Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rayhan ne na faɗa mata ta ɗauki lamarin a matsayin *wannan ce qaddararmu* dani daita
"Bata son shi ne daman ko me ?"
"Eh bata son shi na sha fama daita amman taki gashi abbanku ya zartar da hukuncin da bazan iya bijere masa ba"
sai da ma'aruf ya ja numfashi kafin yace "amma na ɗauka soyayya suke daman can ?"
Mama ta girgiza masa kai alamun a'a.
"shikennan mama kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki ki daina wannan kukan komai zai zo da sauki , ni zan samu rayhan din muyi magana ta fahimta dashi dan....."
Katse shi mama tayi da sauri yi "a'a ka barshi kawai karka ce masa komai idan maganar ta kai ga kunnen abba ko inna wani tunanin za'a yi daban ni kuma banason tashin hankali a wannan halin da nake ciki" mikewa yayi tare da fad'in "Allah ya kyauta ,ya saki hannunta ni zan tafi asibiti duba jikin mahaifiyarta suhaima yayi maganar yana kallon mama "allah sarki a she bata ji dadi ba ?
"Wallahi yau kwanata uku kenan a asibiti " Allah ya bata lafiya ka gaishe min daita " ko kallonsa ummita batayi ba sannan ba tace uffan ba , amman aranta tana jin babu dadi , ya gansu cikin damuwa da tashin hankali amman shi yana ƙoƙarin zuwa neman gindin zama , ta rasa gane dalilin haushinsa da taji a ranta ,rud'ewar damuwar da take ciki ne yasa taji hak'an aranta ko me ita dai bata sani ba,amman bata taɓa jin haushinsa irin na yau ba .
Yadda bata kalleshi ba haka shima bai kyalleta ba, dan ya fita jin abinda take ji acikin ranta tana jin takunsa yana cewa mama" sai ya dawo , yayinda zuciyarta ya tsananta dokawa har sanda ya fice daga d'akin ....

*******
Abu kamar wasa cin abinci ya soma gagarar ummita uwa uba rashin isasshen bacci ga zuciyarta dake wani irin mahaukaci bugawa da karfin gaske , ko ya-ya ta motsa sai zuciyarta tayi rawa tare da tsinkewa , duk yadda ta kwanta bata jin dadin rayuwarta sannan bata iya runtsawa , yadda take ganin rana haka take ganin dare ,ta rame sosai saboda ta sakawa zuciyarta damuwa suna zaune tare da meenal a parlour'n mama suna hira dan ta ɗan rage mata damuwar data lura tana tattare daita .
"ummita ki rage damuwar nan ta soma fasa jikinki kowa ya ganki yasan kina cikin damuwa , ki d'aurewa zuciyarki ki aure ya rayhan zakiji dad'in zama dashi saboda yana sonki fiyye da komai,uwa uba gashi had'ad'd'en gaye ne shima" tsaki ummita taja kana tace "meenal kenan ki daina tuna min auren ya rayhan da zanyi saboda zuciyata sam bata son rayuwa dashi ,koda bamu san irin wahalar rayuwar da mama tayi a gidan nan ba ,mun taso mun ga wasu daga ciki , dan me zanyi farincikin aurena da ya rayhan?
" bakya ganin kamar tarihi ne zai sake maimata kanshi ?
mahaifiyarsa bata son mama bata kaunar ta bud'e idanunta ta ganni, nasan ko inna bata bamu matsala ba ummansa zata kawo bare kinsan bakinsu ɗaya ,ni bama matsalarsu ce tafi damuna ba illa rashin son shi da banayi ne damuwar" ta K'arasa maganar tana sauke naunauyen ajiyar zuciya.
"nasani ummita Kuma nasan zasu aikata komai amman idan har kin tabbatar da bakin son aurenki dashi kuma bazaki iya rayuwar hakurin da mama tayi ba ki sheidawa iyayenmu tun wuri" da sauri tace "bazan iya ba meenal ,bazan iya kallon idanun Abba nace masa banaso ya rayhan ba , ni dai kawai ki ta yani da addu'a Allah ya kawo min dalilin da zai sa a fasa auren nan ....." ta karasa maganar tana sauke ajiyar zuciya tare da runtse idanunta , "Insha Allahu zan tayaki addu'a mafi alkhairi Allah ya za'ba miki" meenal ta fada tana tausayawa yar'uwarta .."ameen meenal na gode da kulawarki "
dogon lokaci suka ɗauka suna muhawara a tsakaninsu yayinda kirjin ummita ke wani irin dokawa da matsanancin karfin gaske , babu abinda ke d'aga mata hankali kamar yadda bugun zuciyarta ke sake k'aruwa da tsinkewa .

********

Da misalin ƙarfe shabiyu na dare ma'aruf ya dawo daga birthday party d'in abokinsa saleem , lokacin da ya shigo gidan bai jin motsin kowa ba ,yana shigowa kai tsaye yayi bangaren mama dan yasan da wuya idan ta kulle bangarenta dan sai taga shigowarsa sannan take kullewa , a hankali ya murda kofa parlour'n Ya shiga ya kunna wutar parlour'n ya nufi hanyar kitchen dan samawa kansa abinda zai ci ,bayan ya fito daga kitchen hannunsa rike da plet yana kokarin kiran mama tazo ta rufe kofarta idanunsa ya sauka akan kujera , ummita ya gani kwance idanunta biyu , ayi Sa'a itama ta waigo idanunta inda yake tsaye take zuciyoyinsu suka buga a lokaci daya sakamakon idanunsu da suka sarke cikin juna , wani irin shock yayi da ganinta kwance a parlour a daidai wannan lokacin saboda bai yi tsammanin haka ba, kirjinsa ne ya dinga dokawa kamar zai fito waje, sosai ya kafeta da manyan idanunshi , Ummita ta tsura masa fararen idanunta dake bushe tana kallon shi saboda yanayin shigar da yayi , bata kushe shigar ba acikin zuciyarta , sannan kuma bata yaba ba , yayi kyau sosai har da su sarka a wuyansa ga agogo diamon me shegen kyau da tsada d'aure a tsintsiyar hannunsa ,sai kamshi turare white aud yake bazawa kamar a lokacin zai fita , ita kanta tasan yana da kyau na bugawa ajarida, ko da fad'ad'd'en kirjinsa aka bar mace dashi ya isa ya dilmiyar daita cikin tafkin sonshi ,shi din irin halittar da mafi yawa daga cikin mata ke muradin mallaka ne , uwa uba ga tsayinsa da tsarin jiki mai kyau da Allah yayi masa , shi ba mai kiba ba kuma ramamme ba ga idanuwansa kamar mai jin bacci .
gaba-daya tsurawa juna ido suka yi suna kallon kwayar idanun juna Bata an karaba taji yaja dogon tsaki ya juya ya bar d'akin , nan take zuciyarta ta raya mata yanzu haka daga wurin yan matansa yake,amman kuma kamar a buge yake,"to ko shaye shaye ya koma yi ne ?
Ta yiwa kanta tambayar ai kuwa Ummita batayi bacci ba sai juyi take a parlour'n har sanda mama ta sauko ta rufe ko'ina idanunta biyu "ki tashi ki koma sama ku kwana tare dasu asiya mana "a'a mama zan kwana a nan ki barsu kawai, mama batace komai ba ta koma d'akinta sai goshin asuba tukuna bacci barowa ya saceta.

washe gari Ma'aruf bai so tashi da wuri ba saboda gajiyar dake tattare dashi amman ihun hajiya inna ne ya tashe shi, ya yunkura da kyar ya fito daga shi sai gajeren wando short niker da vest "me ye haka ne inna duk kin bi kin cikawa mutane kune da ihu shiyasa fa nake Allah Allah na bar gidan nan na huta da ihunki ?
"dan wannan ihun naki zai iya sa mutun kamuwa da hawan jini, haba mutun babu hakuri komai ihu ihu ke ba kya gajiya ne da ihu?
"kai babana kamin shiru anan abu akayi kuma dole ne nayi magana ta fadi haka tana hakikancewa da tada jijiyoyin wuya "koma dai meye dan Allah kiyi shiru haka ina son na kwanta na huta, "to shikenan naji, wallahi anci darajar bacci zakayi da yau sai.... "aka ce ya isa kiyi hakuri ki koma part dinki "shikenan ta sake furtawa sannan ta juya shi kuma ya koma part dinsa yana jan tsaki "haba mutun sam shi yace ba zai yi hakuri ba, komai sai yayi magana "

Sai misalin ƙarfe shabiyu na rana ya fito koda ya fito side din mama ya nufa yana shiga ya iske baki mata guda biyu take ya fahimci shine dalilin daya sa ummita kwanciya a parlour jiya , ahankali ya samu wuri ya zauna yana jiran mama ta gama lazimin sallar walha data idar , can ya mike yana dan dube dube kamar mai nimar wani abu wanda hakan yasa bakin mikewa sukayi sama , mama na gama lazimi tace "ma'aruf ka shigo" "eh" kawai yace mata "toh aka wo maka breakfast ne ?
yace "a'a ba yanzu ba , bana jin cin komai" kallon sa tayi sosai "toh ai shikenan, ina kaje jiya ne baka shigo gida da wuri ba" a take zuciyarsa ta raya masa wani abu , may be ummita tayi gulmansa ne , muryarsa a sanyaye yace "birthday din Salem naje , shiru mama tayi ba sake cewa komai ba sakamakon karar da wayarsa ta ɗauka, ya mike ya bar d'akin cike da sanyin jiki yana mamaki acikin ransa ..

Kai tsaye ɓangaren inna ya shiga nan ma ko gaisawa basuyi ba inna ta jiho masa tambayar babana ina kaje jiya ?shiru yayi yaki ce mata komai "babana magana fa nake da kai tsiyata da kai wannan dan banza miskilancin naka "karki dameni tsohuwar nan dazu kin hanani bacci mai dadi yanzu kuma kina son ki dameni da tambaya to naje gidansu Salem ne .....menene kike tmbyta?
inna tace "aha shi yasa ban yarda da maganar jairan yarinyar nan ba ,nasan wani abu ne ya tsayar da kai dan baka yawon dare , dazu nake jinta tana fada wa uwarta " wai yawon dare kake yi har ma da shaye shaye ga jarabar son mata tsiya karewa ma son matanka ran da zaka bar duniya za'a haifi wata mace inji wannan jairar mara kunyar yarinya shine kaji ina surfawa ita da uwarta, kai kuma da ɗan banzan salo kazo ka hanani ,amman naci alwashin kamar a kunnenka dan kaji dadin murje bakin rashin kunya " ina ruwana da maganarta ke yanzu kin yarda da abinda ta fadawa kenan ?
" saurin girgiza kai inna tayi "ina fa zan yarda da maganar wannan makirar babana, ai nasan kai d'a na gari ne ba bata gari ba ,ai kaine kake shishigewa ita da wancan munafakar uwartata me fuska bi....."a'a inna abinda zai sa muyi faɗa dake kenan yanzu babu ruwanki ,bana son ana aibanta mama agabana "tunda kanwar uwarka ce ba ?
Tayi masa tambayar tana karkata kai "koma dai menene babu ruwanki ke ko yankani zasuyi gunduwa gunduwa karewa maganata ki barsu suyi .. ....
yana gama faɗar haka ya mike ya baro d'akin "ai kuwa basu isa ba daga ita har uwartata mai fuska biyu , bazan taɓa yarda ba, ace ana sonka amman an iya zama ana zaginka wannan ai cin amana ne ...
bayan ma'aruf ya fito daga cikin gidan ya wuce masallacin shida wani bako da sukayi .

Bayan kwana biyu
da yammaci ma'aruf ya dawo daga kallon ball hannunsa rike da farar leda guda biyu yana shiga ya tarar da abbati bakon da sukayi zaune
a harabar gidan akan daya daga cikin fararen kujerun dake ajiye agurin madadin ya shige ciki ,sai kawai ya nufi inda yake , abbati na hangoshi ya washe baki har sanda ma'aruf ya k'araso ya janyo masa kujera , ma'aruf ya zauna "ya'akayi ne abbati hope kana jin dadin garinmu ? Ya K'arasa maganar yana buɗe daya daga cikin ledaodin dake hannunsa, takecare way ya ciro ya bud'e kayan fruit ne acikin ya d'auki daya ya kai bakinsa abbati yayi murmushi kana yace "sosai kuwa ai garinku akwai dad'i ga sanyi ni'ima ni Ina ganin ma anan su mama Asiya zasu barni ..
A hankali suka shiga tautaunawa suna shan fruit har abbati ya shigo da zance ummita "kasan sa'insan dake tsakaninka da ummita yayi yawa ,kuma fa irin wannan abun soyayya mai karfi yake komawa "rufa min asiri ko an kasa a kasuwa bana so "Allah kuwa da gaske irin wannan abubuwan da gaske yana faruwa, sai kaji iyaye sun ce ka aureta.
" kai dan Allah malam ya kake zakewa haka dayawa bayan nace ka rufa min asiri , ko babu maganar auren dake kanta da rayhan bazan aurenta ba , kai ama ture komai, nifa idan na auri ummita to dole zanyi kwanan parlour ,Kai har kukan bakinciki sai nayi wallahi ma'aruf ya K'arasa maganar tare da cewa " dan haka maza maza ka rabani da zanceta , bari na samu wanda zan tura ya kai wa mama kayan fruit dinta ,Yana waige waige neman yaro sai ga ummita ta fito sanye cikin doguwar riga baka har kasa rigar tayi mata kyau sosai, sai dai ta rame fuskarta tayi fayat tamkar wacce ke jinya, kana ganinta kasan tana cikin damuwa, ma'aruf na ganinta yayi shiru haɗe da kawar da kanshi gefe guda saboda bayason su haɗa ido daita ,abbati yace "lafiya kuwa naji kayi shiru ?
" babu komai kamshin turarenta ne ya ankarar da abbati ,dan haka ya maida hankali gurinta "yauwa ga ma ummita nan ta fito idan zata koma ka bata ta kai wa mama fruit din "a'a ya bashi amsa ataikace "
"Ko me yasa .... ?
"kai nifa idan na raina kasuwa ko sautu banyi, dan wannan yarinya ni ba shiga shirginta nake ba"kana da gaskiya dan nima gani nake kamar bata da mutunci fa, tana da shan kamshi maseefa yarinya kamar jinin sarauta kowa kallon gani gani take masa ta gabansu ta wuce batare da tace musu uffan ba haka zalika bata kallesu ba duk da jikinta ya bata maganarta suke , Maaruf yayi murmushi yace "haba abbati yanzu daga zuwanka har ka fahimci alkibilarta?
"I think yau ne fa ka cika kwana biyar a gidan nan ?
"Ko yau nazo na karanceta tsab saboda ina da saurin fahimta , ba shi yasa na lura da rashin shirin da kuke ba , gaskiya yarinyar tana da girman kai da d'agawa ga dan iskan miskilanci ,magana idan za tayi da kyar, abinci idan zata ci a yangace ,kai komai nata daban ...
" haba kai da zaka ringa janta da hira har ku saba ...
" a'a babu ruwana ni kam na fita hanyarta tun daga tana min kallon gani gani , ma'aruf ya haɗe fuska sosai "amman shine dan wulakanci kake auna aure a tsakanina daita bayan ga suhaimata can yariya mai ladabi da biyayya da sanin darajar mutane ,yarinyar da ko kara na saka bazata matsar ba ..
take abbati ya shiga kawo illolin Ummita daya karanta agurin ma'aruf , shi kuwa ma'aruf sai kushe ummita yake agurin abbati yana ji dadi sosai acikin ransa dama haushi abbati yake ji saboda yadda yake shishigawa ummita ....

Two friend's (bsbs)
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~TRUE LIFE STORY~

FREE NOVEL NOT FOR SELL


AL'QALUMAN



*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*


~DEDICATED TO~
*HASSANA DAN LARABAWA BESTY NAH, ITA KAD'AI NAKE KIRA DA WANNAN SUNAN KAF MEDIA, SON SO FI SABILILLAH*

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim


PAGE 21


...... Ya rayhan ya lura gabad'aya da yadda jikin ummita ya sake yin sanyi a tun sanda maganar aurensu ta bullo ,sam ta rage walwala da farinciki saɓanin lokutan baya , shiru yayi tsaye a bakin kofar parlour'nsu yana kare mata kallo mai ɗauke da alamomin tambaya iri iri, a cikin ransa yake aiyana abubuwa da dama , sai dai baya son jin komai a halin yanzu , domin sanin halin da take ciki bashi da wani amfani tun da yasan abinda ke damunta .
"yasan abinda ya canzata haka , amman da sannu komai zai daidaita da zarar sunyi aure , tun da yasan ba wai son shi ne bata yi ba ,rayuwar aure ne kawai bata bukata yin da shi ,sai dai yayiwa kanshi alkwarin da sannu zai koyar daita yadda zata so shi .
ya dade tsaye yana kallonta yayinda soyayyarta ke sake k'aruwa tana huda zuciyarsa da gangar jikinshi , baya jin duk runtsi duk wuya zai iya hakura daita , zai rayu da ita muddin rai matukar yana numfashi ...
Zuciyarsa na wani irin matsanancin dokawa kamar zai fasa qirjinshi ya k'araso inda take ya ja ya tsaya yana cigaba da kallonta ta rame sosai har ana iya ganin kashin dake zagaye da wuyanta .
"tun lokacin daya shigo parlourn jikinta ya sanar daita ya shiga saboda jin kamshin turarensa bugu da ƙari idanunshi dake yawo a sansar jikinta, sai dai bata d'aga kanta ta dubi inda yake ba har sanda ya k'araso ya tsaya a gabanta tare da kafeta da idanunsa .. zama yayi a kusa daita still idanunshi na kanta yana jin babu dadi a ranshi dan baya son ganinta cikin damuwa .
kusan minti goma ya ɗauka zaune a gefen bata waigo kanta ta dubeshi ba sannan bata ce masa komai ba illa ajiyar zuciyar da take saukewa da kyar .
Gajiya yayi da zaman shiru , gashi ya lura bata da niyyar kulashi ko ce masa wani abu, kuma yasan halinta ko zasu kwana a gurin bazata yi masa magana ba matsawar bashi ne yayi ba .
jikinsa a matukar sanyaye yana dubanta ya kamo laulausan tafin hannuta cikin nashi ya matse da karfi .. ƙara ta saki mara sauti haɗe da cewa "ashhhhhh Please yaya zafi ......
A hankali ya runtse idanunshi sannan ya sausauta rikon da yayi hannun nata yace " am really sorry sauraniyata , kiyi hakuri nasan duk ni ne silar danuwar nan taki amman ......
"karka fad'i haka ya rayhan ba kai bane kawai dai bana jin dadin zuciyata ne ta katse shi ta hanyar faɗar haka .. ... "meke damunki tashi muje muga doctor husain ya duba min ke bana son ganin haka ?
Girgiza masa kanta tayi batare da tace komai ba , dan a halin da take ciki idan tace zata sake cewa wani abu to kuka ne zai biyo baya .
Hawaye ne ya cicciko a cikin kwarnin idanunshi saboda yasan shine silar fad'awarta rayuwa kunci a wannan lokacin, saurin maida hawayensa yayi ya shiga kwantar mata da hankali , sosai ya dinga rarrashinta yana kwantar da kai tamkar karamin yaro duk kalmar daya san zai sakata farinciki ita ya dinga furta mata dan kawai ta samu natsuwar zuciya, shi kanshi yana jin fiyye da yadda take ji a zuciyarta , tunda me ye amfanin kana son mace ita bata sonka ? "Babu zuciyarsa ta bashi amsa da haka ,"ya san ummita tana son shi amman ba son irin na aure ba ,shi da zai iya hakura daita wallahi daya barta ko dan kwanciyar hankalinta, amman bazai iya ba .....
" kullun zuciyarsa dokawa take akanta tare da ninkin kaunarta, itace rayuwarsa duk saukar numfashinsa da tunaninta yake sauka , komai zai yi sai tunaninta ya sanyo kai ciki , yanzu haka zuciyarsa ciwo mai tsanani take masa akanta , ko daya tuntubi likita ce masa yayi ya rage tunani domin yana daf da kamuwa da ciwon zuciya , itama kuma abinda ke rubuce a

2 Comments On WANNAN CE QADDARARMU
avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment