Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tare da ma'aruf "okay Bari na duba maka gidansu domin a irin wannan lokacin zai yi wuya ka ....
"Karka damu tana ciki ,na jima anan ina jiran fitowarta ,dan a ƙalla tafi awa biyu ,ina nan ta shiga ....

Two friend's ( bsbs)
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~TRUE LIFE STORY~

FREE NOVEL NOT FOR SELL


AL'QALUMAN



*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*


~DEDICATED TO~
*RAHMA LADINGO YAR MUTAN NIJAR NA GODE KWARAI DA KAUNAR DA KIKE MIN ALLAH YA BAR KAUNA*

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim


PAGE 22

...."shikenan ba na shiga na turo maka ita " ummita shanyar da kika yi a waje ta bushe sai ki fita ki kwashe, "maganar Umar ce ta katse hirar da ummita da nadiya kenan "shiru tayi tana dubansa batare da tace uffan ba "to me maganar ya Umar yake nufi ?
" ba dai har zuwa wannan lokacin Mayataccen mutumin data taki fita saboda shi yana waje ba ?
"Take kanta ya d'aure "me kake nufi na baba, ba dai wani ta bari a waje ba tayi likimo anan ?inji cewar mama rukkaya dake tsaye a bakin dokin d'akinta "Allah Hajiya mutumin data shanya cewa yayi awa biyu yana jiranta dan taga zuwansa .
take mama ta d'aure fuska "gaskiya ummita baki kyauta ba yanzu .....
"Nifa ba gurina yazo ba abokin ya ma'aruf ne, idan kuma yace gurina yazo ai na rigada na faɗa masa babu ni babu shi ..
"Ke dai wallahi har yanzu kanki yana tukunya kin kiyin wayyohlly koda yake yan fari fa haka suke da saunanci , had'ad'd'en guy irin wannan mai tsada ga kirki wannan mutumin yasan kanshi sannan su ke tashe yanzu a cikin agege ta kowani bangare yayi kyau ilimi ga kudi daya zauna masa "malama ki tashi kawai ki tafi kar ya canza ra'ayinsa akanki inji cewar Umar .
cike da hassala tace "bafa zani ba sai dai idan jana zakayi ka kai ni gurinsa canza ra'ayi kuma da zai yi wallahi har da azumi zanyi dan murna tayi maganar kamar zatayi ..
"Ba zai jaki ba da kafafunki zaki haba ummita wulakanci fa babu dadi sannan ki dinga tausayawa uwarki a wannan lokacin aurenki shi zai sake kwantar mata da hankali ,idan kika auri irin wannan mutumin kin wuce raini a gurin sauran yan'uwanki , dan Allah ki d'aure kije kinji diyar albarka inji cewar mama rukkaya bata sake cewa komai ba ta soma kokarin mikewa sanin ko me zata fadawa mama rukkaya ba amincewa zatayi ba , taso ma ta fada mata hukuncisu Abba akanta amman kunyar faɗa take taji a bakin mama .
cikin siririyar muryata ta kira nusaiba da suka zo tare ta rike hannunta suka fice Umar yana mata dariya bata kula shi ba ta fice a ranshi rigimammiya sarkin shan kamshi wannan mijinki na da aiki dan ko da yangarki kaɗai aka barshi ya isheshi fama ..


muhd Sa'id daya soma cire tsakanin da fitowarta nan da nan fuskarshi ta washe tamkar wanda aka aikowa da sakon rahma ya nufota ..
Ta kalli inda yake ma sai take ganin kamar babbar asara ce a gurinta , tana tafiya a hankali kamar hawainiya shi kuma yana Binta a baya yana furta mata kalaman da take jinsu kamar wuta ake diga mata cikin zuciyarta , duk saukar kalmarsa daidai suke da ninkuwar bacin ranta ",idan kinyi fushi dani subai'a ba ribar da zakiji a cikin zuciyarki domin Allah ne ya jarabbeni da sonki, ba zan taɓa yin fushi dake ba koda kuwa zaki dinga min korar kare a unguwarku ,kin kasa gane shi so jarabawa ne, ni tawa jarabawar ita ce kaunarki ina sonki subai'a son da bazai misaltu ba ......
Yana wannan banzar shirmen nashi ne ta samu nasarar shigewa cikin gidansu da sauri kasancewar sunzo kofar gidansu .
murmushi yayi tare da d'aga murya " i love you subai'a more than words Allah ya bamu alkhairi ......
Zuciyarsa cike da nishadin ganinta ya cigaba da tsayuwa agurin baya jin zai iya barin unguwar ,so kenan bashi da magani sai hakuri yana nan tsaye sai ga ma'aruf da jafar sun fito fuskar ma'aruf a daure tamkar wanda aka aikowa da sakon mutuwa shi kuwa jafar yana ganinsa ya saki fuska cike da tausaya wa yayinda muhd Sa'id yayi hanzarin qarasawa gurinsu ya mika masu hannu suka gaisa sannan sukayo waje gaba-daya ..

a wannan lokacin da ummita ke sanar da meenal abinda ya faru , rufeta tayi da faɗa" banza kawai shine zaki zauna kina hasarar hawayenki akanshi ,in ban da kina son ya rainaki me zai hana ki fito ki zage danginsa kaf tunda shi mayatacce ne , idan kuma ke ba zaki iya ba tunda yanzu kin zama kurma , me zai hana ki kirani wallahi bazan duba halakarshi da ya ma'aruf ba, sai na zageshi tsab ,bayan ta gama maseefar ta koma rarrashin ummita dan a zahirin gaskiya babu abinda meenal ta tsana irin 'bacin ran ummita ...

Zaune su ma'aruf suke a kofar gidan yayinda Muhd Sa'id ke faman rokonsa "dan Allah abokina ka taimaka kasa baki a cikin lamarin nan , bazan iya hakura da yarinyar nan ba, sonta kullum sake k'aruwa yake a cikin zuciyata ,ni kaina ina tausayawa yanayin da nake ciki , wallahi babu wata macen da zan iya rayuwa daita bayan subai'a , subai'a daban ce "da kasan yanda nake jin yarinyar nan a zuciyata da tuni ka taimaka min ba wai ƙoƙarin nisantani daita ba , babu wata mace a duniya da nake so kamar subai'a i love her more than my life plz ma'aruf don't leave me like this ......
tun sanda muhd Sa'id ya soma magana Kirjin ma'aruf ke aikin dokawa da matsanancin karfin gaske ,yayin da zuciyarsa da ilahirin gangar ke kyarma yana jin maganarsa na masa kuwa a cikin kunnuwansa ....
gaba-daya ya kasa kwakwaran motsi a zaunen da yake , dan maganganun muhd Sa'id haushi suka dinga bashi, a matuƙar hassale jin sai cigaba da naci muhd Sa'id ke sake masa yasa , ya kira sunansa muryarsa a kausashe "muhd Sa'id ya isa haka please , na gaji !na gaji haba !! "Maganarka ta dameni , dan girman Allah
Ka canza magana kana caza min kwalkwaluwa da shirme me kake son nayi yanzu ?
" Yarinyar nan na faɗa maka an rigada an saida mata miji lokaci kawai yayi saura ,daɗin dad'awa Muhd Sa'id ko ba'ayi mata miji ba . ......
Sai kawai yayi shiru ya kasa K'arasa maganar yana huci tare da rike gaban goshinsa saboda kanshi daya ji ya soma sarawa , shi kuwa muhd Sa'id kasa motsi yayi tare da rakfa tagumi, da zullumi ,da rashin sanin madafar dafawa, a qalla sun ɗauki tsawon minti goma suna zaune ma'aruf bai sake yunkurin cewa komai ba, haka muhd Sa'id da jafar, jafar ya so yayi magana amman yana jin tsoron abinda ma'aruf zai faɗa masa dan yasan halinsa ....
Naunauyen ajiyar zuciya muhd Sa'id ya sauke da karfin gaske kana yace "kayi hakuri ma'aruf , abinda yasa kaga ina binka da batun yarinyar gani nayi yar'uwarka ce asalima a d'aki daya kukayi rayuwa ..

" Tabbass d'aki ɗaya muka rayu amman common magana baya had'ani daita bare kace nayi maka yakin neman soyayyarta ,idan ma maganar tashigo sai dai .....ya sake yin shiru yana cizan gefen lip's d'insa na kasa ,muhd sa'id yace "ina jinka sai dai me ?

Numfashi ma'aruf ya fitar mai zafi sannan ya cigaba "sai dai idan ta tashin hankali zamuyi sannan tayi min magana amman ni daita bama magana ?
jafar yayi murmushi yana sake duban ma'aruf " kai ban ce maka idan tasan muna magana da sadiya diyar aunty asiya sai tayi duk yadda tayi poison maid dinta ta daina min magana ba , to in gaya maka yau satinsu daya a gidan amman cikinsu babu wacce ta sake yi min magana ..
ni ko ajikina gaba ta kai ni, dan daga ita har su iskar data d'auko su ma bansan da zamanta ba ..

"Bangane ba har kiyayyar ta kai haka aboki ? Inji cewar muhd Sa'id
"ta wuce tunaninku , ni yanzu bata ita nake ba Matsalata ma ta isheni naji da bala'i da nake ciki , a kwananki baya da nake jin zuciyarta wasai nayi tunanin 'bata ma shegiyar yarinyar fuskar da take ɗaukar hankalin maza dashi , lamarinta na mugun daure min "

"To ita me yasa take yi maka haka ? Inji cewar jafar "kai muddin macen data san tana mu'amula daita take min magana sai tasan yadda tayi ta daina min magana jafar ya sake yin murmushi "bala'i kenan "sannan a yadda na lura daita bata son cigabana duk abinda na tsiya sai ta min bakinciki , kai ko shegiyar wayar nan na canza sai shegiyar yarinyar nan ta min bakinciki "
"Shekaranjiya da daddare suna zaune tare da sa'ada suna hira a parlourn na shigo da kudi , haka nan zuciyata tace na bata ta ajiye dan mama tayi bacci lokacin kuma bana son na taɓa kudin , da safe dana shiga amsar kudin sai mama take ce min kudin waye na bawa ummita ajiya ta barshi a parlourn an shigo ɗauke kudin ,nayi shiru saboda nasan har ga Allah ba daukesu akayi ba suna hannunta bakinciki kawai ne , banga laifinta ba sai nawa dan koma da kudina ba ina tsaye sai kawai mama ta d'auko kudin "na wane kudin?
ta min kudi "gashi ka cire kudin " naki kar'ba na qara gaba saboda bazan amsar kudin mama ba .
"gaskiya wannan yarinyar yar matsala ce mijinta na da aiki "
Murmushi muhd Sa'id yayi "babu wani aiki sai dadi da zan ji dan inshaallahu ni ne mijin " "kai raba kanka da Wannan yarinyar
"ai ni yanzu abinda yake bani mamaki "me nayi mata take min irin wannan tsanar , abinda yake bani haushi kenan daita ..
"Ban mata laifin komai ba ,amman take min bakinciki ,"a rayuwarta kowa so take ya tsane ni kamar yadda ita ta tsane ni ,wallahi darajar mama take ci saboda ita nake raga mata amman ,ranar da abun yayi spack dina zan iya canza mata kamani gaba-daya ....
" wallahi da ba dan bana son rayuwar waje ba ,a wannan lokacin da zuciyata ke zafi da tuni na bar gidan "to kaje ina ? "ai gidan nan dolenka ne, dan idan ka tafi abba bazai ji dadi ba "ni zaka ƙalla kace in je ina ?
"Bari na gaya maka idan ina ra'ayi da tuni an wuce gurin ,dan ina da kudin da zan iya kama kowani irin gida nake da bukata a fadin garin nan " ku nifa yanzu ta damuwata nake da yadda zan yakice auren sakina nake ba wata ummita ba, ya juya ya fuskanci muhd Sa'id " kai kuma idan kaga dama ka cigaba da sonta har zuwa sanda zaka matu, "yaya zanyi ma'aruf ?
"ina matsanancin sonta bazan iya daina wa ba , idan na rasa ta zan iya mutuwa zakayi hasarata ..
Tsaki ma'aruf ja "wannan kuma damuwarka ce ba tawa ba ,karka sake kawo min maganarta ka barni naji da damuwata a halin zuciyata ke ciwo har ina jin felling d'insa na Kuma san tunani ne yana cikin magana kawai idanunshi ya sauka akan wani matashi dake d'ayan ɓangaren da suke zaune wanda ya tsurawa kofar gidan idanu tare da tunani , hannuwansa duka zube cikin aljihun wandansa ,kamar an tsinkari ma'aruf ya mike a hankali shima duka hannuwansa soke cikin ajihun wandonsa ,har lokacin daya K'arasa gurin matashin bai sani ba , sautin muryar ma'aruf ne ya katse masa tunani "lafiya malam kake kallon gidanmu irin haka ? Ma'aruf ya fad'i haka saboda sanin yanayin garin yasa yayi masa tmbyr , a mutukar firgice matashin ya ciro hannunsa ɗaya daga cikin aljihun wandonsa tare da tsotsa keyarsa alamun rashi gaskiya "eh wani nake jira ......
Ya bashi amsa atakaice jikinsa na d'an rawa, hakan nan zuciyar ma'aruf taki amincewa dashi , ganin irin kallon da ma'aruf yake binsa dashi yasa yayi saurin juyawa ya soma tafiya cikin sauri ma'aruf yayi saurin biyo shi "ka tsaya mana ina kuma zaka ?
a daidai wannan lokacin tuni matashin ya karya wata kwana mai shegen duhu ya kwasa a guje ,gaban ma'aruf ya ɗan fad'i amman ya tsaya shiru yana bin bayansa da kallo cike da farga

******
Bayan kwana biyu
Abba da injiniya suka je gun mahaifin Suhaimah, an tarɓesu ciƙe da mutuntawa, aka saukesu a had'ad'd'en parlour'n gidan ,bayan sun zauna , suka ƙara gaisawa a tsakanin su , kan kace me tuni an ciƙe musu gabansu da kayan marmari da ruwan roba tare da sauran abubuwan sha , ko cikakken minti goma ba suyi ba sai ga amini nan mahaifin suhaimah guda biyu sun shigo , gaigaisawa suka shiga yi tare da mikawa juna hannu , bayan sun Gama gaisawa suka ce sune wakilan ma'aruf nan suka musu bayanin akan abinda ya kawo su ,sunzo nemawa d'ansu ma'aruf auren suhaimah ne , ba tare da Bata lokaci ba mahaifin suhaima ya amince musu , hade da tsaida ranar biki wata biyar masu zuwa kamar yadda aka saka na ummita da rayhan .. ..

Da misalin ƙarfe biyu na daren ranar , kwance yake a d'akinsa a saman tintimemiya katifarsa , sanye yake da boxer jikinsa iya cinyarsa babu komai sanye ajikinshi ,yayinda gashin qirjinsa dana cinyarsa ke kwance luf luf tamkar na jarirai sai sheke suke , haka jikinsa wani irin mayataccen kamshi turare yake fitarwa na white aud yayinda kunnenshi ke manne da waya yana hira da suhaima motsin dirowar mutane ya ji yayi shiru ya kasa cigaba da waya ,a hankali ya mike tsaye ya isa jikin window gilmawar mutan ya gani sanye da bakin kaya yana nan tsaye ya sake ganin wucewar wani a haka yaga wucewar mutun huɗu take gabansa yayi mummunar fadawa ya cila wayar saman katifarsa batare daya kashe ba .. ya bude kofar d'akinsa a hankali ya fito sannan ya janyo kofar ya rufe yana bin bango a hankali idanushi ya sauka akan mutane suna ƙoƙarin bude d'akin mama da key soma shiga "Inna lillahi wa Inna lillahi rajiun ya furta a kasan rashi "kar dai barayi ne suka shigo ?

Ummita dake kwance a parlourn sai faman juyi take saboda ta kasa bacci, wani juyi tayi ta sauya kwanciya idanunta na runtse tana son tilastawa kanta bacci sai dai tasan wannan karya ne , ba kasafai bacci a irin wannan lokacin take iya bacci ba saboda damuwar data yi mata yawa ,ta juya yafi sau arba'in a wani juyi datayi ne taji motsin ana buɗe kofar parlour'nsu take gabanta ya fad'i zuciyarsa tashiga dokawa ,da sauri ta zabura ta mike tsaye jikinta na wani irin rawa ta koma bayan kujera ta la'be, jikinta ne ya bata babu lafiya , duk wanda zai shigo bangarensu a daidai wannan lokacin ba mutumin kirki bane , dadin dad'awa mukulin parlourn na hannunta, gashi yanzu taji ana ƙoƙarin buɗe kofar , tana durkushe a bayan kujera taji motsin mutane suna shigowa daya baya har suka shigo duka tare da dallera parlourn da tochlight mai shegen haske domin ganin inda makunnin wuta yake, take parlourn ya karade da haske ,ta mutsetsike idanunta ta gani shin gaske ne ko karya , barayi take gani a cikin parlournsu sanye da bakaken kaya ko kuwa mafarki take ? Ta mintsini gefen cikinta domin taji mafarki take ko kuwa gaske ne zafin da taji ya ratsata yasa ta fahimta duk abinda suke idanunta na kallonsu, kowanensu sanye yake da bakeken kaya da maks na fuska wanda ya rufe kansu gaba-daya ba'a iya ganin komai nasu hatta tafin hannunsu ....
Gumi ne ya shiga tsatsafo mata a ilahirin jikinta tare da kyar ta tabbatar wa kanta komai karshe gareta a lokacin dataji tsayuwar mutun akanta kaminin minti goma yana tsaye akanta bayansa tabi da kallo tare da rufe bakinta da hannuwanta duka, tuni fitsari ya nemi kufce mata yadda jikinta ke rawa haka zuciyarta ke dokawa ,"zaki ku tsaya anan nida damusa zamu haura saman mu sauko daita nan "okay oga babu case kuje kawai "inna lillahi wa Inna lillahi rajiun ta furta jikinta na sake ɗaukar kyarma wannan maganar ta oga baa kunnen ummita kaɗai ta fada har kunnen ma'aruf ta fada dan a daidai lokacin yana jikin window ..ganin mutun biyu sun haura yasa ta rarrafa ta bar bayan wanda aka kira da zaki ta shige kitchen tana shiga ta mike a matukar gigice jikinta na rawa ta shiga bude kofar kitchen garin buɗe plet din abinci ya fado kasa jikake taratsatsa aiko ta saki wata razananniyar kara tare da fadin "wayyohlly Allah tana cigaba da buɗe kofar da sauri zaki ya haske kitchen din a daidai lokacin data gama budewa har ta sanya jikinta waje "ke ki tsaya tiaga ga yarinyar da muka zo nema aguce ta karasa ta kwasa aguje tana ihu ji tayi an fixgo da karfi aiko ta sake sakin wani razananniyar kara data karade gidan, manneta yayi sosai ajikinshi tare da haɗe bakinsu guri ɗaya .. kamshi turarensa daya kaiwa hancin ziyara yasa ta fahimci a kirjin wanda take kwance sosai ta sake shige jikinsa ta kamkameshi tana kuka da shaƙar mayataccen kamshin turarensa , idanu ya zubawa mata yana kallon bayan sosai zuciyoyinsu ke bugawa kusan minti biyar ya zare bakinsa cikin nata , muryarsa can kasa kasa tamkar mai koyon magana

2 Comments On WANNAN CE QADDARARMU
avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment