Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

ummita yayi sanyi ,naunauyen ajiyar zuciya ta sauke da karfin gaske idanunta na kallon cikin kwayar idanunshi wani irin abu yaga suna fitowa daga cikin idanunta suna shiga nashi jikinsa ya mutu yaji kamar ya shige jikinta dan ji yake kamar za'a kwace masa ita .
"ka kwantar da hankalinka
yaya inshaallahu zan...sai kuma tayi shiru ta kasa karasawa tana gudun tayi subul da baka irin wanda tayi agurin muhd Sa'id ..
"Inshaallahu me ki faɗa min abinda ke cikin zuciyarki har yanzu Ban tabbatar da kina sona ko ina da matsayin acikin zuciyar ba ,ina son ki furta min matsayina daidai kwayar zarar ba zan raina ba , ina son najita daga bakinki tayi murmushin gefen baki "karka damu yayana ai ina sonka kai fa d'an'uwana ne"
"No ummita ba maganar soyayyar ta yan'uwantaka nake nufi ba ,ina miki magana ne akan soyayya irinta zuciya da zuciya irinta ma'aurata , ta bude bakinta kenan zatayi magana sai ga mama ta sauko dan haka tayi shiru da bakinta tare da zare hannuta cikin nashi , ta kalleshi tana murmushi ..."ga mama nan fa ..juyowa yayi inda yafi tunani ganin mama ,
Ganin mama tsaye yana dan bugar da zuciyarsa dan yasan babu abinda zata sake cewa ,dan haka ya runtse idanunshi gam tare da dafe gaban goshinsa da hannunsa ɗaya.

"rayhan yaushe kashigo ?
"Yanzu mama kuma fita zanyi yanzu "lafiya dai na ganka wani iri kamar baka jin dadi ?
"Lafiyata lau ..
Idanun mama ne ya sauka akan fararen lododin dake ajiye ,take ta fahimci abinda ya sauya rayhan ,ya ga ummita da bakonta kenaan , tana kallonsa ya mike ya fice daga parlour'n ...

Qarasawa mama tayi ta soma buɗe ledodin a hankali , itama ummita kayan take kallo masu shegen kyau da tsada maimakon taji son muhd sa'id a zuciyarta sai taji tsanarshi ta shigeta , tambayoyi birjiki tayi ƙwaƙwalwarta ,batayi mamakin kudin daya kashe ba dan tana da labarin yadda yan caji ke kashewa mata kudi idan suna son su .

Tunaninta anya muhd Sa'id yana da hankali da har zai kashewa yarinyar da bai gama sanin matsayinsa a zuciyarta ba ,wayan nan makudan kudin kayan sun isa hada matsakaicin lefe kai ko babba ma tunda dai ai kowa da bazarsa yake takama , anya kuwa mai cikakken tarbiya ne wannan ?
"kila da yana da masu faɗa masa yaji ,da bazasu bar shi yayi haka ba ..
Gashi a fuska yayi kama da natsatsu kuma ma'abocin ilimi amman idan mai hankali ne Yakamata ya jira lokaci , ba yanzu ne lokacin da ya dace yayi hidima ba duk wadatar shi ...

Hajiya mama data zuba tagumi cewa tayi "kai Allah kayi mana maganin abinda ba zamu iya magantawa kanmu ba ,"ummita halan yaron nan dan wani attaijiri ne acikin garin nan ..

Ummita ta yatsina fuska" mama wannan abokin ya ma'aruf ne , dogon fari sun ma taɓa shigowa tare dashi ," dan waye canji .. ni na manta sunan babansa amman idan kika gashi zaki ganeshi "ummita nifa abin ya bani tsoro dan gaskiya mutane ya yanzu abun tsoro ne, yanda zamani ta lalace don abun duniya ya zamewa jama'a karfa,kar dai yaron nan dan yanka kai ne muna zaman zaman mu lafiya ya cucemu, koda yake ai kince abokin ma'aruf ne?
ummita ta daga mata kai .

"kin ma sanshi fari sani , nima wallahi tsoro yake bani hatta kayan ma tsoronsu nake ,dan Allah mama a fitar dasu waje kawai a zubar , cikin haka su Maryam suka fito suka bi kayan da kallo kafin daga baya suka isa ga kayan "kar dai bakon ne ya kawo mana waɗan kayan ?
Meenal ta tambaya tana duba kayan daya bayan daya "shine kayan da suka 'batawa ya rayhan dina rai, baki ga yadda gaba-daya ya sauya ba Ni dai mama dan Allah asan yadda za'a da kayan nan if possible a fitar dasu a zubar.

"kin jiki da wata magana a'a bola za'a kai ba fitarwa ba inji meenal "kunga ni ki hado min nawa kawai nasha sha'anin dasu "kunga ni ku tattara kayan ku mai dasu cikin ledar na kaiwa abbanku yasan halin da'ake ciki kar daga baya yaga laifina "
"A'a mama karki nuna masa dan ni daga yau bazan sake fita ba tsoro yake bani ...

"Dole ki fita yarinya matsawar baki tsaida na aure ba , nifa aure nake son kuyi gabad'ayanku Allah dai yayi muku zabi na alkhairi tayi maganar tana nufar kitchen ..

Ganin yadda uwar gidansa ta rude lokacin daya fara ƙoƙarin duba kayan yasa yayi kokarin kwantar mata da hankali duk da shima al'amarin ya daure masa kai ,kalamai masu taushi ya shiga jero Mata, dan ta samu natsuwa yace "kinga ajeye min kayan anan gurinki idan Allah ya kaimu zamu haɗu da injiniya musan abun yi ...

*******
Ma'aruf iya tunaninsa ya tafi ne akan yayi aure ya tattara ya bar gidan ,ya daina ganin ummita, dan ganinta kaɗai na haddasa masa cuttuka kala daban daban, dan haka a daren ranar da kanshi ya samu Abba da zance , ahankali yake sanarwa Abba batun yana son aje masa gidansu suhaima neman aurenta..
Abba yayi shiru kafin daga baya yace " shikenan Allah ya bani iko "waye mahaifinta kuma a wani unguwa suke ,?
"Nan take yayi wa abba bayanin komai akan suhaima , bayan fitarshi da kamar minti goma mahaifiyarsa hajiya ummah tashigo kasancewar itace da girki, anan abba yake sanar mata abinda ma'aruf yake da bukata, murumushi tayi tace "haba baban yara , karma ka sauraresa duka yaushe ya soma aikin, kuma ma idan auren zai yi ai ga sakina gidan baba sarki nan ,yarinyar tana sonshi sosai , gida bai koshi ba za'a kaiwa waje ,bama haka ba ni fa ina da wacce zuciyata tafi kwanciya tayi rayuwa dashi ..
"Haba uwar marayu da yake hakan yake ce mata a tun sanda marigayi yayansa ya rasu "karki ce haka kiyi hakuri karki kawo masa matsala da aurensa ,ki barshi yayi yadda yake da bukata, kowa da ra'ayinsa ta yiwu da zabin naki da ita sakinar baya son daya daga cikinsu ,kiyi masa addu'ar Allah yasa ita yarinyar da yake so mai tarbiya ce "umma tace shikennan tun da haka kace ,Allah ya tabbatar da alkhairi amman idan son samu ne ya haɗa da sakina ya aurensu duka "
Abba yayi murmushi "hakan ma karawa yarona kwarjini zai yi ,sanan kuma d'ana yana da mazantakar da zai rike mata har hudu ba biyu ba ......
murmushi umma tayi "Allah idan bai aure sakina ba a yadda take son shi ba za'a shiga damuwa , taki kulawa kowa fa ,shi kuma da zarar anyi masa magana yace yayarsa ce ,shekarursu fa daya daita kwana arba'in ne a tsakaninsu "Allah dai ya tabbatar da alkhairi zamuyi magana dashi muji idan yana da bukatar haka duk mai sauki ......


********"
Kwanaki dayawa kenan da ummita taga ma'aruf ya fita harkar kwatakwata ko kallon inda take baya yi, duk abinda zata yi baya daga idanunsa ya kalleta , ta daura ayar tambaya akan lamarin, tunanin duniya tayi amman ta rasa gane dalili faruwar al'amari , a karshe zuciyarta ta fahimtar daita wata kila faɗa sukayi da sahebarsa suhaima , tunda gashi kwana biyu bata ji yace wa mama suhaima tana gaisheta ba, ko zama ayi hirarta da sauransu , taja tsaki ,"ai duk inda kaje neman aure da wannan mugun halin naka ,tsiya tsiya zaku rabu , babu shegiyar da zata 'batawa kanta lokaci akanka ,duk wata mai cikakken hankali da sanin ciwon kanta ba zata aureka da wannan bakar zuciyar taka ba .
"mutun da bakar zuciya kamar ta mutane farko ,tabbas faɗa ma sukayi tunda har a fuskar wayarsa ya cireta saɓanin da da itace akan wallpaper dinsa .....

A bakin kofar shiga part d'insu ta hangoshi tsaye rungume da hannuwansa duka akirji sanye cikin riga ta shirt ja da wando baki , yayinda gefenshi abokinsa jafar ne tsaye suna magana kasa kasa, tamke fuskarta tayi sosai tamkar wacce aka aikowa da sakon mutuwa ,tun daga nesa take kallonsu a wulakance
har takaraso bai yi kokarin matsawa a bakin kofar ba ,haka itama bata bude baki tace masa ya matsa ko zata wuce ba ,ta gefen jikinshi tabi ta raba tare da matse jikinta dan kar ya hadu dana shi, amman duk da haka sai data goga kafadarsa ta wuce ta kiyi masa magana ,sosai yaji zuciyarsa ta buga wani irin haushi yaji ya caki tsokar dake makale da kirjinsa kamar ya janyota ya waska mata mari amman ya kyaleta saboda tunanin maganar mahaifiyarsa ,
Shi ne abinda ya katse masa hanzari ,dan haka ya sauke hannuwansa ya tura cikin aljihun wandansa yayi hanyar harabar gidan batare daya cewa jafar komai ba , biyo shi jafar yayi a baya yana masa magana "na rasa gane kan wannan tsana dake tsakaninka da yarinyar nan ummita yaruwarka ce fa babu .....
"dakata dan Allah malam ya tsaya cak tare da juyowa yana fuskantar shi "me ye ruwanka ko me ye damuwarka ?
"Babu jafar ya bashi amsa a takaice ..
" To daga yau babu ruwanka da wata yanuwantaka dake tsakaninmu daita , dan muna yan'uwa sai akace ta dinga min abinda taga dama, kai ma kasan abinda take min amman sam baka ganin laifinta sai nawa ..
"Dan haka karka dame ni, kai kar ma ka sake min zamceta kayi abinda ya kawoka ka kama gabanka .....
Ya K'arasa maganar yana sake juyawa ya fita daga gidan gabad'aya...

ya karasa kofar gidansu ya zauna akan dogon banci , shima jafar zama yayi a kusa dashi bai sake yunkurin ce masa komai ba, a qalla sun kusan minti talatin zaune babu wanda yace kala ,a hankali jafar yaja qaramin tsaki bai san me ya kawo shi gidansu ba gashi ya bata masa rai a karon banza, daga gyara kayanka ....
har kusan la'asar Ma'aruf bai da niyyar sake yi masa magana tun yana charting da shiga bangaren adana lambobin mutane har ya gaji ya hakura ya mike ya soma ƙoƙarin barin gurin ,kallonsa kawai ma'aruf yayi yana ta'be baki sannan ya mike shima ya koma ciki yana furta shishigin banza kawai .. ... ..

******
Kullun muhd Sa'id zai zo gidan da zumar ganin ummita amman baya samun ganinta, yayi kokarin samun numberta agurin yaran gidan, amman tunda ya kira taji shine ta katse kiran bata sake ɗauka ba, hankalinsa ya tashi matuka kamar wani zautacce ya rasa yadda zai yi, ma'aruf ne kaɗai zai taimaka masa shi kuma basa shiri suke daita ba , gabad'aya ya kasa hakuri ya tabbatarwa kanshi da dole sai ya dangana ga Ma'aruf zai samu mafuta ...


****

Ma'aruf ya fita harka ummita kamar yadda mahaifiyarsa ta umarceshi, sai dai tsanarta na nan daram acikin zuciyarsa babu abinda ya ragu ..Yayinda
itama hakan ce gareta ....dan tsanar da tayi masa tana nan daram acikin zuciyarta ,wanda Ita kanta wani lokacin ta kan yi mamakin me yasa ta tsaneshi irin haka alhalin suna yanuwan juna ?
Ta tsaneshi ya tsaneta irin tsanar da zai so yaji wani mugun abu ya sameta ,itama yanzu da'ace za taji wani mugun bala'i ya sameshi dadi zataji sosai ...

A hankali ya sanyo kai zai shigo parlour'n mama , yaji tana bugan cikin mama tana son taji da gaske auren suhaima zai yi ko da wasa ne ba yi zai ba , tana son tasani da gaske ne abinda take son ta tabbatar kenan ...? Ya tsaya yaki shigowa zuciyarsa na dokawa da sauri
Muryarta ya sake jin ta doki dodon kunneshi "Da gaske mama zai aureta ?
"ban da abunki ummita ai wannan nufi ne na Allah "Kai mama babu wani aurenta da zai yi ,zai dai yaudari yar mutane ne kawai ba aurenta zanyi ba," ya shirya auren ne, idan ma auren zai yi yana da kudin auren ne ?
abinda ta faɗa wa mama ya bala'i tsaya masa arai ya ɗan cigaba da tsayuwa yaji me Mama zata ce " ai shi kudin aure ba'a tarasu ummita kuma ai yana da aikinsa ko...?
"Yaushe aka soma aikin da zai wani tattago muku aure, dan nasan Abba dake kawai yake son wahalarwa dan yasan ba sisinsa da zai kashe idan ma auren zai yi ...
"Ke kuma kina bakinciki ba ?
"Wallahi kamar kin sani mama ,idan kika ji yadda zuciyata take bakinciki idan Abba ko ke kuka yi masa ba..
"Banason cigabansa mama ,duk abinda zai zama bakincikinsa dadi nakeji, farincikinsa haushi zake ji ,"kul ummita bana so ..
"Bana son kina faɗar haka akansa "ki fita hanyarsa ummita ki daina masa mugun alkaba'i, idan baki daina ba zaki samu matsala dani"ai nasani mama kinfi son shi dani "kwarai kuwa shi nasani kafin na sameki a duniya ,ki daina masa mugun fata kinji na fada maki...
"To naji ...
"Ba to kinji ba kice kin daina "
"Na daina ta karasa maganar tana turo baki sai da yaji sunyi shiru sannan ya shigo bakinsa ɗauke da sallama mama na ganinshi ta saki fuska tana murmushi tare da amsa masa sallamarsa ita ko ummita duk da sanin mahimmanci sallamar kin amsawa tayi dan shima haka yake mata duk lokacin da sautsayi yasa ta shigo inda yake da sallama batare da sanin shine ba baya amsa mata , ya samu guri kan kujera mai zaman mutun uku ya kwanta yana "furta washhhhh Allah nah .."sannu ka gaji ko ya aikin ?
"Babu dadi mama munje mun tadda aiki sosai ,"to Allah ya taimaka yayiwa rayuwa albarka ,yace "ameen mama na gode sosai ina alfahari dake "nima haka a kawo maka abinci ?
"Sai zuwa anjima yasan ko yace a kawo fat lion ce zatayi ....

a parlour'n ya dauki shiru can ummita tace "mama ki aramin caza ,mama tace bazan bayar koda nasan inda tawa take bare banganta ba , ke ina taki?
" ta lalace tun zuwan su Maryam da tawa suke amfani fashi sun lalatawa mutun kayanshi ta k'arasa maganar cike da shagwa'ba " sai ki hakura ko kuma ki tambayi yayanki Ma'aruf tashi, ta kalleshi kawai ta watsar dan bazata iya tambayarsa ba ko mutuwa zatayi Gara ta margaya akan ta tambayeshi abu .....

Mama ta mike ta bar part din zuwa bangaren Abba dan itace da girki cikin haka sai ga maryam tashigo parlourn tana need din caza,ummita ta ta'be baki "gashin ta lalace sai kowa ya hakura " kai ummita ban da wulakanci fa "wallahi batayi nima yanzu na gama karamar murya agurin mama Amman ta Hana , Kawai Maryam taga tashin Ma'aruf da sauri tace "a'a ya Ma'aruf a she ka dawo ina yini ?
Bai kula ba ya dauko mata caza mai baki biyu dana iphone dana blackberry , har maryam ta juya ya kirata yace" gashi kiyi caji idan kingama ki ajiye min fuskar Maryam cike da mamaki tace" tau.....
Na gode Allah ya saka da alkhairi ...bai ce komai ba ya fice daga part din gabad'aya ..

Yana fita, aranta tace "anyi abu arziki nasan dan naji haushi ne ya baki ,taki na cika zan yi maza nasa tawa , dan mai mugun halin tsiya ...

Washegari da safe sai yaga cazar a hannun ummita a wajen kanta da alamun agurinta cazar ta kwanta dan yasan Maryam ba part din mama ta kwanta ba, kar'ba tayi a hannunta tayi amfani dashi bai yi magana ba dan baya son abinda zai sake hadashi daita ya dauki cazarsa ya saka cikin ajihunsa ya ƙara gaba .

*******
Tsawan watanni uku kenan da soma aikin ma'aruf kuma har lokacin bai taka zuwa gidansu suhaima ba, iyakacinsa daita waya shima ba koda yaushe ba, tayi naci tayi kuka amman yaki zuwa sai dai yayi alƙawarin duk randa aka je masa zai cigaba da zuwa gurinta kamar da, ɗan bazai juri zuwa tana cazashi da salonta ba .. ....


Two friend's (bsbs)

💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~TRUE LIFE STORY~

FREE NOVEL NOT FOR SELL


AL'QALUMAN



*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*


~DEDICATED TO~
*JIKAR KULU*

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim


PAGE 14

......kamar yadda ma'aruf ya fahimtar da Abba cewar aure yake da bukata , haka shima rayhan ya cire kunyar dake tsakaninsa da abba ya sheida masa cewar ummita yake so da aure , wannan al'amarin yayi mugun d'agawa Abba hankali matuka, saboda a tsarinsa ba rayhan yaso ya auri ummita ba ,amina yake da burin bashi a matsayin matar aurensa ,ita kuma jiddah ta auri malik , amman babu yadda zai yi tunda har shi yaron ya rigada ta furta .
dan haka cike da sakin fuska ya bayyana farincikinsa a fili tare da sanya wa lamarin albarka , Abba bai yi sanya a gwiwa ba a ranar ya nemi d'an'uwansa daya rage masa a duniya injiniya sagir ,wanda ya kasance mahaifi ga rayhan . ....


Injiniya sagir da Ibrahim wato abba da mahaifin ma'aruf shuaib ,da mahaifiyarsu aslamiyya ummasalma , uwarsu daya ubansa daya , dukkaninsu ya'ya hajiya inna ne .

Shuaib shine babba , sai Ibrahim sai sagir wanda suke da tazara sosai atsakaninsa da Ibrahim , dan hajiya inna tayi bari biyu kafin ta haifeshi ,sai auta ummasalama ..
Sun taso cikin gata da kulawa agurin mahaifinsu alhaji Ma'aruf wanda ya kasance haifanfen jahar lagos , iyayensu ne suka zo cirena suka haifesu babu laifi mahaifinsu alhaji shehu shinkafi tsayayyen namiji akan iyalinsa yana da rufin asiri daidai gwargwado , yana daya daga cikin masu sauke abinci kayan masarufi acikin garin agege yana manya manyan shaguna a kwakwauku da ake sauke masa wake ,giro da duk wani nau'i na masa rufi ,ya shahara sosai ata wannan Sa'a, duk wanda ya kwana ya tashi yasan da zaman alhaji Shehu , ta kowani bangare yana kula da yaran sa da ƙoƙarin ganin ya basu wadataccen ilimi ,duk cikin yayansa babu wanda bai yi karatun boko ba dana addini ba sannan babu wanda bai mallakawa shago kayan masarufi domin tsayuwa bisa kafafunsa ,haka suka taso har girmansu maza suka yi aure haka ma matan sukayi suka gina babban family ..

a tun farko tasowarsu shuaib da Ibrahim sun taso da rufin asiri sosai ,yayinda shi injiniya babu , dan ko aiki ba yayi a lokacin ,duk da ya kammala karatunsa .
injiniya yayi karatu sosai , dan shi bama a kasar yayi karatu ba, yayi karatu ne a karkashin gwamnati jaha sakamakon injiniya sagir Ma'aruf akwai tarin ilimi dan akwai shi da nacin akan karatu .
gabad'aya karatunsu tun daga primary har zuwa University anan kasar sukayi , injiniya ne kawai yayi a wata ƙasa, ya fito da mafi kyawun sakamako kamar sauran yan'uwansa , basirarsa yasa jaharsa ke alfahari dashi , sai dai lokacin daya gama karatunsa ya dawo kasarsa ya rasa aikin yi ...
bai dogora da tarin dukiyar da Allah yayiwa yan'uwansa da danginsa ba ,sannan bai nakasa zuciyarsa ya koma zaman jiran tsammani daga garesu ba ,ya samu aiki a hukumar nepa , har zuwa sanda ya taka matsayin da yake yanzu da taimakon yan'uwansa , shekararsa biyu a ma'aikatar nepa ya samu canji wajen aiki zuwa hukumar kasa (land and survey) lokacin ummasalma tana matakin karshe a secondary ..

Shuiab da fatima auren zumunci akayi musu wato mahaiyar Ma'aruf da mahaifinsa ,ita hajiya fatima wacce ta koma hajiya umma a yanzu diyar yayan hajiya inna ce da suke ciki daya, asalima a hannunta ta taso har zuwa , lokacin data isa aure, shuaib ya ganta yace yana so cikin yarda Allah suka daidaita kansu har ta kai su ga aure .

shi kuwa Ibrahim a wani zuwa daurin auren abokinsa da yaje kasar cotono yagano mairo mahaifiyar ummita ,
Wanda ya rage sauran shekara daya ta kammala karatun ta na zama malamar likita .
"tunda ya daura idanunshi akanta ya rasa sukani da walwala har sai da yasa akayi masa magana daita ,mairo bata kasance mai son kula samari ba, amman
DOWNLOAD
DOWNLOAD

2 Comments On WANNAN CE QADDARARMU
avatar
amina-4

11 months ago

Reply

Interesting novel

avatar
amina-4

11 months ago

Reply

Interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment