Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

ya koma kanta " a'a ke kuma ya haka kinyi shiri kamar wata almajira lafiya ko wani ne ya mutu a danginku ko me ya faru haka ?
dukkaninsu kallonta suke a hankali meenal ta kwashe da wata uwar dariya , ita kuwa ummita ko ajikinta da dai ta gama magsnarta ta fita harkarsu , duk abinda tayi akan idon ma'aruf da abokinsa jafar, shi kanshi jafar dariya yayi sosai har da rike ciki " wannan yarinyar case ce fa , "shiyasa na tsaneta , saboda bata kwantarwa da mama hankali ya K'arasa maganar yana jan tsaki yana tunanin irin dukan da zai yi mata idan ya ka mata ....

Ita kuwa Khadeeja da raliya ransu a 'bace suka nufi bangaren mama kai kara, baiwar Allah tana ganin fuskarsu gabanta ya fad'i tasan da dalili , nan suka shiga faɗa mata abinda ummita tayi musu hakuri ta basu tana rarrashinsu , tsokanar ummita na bakanta ran mama sosai ....

Ummta na son mahaifiyarta kamar me saboda tsanar data ga inna ke yi mata, hakan yasa bata ragawa hjy saudat da inna duk da mama na taka mata burki , mama sam bata takurawa ummita gurin aiki dan ta lura bata son yin aiki duk lokacin data sata yin aiki zata haɗu da 'bacin rai dan haka ta daina sakata komai idan ma'aruf ya shigo yaga mama na aiki ummita na kwance tana kallo ,haushi yake kamashi yayi mata duka sannan yace dole sai tayi ,sam basa jutuwa dashi dan haka tafi son rayhan da Usman basa takura mata sai dai su su taimaka ma mama suyi mata komai .

***

Wata rana ummita suka haɗu da rashida a harabar gidan ta fito daga ciki ita kuma ummita zata shiga cikin gida , rashida ta kalleta tayi murmushi tace "a'a su ummita dai "
Ummita ta ta'be baki tana kallonta batare da tace mata komai ba rashida ta dafa kafad'arta " ya naga kina haske haka ?
Rashida kanwar hajiya hjy saudat ce Kuma matar aure ce da ya'yanta , the nest thing ummita ta cire hannuta a kafad'arta tace ", a beg oooooo am not bleaching it my skin oooo am just glowing in grass and disiar kwanciyar hankali, I know you are my enemies members plz don't put eye's in my life , I know you have PhD in , plz minding your business and tell the enmis am doing well munafukai kawai ....tana gama faɗar haka ta juya tayi bangare su .

aiko a zuciye rashida ta koma cikin part din hajiya saudat ta koro mata duk yadda suka yi har da karya ko gama ji hjy saude batayi ba tayo part din hjy mama ta dinga zazzaga bala'i Wai ummita ta zagi rashida " aunty Rashida A she asaran kudin tara akayi ta ina na zageki ? "Faɗa min
maganata tayi kama da zagi ne bancin kalmar munafukai da nace "uwarki ce munafuka gata nan agabanki tsaye shegiya jikar agumawa masu asiri ..... tunda hjy saude ta soma zagin mama ta rike kirjinta da kanta da taji yana jujjuya mata , kuma hakan bai sa hajiya saudat tayi shiru ba, har sanda ma'aruf da rayhan har ma da Usman suka shigo parlour'n , take rayhan ya riko hannun hjy saudat shi kuma ma'aruf yayi gurin mama yana rungumeta ajikinsa tare da kiran sunanta .

" haba mama me yasa kike yin haka inji cewar rayhan , haka babu kyau fa har bangarenta zaki bita kina zaginta ,"kai kasan abinda shigiyar yarinyar nan tayi ne ?
"Koma me tayi mama bai dace ba dan Allah ki daina biyewa hajiya inna har part dinta ya kaita yana mata faɗa yana ƙoƙarin dawowa d'akin mama ya ga Usman da ma'aruf sun riko mama da sauri ya k'araso garesu a kidime yana duban fuskar mama kwata kwata bata numfashi da sauri ummita dake kuka ta bude bayan mota suka sata suka nufi asibiti daita, gwajin farko likita ya fahimci jininta ne ya hau nan suka shiga ƙoƙarin bata taimako gaugauwa ..
Likita ya fito daga d'akin yace mutun ɗaya ya biyosa dukkanknsu suka shiga dakin cikin tashin hankali ..

Da sauri ummita tashiga d'akin da aka kwantar da mama ta tsaya akan mama hawaye na zubowa daga idanunta, a lokacin tunanin rayuwar da ita da mahaifiyarta ke yi acikin gidan ke dawo mata , irin rayuwar kunci da suke yi da mahaifinyarta acikin gidan tamkar marasa galihu kallon mama take yi wadda ita kaɗai ce gatatan a yanzu a duniya gashi itama a kwance rai a hannun Allah a sanadiyyar rashin jin maganarta, sai ya'yan da ba nata ke jin maganarta da tausaya mata , tunanin yadda zata sauya rayuwarta ta zamo abar alfaharin ga mahaifiyarta take ,tana cikin wannan tunani taji ana sallama ta amsa haɗe da juyowa domin ganin mai shigowa ganin wanda yayi sallama yasa gabanta mummunar faduwa kafin tayi yunkurin mikewa ya soma surfa mata bala'i "shegiya munafuka, mayyah kin wani marairaice kamar ta Allah kina kukan munafurci wallahi yau shine zai zamo karo na karshe da mama zata samu wata matsala akanki shashar banza kowa yasan darajar uwarsa amma ban dake kamar ta rama amman taji hannun mama akan nata hakan yasa tayi shiru taki cewa komai ma'aruf na ganin mama ta farka ya K'arasa da sauri ya riko hannunta cikin nasa "sannu mama," ya ya kike jin jikinki yanzu?
" zuciyarki ta daina bugawa ? Gaba-daya yayi mata tambayar ajere yana kallonta jikinsa na rawa "alhamdullahi ma'aruf naji sauki sosai , ma'aruf Allah yayi maka albarka Allah yasa ka gama duniya lafiya , Allah ya jibanci lamarinka ban haifeka ba amman ka zame min abun alfahari ",ameen mama Allah ya baki lafiya ....

Kuka ummita ta fashe dashi haɗe da durkushewa kasa bisa gwiwonta ta rasa abinda zata faɗa tana bukatar rayuwar mahaifiyarta tana bukatar mahaifiyarta araye ...
Tsaki yaja yana fadin munafuka banza sai anyi magana kisawa mutane kuka kamar ta Allah , Usman daya shigo ya dafa shi "is okay ma'aruf ka rabu daita haka, yanzu ta lafiyar mama muke bai sake cewa komai ba, ya juya ya bar d'akin tare da kunar zuciya da kunar rai ,sun fi minti goma a tsaye sai daga baya Usman ya kamo hannuta jikinta na rawa yace "ki bawa mama hakuri ki bata hakuri cewar bazaki sake ba muryarta cike da kuka tace "bazan sake ba ta sake matsowa kusa da mama hawaye na zubowa daga idanunta ta kamo hannun mama cikin nata ta damke sosai tana kuka "mama kiyi hakuri ki
yafe min bazan sake ba " ummita na yafe miki duniya da lahira Allah yayi miki albarka Allah ya shirya min ke , Allah ya albarkaci rayuwarki ya baki miji na gari Allah ya juyo da hankalinki , Allah ya sanya miki natsuwa a zuciyarki , kiyiwa yayyenki biyayya ma'aruf da usman cikin kuka tace " ya Usman dai mama amman shi... ...sai kuma tayi shiru ta kasa karasa maganar ,kwana mama uku aka sallamota ta dawo gida ,bayan Hajiya umma da injiniya babu wanda yashigo dubata a manya gida sai kuma yara ..
ma'aruf ya sake tsanar ummita kamar me sakamakon bayanin likita na hawan jini ya kamata kuma yasan duk ummita ce sanadi , kwata kwata baya son ganin ummita ganinshi so take ta kashe mama a tunaninsa idan mama ta mutu su ne da harasa ita bata da ...


Tun daga wannan lokacin ummita ta dawo normal ta daina tsokanar kowa ta daina yawo duk wani rashin ji ta ajiye ta rungumi karatunta da mahaifiyarta sai dai duk wanda ya takata bata kyalewa sai ta rama koda kuwa hajiya Inna ce .....


Two friend's (bsbs)
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~TRUE LIFE STORY~

FREE NOVEL NOT FOR SELL


AL'QALUMAN



*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*


~DEDICATED TO~
*HUSAINA D'ANLARABAWA ABOKIYAR BESTY NAH, YAR PARTYN ABBA GIDA GIDA ,AKWAI AMANA DUK RUNTSI KANO SAI ABBA GIDA BIDA*🤗🤗


WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim


PAGE 18

..... Bayan shekaru huɗu da suka k'aru akan shekarun ummita , ta ƙara girma , kyawunta ya sake fitowa sosai , duk wani halitta na kyawun d'iya mace da daukar hankalin d'a namiji sun gama bayyana a jikinta, doguwa ce sosai sai dai yar sirirya ce , fara sol irin farin nan dake sheki tamkar wacce take shafa madara a jikinta , haka yanayin tsarin jikinta irin figure 8 din ce , mai cikakken kirji ce ,dukiyar fulaninta masu shegen kyau da ɗaukar hankali daidai kirjinta , sannan a tsaye suke cak masu gindin tasa , fatar jikinta a kwance take luwai luwai ga kyau ga laushi ko zata shekara bata shafa mai ba skin dinta bazai yamutse ba , tana da madaidaita faffad'an kugu mai haɗe da hips madaidaita , batun bombom sai zuwa gaba saboda rashin jikinta bai gama bayanasu ba ,tana da dara daran idanu masu kyau waɗan da suka wadatu da gashin ido masu matukar birkita kwalkwaluwar duk wanda ya kalli cikinsu , hakoranta masu haske ne dauke da dadashi mai duhu ,gata da siririn hanci da karamin baki da dimples Wanda ko magana tayi sai sun lu'bo ,ko cikin 'bacin rai take sai sun nuna , da zarar tayi murmushin kuwa ji zakayi kamar ka sureta ka gudu , sai wadataccen suman kai da gashin gira wanda suka kusan had'ewa da gashin kanta tsagun bakin da akayi mata suna sai maka mata kyau da sukayi kasancewarta fara , ga wani maseefaffen jin kai daya sarkafeta , da zarar ta gama aiki , sai karatu da kwanciya sai kuma kallo tare da narkewa a jikin mahaifiyarta, kullun mama na cigaba da rarrashinta tare da mata nasiha akan rayuwar duniya "tabbass nasihar mama na shigarta sosai , girmanta ya zama so boring saboda ta taso babu walwala da sakin fuska sannan babu yawon magana , acikin gidan taka tsantsan take da kowa har uban gayya ma'aruf, fuskarta babu annuri ko kaɗan , sai dai duk lokacin da aka ci mata fuska ko mamanta bata yarda sai ta rama , amman idan baka shiga lamarinta ba babu ruwanta da mutun .

Alhaji Ibrahim ya samu cigaba sosai a rayuwarsa bisa matsayin mahaifin ma'aruf daya maye gurbi a kamfaninsu na oil and gas gaba-daya su suna zaune a astate din small London dake unguwar daji, gidan da Alhaji Ibrahim ya ƙera yayi shi bangare bangare , kyakkyawan gida ne ginin zamani mai kyawun gaske ,samarin gidan sune ke zaune daga farkon shigowa, shi kuma injiniya yana ɓangaren hagu, alhaji Ibrahim na bangaren dama sai bangaren inna dana hajiya umma da Hajiya mama kowa bangarensa daban kuma duk sama da kasa ne har na hajiya inna bene ne sai dai ita a kasa take rayuwa saman tabarwa barwa jikokinta na gurin aunty Salma ....

A wannan lokacin Kabir dan aunty Salma yana da kanne huɗu Aysha, suwaiba wacce suke kira da aslamiyya ,Maryam ammar ,bangaren saudat kuma tana da yara bakwai abdulmalik ,rayhan Khadeeja ,Sa'adatu sadam , saifullahi sadiq.. a d'akin hajiya umma tana da yara huɗu Abdurrahaman ne ya kasance babba sai ma'aruf sai Hauwa wacce suke kira da jiddah sai ameena..

Har lokacin kan injiniya da Alhaji Ibrahim a haɗe yake Alhaji Ibrahim mutun ne mai mutunci da tarin tsaftataccen dukiya wacce ake sarrafata ta hanyar data dace .

duk yaran gida karatunsu na secondary a sanjosaf international School suka kammala ,ba kananan kudi Alhaji Ibrahim yake kashewa akan karatun ƴaƴansu dana kanwarshi ummusalma da injiniya yake ba ,ba dan gazawar iyayensu ba sai dan kyautata da kuma kauna irin ta y'an'uwanta ka ,har wannan lokacin Hajiya mama da Hajiya umma kansu a haɗe yake tamkar 'yan biyu hakan ya basu damar hada kan yaransu idan ba kayi musu kyakkyawan sani ba zai yi wahala ka bambacesu tsakanin dan wannan dakin da wannan d'akin ko kamanin yaran gida irin daya ne most especial ma'aruf da ummita tamkar an tsaga ƙara , komai nasu iri ɗaya ne babu wani bambanci idan ma akwai bambamci shi ya kasance namiji ita kuma ta kasance mace .
Ummita da ameena shakuwar da take tsakaninsu ta wuce a kwatantawa domin hatta bacci baya rabasu sukan kwana a duk inda suka so, sosai Hajiya mama ke jansu ajiki ,dan ita mace ce mai barkwanci ta mai dasu tamkar kawayenta duk inda take suna like daita har lokacin diyar hajiya mama ɗaya bata sake samun wani haihuwar ba .
kullum sake godewa Allah take da ya azurtata da samunta arayuwa, yayinda alokacin sheakarar ma'aruf ashirin da bakwai cif a duniya yana matakin karshe a jami'ar Bayero shi da rayhan shi kuma Usman yana cotonue gurin mahaifinsa, tun da suka kare secondary School mahaifinsa ya bukaci ya dawo ba dan ya musgunawa mama ba sai dan ya rage mata saukin wahala daga hajiya inna da take kallon kamar ana wahalar mata da ɗa da dukiyarsa ne, hakan kuma yasa ma'aruf ya fahimci lailai ba mama ce ta kawoshi duniya ba , duk da an sha faɗa masa hakan bai yarda ba ,ko daya san da hakan bai taɓa sauya mata ba ,yana nan tamkar ɗan cikinta dan ko mahaifiyarsa bata nuna masa wani abu ko nuna cewar itace ta haifeshi tsakaninsa daita gaisuwa dan komai nashi na dakin mama yayinda
Alhaji Ibrahim shi kuwa tamkar dan d'an'uwansa ya dauki Usman baya bambamta shi da ya'yan yan'uwansa ,sam bai ji dadin komawar Usman ba amman babu yadda ya iya tunda mahaifinsa yace zai dinga zuwan musu hutu duk lokacin da hakan ya samu ..

A zamantakewar mu'amula saudat har lokacin tana nan kamar yadda take ,bata da kirki sannan bata da haba haba da mutane saɓanin yaranta ,sam bata da .saukin kai ga zafin rai basu fiyye jituwa da mutanen gidan ba ga mugun son ya'yanta akan yayan mutane babu abinda bazatayi ba akan yaranta ta sha biyo ummita har daki akan sunyi faɗa da yaranta , idan ummita tayi galaba akansu haka zatazo tayi ta zage zage agaban hajiya mama Amman Sam bata d'aga kai ta kalleta sai dai idan ta fita , mama ta janyo ummita tayi ta rarrashinta tana mata faɗa, ummita ta rushe da kuka mama har ta yata kuka take tana son barin Ibrahim da danginsa amman idan ta tuna ummita sai ta sake sanyawa zuciyarta hakuri a lokacin takaicin kanta ta dinga yi da bata bar gidan tun kafin ta haifi ummita ba ,suyi rabuwar har abada .....
Bangaren matsalar inna kuwa ma'aruf ne ya ruguza dukkanin wani iskancinta da tayiwa mama yake rufe ido ya gurza mata har da dogon gaba ba ,gashi ita kuma Allah ya jarabeta da kaunarsa bata iya dogon fushi dashi ko fushi yayi daita sai tayi zazzaɓi dan haka ta rufawa kanta asiri ta dan saduda ta rage wani abun..
injiniya ya d'aukewa abba nauyi kai yara makaranta tun lokacin daya tsiyawa malik mota wanda ya soma dawo wa daidai shaye shayensa yayi sauki ba kamar da ba dan lokaci kokari ake a masa aure domin ya sake samun natsuwa dan tuni Abdurrahaman da Kabir sunyi aure , Abdurrahaman ya auri Aysha diyar aunty salma suna zaune a depemo shi kuma Kabir yana auren diyar aminin mahaifinsa ....
A daidai wannan lokacin walimar saukar Alqur'ani su ummita ya tashi ita da meenal da Sa'ada ,ana washegarin walimar mama ta bawa ma'aruf stone tace ya sawa ummita ajikin shaddarta sannan ya goge mata kayan ,babu mutsu ya amsa kayan darajar mama dan babu abinda zata saka shi yaki ,
gurin walimar ya cika makil da jama'a ,baka gane mutane kasancewar babbar makaranta ce data amsa sunanta ,sannan ta tattara manya malamai, kowace daliba ta sha farar shadda sol da a baya da mayafinta , maza kuma farar shadda kawai da hula , babu wanda bai je ba a family dinsu hatta ma'aruf yaje saboda mama , sai dai har lokacin da aka soma kiran dalibai uku uku suna karatu saboda da yawansu ummita bata hallara ba tana gida bata gama shirinta saboda sanyi jiki yayinda rayhan ke tsaye jaman jiranta yana tayata wasu abubuwa har sai da ran mama ya kai ga ɓaci sannan ta hanzarta ta fito cikin takunta na yanga ta shiga gaban mota suka bar gidan ,daf da inda jama'a suke yayi parking suka fito alokaci daya ,tana fitowa idanun mutane sukayi caaas akanta day day wani mutanen da basu kalleta ba saboda kyawun da tayi ahankali take taka kasa kamar mai tausayin takawa ya rayhan na biye da ita "ki saki ranki plz yau fa ranar farinciki ce duk yadda yake mata naci ,kin sakin fuskarta tayi saboda idanun mutane da taji suna yawo ajikinta gani faduwar gaba da kirjinta ke yi ,sake tamke fuskarta tayi har ta k'araso gurin zaman daliban amman bata daina jin idanun jama'a akanta ba yayinda rayhan wanda ke biye daita ya juya ya koma ,"wani malamin islamiyyarsu dake mugun sonta malam annafi ya dubeta yayi murmushin "nasan sai kinzo latti ai amman zamu haɗu a makaranta ne sai na miki bulala a shirin masu kyau , tayi murmushin kawai ta samu guri cike da sanyi jiki ta zauna akan kujerar data kasance tana jiranta , lokacin da aka kirata karatu babu wanda yasan an kiranta daga cikin yan gidansu saboda yawon mutane sai ma'aruf ne ya gayawa musu an kirata sannan suka tasu lokacin har ta fara karatun suratul Ibrahim cikin zazzakar muryarya mai dadi da saka natsuwa duk tarin jama'ar dake gurin babu wanda bai samu natsuwa a dalilin sautin muryarya data karade gurin ba
DOWNLOAD
DOWNLOAD

2 Comments On WANNAN CE QADDARARMU
avatar
amina-4

11 months ago

Reply

Interesting novel

avatar
amina-4

11 months ago

Reply

Interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment