Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

" kallo ɗaya zaka ma ummita ka fahimci a firgice take dan hatta suman Kanta sun baje a gadon bayanta wanda take zaka fahimci mai dauke dashi tana cikin wani hali .
" ke dan uwarki ba zaki sake shi ba ko ba magana nake miki ba kike sake makale masa , kin wani manne masa ajiki so kike ki dilmiyar min da jika ?
"da iskanci ma me ya kawoki d'akinsa ?
" so kike ki kulla masa kullaliya ta barin gari ko a ɗauka shima ɗan iska ne irinki ?
Da sauri ummita ta girgiza mata kanta alamun "a'a , magana take son yi amman bakinta ya kasa furta daidai da kalma ɗaya "to ta Allah ba taki ba makira ina allonki?
" allonki yana jahannama ....... Tayiwa ummita tambayar tare da bawa kanta amsa ..

Abba wani irin kallo yake musu fuskarshi da zuciyarsa kuwa cike suke da mamaki da alamomin tambaya iri iri ,a cikin ransa yake jin zafin furuncin inna akan ummita a tunaninsa koma me zai faru a tsakanin ummita da ma'hruf bai dace ta dinga furta munanan kalamai akanta ba, ai shi a ganinsa da ummita da ma'hruf duk abu guda ne agurinta , sannan a saninsa da tunaninsa yasan ma'aruf ba zai taɓa aikata wani abu na 'batanci ba , ya yarda dashi , ya aminta dashi fiyye da komai da kowa , duk wuya duk runtse ba zai jahilcesa ba ..
Inna mahaifiyarsa ce babu yadda zai yi daita dan bazai canzata ba, da zai iya daya tattara yayi kaura zuwa wani bagiren da iyalinsa , amman bazai iya guje mata ba suna nan tare har sanda mutuwa zata raba ...
inna kuwa ta inda take shiga bata nan take fita ba tana zagin ummita.
Jin jiniyar motar yansanda a kofar gidan yasa Abba juyawa da sauri ya bar d'akin zuciyarsa na kuna .

ummah ta dubi inna ranta a matukar 'bace "haba inna me yasa kike yi haka?
" me yasa ba zaki canza ba kullun fa girma kike ? Kamata yayi kibi komai a hankali tunda kike kin taɓa ganin ummita a d'akinsa idan ba da wani dalili ba ?
"Yanzu ma ki kwantar da hankali ba abinda kike tunani bane ina da tabbacin haka domin tarbiyar mairo bazata aikata wani abun asha ba ,"Idan kuma maganar gaskiya za'a faɗa lokacin da muka shigo d'akin nan waye rike da wani ?
Inna tayi saurin cewa "wannan jaira ce da idanuna na ganta shiyasa ma na kiraku ku zama sheida dan zaku iya karyatani saboda kun iya d'aurewa karya gindi tayi maganar tana ƙoƙarin damko ummita a matukar haukace.. "munafukar Allah ta'ala kawai maza bar d'akin nan , ummita ta saki ƙara mara sauti tare da saurin ra'bewa a gefen ma'hruf hawaye na bin kuncinta .
"ashhhhhh ya furta da sanyayyiyar muryarsa yana tare hannu inna da take kokarin kaiwa ummita dake makale da jikinsa duka , dan yasan halinta ba karamin aikinta bane ta kai mata duka ko rankwashi .
a hankali ya waiga ya duba bayansa inda jini ke fita har lokacin "matsa daga jikinsa aljana a kwaba ina ma 'barayin nan sunyi gaba dake mun huta da jaraba .... ....

Ran ummah a 'bace ta mikawa ummita hannu taso muje hankalin mamaki na can a tashi matuka, sai lokacin ummita ta samu damar buɗe bakinta da kyar tace "ummah jini a hannu ya ma'hruf 'yan daba sun jefeshi da tayis ta K'arasa maganar tana nunawa ummah gurin ..
ta gefen idanunshi yake kallonta tar da tsantsar mamaki a fuskarshi ,
yayinda har lokacin wasu zafafan hawaye ke bin kuncinta kallon second biyu yayi mata da idanuwanshi da suka Kad'a sukayi jajir dan har wani yaji yaji yake jin suna masa sannan zuciyarsa na sake dokawa akan kukan da take wanda bai san dalili ba ,yana jin kamar ya d'auke mata hawaye, jin tausayinta na ƙoƙarin cika tsokar dake makale da kirjinsa yasa yayi saurin kawar da zuciyarsa da idanunshi akanta dan baya son duk wani abu makamanci tausayi ya shiga tsakaninsu , shi duk abinda yayi mata saboda da Allah ne da kuma darajar mama dan mama ta wuce komai a gurinsa itace duniyarsa ko kara ta ajiye bazai iya tsallake shi ba .....
sai lokacin hankalinsu Inna ya kai gurin ciwon ..
Gaba-daya inna ta rud9e ta gigice tayo kanshi tare da fashewa da matsanancin kuka a lokacin da taga jini ,ga nama gurin har ana iya hangowa nan hankalinta ya sake tashi "nasan kaje taimaka wannan tsinanniyar jikar agumawar ce da bata kaunarka tsautsayi ya afka maka,"me yasa ka taimakawa yar banza yarinyar nan bakayi zamanka ba ?
"Maza taso muje asibiti ga yansanda can sun karaso ...
kanshi kawai ya girgiza mata ,"ba wani rauni bane zan je daga baya, sannan ya d'ago ya dubi fuskar ummita dake sharkaf da ruwan hawaye , two second yayi yana kallonta sannan yayi saurin ya mike ya sauko batare daya iya kallon maman rayhan da ummanshi ba, ya soma neman abinda zai sanyawa jikinsa tayi saurin matsowa inda yake batare da ta sauko daga kan gadon ba ,"yaya dan girman Allah kar ka bar kanka haka wata cutar zata iya shiga gurin ,ka d'aure ka ɗauki shawarar Inna....
Saurin katseta yayi kafin ya furta mata "kiji da kanki malama babu ruwanki da raunin dana ji, sannan ki san inda dare yayi miki ko banje ga likita ba zan warke....
a sirri yayi maganar a tsakaninsu cikin rad'a batare da makusantarsu sunji mai yace mata ba, sai tsintar fuskarsu sukayi cikin wani yanayi na damuwa mai wuyar misaltuwa , ta gefen ummita ya raɓa ya shige bathroom , tabi bayansa da kallo zuciyarta na wani irin mahaukacin bugu .....
umma ta k'arasa har inda take ta kamo hannayenta duka biyu ta mikar daita tsaye tana dubanta fuskarta cike da damuwa ta juya ta bar d'akin.
a hankali maman rayhan ta juya itama tana jan tsaki "lallai a irin wannan lalacewar za'a bawa d'ana natsatse auren wannan yarinyar ?
" ina bazai yiwu ba wallahi da sake duk ma yadda zanyi a fasa auren nan sai nayi ..
Daman tun farko bata son haɗin auren rayhan da ummita idan tana kaunar auren tana kaunar mutuwarta ..
Allah Sarki dan Adam kenan ita ta manta sadam danta yafi dan kowa lalacewa acikin zuri'a amman haka umma ta yarda kuma ta amince a aura masa jiddah ...
Kowa ya bar d'akin amman banda inna data kasa ta tsare ta kasa barin d'akin mahruf , tana zaune har ya fito yana goge fuskarsa da farin towel fari Kal da kallon mamaki ya bita dashi, duk tabi ta rud'e tana ƙoƙarin taimaka masa cikin saurin murya yace "no !no !! Inna"
"No Kuma babana kana ganin halin da kake ci ?
furzar da iska mai zafi yayi yana dafe kanshi"gaskiya inna kina da damuwa wallahi duk kinbi kin cikawa mutane kunne da hayaniyarki ..
Ya karasa maganar yana wurgi da towel saman gado sannan
Yayi hanyar fita waje , ta biyosa da sauri tana kiransa kamar zata tashi sama , har yayi nisa yaga shi take bi ya tsaya ta karaso inda yake tsaye "muje ko "muje ina ?ya tambayeta yana haɗe fuska ..
"Ki koma ciki Inna ki hutawa ranki ,dan girman Allah Inna ki dinga hutawa ranki fa .
"muje ki koma d'akinki ki huta koda yake lokacin sallama ma yayi nima da police sun kama gabansu zanje ayi min treatment din hannuna kinji innata , nasan duk saboda ni kike yi komai ma'hruf ma yana son Inna sosai muje kinji ,da kyar ya samu ya lalla'bata ta koma bangarenta ..

Ma'aruf na isa harabar gidan yaci karo da gangar jikin mutu sanye da bakin kaya da bakin face marks kasancewar filar wayarsa a kunne yake sannan ya karasa inda ya hango mutanen gidansu har ma da wasu daga cikin makwaftansu makil ga polisawa suna tambayar yadda abun ya faru , injiniya ne ya ci-gaba da magana "gaskiya ba zamu iya karar da komai ba saboda muna bacci abun ya soma faruwa hayaniyarsu ce ta farkar damu amman akwai yarona da kusan abu ya faru agabansa tun kafin police ya sake yin wata tambayar ma'jruf ya karaso gurin "yauwa gashi nan ma injiniya ya nuna ma'hruf ,nan fa yansanda suka shiga tambayarsa yadda abun ya kasance bai boye musu komai tun daga farko har karshe, ɗaya daga cikin police din yace" ko kuna suspeting din wani da aikata haka ?
ma'aruf yayi shiru yana ciza lip's d'insa na kasa ƙwaƙwalwarsa na zurfafa tunani akan wani abu daban da yake ji a sansar jikinsa mai kama da shocking a tarrayarsa da ummita a wanin da suka gabata , jin maganar police yasa ya dawo daidai ya dubi shi a hankali saboda ganinsa wannan banzar tbaya ce yayi ...
dan haka bai yi sanya a gwiwa ba yace "wannan kuma wace irin tambaya ce yallabai?
" suspeting kuma ? "alhalin ga shieda can ya nuna masu inda gangar jikin zaki yake yashe a kasa yana fidda numfashi sama sama saboda tayis din daya same shi a bangaren zuciyarsa ..
sai lokacin idanunsu da hankalinsu ya kai gurin a hankali police da mutane suka k'arasa gaba-daya domin ganin zaki .....
Kwance yake yana fidda numfashi da kyar , daya daga cikin police ne ya bude masa fuska nan take fuskarshi ta bayyana ,kana suka soma dube dube a harabar gidan ko zasu samu wasu abubuwa da suka danganci makami suna sake aikawa ma'hruf tambayar shi kuma yana basu amsa a dake duk sun dudduba ko'ina amman basu samu abinda suke tsammanin gani ba , sun jinjina wa ma'aruf matuka har ma suka cewa injiniya "aikin soja ko wani jami'in tsaro Yakamacesa , saboda karkafaffiyar zuciyar dake garesa amman aikin me yake yi ? Kallon dan sandan da yayi tambayar injiniya yayi kana ce " yana aiki ne a oil and gas ya bashi amsa da haka sannan suka cigaba da magana ..

a cikin gidan kuwa ummita na shiga parlournsu inda mama take kuka har lokacin ta zabura ta rungume ummita ajikinta tana wani irin kuka mai ban tausayi kamar ranta zai fita zuciyarta cike da tashin hankali ganin ummita bai sa hawayenta sun tsaya ba, ummah dake saye akanta tana bata hakuri tare da karfafa mata zuciyata " godiya Yakamata kiyi da Allah ya takaita wahala yasa abun ya tsaya iya haka ...."
Daga mata kai mama tayi hawaye na gongaro mata ta sake rungume ummita ajikinta tana kara tabbatarwa hajiya ummah "dole nayi kuka ,hasalima kuka murna ne ,da wani abu ya sameta ban san yadda zanyi ba , ni kaɗai nasan wahalar dana sha kafin na sameta a rayuwata "na sani amman tunda gashi Allah yasa an ganta cikin koshin lafiya babu abinda ya sameta sai mu godewa Allah "alhamdullahi Allah Na gode maka , Allah idan zaka jarabemu ka jarabemu gwargwadon imaninmu , addu'oi ta shiga karantowa zuciyarta na dokawa tana sake kwakwame ummita ,itama ummita kuka take sosai .. ...
Maman rahyan dake tsaye ta yatsina fuska "shiyasa d'a ɗaya bashi da wani amfani yanzu da mutuwa tayi shikenan sai tarihi ba mama ba hatta Jiddar da ba wani shiri take da ummita ba adalilin ma'hruf sai da taji babu dadi a ranta .
"dakata me ya kawo wannan maganar inji cewar umma ?
" Kema ai ba wani aikin ibada kika yiwa Allah ya baki fiyye da daya ba ..ki dinga sanin abinda zaki dinga faɗa ,ita rayuwa duk yadda Allah ya rubuta maka babu wanda ya isa ya canza maka ita, kaddara kuwa tana kan kowa mun godewa Allah daya bamu guda ɗaya a lokacin da muka cire tsammani ,kuma wannan dayar da kika raina wata rana sai ta zame miki dan hakin da ka raina ,dan ba'a yiwa Allah shigi acikin lamarinsa ....

Abba ya kira sunan daya daga cikin yansanda " "Sunday ogunnikan na gode sosai kada kuyi sanya gurin tsananta bincike ,zan iya kashe ko nawa ne akan sauran da suka gudu, yansanda sun dan jima ana tautaunwa dasu kafin daga baya aka kama zaki da tunin kafarshi ta soma kunbura dan da kyar yake iya takawa saboda bakaramin rauni yaji a ƙafarsa daya da bangaren kirjinshi da tayis ya caka ba akayi motar yansanda dashi domin kai shi hospital aba shi taimako sannan a shiga bincike ....

Injiniya ya dubi ma'hruf da har lokacin bai nufi asibiti ba, yana dafe da hannunsa mai ciwo yace "maza ka hanzarta zuwa asibiti ayi maka trement din gurin kada yayi maka tsami , a hankali ya juya ya nufi inda motarsa ke pake batare da yace komai ba "kai rayhan ka bishi mana kuje tare "tou dady rayhan ya amsa da haka yana biyo bayan ma'aruf da sauri ya buɗe masa dayan bangaren motar , jikinsa a sanyaye ya shiga motar ya zauna a kujera mai zaman banza zuciyarsa na bugawar daya rasa dalili sannan ya zagaya ya shiga mazauni direba ya tayar da motar suka nufi asibiti.
"ma'aruf gaskiya kayi namiji kokari Allah dai ya saka da alkhairi idan akace zakayi irin wannan taimakon ga ummita bazan yarda ba sai gashi kayi nagode sosai dan ni ka yiwa wannan taimako ,Allah ya bar zumunci ..
"Ka daina gode min....." "what ?
Ya waigo inda yake zaune yana kallonsa sam bazakace shine yayi maganar ba ya kada kanshi " Ai dole na gode maka kuma zan cigaba da gode maka har karshen numfashina domin da wani abu ya sameta bansan yadda rayuwata zatayi ba .. ma'hruf ya ja ƙaramin tsaki acikin zuciyarsa ya maida idanunshi gefen titi sannan yace "karka sake gode min saboda ba dan kai nayi ba duk ƙoƙarin nan nayi ne saboda inganta rayuwar mama ,dan ta rayu cikin kuncin rayuwa da wahala a gidan Abba idan wani abu ya samu yarinyarta tillo alhalin ina da halin taimaka mata banyi ba hakika banyi mata adalci ba .."haka ne kam Allah ya sake kiyayewa, wani asibiti zamu nufa yanzu ?
"Daji ya bashi amsa atakaice yana duba wayarsa ransa a matukar bace" dan me zai yi masa irin wannan tambayar kamar bai san asibiti da suke zuwa ba ?
rayhan bai sake magana ba ya ci-gaba da tuki haka ma'hruf da zuciyarsa ke tattare da kunci suna kaiwa daidai wani special hospital na kudi me suna tomi & Jerry special hospital yace "tsaya anan babu mutdu rayhan ya taka burki ya tsaya ma'hruf ya fito " ka jirani anan na shiga na fito ..
"Bangane ba ai dan na taimaka maka yasa dady yace na biyoka?
yayi maganar yana kashe motar haɗe da zare key ya fito cikin hanzari yayinda tuni ma'hruf ya soma d'aga zara zaran yatsun kafafunsa ,a hankali ma'aruf yake tafiya har ya shigo cikin hospital din shi kuwa rayhan tuni ya rigashi isa ciki suna magana da wasu daga cikin nutse din daya tarar akan duty bayan ma'aruf ya shiga , daya daga cikin nurse din dake tsaye ta kafe shi da idanun tana kallonsa kamar zata cinyeshi ,kallo ɗaya tayi masa taji yayi mugun tafiya da imaninta shi kuwa kallo ɗaya yayi mata ya dauke kanshi yana kallon wani guri , cike da rawar jiki ta nufi wani madaidaicin daki dashi ta nuna masa gurin zama duk idanunta na yawo a sansar jikinshi ta matso sosai tana ƙoƙarin kai hannunta daidai gurin shashin data ga alamun jini ,a atsanake ya ciro hannunsa mai ciwo batare da yace mata komai ba, dayan hannu na kan cinyarsa ya tokare , cikin murya irinta yan duniya tace "ka cire rigar mana domin na samu damar gudanar da aikina ,nan ma bai ce mata komai ba ya cire ya saura daga shi wando da farin singlet wani irin shumin kallo tabishi dashi saboda ganin arzikin jikinsa da yake singlet din ta kama jikinsa sosai dan har shashin nipples dinsa ya fito sosai , taji kamar ta kai hannunta ta shafa haɗe da murzawa bayan ta gama kallon ciwon ta janyo kayan aiki ta goge masa fuskar ciwon sannan ta saka auduga a kafad'arsa saboda ciwon ya shiga sosai ..

A hankali nurse ta dinga goga masa auduga shiru yayi tare da runtse idanunshi haka nan ƙwaƙwalwarsa ke hasko masa abinda ya faru tundaga shigowar yandaba gidansu har zuwa sanda yayi kokarin kareta, bai san lokacin da da nurse ta ɗauka tana aiki ba sai dai ji yayi aikin nata ya canza salo zuwa wani abu daban domin hannunta yaji yana sauka a wasu bangare na jikinsa tana shafa masa wuyansa zuwa cikin kunneshi da dayan hannunta da babu komai , take ya dawo haiyacinsa sai dai baiyi magana ba yayi shiru yaji ko zata sake yi, cigaba tayi saboda taji yayi shiru tunaninta ko sakonta ke aiki ajikinsa ganin bata daina ba tana son wuce gona da iri kuma tun farkon shigawarsa ya lura da yanayinta irin yan isakan nurse din nan ne marasa kamun kai ta d'ago idanunsu ya tsarke cikin juna amman bata daina ba tacigaba har da ƙoƙarin zira harshenta cikin kunneshi bai ce mata komai ba zaraf ya rike tsintsiyar hannunta ya murd'a da karfi ta saki razananniyar ƙara tana rufe bakinta da hannunta ɗaya, ya biyo daita gabanshi suna furkantar juna ya tsareta da idanunshi da suka Kada sukayi jajir , nurse na son tayi kuka amman babu hali gashi kuma still ma'hruf na rike da tsintsiyar hannunta a hankali ya motsa bakinsa "ki cigaba mana da abinda kike yi karamar yar iska da batasan ciwon kanta ba tayi saurin girgiza masa kai alamun bazatayi "ai na gama tayi maganar cikin matsanancin tsoro ma'aruf bai saki hannun ba yace "munafukar yar iska idan iskanci kike bukatar yi ki nemi daidai dake dan ko iskanci zanyi bazan yi da mace irinki ba da qirjinta ke shafe kamar silifas ba ,yafi minti goma kafin ya sakin hannun yana wurgi dashi haɗe da furzar da iska mai zafi ,jikinta na rawa ta soma hada masa magani da hannunta daya dan dayan hannun ko iya motsashi batayi hannunta na rawa ta mika masa farar leda bai amsa ba ya nuna mata kan wani karamin table ya dauki rigarsa ya rataya a kafadarsa tare da ciro wallet daga aljihun wandonsa "nawa ne kudin aikin ?
"Dubu biyar ne sir "dubu daya day ya ciro guda goma ya watsa mata a fuskar ya wuce abinsa yana jan tsaki, a reciption ya wuce rayhan yana zubawa wata nurse surutu Kai tsaye inda suka faka motarsu ya nufa yana sake jan tsaki da sauri rayhan ya mike yana wa nurse sallama ya biyo bayansa da sauri wanda har ma'hruf ya soma kokarin tada motar ya karaso" am sorry ma'hruf na tsaya tbayar wani magani ne ,ma'hruf bai yi magana ba sbd yadda yake jin zuciyarsa har suka isa gida babu wanda yayi magana ...

*******
Tunda garin Allah ya waye mutane ke shigowa yiwa mama jaje yayinda ummita ta kulle kanta a dakin mama tana ƙoƙarin neman layin ma'hruf da wayar mama amman number taki shiga ana faɗa mata matsalar network ne gaba-daya hankalinta da tunaninta suna garesa tana son sanin a wani hali yake ciki, jikinta a matukar sanyaye ta jingina da bangon d'akin mama gaba-daya ta rasa kwanciyar hankali a halin yanzu zuciyarta cike take da fargaba da zullumi a hankali hawaye taji yana zubo mata lokacin data tuna ƙoƙarin da yayi duk akan yaga ya kareta "tabbas ta yarda da maganar mama ,"nasan haka nan ma'hruf bazai tsanaki batare da wani dalili ba ki canza ki gani ....
A hankali ta soma tuna rayuwar kuncin da sukayi a baya duk yana tsaye akansu ita da mama baya son ganin bacin ranta idan kuwa tayi kuskuren 'batawa mama rai sai yayi matukar bata mata ....

TWO FRIEND'S ( BSBS)u


💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~TRUE LIFE STORY~

FREE NOVEL NOT FOR SELL


AL'QALUMAN



*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*


~DEDICATED TO~
*AYSHA BAGUDO FANS I REALLY APPRECIATE ALL LOVE YOU SHOWED ME , LOVE YOU SO GUY'S ,FOR NOT SEE MY UPDATE I'M SO BUSY THANKS FOR THE LOVE & CARE*



WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim


PAGE 25


......runtse idanunta tayi sosai tana jin zallar damuwa da rashin jin dadi a cikin tsokar dake makale da zuciyarta,
ta rasa abinda ke mata dadi ,ta dinga jin kamar taje d'akinsa ta dubo lafiyarsa da halin da yake ciki, amman zuciyarta ta dinga kwa'barta da aikata hakan , gyara kwanciyarta tayi akan makeken gadon mama tana jin wani iri a gaba-daya ilahirin jikinta kafin daga baya ta sake rushewa da wani sabon kuka tamkar wacce aka aiko mata da sakon mutuwar uwarta da ubanta .
kuka take sosai a kwance a wajen wanda ta rasa dalili har mama ta shigo dakin bata sani ba ,mama ta karaso wajen dake kwance da saurinta tare da dafe qirji data ji yana bugawa a sanadiyar

2 Comments On WANNAN CE QADDARARMU
avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment