin taga reaction d'insa akan abinda  tace ,   ya    kai hannusa   saman hannunta tayi saurin damkewa  "na  gode suhaima  yayi  shiru  yana  lunshe   idanunshi  sai  a yanzu yake kaara sanin  mahimmancinta arayuwarsa,  tana  tsaye akansa  da alamuran gidansa   shi  kuwa me zai yi ya faranta  mata ?
"Ka  soni  so na har abada  habibi ,ina sonka son  da ban ta'bawa yiwa wani mahaliki irin  shi a  duniya   ba...
jin  amsarta  ya fahimci a  filli yayi maganar ya sake  damke hannunta gam  cikin nashi yana murzawa ..

Jikinsa a sanyaye ya ciro  wayarsa ya  bugawa Abba  ya sanar dashi abinda  ya faru da Ummita ,abba  yaji ciwon abun  sosai  dan shima ya  kwallafa ranshi akan  cikin  amman  tunda ga yadda  Allah yayi ikonsa hakuri  zaiyi , lokacin da mama taji har da kuka tayi  a  boye   , hajiya Inna kuwa  tamkar wacce akayiwa  albishir da gidan  aljanna daman kullum  addu'a kenan  Allah  yasa cikin ya  zube  da cikin dan ita har lokacin bata yarda cikin na mahruf bane.

  a parloun'n mama yan'uwa suka  cika  ana jajantawa  juna , Inna kuwa na  d'akinta tun da tace  wa Abba Allah ya kyauta  bata sake tofa albarkacin  bakinta ba sannan  bata tako part din  mama ba  ,duka gidan  hankalinsu ya tashi  hajiya umma tayi kuka sosai ba dan mahruf ya kasance d'anta ba   saboda   mama ne dan lokacin da  zance cikin ummita ya fito taji dadi sosai mama zata sake samun zuri'a amman sai gashi sun rasa  take  ta soma magana "anya  kuwa babu sanya hannu  a fitar cikin nan ,jikina na bani akwai wani abu ..  ?
Mama  tayi saurin  cewa "kai  haba mufa muslimai  ne  bai  kamata  muna  kawowa zuciyarmu  irin  wannan tunanin ba , Allah ya bayar  kuma  ya amshi abunsa , dole  hajiya Umma  tayi  shiru ..
  aunty ma data zo    sai da tace  akwai wani abu  "ina jin tsoron dagin suhaima  fa sam babu imani  a zuciyarsu zasu iya aikata  komai  gaskiya ban yarda da zamansu  tare ba gara ummita  ta koma bangarenta daga kwana biyu har sunyi wata a guri daya .
mama  tace " koma dai menene  mu barwa Allah komai  zato zunubi ne koda  ya kasance gaskiya ne  muyi musu addu'a kawai  "kunji matar  nan wai muyi musu  addu'a suwa  kenan   ..?
"Kinga  ni  diyata kawai na sani  ,kuma ita kadai  zan yiwa addu'a ba waɗan nan  shedanun  ba, kune   baku da labari  auren  ita dayar yaya suhaimar ya dade da mutuwa wai mijin  ya bude  wordrob din  kayanta zai dauki turare  yaci karo da tukunyar  tsafi shine fa yayi mata dukan mutuwa ya  korota gida da takardar saki uku.."to Allah ya kyauta ya ganar  dasu  gaskiya suka ce "ameen daga nan suka shiga shirin zuwa  asibiti .

Duk yadda suhaima ke rawar jiki akan ummita a banza dangin ummita suke kallonta har ta sha jinin jikinta ta kebe kanta gefe dan irin kallon tuhumar da suke mata babu sauki ..

  Ummita  bata  farfaɗo ba  sai  cikin dare kuma har lokacin mahruf  yana tare daita  zuciyarsa cike da tausayinta,   ta wani bangare   kuma zuciyarsa  na jin haushinta ganinsa har da gangancinta  yasa suka rasa babynsu ..
A hankali ta bude idanunta  sama  tana kallon  celling d'akin jikinta  babu kwari ta waigo  inda mahruf yake zaune  kusa daita idanunsu  ya  tsarke cikin  juna  take  ta gano inda take da abinda ya faru daita   ,yadda  taga ya dawo a cikin  lokacin kankani yasa  tausayinsa ya kamata  musamman yadda ta lura yana son cikin  jikinta   addu'a ta soma  yi Allah yasa bai rasa  cikin ba , ta kai hannunta  saman cikinta  taji  wayam babu tudun cikinta  ta sake waigowa inda  yake da   saurin
Saurin  kawar da fuskarshi yayi  yana sauke  numfashi da kyar , shiru  yayi  cike da d'acin zuciya   alhankali ya soma  magana "burinki ya  cika tunda gashi kinyi sanadin  da na rasa babyna ,daman kuma kin furta  sai a zubar  min dashi ,sai  ki kwantar da hankalinki banda ma bakinciki irin naki ai  kanki zaki yiwa yan'uwa amman kika bari gangancinki ya janyo aka rasa   ....

ta tsura masa idanunta tana  kallonsa  ranta na kuna  da kyar ta bude bakinta "ta nan  kuma zaka biyo ?"Bata nan zan biyo ba ta sama  zan biyo har suhaima  nayi miki magana  ki daina tsalle tsalle  amman kika mata banza  wa kika cuta yanzu  ?" Ni ina da wata matar  da zata haifa  min yara kanki  kika   cuta  wawiya kawai  da bata san ciwon kanta  ba ,ta yunkura da kyar ta mike  zaune ta zuba  masa  idanunta dake  narkar  masa da zuciya sai dai yau babu abinda yayi tasiri acikin zuciyarsa illa haushinta da bakinciki  "me  yasa tun farko  bata haifa maka ba ?
"Ko  ita  baka  auratayya daita  ne ?
"Kin  min shiru  da wannan banzar  dakikiyar  kwakwaluwartaki  ,ko  dan baki ga na rufeki da mahaukacin  dukan  hasarar  ya'ya maza  biyun  da kika janyo min  saboda bakinciki irin naki ,koda yake   daman  ba tun yanzu nasan da zaman  kina  min  bakinciki  akan duk  wani abun   farincikin da zai sameni a rayuwata ba   ...
Bata san sanda ta riko hannunwansa  duka cikin nata a gigice  ba  "yara biyu   maza  fa  kace  ?
ya galla mata katuwar harara  yana ƙoƙarin fixge  hannunsa cikin nata "ban sani ba ta narke   idanunta cikin nashi  tana  girgiza masa kai "wallahi  yaya  ba da ganga  bane , banyi maka ganganci  ba ,ko zanyi ganganci  ,bazanyi ganganci da rayuwata ba , wallahil azim kitchen  zani domin dafa  indomi saboda  shi nake kwadayin  ci  kawai naji an turo ni ta baya amman  nafi tunanin su....
"Shiiiiiiiiiii  karki  sake ki sako sunan matata ciki  daman  kina da niyyar aikata  hakan  kije ke da Allah    dan bani da abinda  zan miki .

jikinta na rawa ta sake damke   hannunta cikin nashi "wallahi  ba da ganga nayi ba  babu sanya  hannuna ka fahimceni  wallahi  turoni akayi  ,ya soma ƙoƙarin zare hannunsa  yana jan tsaki  ta sake riƙe yatsunsa  gam "shikenan  koda bazaka yarda dani ba ka rufa min asiri  dan Allah karka fadawa mama  hankalinta zai tashi  ,nasan muddin ka faɗa mata ɗauka zatayi da  gaske  ne da karfi ya fixge hannunsa  ta  koma ta kwanata sharaf  akan katifa tana kuka kwakwalwarta na neman mafuta ranar dai karasa  kwana tayi cikin  kukan rasa ya'yanta yana zaune yana jinta  yayi mata banza   ..

Washegari tun da sassafe suhaima    ta tashi ta haɗa break fast  ta nufo hospital tana shiga ta isa gaban gadon ummita tana taɓa jikinta "sannu ummi ya jikin .?
Tayi mata banza batare data kalli inda take ba har tagama zuba surutunta ta samu guri ta zauna kusa da mahruf tana tambayarsa mai jiki "da sauki kawai yace atakaice ..

Yan'uwana suka cika asibiti  banda  mama domin duba jikin Ummita  duk bayan minti ashirin  mahruf  zai  shigo duba jikin ummita  sai dai    byn  ya jiki baya sake cewa daita  komai zai fice  ,tun aunty na basarwa  har sai da ta kirashi gefe  "haba baba me  yasa kake yin haka ?
"hakuri duk zamu taru muyi  ka saki ranka ka nunawa  matarka kulawa gaskiya  bana jin dadin wannan shan kamshin da kake ,ya kake son yarinyar nan tayi ,ka kuwa san yadda uwa take ji akan ya'yanta idan ta rasa  ? " A yanzu ita kadai tasan abinda take ji a zuciyarta  ,  ya dai  jita amman  baya jin zai wani saurara mata a yanzu .

satin  ummita  daya aka sallamesu  jiki a sanyaye ummita ta fito tana takawa aunty ta buɗe mata gaban mota ita da suhaima  suka dawo gidan baya mahruf ya  tada mota suka bar hospital zuwa gida  bai tsaya akoina ba sai a tafkeken get din gidan yayi  hon mai gadi ya bude musu, ya shigo   kai tsaye inda aka tanada domin ajiye motoci ya nufa yayi parking  daya bayan daya suka fito ummita na takawa a hankali sakamakon kafafunta da sukai nauyi saboda allurai da'akayita mata a asibiti ganin yadda take tafiya tamkar wace kwai ya fashewa a cikin  ya  tsura mata ido yana kallon every step of her wanda ke sashi jin wani irin sanyi a sansar jikinsa tuntube tayi sakamakon idanunshi dake yawo ajikinta "washhhhh Allah ta faɗa tana tsayawa haɗe da runtse idanunta  aunty tayi saurin dafata "menene ummita ?
Ta  runtse idanunta "kafata  aunty " me kafarki tayi ?
"Ta rike bana jin zan iya takawa ..tayi maganar tamkar zatayi kuka a hankali ya k'araso ya tsuguna a gabanta ya rike  daidai idon sawunta yana mammatsa mata kafar, batare daya kalleta ba ya dinga murza gurin , mutuwar tsaye suhaima tayi zuciyarta na tafarfasa tamkar ta kama da wuta kusan minti goma sannan ya d'ago ya sanya kwayar idanunshi cikin nata "how do you feel now ?
"Better ta bashi amsa tana rausayar da idanunta cikin nashi ya lumshe idanunshi tare da mikewa tsaye taku daya tayi ta sake tsayawa tana kiran "wayyo Allah bazan iya ta  ... ..
bai tsaya   jin abinda zatace ba ya sureta ya rungumeta ajikinsa ya soma tafiya daita a hankali take kallonsa tamkar wani sabon halitta a gabanta,  yana jin yadda take kallonsa har ya isa   bangarenta yana ƙoƙarin  kwantar daita akan kujera a parloun, amman still  bata daina kallonsa ba ya kwanto jikinta sosai har suna jiyo numfashin juna "kallon fa na menene ko na canza miki ne?tayi saurin runtse idanunta tana sauke ajiyar zuciya adaidai lokacin da  aunty ta shigo  haka nan  taji gabanta ya fadi ta shiga bin parloun  da kallo duk  an gyara ko'ina, a hankali idanunta ya sauka a bakin kofar dakin  ummita ta tsurawa gurin ido  tana nazari kamar an fasa gurin , gabadaya yanayin gurin ya bambamta ,bata yi sanya a gwiwa ba ta ciro  wayarta  ta shiga neman layin malam musbahu  ..

tana tsaye mah'ruf  ya fita  ya bar part din zuwa na  suhaima, Suhaima kuwa  a parloun'n ta tsaya tana zaria tana ciza lip's dinta bakinciki kamar ta mutu, ranta duk babu dadi taji haushin daukar da mah'ruf yayiwa ummita, can  tunanin  shirinta ya fado mata  a hankali ta  gizgiza  kai tana murmushin mugunta    "wallahi kota karfin bala'i sai na fitar dake a gidan nan, ba dai kema  kin iya kissa ba , babu fa abinda ya samu kafarta tsabar iskanci ne kawai , haka ta dinga zance zuci daga karshe ta sake yin murmushin mugunta "na gama cika aikina na farko yanzu zamu shiga na biyu da ni kike zance ,makircina na biyu banyi niyyar aiwatar dashi yanzu ba amman  zanyi  dan kuntata miki ,zan sa ki shiga haula'i ,zan sa kiyi kuka jini da idanunki ,zan yi abinda da bakinki zaki furta bakya auren mah'ruf   tana  cikin zance taji sallamarsa tayi sauri juyowa tana hadiye maganarta ta k'araso jikinsa ta rungumeshi "sannu habibi ta kamo shi ta zaunar dashi bari na kawo maka ruwa ka sha  nasan ka gaji ta rikosa  ta zaunar dashi, taje ta bude fridge ta d'auko  ruwa mai sanyi ta tsiyaya  a glass cup, ta dawo inda yake ta zauna tare da mika masa ka sha kaji sanyi nasan har yanzu kana tattare da damuwa, dan Allah ka bari  komai mai wuce a zuciyarka , ya  amshi  ruwan  ya sha kadan ba dan yana bukatar sha ba   .

"Habibi ta Kira shi tana kallon cikin kwayar idanunshi shima ita yake kallo  "dan Allah ka natsu  ka daina yawon  damuwa da damuwar  ummita dan wallahi da gangan tasa mukayi hasarar babymu  ,kawai dai ban   faɗa maka  abinda naji tana fadawa amina  da tazo last week ba,  dan banason haddasa fitina  amma wallahi tana  sane ta bari mukayi hasarar babynmu ya  tsura mata idanunshi sosai hankalinsa a tashe yace "ki faɗa min me ya  faru   ?
"Banason haddasa fitina   dan haka ba sai na faɗa maka ba kayi hakuri kawai ni zan sameta nayi mata magana ta karasa magana tare mikewa taku daya tayi  ya fizgota da karfi ya kafeta da idanunsa "kina hauka ne ki faɗa min  .......

  ta sauke naunayen ajiyar zuciya tana jin  dadi  sannan   ta kai hannunta ta janyo jakarta ta ciro wayarta ta kunna masa voice note din data nad'a a ranar da menal tazo  , take ya soma jin magana kasa kasa hirar ummita da meenal ,meenal ke faman bata hakuri ita kuma ummita  na  cewa "gsky bana son cikin nan duk yadda zanyi a ciresa  zanyi,  yana gama ji yayi wata irin zabura ya mike   kamar mahunwanci zaki jikinsa na rawa take zufa ya shiga tsatsafo masa  kamar ana watsa masa  ruwan zafi a jikinsa ya juya a fusace tayi saurin riko hannunsa da sauri  jikinta na rawa "haba habibi kai kuwa ina zaka daga jin magana  ?
"Ban faɗa maka dan kaje ka sameta ba ,na faɗa maka ne dan ka sani , sannan ka  daina yawon damuwa akanta tunda  tana sane ta zubar "ki barni naje na ladabbatar da jikinta sannan na sheida mata nasan  abinda tayi .
"no ko zakayi wani abu ba yanzu ba ka bari sai  aunty ta bar gidan nan dan yanzu kana zuwa  zata ɗauka ko ...
"Ko  me ?
"ni dai plz  dan Allah karka janyo min bakinjini agurinsu  azo ana jin haushina  ni kuma banason na samun matsala da yan'uwanka kaga ita tasu ce duk runtsi duk wuya bazasu sa ta bar gidanka ba nifa ?
Yayi shiru yana huci sannan ya koma ya zauna jagwab akan kujera yana fidda hucin numfash mai zafi  ta dawo kusa dashi da kyar ta samu ta shawo kanshi..

Cike da sanyi jiki ya mike ya nufi d'akinsa ya faɗa kan gadonsa ransa duk babu dadi  yana kwance ta biyosa ta kwanta jikinsa tana shafa kirjinshi ya mike "ki barni bana jin dadin zuciyata ya barta ya shige bayi ta girgiza  kai kawai tana jin haushi "to ni meye nawa wallahi bazaka shiga hakina akan wannan shashar ba tayi tsaki ta fita , yayi wanka  ya canza kaya zuwa kananan kaya riga blue da ratsin yellow  duk ransa a bace yake hakan bai hanashi kyau ba kasa ya sauko  bai yi mata magana ba  ya wuce dining table , tana ganinsa ta mike ta zuba masa abinci ta turo  gabansa ya soma cin abinci yana kallon agogon daya sha ado ajikin bango parloun'n dake walwali da hasken fitilu ya kara haskaka wa  ..
Bai wani ci abinci kirki ba ya mike ya fita batare da yayi mata magana ba kai tsaye gidansu ya nufa ya wuce bangaren   mama  a parloun'n kasa ya sameta dan haka shima ya samu guri ya zauna suka gaisa "ya me jiki ?
"Taji sauki dazu muka dawo gida "to Allah kara sauki karka sakawa zuciyarka damuwa Allah daya bayar zai sake baku wasu masu albarka kamar ya fadawa mama ganganci da ummita tai masa sai dai ya share yana tare da mama har kusan magariba sannan ya  wuce massalaci yayi Sallah ya  koma gida part din suhaima ya wuce   ..

  Ranar dai  bai sake daura idanunshi akanta ba sai washegari shima ya shiga ne saboda aunty dan yasan muddin ya fita bai shiga gurinsu ba zatayi magana ,  sama sama yayi abinda ya kai shi  batare daya  kalli inda take ba  zai wuce gurin  aiki ta dakatar dashi tana nuna masa abinda aka ciro  "daga ina aka ciro wannan sharmen ? "a bakin kofar shiga dakin ummita gasu nan layu ne  "to me ya kawo layu nan ?
"Kai da matarka za'a tambaya tunda kune a cikin wannan part din yayi shiru yana nazarin maganar idan dai zai fahimta zargin matarsa take  ?

    TWO FRIEND'S BSBS
💗💗💗💗💗💗
     WANNAN CE
   QADDARARMU
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~TRUE LIFE STORY~

FREE NOVEL
            
      
AL'QALUMAN


*AYSHA  A BAGUDO*           
*FAIZA  HAMMADU*

*SUBSCRIBE TO MY CHANNEL HAUSA BAKWAI*

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

PAGE 57

cike  da jin haushi ya juya yana ma aunty  sallama "ni na wuce office    , har ya juya     tace "dawo  ka  zauna  ina son magana da  kai   ya dawo jiki a sanyaye ya  zauna yana
fuskantartata ,aunty ta numfasa kana ta soma magana a tsanake "wannan layun  da  aka ciro   sihiri  ne aka yi  dan  a shiga tsakaninka da matarka a hanaku  zaman lafiya da juna, ina maka magana kana ƙoƙarin   wuce wa saboda ka maida maganata  banza   .

Yayi  shiru yana kallon aunty zuciyarsa na kuna da tafarfasa a dan fusace  yace " aunty wa kike tunani zai yi  asiri a gidan nan daga ni sai suhaima  ne ,ita kuma nasan ba zata aikata haka ba  ? yayi  mata  tambayar yana furzar da iska mai zafi  .

" ni  dai yanzu bana son wani  dogon  turanci ko wani  tashin hankali  ,
abinda  nake  so da kai  ka sanya idanunka  sosai a cikin gidanka  sannan ka tsananta  addu'a dan kai kanka  baka  tsira ba ,ko wannan matsalar data faru ta  rasa bby's  din da'akayi  ba  laifin  ummita  bane bare ka dinga  jin  haushin yarinyar mutane kana tsagwamarta   babu  garai babu dalili, babu uwar da zata ɗauki ciki ko na kwana uku ne  taso ta rasa  d'anta ko yarta bare har ya'ya biyu a lokaci daya ,  ko  kai  uban cikin baka  kai ta son ya'yanta data rasa  ba ,   Allah shi kaɗai  yasan  wanda yayi wannan mugun aikin  kuma shi  zai saka mata , amman  kasa ido sosai Allah kuma ya tona asirin duk wanda yake da sa hannu tashi  kaje Allah ya tsare ..

"Ameen ya furta haɗe da
mikewa  cike da jin haushin ummita a cikin zuciyarsa,  a ransa yace   " sharri zata  yiwa matarsa kenan   duk  abinda  take mata  bata gani  ,  da sharri zata saka mata dashi ? tunanin matakin da zai ɗauka akan wautan da  ummita tai masa da kuma  sharrin data yiwa matarsa  yake har   ya qarasa office ,aiki yake amman zuciyarsa da gangar jikinsa na gurin ummita , wani iri ya dinga ji akanta ,qirjinsa ke wani irin mahaukacin dokawa da karfi duk saukar numfashinsa da tunaninta yake sauka da baby's d'insa daya rasa, zuciyarsa na matukar zafi ya tashi ya  qarasa inda fridge yake   ya buɗe ya ɗauki  goran  ruwa ya dawo kan  kujera mai zaman mutun uku dake ajiye a office din ya kafa a bakinsa sai daya shanye tasss sannan yayi wurgi da roban   ya dafe goshinsa da hannu daya yana furzar da hucin numfashi ,a hankali maganar aunty ke dawo masa ya mike tsaye ya rungume hannunwansa duka  a qirji "daga shi sai suhaima ne a gidan shi dai yasan ba shi ya binne layun ba, haka  baya zargin  suhaima ,  yasan tana  da tsananin kishi akansa amman kishinta bai kai ta dauki  hakin rayuka biyu da binne wannan layun da aunty ta nuna masa  ba ,"to wanene idan bashi bane kuma ba ita bace ta aikata haka?  ya  jefawa wankakkiyar kwalkwaluwarsa tambayar "lallai ya tabbata akwai mai kawowa rayuwarsa farmaki "to waye wannan ? ya tsaya cak a tsakiyar office din  yana nazari da son gano wanda ke ƙoƙarin kawowa rayuwarsa hari shiru yana tsaye kusan minti goma sannan ya koma mazauninsa ya cigaba da aikinsa ..

Matakin farko da mah'ruf  ya soma dashi shine  shariya,  ya share ummita  iyakacin ya shigo bangarenta  ya duba lafiyar jikinta ya kama gabansa ,wannan abu ya tsaya  wa  ummita a rai matuka ga kuma  rasa ya'yanta  har biyu data yi abun  ya dameta kwata kwata  taki      kwantar da hankalinta kullun kuka, shima bangarensa  dauriya kawai yake amman zuciyarsa da hankalinsa na kanta , aunty  na  iyakacin  kokarinta gurin  bata   kulawa ta kowane bangare amman jikin  ummita  sai sake sukurkucewa yake  babu wani   cikowa da tayi   , har tsawon kwanaki uku  da dawowarta  babu wani canji   zuciyarta na tattare  da damuwa, tana   jin ciwo da rad'ad'in  rasa baby's dinta da tayi,  suhaima na shigowa jifa jifa   duba  jikinta da kawo mata  kayan motsa baki   sai dai duk abinda take  idanun aunty na kanta  sannan ko da wasa  aunty bata yarda su ci abinda take kawowa ba , haka  zai  gama gantalinsa ta zuba a leda ta kai shara.

Zuciyar aunty ta kasa hakurin  abinda idanunta suka  gani  , ta nemi hajiya umma  tace " tazo su tautauna akan wata matsala , hakan ce ta kasance,  Abdurrahaman ne ya kawo  hajiya umma ya kama gabansa da zumar idan ta gama ta kirashi yazo ya maidaita gida , suna zaune a parlou'n  ummita ,aunty ta tashi  ta d'auko laya data adana a cikin flowers din dake zagaye da part din ummita ta nuna mata tare da yin shiru tana dubanta ,"menene wannan salama ? "  Ki bude ki

2 Comments On WANNAN CE QADDARARMU
avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment