Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


"kuma  ita  yarinyar  ma da  kake  ƙoƙarin  illata zuciyarka  akanta bata  sonka , hasalima baka cikin  tunaninta ,kayi hakuri  ka raba zuciyarka da soyayyarta , idan so cuta ne ai hakuri magani ne  , duk kabi ka canza  akan common mace  ,macen ma da bata  sonka .......
" ni yaushe zan iya wannan wahalalliyar soyayyar ya matso kusa dashi sosai ya dafa kafad'arsa  " haba  kamar   ba  muhd Sa'id  din dana sani ba  mai  manyan yammata , kana fa da  budurwar  data fi ummita  komai  ka rabu daita ka hutawa rayuwarka  .....
  
  Sai  lokacin  muhd Sa'id ya d'ago kwayar idanunshi   ya  dubeshi  zuciyarsa na wani irin harbawa da kyar ya buɗe bakinsa  "  wallahi  babu  kamar  subai'a  acikinsu , subai'a ta  daban ce  acikin matan duniya a zuciyata ,   amman   zanyi  hakuri  tunda abun ya  kai  ga  haka , sai dai kasani   bazan  taba  daina   son subai'a ba  a rayuwata   muddin  rai  ina  tare  da  kaunarta .

" waɗan  kayan  kuma  bazan  ɗauki  ko ɗaya acikin su  ba,   ya buɗe   motarsa  ya ciro wasu  kayan, manya ledodiji ne  guda   huɗu  har da  karami  guda  biyar ka haɗa  mata  dasu duk na bar mata  ,ba kaya ba ko zuciyata ce a hannunta bazan iya amsa ba  bare wasu  kayan banza ..... ..

Tausayinsa  ya  cika zuciyar ma'hruf  ,   sosai  zuciyarsa  ke mamakin taurin  zuciya  irin na  muhd  Sa'id  akan ummita  , ina ma tana son shi ?
"Ina ma Abba  bai yi mata miji ba tabbas da tayi sa'ar samu nagartacce   miji a rayuwarta   ya yarda ya  amince  da irin kyakkyawar soyayyar da yake  mata , a kallon da yake masa  yasan   yana  matukar  bukata da kaunar  ummita  arayuwarsa , irin namijin  da  kowace mace take fatan  samu  kenan namiji  da  zai  soka  da d'aukacin rayuwarsa .......

  Ya  runtse idanunshi na second  biyu sannan ya buɗe  cike  da tsananin  tausayawa sai dai hakan bazai hanashi ya fahimtar dashi gaskiya ba  "Muhd   Sa'id  ka ɗauki  kayanka  kaga   wanda  ka kawo  kwanaki ma  ba'ayi  amfani dasu ba ,matukar  ka  bar kayan  nan  ni zaka kulle ciki  tashin hankali ..
muhd  Sa'id  bai ce  masa komai  ba , ya k'arasa  ya shige   motarsa  ya soma ƙoƙarin  tayarwa  "duk  ma  abinda  zai  faru  da  kai  ya dade bai  faru  ba amman   bazan  ɗauki  kayan ba , ya tashi motarsa mai  gadi  ya buɗe  masa tangamemen  get din gidan   ya   wuce a guje  ya bar ma'hruf  tsaye yana  kallon get ....

Sadik  da  sadam  ma'hruf  yasa suka sake d'aukar    kayan   zuwa d'akinsa   tun  Abba bai dawo  ya  gansu ba sannan  ya  nufi bangaren  inna  yana huci gabad'aya ya rasa me zai yi .....
Yana  shiga  ya iske hajiya inna  zaune tana shafawa goshinta man  aboniki  "lafiyarki  inna ? Ya faɗa da sauri  kuma hankalinsa a dan tashe saboda ganin yadda take mulkawa goshinta man zafi .
"Lafiyar  nan  dai da  sauki babana kaina ke ciwo  kamar ya cire tun jiya  "
Ya zauna akan kujera yana fuskantarta  "to ko asibiti zamu a duba min lafiyarki ?
"Mu bari dai  zuwa gobe mugani idan banji sauki ba sai muje "
"Yauwa  babana ni kuwa ina  son  nayi maka wata magana akan aurenka  "
ya  gyara  zama tare da ciro wayarsa daga aljihun  wandonsa  "ina  jinki  iya rigima .
"wacan dangin agumuwar  uwar taka ce iya rigima bani ba ",to ya isa Karki zagar  min uwa a canza  magana  ina jinki "
"Yanzu kai me yasa ka zabi auren mata biyu da kuruciya ?

Ya lumshe  kyakkyawan  idanunshi  cike  da takaici  , inna  ta tsotsa masa inda ke  masa kykyai a dan fusace yace  " wa  yace miki ni na za'ba ?
"Iyayenka  mana  nan suka zo suna babatunsu  abu  kamar  a garin mahaukata.
Ya  ja  tsaki  sannan yace   "bani nace zan aureta ba sune dai  suke son hadin  amman ni me zanyi da wata sakina "
"haba  abun kam  da mamaki  ace kai ne kace kana sonta   nasan da wuya , shine kai kuma ɗan munafurci ka amince  da zaka aureta  ?
"To ya  zanyi  da iyayena inna ? ya bata amsa yana furzar da huci mai zafi daga bakinsa  ...

"A'a  babu wani  zance ya zakayi ko kana sonta    zabar  ɗaya zakayi a  cikinsu ko sakina ko ita wacan  yarinyar    "
"Sai gashi kuma bana sonta ba ,bare akai   da zance  zaba  ,wallahi  inna bana  sakina  bana jin sonta a zuciyata  zan dai aureta ne kawai saboda umarnin iyayena ....
Hajiya inna ta tabe baki "A she kuwa zakayi auren takaici baka son mace zaka yi wani  zaman aure  daita   tayi  maganar tana kwa'be baki bare babu komai acikin  auren mata biyu sai ciwon hawan jini  .
"Ki ajiye wannan zance dan na  dade  ina jin haka ajikina  , ko ban auri sakina  ba zan ƙara aure a nan gaba  "to ai shikenan Allah ya sanya alkhairi  kaine  zaka  tsufa da  wuri  ai , haka kurum da kuruciyarka amaida kai tsohon karfi da yaji "ke wa yace miki auren mata biyu  yana tsufar da mutun ?
"Babu wanda ya faɗa nice naga misali akaron kaina kaga mai sunanka har ya koma ga Allah bazakace shekarunsa sun  kai saba'in ba saboda yanayin jikinsa  to babu hawan jini  babu ciwon   sugar  a   jikinsa nima kuma bai had'ani daita ba  dagani sai ni, murmushi  mah'ruf yayi saboda ya fahimci inda zanceta ya dosa    "nan suka  cigaba da hirarsu  har  bakwai saura   ya mike ya  shiga bayinta  ya dauro  alwala ya fita zuwa massalaci .
    bai dawo gidan ba sai bayan  isha'i, kai tsaye  bangaren  mama ya shiga  domin cin abinci  yana  shiga  da  ummita  idanunsa ya soma yin tozali    tana  shirya dining  table   sanye cikin wata  atamfar  cotedevo mai ruwan   blue  da zane fulawa mai ratsin baki , tayi kyau sosai  sai sheki fuskarta keyi  , kallo second  biyar  yayi  mata  ya  ɗauke idanunshi  akanta  yana lumshe  idanunshi   dan  baya son   yawon  kallonta  hakan na haddasa masa shiga wani hali .
  yadda   bai   sake   kallon inda take  ba  haka     itama  bata  sake kallonsa ba ,  ya  dauki remut ya  samu  guri akan  kujera  ya zauna tare da  canza   chennel zuwa  aljazera  ya soma kallon labarai  yana jin wani iri a gaba-daya jikinsa wani sanyin shauki ke ziyar gangan jikinsa  yana tabo masa emotion din da yake  ƙoƙarin dannewa acikin zuciyarsa  .

A hankali  take tafiya tana rausaya wanda ya  zame mata jiki har tazo ta wuce  ta  gabanshi  kamshin  sanyayyiye  turarenta mai tsuma zuciya   ya kaiwa hancinsa  ziyara , dole  ya  lumshe idanunshi  ba  dan yaso aikata  hakan ba ya d'ago da niyyar satar kallonta itama akaci sa'ar zata saci kallonsa idanunsu ya sarke cikin juna , a lokaci daya suka  ɗauke idanunsu ta cigaba da tafiya    ya   jan tsaki a  fili   " an sani ake take  sani ,hukunci wanda ya sani ya take yafi  wanda  bai sani ba  ......

Ta ɗan  tsaya  jimmmmm  tare  da  juyowa  domin ta ga da wa yake magana,  ganin  babu  kowa sai ita  yasa  ta  fahimci daita   yake   ,  bata  ce masa  kala   ba  ta tsura masa fararen idanunta  masu bala'in kashe masa jiki a duk sanda ya kalli cikinsu tana kallonsa zuciyarta na wani irin  tsalle  tana nazarin  maganar da yayi yanzu , shima kallonta yake fuskarsa babu yabo babu  fallasa   , a hankali ta  juya abunta ta cigaba da  rausaya qirjinta na dokawa  ya sake  jan  tsaki   yana  takure jikinsa  saboda wani sanyi daya    ziyarci  ilahirin  jikinsa har ta 'bacewa ganinsa bai daina jin abinda yake ji akanta ba , a hankali ya dinga fidda numfashi haɗe da sauke  ajiyar zuciya   qirjishi na sama da kasa yana ƙoƙarin kawar da abinda yake ji .....

yana  zaune  yana felling abinda    bai san ko meye ba da  dalilin jin haka    ya rayhan  ya shigo,  yana  ganinsa     ya   saki fuska yana    murmushi  haɗe karasowa  ya   mika masa hannu suka gaisa ya samu guri ya zauna  yana dan jan mah'ruf  da hira "Mah'ruf meye shirinka ne akan bikinmu  ?
Ma'hruf ya gyara zama ya kwanta akan  kujera "kai  shirin biki ya dama , ni dai  kawai a shafa fatiha shine babban burina  "haba dai ko bakayi komai  ba nasan abokanka  zasuyi "wannan kuma damuwarsu ce ba tawa ba "Nan kawar da batun aure  suka cigaba da hirar kwallo  atsakaninsu   cikin  haka ummita ta  sauko  tare da mama  ,suna ganinta kowanensu  ya gaisheta cike da girmamawa ta amsa  cikin sakin fuska ",sannuku yarana ya weekend ?
Duk suka amsa mata da  " lafiya  "
my  princess zubo  mana   abinci  ni da d'an'uwana mun kwana biyu bamu ci abinci tare ba   muryar   ya rayhan taji  ,
take   tayi  hanyar dining  tana ciccin magani  tace "ka jika da  shishigi da neman suna  shi yace maka  zai ci ne  ko kuwa shishigi   zakayi masa ?
" zuba mana tare  .....
On-expecting taji  saukar muryar da batayi tsamanin  ji ba  ta doki cikin dodon kunneta da zuciyarta wani  irin zirrrrrrrrrrr taji a  gaba-daya  ilahirin  jikinta  mai kama da shokin ,take jikinta  yayi  sanyi  "ai shikenan tunda  kinji daga bakinsa sai ki  kyale min yarona ki daina zakewa   mama  ta fad'i haka tana barin parlourn  zuwa part din Abba  ...

Ummita ta rausayar da idanunta sannan ta soma   zuba   musu abinci  tare kamar  yadda  rayhan  ya faɗa  ,ta  saka musu  spoon guda  biyu, duk abinda take gabanta na faduwa haka jikinta na rawa tana jin yadda  idanunshi ke  yawo a sansar  jikinta  sai dai da  zarar   ta  d'ago sai taga ba ita  yake kallo ba .
 
a  hankali  take takowa  zuwa tsakiyar parlourn inda    center cafet  yake ta  ajiye plet din abinci still tana jin idanunshi akanta da yadda yake jan tsaki akai akai , ta koma ta d'auko musu ruwa da lemo mai  sanyi   ta kawo musu  duk tana jin wani irin ajikinta ko rantsuwa tayi bazatayi kaffara ba kallonta ya mah'ruf  yake  sai dai abun mamaki idan ta d'ago sai taga idanunshi na kan tv ko waya ko yana jan tsaki  "yauwa  my   princess  shiyasa nake  ..... ..
wata uwar hararar  Mah'ruf ya banka  masa  take  ya katse  abinda   yayi niyyar cewa muryarsa can kasa yace  " kaga malam  idan  kasan wannan shirmen zakayi tun wuri na kama gabana?
"kai fa matsalata  da kai kenan  girman kai  wallahi  me nayi wanda ba daidai ba yanzu  da   har  zaka .....
"ya isa dan Allah malam banason dogon magana ya  d'aga masa hannu  bai sake  cewa komai ba ya soma cin abinci yayinda ummi ta juya zatabi  bayan mama , rayhan  ya dakatar daita  "my princess ki dawo ki zauna kusa dani  ina ci kina ɗebe min kewa  "oh my Goddess god  rahyan wai meye haka ne  saboda Allah?
"Shiyasa kullun  yara basa  ganin mutane da daraja  ku tasa yara kanana a gaba kuna zuba  shirme  ya karasa maganar yana  mikewa   tsab yayi hanyar fita  "to ka tsaya muci abinci mana banza yayi masa yana jan tsaki  ummita dake  tsaye a kusa da kofar fita  tayi saurin matsawa  kar ya sauke fushinsa  akanta qirjinta na matsanancin bugawa da karfi  ,har ya rabe  ta gefenta ya  bar parlourn hankalinta bai gangar jikinta   .
haka nan ta tsinci kanta da rashin jin dadi fushin da yayi  ,ta juyo ta fuskanci ya rayhan  ,"kai ma kasan halinsa  abu kaɗan ke hassalashi me  yasa kayi magana  gashi kasa  yayi fushi  da abincin  ? Tayi maganar kamar zatayi kuka
Rayhan yayi shiru  tare da tsura mata ido  yana kallonta yana mamakin jin furucinta , abubuwa da yawa ya gani a tattare daita wanda ya kasa fahimtarsu daidai "yau ummita ce ke jin haushi dan ran mah'ruf ya baci ko me ?
Ganin irin kallon tunhumar da yake mata yasa ta kasa fita ta dawo kusa dashi ta zauna " kaci abincinka mana ka tsaya kana kallona kasan dai  idan kaima  baka ci abincin nan  ba kuka zanyi wallahi ,dan yau nice nayi girkin ba mama ba kuma na sha wahala sosai  ta k'arasa maganar hawaye na ciccikowa a idanunta tuni rayhan ya manta komai  "no Karki min hasarar hawayenki kinsan banaso"to ka samo ci a hankali yake ci suna hira har ya kusan takewa da  abinci ta tsiyaya lemu  a glass cup ta mika masa "kai my princess kina shagwa'bani  shiyasa nake ji tamkar nafi sauran mazan duniya Sa'a da zan mallakeki ,kin iya tattali ,kin iya kwantar da kai ,kin iya girki uwa uba kyau kina bayansu ma kina baiwa kala daban daban ina matukar farinciki da zan mallakeki  "ni kuma ina bakinciki da zan yi rayuwar aure da kai  tayi maganar a kasan zuciyarta yayinda a zahiri  kuwa  rausayarwa  da idanunta tayi  cikin nashi "ka daina   zugani fa ,"babu wani batun zuga anan ke din kadarace babba d'azu na samu labarin wannan natattacen  saurayin naki  yazo .
"wa kenan?
Tayi magana tana yatsina fuska .
"Wannan abokin mah'ruf din mana  sai dai naji dadin yadda Abba yayi masa langwa'bar da kai tayi sannan ta mike ta tattara kayan abinci ta shigar dashi kitchen ta dawo "kana nan ne  ko zaka wuce ?
"Menene ? Ya tambayeta yana tsareta da idanunshi "ina son zan shiga part dinsu meenal ne" ta bashi amsa tana wasa da yatsun hannunta "okay muje daga nan naje na bawa wannan sarkin fushin hakuri dan yanzu akan wannan  yar magana  sai ya dauki gaba da mutun ni kuma kinsan ban iya gaba ba  .
ba tace  masa komai ba suka fito tare ta kulle kofar ta zare key kamar yadda mama ta koyar daita ,tare  suka jera suna hira "my princess ya kira sunanta  "Na'am ya rayhan "me yasa bakya son shiga gurinsu Khadeeja ne?
   ki dinga shiga gurinsu mana  kuna gaisawa kamar yadda kike shiga part dinsu menal  "tayi jimmmmmmmm tana sauraronsa har ya dasa aya  sannan tace "mutun yana zuwa inda ake maraba dashi ne ba inda zai je ana hantararsa da nuna zallar kiyayarsa ba , ta tsaya a  daidai lokacin da suka kawo tsakiyar hanyar da zata kaita part dinsu meenal "to ya rayhan anan zamu  rabu sai kuma gobe idan Allah ya kaimu ka kular min da kanka ,sannan  karka manta  da shan  maganinka  kafin ka kwanta tana gama fad'ar haka  ta wuce "wani iri yaji  a zuciyarsa saboda yasan  maganarta ba akansu Khadeeja tayi ba akan mahaifiyarsa ce ..
Ya ɗan jima tsaye sannan ya juya ya bar gurin  ...

Bata  wani  jima a bangarensu meenal ba ta soma ƙoƙarin  barin part din  saboda kar  mama ta dawo bata sameta ba ,gashi kuma garin ya haɗe  da hadari tana fitowa ana fara yayyefi da sauri ta k'araso  bakin part dinsu ta buɗe tare da cire key  ta  shigo sannan ta maida key jikin kofar  batare da ta murza ba , ta tsaya tana  kakkabe jikinta sannan tayi saman .
Ta shiga  d'akin  mama  ta kwanta akan gadonta tare da lumshe idanunta  ko cikakken  minti goma batayi da kwanciyar  ba muhruf    ya shigo da ɗan  gudunsa  wanda   ruwan sama  ya koro  dicret yana shigowa  yayi uwar dakan mama ganinta yayi kwance ta ta kamkame jikinta guri  daya yasa ya tsaya akanta  tare da tsura mata ido yana kallonta  ,maganar muhd Sa'id ce tashiga dawo masa ummita ta dabance acikin matan duniya tafi sauran mata ,komai nata da daban ne  aranshi yace dan mata baka ci karo da dukiyar fulaninta ba da watakila haukacewa zakayi    ,jin  kamshin turarensa da tsayuwarsa akanta yasa    numfashinta ya soma  barazanar d'aukewa  daga gangar jikinta ta ɗan  bude idanunta  kaɗan taga ita yake  kallo har lokacin  yana murmushin da batasan ko na meye ba .
a hankali ta bude idanunta  ta zuba masa lulu eye's d'insa take ya waske yana sosa keyarsa yayinda  murmushin dake fuskarsa ya dauke ya maye gurbinta da kunci da bacin rai, hararata ya sakar mata  yana   ja tsaki  sannan  ya soma ƙoƙarin juyawa ya   bar d'akin sakamakon ganin  ta kamashi yana satar kallonta    ya dawo parlourn ya kwanta akan doguwar  kujera yana sauke numfashi "meye haka kayi kaje kawai kana kallonta to meye ma dalilin kallon ?
Yayi wa zuciyarsa tambaya yana lumshe idanunshi .
can bayan ruwan sama  ya tsaya ya hangota tana saukowa daga saman bene  ,yana ganin saukowarta ya runtse idanunshi kamar  mai yin  bacci ,har sanda ta k'araso ta tsaya akanshi tana kallonsa tana murmushi tana zagayeshi zuciyarta na dauke da lissafi iri iri  can data  ga  alamun zai motsa  sai  tayi saurin  shigewa  bayin dake manne da parlour'n  ,tayi alwala tazo ta ɗauki hijabinta dake ajiye agun sallarta  na parlour'n ta  tada sallah .
Zuciyarsa ta cika da mamaki saboda yasan da baya parlour'n kwance  a d'akinta   zatayi sallah ko d'akin mama  yayita lissafi yana nazarin irin kallon data dinga masa mai kamanceceniya da wanda yayi mata ya rasa gane ma'anarsa  ta idar da sallah nazarinta yake  cikin haka kiran  suhaima ya shigo wayarsa  ya yunkura hannunsa rike da  wayar  ya  mike tsaye  batare daya  d'aga wayar ba ya  motsa lab'bansa a hankali tamkar wanda bai son yin magana  "kije  kiyi wanka  sarki  sannan ki dawo ki sake  wata sallah  a matukar firgice take  kallonsa tana maimaita maganarsa gaba-daya ta rasa a wani mazauni zata ajiye maganarsa ita ba janaba tayi ba ,   wankan uwar me zata yi ?
  har ya  bar d'akin idanunta na kanshi tana kallonsa fuskarta da tsantsar mamakinsa  naunauyen  ajiyar  zuciya ta sauke tare da jan tsaki "aikin  banza kawai , kai kasani kinibabbe kawai  ni  babu  wani wanka da zanyi  tunda ba jini  nayi ba ko iskanci  ta mike tana ninke abun Sallah..

*****
Daren ranar  kasa runtsawa tayi kamar yadda  rayuka da yawa suka tsinci kansu cikin kasa bacci  ,ummita tunanin maganar mahruf daya faɗa mata take , Mah'ruf tunanin abinda bai san ko meye ba wanda  yayiwa zuciyarsa diran makiya ya hanashi sakat , suhaima tunanin rashin lafiyar mahaifiyarta ga bikinta yana karatowa bata shirya komai ba , rayhan tunanin mahaifiyarsa  da ummita  yana son kowanensu arayuwarsa , abu mafi  bakinciki garesa shine  rashin sonsa da ummita batayi  ba ,muhd Sa'id soyayyar ummita da tayi masa kamun kazar  kuka  ,sakina tunani da  shawara  barin rayuwar  mah'ruf  ,yayinda hajiya  inna ta kwana  zazzabin ciwon kai .
  washegarin  ranar  lahadi tun da  sanyi safiya mah'ruf ya  ɗauki hajiya  inna a motarsa sai asibiti , an dudubata tare da bata magunguna , suna kan hanyarsu  ta dawowa gida ne  hajiya inna  ta  hango ummita tare da meenal suna tafiya a gefen  titi  "kaga  ja'irar yarinyar  nan  ji yadda take tafiya akan titi kamar  zata balle  ko tsoron titi bataji  ,tayi saurin  yin kasa da glass din motar  ,"ke  yar agumawa jikar agumawa   can inna ta kurma ihu  adaidai lokacin da wata mota ta kwaso aguje zatayi kansu  wani irin burki  mah'ruf  ya taka yana dukan sitiyari  tare da duban inna da hankalinta gabadaya yake gurinsu    "ba zaki  masa ba yar banza  sai mota ta bugeki    kinyi da kanki kamar  na miciji, shegiyar yarinyar sai kin haifawa ubanki  hawan jini  koda yake   idan kin mutu ubanki  bai  da harasa sai wannan uwartaki  ..

ummita  dake gefe  ta watsawa hajiya inna  katuwar harara ",ina ruwanki idan motar ta bugeni ?
"Sannan kin damu kanki da agumawa ai  suma  mutane ne  kamarki  killa ma agurin Allah sun fiki jin tsoronsa  "Inna Lillahi wa Inna lillahi rajiun "babana kana jin abinda shegiyar nan take faɗa min  ,ni agumuwa suka fi agurin Allah ?  Kai  buɗe  min murfin mota  na  fita naci uwarta la'ada waje ,ni wannan yarinyar zatakawowa iskanci irin na mai shayi  ya sai da uwarsa  ya sai gayen shaye ?
Tana ƙoƙarin  bude kofar Mah'ruf ya falla da gudu bai  tsaya a  koina ba sai a haraban gidan, mah'ruf na bude kofa ta fito  ai kuwa  tana  gama fitowa ta zunduma ihu da kururuwa take mutanen gidan   suka  fito suna tambayarta  "lafiya hajiya  inna ?
injiniya dake labary a  bangarensa yana karatu ya leko ta window ganin inna  ya dafe goshinsa  ,sannan ya fito yace  kowa  ya koma  ciki.
Take mama ta dake ƙoƙarin fitowa ta  juya ta koma    cikin gida ,su hajiya ummah  suka cigaba tsayuwa dan lamarin hajiya Inna babu sauki  "lafiya inna wannan ihun  fa  ke da wa ?
"Ina fa lafiya yau a gidan idan baku  ci min uban ummita  ba hankalina bazai  kwanta  ba ,wallahi tallahi sai hawan jini ya kamani kai har dogon suma zanyi .. ....
"Kwantar  da hankalinki Inna me ummita miki ?
"Wai kamar ni ummita zatace  agumawa sun fini daraja agurin Allah ta k'arasa  maganar  tana kuka ,a gaban babana ta faɗa min haka gashin nan  ka tambayeshi idan karya ne ...
Injiniya ya dubi Mah'ruf domin son  jin gaskiyar lamari a daidai wannan lokacin ummita da meenal suka shigo harabar gidan .

" Ke  ummita da dukkanin  alamun fa Inna makirci zatayi miki  "sai tayi   ta  Allah ba  tata ba Allah yafi karfinta , ganinsu  yasa injiya ɗauke  idanunshi akan inna ya meida akansu .

A hankali suka k'araso "sannu  da gida  dady suka hada baki gurin fadar haka  "sannu da  gidan uwarki  ni zaki kalla a bayyanar nasi kice agumawa sun fini  daraja  agurin Allah ?
Wallahi  yarinyar nan kin cuceni kin gama da rayuwata  tayi kan ummita gadan-gadan zata cafkota .
"dan  Allah ni inna ki rabu dani   ummita ta fad'i haka tana buge hannu inna dake ƙoƙarin sauka ajikinta  nan  take zuciya ta zowa mah'ruf  wuya ransa  yayi  maseefar ɓaci  bai san sanda ya k'arasa  gurin ya ɗauke ummita  da wani gigitaccen mari  Tasssss kake  ji  batare da yayi magana ba , gaba-daya mutanen dake gurin sai da  zuciyarsu  yayi tsalle hatta mama dake bangarenta  sai da taji  gabanta ya fad'i ....

"yauwa babana tsohon albarka  ka min daidai  wallahi ,kuma sai yau na tabbatar da kana sona kana kaunata , haka nake so ,ka gama min komai  tunda ka wanke min fuskar  mara kunya da mari wuce muje  .
injiniya ya sauke naunauyen ajiyar zuciya ya juya ya  wuce  shima  ransa a bace ,ummita kuwa kasa kwakwaran motsi tayi hawaye ya cicciko a idanunta ta dawo tamkar mutun mutumi a tsaye , ta daina fahimtar komai saboda zafin marin  , hawaye  ne suka  shiga turereniyar fitowa  daga kwarnin idanunta "muje ciki meenal  ta kamo hannuta itama hawaye na gangaro mata da kyar take d'aga kafafunta kamar yadda  mahruf yake daga kafafunshi da  kyar yana takawa qirjinsa na kuguden bugu saboda marin da yayiwa mata,bai  taba nadamar marinta  irin na yau ba , hannunshi ya dunkule guri daya sai da  jijiyoyin gurin suka mike  gabadaya yana jin tuttukin  bakinciki mara misaltuwa .

    ummita na  isa bangarensu ta zube akan kujera, meenal ta zauna kusa daita tana bata hakuri kanta ta d'aura akan cinyar meenal tana kuka  "me nayi masa menal ya mari ..?
"Me yasa baya tausayina ?
"Me yasa yafi son hajiya Inna a kaina ?
"Ki faɗa min  abinda nayi masa  yanzu ya mareni "bakiyi masa komai ba kiyi hakuri Allah zai saka miki ..
Mama ta k'araso ta tsaya akansu tana tambayar menal  "halan ita da hajiya  inna ne ?
Meenal ta kad'a mata kai alamun "eh ,nan ta shiga karowa mama  abinda ya faru "to ita meye yasa ta fada mata haka ?
"Sauna in fada mata duk abinda inna zata faɗ akan dangina kar ta sake ta tanka  bare Inna sa'arta ce maganinta kenan ai baba babba yayi min dai-dai  "tana  gama fad'ar  haka ta hayewarta sama ...

Can bangaren inna kuwa faɗa ne ya kaure a tsakaninta  da Mahruf "sai nacin take masa  tana fadar "sai yau kayi min daidai babana ka sani  farinciki  mara iyaka yau " a fusace yace "ai dole kiyi faricikin tunda kinsa  baki da  gaskiya kin jawo na mareta a karon banza  , 
"Dan Allah  inna Sai yaushe zaki gane Allah daya ne  duk  abinda Allah ya kaddaro babu wanda  ya ... ?
"Ya isa babana banason jin  wannan cacar bakin naka duk ka tofe min jiki  da yawo kana wani hakikancewa  akan nice ban da gaskiya ubanka nayi mata ko uwarka da zakace bani da gaskiya ?
"Duk ma abinda zakice kice amman  wallahi kece baki da gsky me yasa kika zagi mahaifiyarta , na mareta ne  ba dan ta rama zagin da kika yi mata ba , na mareta dan ta kai hannuta  jikinki kuma agaban dady  ,da maganar baki da baki ta faɗa miki wallahi  bazan mareta ba , yana gama fadar haka ya  juya   fuuuuuuuuu  a fusace ya fito  daga d'akin "ka fashe karewar kunburi mara kunya kawai  fitsararre  mai wuya  awa marikin lema a bakin kofa suka haɗu da injiniya
DOWNLOAD
DOWNLOAD

2 Comments On WANNAN CE QADDARARMU
avatar
amina-4

11 months ago

Reply

Interesting novel

avatar
amina-4

11 months ago

Reply

Interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment