Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana kuka a daidai lokacin daya baro gurin window da yake tsaye ya dawo gurin doguwar kujera mai zaman mutun uku ya zauna yana sauraron kukan data fashe masa dashi "kina bata min lokaci da wannan kukan naki gashi aiki ne zube a office .....

Sosai ta dinga masa kuka so take ya bata hakuri ko rarrashinta amman yaki ya cigaba da kad'a kafarsa ɗaya yana ciza gefen lip's d'insa na kasa ,lumshe idanunshi yayi ya cigaba da sauraron kukanta cikin d'acin rai haɗe da bakinciki tace "amman nawa auren za'a fara d'aurawa ko?
"Idan kin dawo akan lokaci ba idan baki dawo ba har ta gama iddar aka tabbatar da bata d'auke da cikin rayhan wanda bama fatan haka , nata za'a fara d'aurawa shiyasa ya rage naki ki dawo da wuri ko Karki dawo ...
Yana gama fadar haka ya katse kiran yana jan dogon tsaki "aikin banza ya furta yana furzar da iska....

Zubewa tayi agurin tana mai kife kanta kan gwiwowinta tana kuka wani irin bakinciki take ji a zuciyarta, a she daman mah'ruf ba sonta yake ba duk zakin baki yake mata ?
"Tabbas tasan da yana kaunarta da bazai zage ya dinga farfaɗa mata duk abinda ya ga dama ba tunda yasan jinyar mahaifiyarta take , ita yanzu bakincikinta bai wuce ummita da zai haɗasu tare ba, yarinyar da kyawunta ya shara, tana da matukar kyan da mah'ruf zai iya juya mata baya, zata so tayi rayuwarta daga ita sai shi ,tana tsananin son shi ,ta ina zata fara sharing dinsa da wata a yadda take kallonsa tasan zai shayar daita dadi a rayuwar aurensu?
wani kuka ta sake fashewa dashi "dan dole na tashi tsaye bazan yarda ya hadani da wannan yarinyar mai siffan aljanu ba ,ta mike tashiga kai kawo agurin tana neman mafuta dan dole tasan abun yi kafin lokaci ya kure mata .

tana wannan zariyar da sambatu auntyta data zo duba jikin mahaifiyarsu ta karaso inda take ta dafa kafad'arta "ke meke damunki ?
"ke da wa kike wannan sambatu haka ?
Ta juyo da sauri idanunta cike da hawaye tana dubanta ,kawai sai ta rushe mata da wani sabon kuka ta rungumeta ajikinta "na shiga uku yayarnmu da yake haka suke kiranta dashi "iyayen Mah'ruf ne zasu bashi matar d'an'uwansa daya rasu watanin baya "
"To shine zaki wani zauna kina kuka akan wannan?
"me ye abun kuka ban da abunki ?
"Maza ki share hawayen idanunki , wannan ai matsala ce mai sauki ,ko matan duniya suka aura masa fitar dasu bazai gagara ba , ki bari ayi auren zan san abun yi ......."
"yauwa yayarmu na gode sosai Allah ya bar mana ke ,nasan muddin ina dake bazan yi kuka ba... ...
Ta shafa bayanta tana rarrashinta ...


****

Rayuwa taki yiwa ummita dadi , kullun zata kasance cikin farinciki acikin mutane amman da zarar ta kadaita kanta sai damuwarta ta dawo sabo da zarar ta runtse idanunta rayhan da mah'ruf take gani yana miko mata hannun Mah'ruf , da zarar bacci yayi nasarar saceta mafarkin ne zai gudana cikin baccin gata tare da Mah'ruf suna kwance guri ɗaya yana aika mata da sakonin haɗe da shafa gadon bayanta mura muran ake nuna mata rayuwata dashi , idan ta farka kuwa bata sake komawa haka har assalatu , dan haka zazzabin dare ya zame mata abokin rayuwa yau dai zazzabin yafi na kowani lokaci tsanani cikin bacci meenal ta farka sakamakon dumin jikinta daya addabi fatar jikinta ta mike zaune ta tsura mata ido tana kallonta "baki da lafiya ne ?
Ta kada mata kai alamun eh ,muryarta can kasa tace "amman karki damu kafin wayewar gari zan ji sauki kullun haka nake fama, bude dorowar can ki dauko min maganina, meenal ta sauko da sauri ta d'auko farar roba mai ɗauke da maganin ta d'auko ruwan roba dake ajiye a kan bedside ,ta taimaka ta mikar daita zaune tare da jingina mata pillow tana mata sannu sannan ta buɗe robar maganin ta fito da magani kwaya biyu ta sa mata baki ta kora mata ruwa .
daren ranar zaune suka kwana ummita ta hana a fadawa mama aiko washe gari tun da asuban fari suka nufi asibiti daita doctor husain Yana tsaye akanta tare da wasu likitoci suna dubata hankalin kowa ya tashi sosai saboda ganin yadda numfashinta yake, tsoro mai tsanani ya mamaye zukanta wadan dangi dake tsakanin son junansu ,hajiya saudat itace kan gaba domin gabadaya tunaninta ya tafi ne akan ummita na dauke da cikin rayhan ne.
bayan likitoci sun gama dubata suka fito daya bayan daya suka bar Dr husain tsaye ya cigaba da bata kulawa .

Zaune mahruf yake a gabanta tare da tsura mata idanunshi yana kallonta kamar zai cinyeta , yayinda zuciyarsa ke wani irin tsalle da tafarfasa shi kadai yasan halin da yake ciki ,ya rasa meke damunta ,ya gaji da waɗan kananun cututtukan nata kullun ciwo ciwo ..
Kullun idan ya kalli iyayenta sai yaji tausayinsu tare da faduwar gaba jin idanunshi ajikinta yasa ta kawar da fuskarta ta yadda ba zata kalleshi ba ,"me yasa kike son boye abinda ke damunki ?
"Me yasa kike munafurtar iyayenki ,ki duba lamarin mahaifiyarki ki duba irin soyayyar ta iyaye ga d'ansu bare ke da kika kasance tilo ga mahaifiyarki ,ko dan soyayyarki dasu Yakamata ki kwantar da hankalinki kullun cikin addua suke miki ya karasa maganar yana kallon likita daya riko tsintsiyar hannunta domin qara mata drip... bata fahimtar komai da Mah'ruf yake faɗa saboda a tunaninta ba da ita yake ba duk da zuciyar tasan daita yake tunda daga ita shi sai likita ne a dakin , hankalinta ta tattara gurin doctor, tasan duk yaji bayananin mah'ruf amman ba zata so yayi masa wata magana ba, muryarta can kasa tace "doctor ka taimaka karka sheida musu komai ina tausaya musu kayi min alkwarin bazakaji sanar musu ba.....
Duk maganarta acikin kunnenshi da zuciyarsa suke sauka shi yasa lokacin da likintan ya fita yabi bayanshi da sauri ta runtse idanunta wasu sabbin hawaye na gangaro mata ..

Yana zaune yana fuskantar Dr husain cikin sarewa ,shiru office din baka jin sautin komai sai na sanyi ac dake aiki yayinda Dr husain yake faman jujjuya file din dake hannunsa " likita ka taimaka ka sanar mana da abinda ke damunta Bama son mu rasata kamar yadda muka rasa rayhan muryar Mah'ruf ta ratsa kunnuwan likita wanda kana ji kasan cike yake da rudani da tashin hankali tattare da fargaba, file din hannunsa ya mika masa cikin rashin sanin abun yi "me zanyi da wannan Doctor ?
Ya faɗa yana tsurawa doctor idanunshi da suka canza kala zuwa ja tsabar tashin hankali ko bai faɗa masa ba yasan wata sabuwar iftilai ne zai same su ...
Shiru doctor yayi na ɗan wani lokaci yana jujjuya biron dake rike a hannunsa ..
"Wannan sakamakon gwaje gwajen da mukayi mata ne bincikenmu ya nuna mana ........





TWO FRIEND'S (BSBS)


💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~TRUE LIFE STORY~

FREE NOVEL NOT FOR SELL


AL'QALUMAN



*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*


~DEDICATED TO~
*ZAINAB LABBO GWANDU CLASS MATE INA YINKI SOSAI MOST ESPECIALLY DARIYARKI*🤗🤗

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim


PAGE 35

"Me ke damunta likita? doctor husain yayi shiru yana rubuce rubuce akan file din wasu ,
" kayi shiru doctor , kayi min magana mana ko ciki gareta ?
Doctor husain yayi murmushi yana girgiza masa kai tare da cigaba da rubuce rubucen da yake kana yace "ba ciki bane, sai dai a zahirin gaskiya tana tattare da damuwa mai tsananin yawan da zai iya ma zuciyarta illa .

" Tana bukatar hutu sosai kamar yadda muka sheida muku a tun farko , a yanzu dai ta samu toshewar zuciya , jijiyon dake gudanar da jini wani daga ciki yayi blooking , ma'ana jini ya daskare ,kwata kwata jini baya gudana yadda ya kamata shiyasa wani lokacin take jin zuciyarta bata bugawa yadda ya kamata, da haka zuciyarta zata dinga kokarin tsayawa har ta daina aiki gabadaya .

"A halin yanzu zuciyar bata tsaya ba amman matukar wanda yayi blooking bai buɗe ba za'a ta iya samun matsala saboda shock din da tayi ta samu lokaci zuwa lokaci ...
dan Allah a dinga kula daita ana kiyaye duk wani abu da zai haifar mata da damuwa ,idan tana samun damuwa zuciyarta zata dinga rawa jikinta zai dinga rawa kafafunta da hannun suma zasu dinga feling haka ,duk waɗan nan abubuwan suna cikin illar ciwon zuciya , ita zuciya idan ta ta'bu tana da hatsari sosai wanda dole ne sai an kiyaye an sa ido ....

naunauyen ajiyar zuciya Mah'ruf ya sauke sannan ya maida idanunshi ga file dinta dake rike a hannunsa yana sauke numfashi , duk yadda yake d'auki jin matsalarta sai da yaji jikinsa yayi sanyi saboda shi kanshi kallon mai ɗauke da ciki yake mata saboda irin rashin lafinyar da take wacce tafi ta lokutan baya, dan wani lokacin ya kan ji tana fad'awa mama tana jin kasala ,sannan jikinta na rawa haka ma zuciyarta na rawa a she duk cikin gigitan mutuwar rayhan ne ....
Gumi ne ya gama wanke masa jiki sharkab a zaunen da yake a gaban likita , haka nan ya tsinci kanshi da jin wani irin bakinciki da fad'uwar gaba, shi duk wahalar da yake yi akanta ya ɗauka ciki gareta ,shiyasa yake ta lalla'bata a she bata ɗauke da komai .
"ya Allah ya furta a hankali ,a halin yanzu babu abinda yafi bukata da muradi sama da ganinta dauke da cikin rayhan .......
Tausayin hajiya saudat da inna ne ya kama shi a lokaci ɗaya saboda yadda gabadaya suka d'aura zukatansu akan ciki ne daita ,zata haifa masu madadin rayhan .
shi kanshi da kace cikin gareta da zai fi jin dadi ,lallai ta debo ruwan dafa kanta agurinsu hajiya Inna .
." yaya hajiya saudat zataji idan akace babu cikin data kwallafa rai ?
Lallai rigima ce kwance sai dai Allah ya kiyayye ," Allah sarki rayhan Allah ya jikanka ya kai rahma makwancinka ya kyautata namu zuwan ..

A galla sai da yayi minti ashirin yana zaune inda yake yana kallon file din tare da shafawa ko kwakwaran motsi ya kasa ,doctor ya gaji da shirun yayi , ya d'ago ya kafe shi da idanunshi yace "dan Allah a kiyaye a dinga bata kulawa , banda aiki ko dukawa shara ba'a bukata dan yanzu bata bukatar aiki ta bari ta samu lafiya tukun ,bangaren abinci sai dai a tuka abata taci amman ba dai tayi aiki ba, kuma wannan warar da jikinta yake kafa da hannu taji kamar zata fadi, karta damu tasawa zuciyarta in taji haka tayi ta sallatin annabi tasbihi inshaallahu da magani da kuma kiyayewa da dokokin likita in Allah ya yard zata samu lafiya ....

Mah'ruf ya mike jikinsa a matukar sanyaye haɗe da mikawa likita hannu "inshaallahu za'a kiyaye doctor Husain ya yayi rubutu acikin wata farar takarda ya mika masa ya fice daga d'akin ....
Yana fitowa hajiya saudat da inna suka rike shi da tambaya "babana amman ba wani abu bane ya samu cikin jikinta kou ?
"Allah ka taimakemu kar murasa cikin nan ..
ya kalli hajiya inna ya Kalli yadda hajiya saudat ta koma kalar tausayi bai ce musu komai ba ya juya ya soma tafiya hajiya inna ta biyo shi tana kokarin janyo hannunsa sukayi gurin siyan magani akan hanyarsu ya so faɗawa inna yarinyar ba ciki bane daita amman yaki dan baya son su tashi hankalinsu asibiti ,gara komai za'a yi ayi agida ..

Da yammacin ranar wani likitan zuciya ne ya shigo d'akin ya iske d'akin cike da tarin yan'uwa suna kewaye daita , kowa na ƙoƙarin yi mata sannu .
yayi masu ya mai jiki suka amsa gabadaya sannan ya soma ƙoƙarin dubata , ganin haka yasa duk suka fita , dakin ya saura daga mah'ruf sai ummita da doctor , fuskarta ummita na kallon bangon d'akin kamar yadda ya taddata , yayinda mah'ruf ke zaune rike da waya yana kallon screen din wayarsa sai dai gabadaya hankalinsa da natsuwarsa na gareta .

bayan doctor ya gama dubata ya janyo kujera ya zauna tare da kiran sunanta daya gani ajikin file dinta , ta waigo haɗe da lumshe idanunta , yasan idanunta biyu dan haka ya soma magana cike da rarashi "nasan doctor husain yayi wa yan'uwanki bayanin matakin da kike ciki a halin yanzu , amman idan ana bi a hankali a hankali zaki warke tunda Allah bai saukar da cuta ba sai daya saukar da magani , sannan ciwo bai san inda rai yake ba ki cire damuwa da tunani ki fuskamci ubangijinki kina gayawa Allah kukanki ki yawaita addua ,kina tashi cikin dare kina addu'a da nafilfili kina kuma bin ka'idodi likita kina kiyaye cin abubuwa masu nauyi ,kamar su tuwon masara, tuwon shinkafa sakwara yanzu duk ba cimanki bane, nama Mai maiko Kamar yadda doctor husain ya sheida miki a tun farko , bazaki cigaba da cinsa ba, sai irin su busashen kifi ko fresh fish Abu mara Mai, sannan dole ki kiyaye cin yaji sai kuma ki dinga shan maganinki akai akai saboda bp dinki yayi high sosai , waɗan magunguna da doctor ya rubuta miki zai daidaita bp na wannan lokacin ,amman inshaallahu komai zai daidaita ba abun tada hankali bane ,karki tada hankalinki ki samu walwala ki samu nishadi .

ya maida kallonsa ga Mah'ruf dake zaune yana kallon yatsun kafafunta dake kama da nashi sak "dan Allah idan son samu ne a dinga fita daita, karta zauna guri ɗaya saboda shi addininmu mai sauki ne ,ibada duk inda kake zaka yi shi ,a dinga kaita gidan sister dinta ana ɗebe mata damuwa, amman ba kuma ta dinga fita anyhow ba ,saboda ibadar da take ,tasa suturarta kamar mai takaba cikin hijabinta ta saka nikabinta da safa daga cikin gida mota ya d'auketa ya kai ta har kofar gidan da zataje a sauketa tashiga tayi hiranta ta ɗan samu nishadi aje kuma a d'auketa a dawo daita gida ajiyeta shikenan in Allah ya yarda idan ana samma mata farinciki kuma duk abinda aka san tana so a yawaita bata kuma a yawaita bata kyauta saboda shi dan adam yana son Mai kyautata masa ,zuciya tana son Mai kyautata mata so yawon bada kyauta yana warkar da mara lafiya ya kan ji Dadi a zuciyarsa sannan a dinga samun labari na nishadi da ban dariya ana yawan bata still zataji Dadi ,zata samu natsuwa inshaallahu .....

A hankali Mah'ruf ya lumshe idanunshi alamun yaji sannan doctor ya sake maida hankalinsa kanta da har lokacin taki bude idanunta "subai'a ya sake kiranta ta motsa tare da ware idanunta akanshi tana dubansa shi kadai, "ki daina kuka mai shesheka wanda yake fitowa daga kasan zuciya irin wannan sheshekar kukan ,idan ba haka zaki tsinci kanki inda baki tsamani ba ,sannan ki jefa ahlinki cikin tashin hankali kin fahimta , shock da irin wannan kuka suke haifar da irin ciwon dake barazanar kamaki... ....
Likita na kaiwa nan ya mike yana mikawa Mah'ruf hannu da kyar ya bashi saboda acikin zantuttukan ya tsinci wasu abubuwa masu yawa cikin ,inda yake cewa ta saka nikaf da safa a ganinsa kanshi yakewa tanadi dan ba tun da suka zo asibitin ya lura da shima sonta yake ba .. ..

Likita na fita ta fashe da wani kuka kwatankwacin irin wanda likita ya hanata ,duk abinda likita ya lisafa waye zai mata ?
"Tasan da'ace rayhan na raye shine mutumin da zai mata komai ,ba zai ta'ba barinta cikin damuwa ba ,duk yadda zai yi ya sakata farinciki zai yi ,amman shi wannan da ake faɗawa me zai mata baya ga kara mata takaici ?

wani kukan ne ya taso mata daga kasan zuciyarta yayi saurin kallon inda take ,idanunshi ya sauka a saman kirjinta dake sama da kasa tana janyo kukan da kyar ...
Yana shirin yi mata magana aka turo kofa aka shigo su hajiya ummah da hajiya saudat ne da wasu daga cikin yan'uwa , kuka ta cigaba yi ,ganinta haka ya sake jefa zukantasu cikin wani tashin hankali, Mah'ruf ya rasa yadda zai yi daita , rarrashinta ake amman taki yin shiru ,gashi kunnuwansa sun gaji da jin kukanta ,kukanta na kona masa rai ya mike ya fita daga d'akin yana furzar da iska mai zafi. ..

A cikin kwanakin gaba-daya ta sake fita haiyacinta tana ganin gara ta mutu kawai ta huta dan bata ga amfanin rayuwarta ba, saboda auren Mah'ruf ma wani sabon tashin hankali ne gareta, a duk sanda ta tuna sauran kwanaki ne ta gama iddarta sai hankalinta ya tashi sosai saboda yadda take jin su Abba na magana tana gama iddarta za'a d'aura musu auren .....
Ta kasa cin komai ,haka ta kasa shan komai likita ma ya rasa yadda zai yi daita duk kokarinsu gurin fahimtar daita illar tunanin da take taki ,kullun cikin damun zuciyarta take , duk wanda yake furta mata kalmar tayi hakuri haushinsa take ji
Hade da tsanarshi saboda yadda take ji babu sauki ,bata son taji ance mata tayi hakuri , kawai mutun ya rike maganarsa bata son ma ayi mata magana .

idanunta sun kumbura sunyi suntum saboda kuka har kwayar idanunta na mata zugin azabar zafi , jikinta kuwa ba'a magana saboda zafin da yayi ita kadai ke ciwo amman idan ka kalli mama zaka ɗauka itama ciwon take saboda ƙatuwar ramar da tayi , tana sallah tana kuka komai agurinta kuka ne bata marmarin abinci sai idan mah'ruf ne ya kasa ya tsare sannan zata tsakura ta ci ta sha magani ,ana sauran sati zata gama iddarta likita ya bata sallama tare da shawarwari masu mahimmanci ..
Suna dawowa gida kai tsaye part din mama ta wuce babu wanda ya matsa mata sai ta wuce bangaren inna saboda kowa lalla'bata yake .....

Daren ranar da suka dawo Mah'ruf ya mikawa abba result din ummita sannan ya kama gabanshi " Abba ya kira injiniya domin tautaunawa akan matsalar " yakamata a sanarwa su inna gaskiya lamari ko ?
" Ummita wani sati zata gama iddarta kar azo ...
"Kar azo ayi me?
"yaya ka rabu dasu kawai inda sun ga an d'aura mata aure da Mah'ruf zasu fi fahimci gaskiya ,Abba yayi shiru yana tunani sannan yace "anya ayi haka ba gara su sani ba ?
nan dai suka cigaba da tautaunawa har suka saida magana akan zasu nemi baba Sarki ..

Bayan kwana uku Alhaji Aminu mahaifin hajiya saudat ya diro gidan a dakin inna aka yi masa masauki bayan kowa ya hallara ya soma da addu'a ga wanda suka rigasu gidan gaskiya ya dinga musu nasiha har ya gangaro zuwa kan abinda ya kawo shi tirkashi gumi ne ya jika jikin hajiya saudat da wani irin kunci mara misaltuwa ,dan har gara hajiya inna "inna lillahi wa inna lillahi rajiun Kawai take furtawa , inna kuwa wata irin sabuwar tsanar ummita ce ta mamaye zuciyarta dan babu wacce ta tsana a halin yanzu sama daita dan tasan duk makirci ne ", ta yaya yarinya na dauke da ciki yanzu azo ana karanto musu karya, "wani irin bata d6auke da ciki aminu ?
"ya muna murna zamu samu madadin rayhan a duniya zaka mayar mana da murnarmu ciki ?
"Ba daga ni bane daga Allah ne wanda yake da iko da kowa da komai , kuma babu wanda ya isa yayi iko sai shi, haka babu wanda zai yi jayya dashi , yadda yake so haka zai yi ,bai gadamar bamu gurbin rayhan ba sai muyi hakuri mu rungumi *kaddararmu*...
Hajiya saudat tafi ƙarfin minti goma sha biyar durkushe a inda take bata ko iya kwakwaran motsin kirki tana kuka ",kiyi hakuri ki ɗauki dangana kiyi masa addu'a Allah yasa can ya fiye masa nan ..
Tayi shiru ta kasa cewa komai baba Sarki ya kafeta da ido "ko bakiji abinda nace miki bane

2 Comments On WANNAN CE QADDARARMU
avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment